BABI NA SHA BAKWAI
Gatan da Muke da Shi na Yin Addu’a
1, 2. Me ya sa kake gani addu’a babban gata ne, kuma me ya sa muke bukatar sanin abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da wannan batun?
DUNIYA ƙarama ce idan aka gwada ta da sararin sama. Idan Jehobah ya kalli duniya, dukan mutanen da yake gani suna kamar ɗigon ruwa daga bokiti. (Zabura 115:15; Ishaya 40:15) Ko da yake mu kaɗan ne kawai idan aka gwada da sararin sama, duk da haka, Zabura 145:18, 19 ta ce: “Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda suke kira bisa gareshi, ga dukan waɗanda suke kira gareshi da gaskiya. Za ya biya muradin waɗanda ke tsoronsa; za ya kuma ji kukarsu, ya cece su.” Wannan babban gata ne da muke da shi, ko ba haka ba? Jehobah Mahalicci mai iko duka yana so ya kusace mu kuma ya amsa addu’o’inmu. Babu shakka, addu’a babbar gata ce da kuma kyauta da Jehobah ya ba kowannenmu.
2 Hanya ɗaya kaɗai da Jehobah yake saurararmu ita ce idan muka yi masa addu’a a hanyar da ta dace. Ta yaya za mu yi hakan? Bari mu tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da addu’a.
ME YA SA MUKE ADDU’A GA JEHOBAH?
3. Me ya sa ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah?
3 Jehobah yana son ka yi addu’a ko kuma ka tattauna da shi. Ta yaya muke yin hakan? Don Allah ka karanta Filibiyawa 4:6, 7. Wannan babbar gayyata ce daga Allah, ko ba haka ba? Mahaliccin sama da ƙasa ya damu da kai kuma yana son ka gaya masa yadda kake ji da kuma matsalolinka.
4. Ta yaya addu’a ga Jehobah kullum take ƙarfafa dangantakarku da shi?
Yaƙub 4:8.
4 Addu’a tana taimaka mana mu zama aminan Jehobah. Idan aminai suna gaya wa juna yadda suke ji da kuma damuwarsu, dangantakarsu za ta yi ƙarfi. Haka yake da yin addu’a ga Jehobah. Jehobah ya gaya maka nufinsa da kuma yadda yake ji a cikin Littafi Mai Tsarki. Ban da haka ma, ya gaya maka abin da zai yi a nan gaba. Don haka, za ka iya gaya masa matsalolinka ta wajen yin addu’a kullum. Idan kana hakan, dangantakarku da Jehobah za ta yi ƙarfi sosai.—ME ZA MU YI DON ALLAH YA AMSA ADDU’ARMU?
5. Ta yaya muka san cewa Jehobah ba ya amsa dukan addu’o’i?
5 Jehobah yana amsa dukan addu’o’i kuwa? A’a. Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa a zamanin annabi Ishaya cewa: “Sa’anda kuke yi mani yawan addu’o’i, ba ni ji ba: hannuwanku cike suke da jini.” (Ishaya 1:15) Saboda haka, idan ba mu yi hankali ba, za mu iya yin wasu abubuwan da za su nisanta mu daga Jehobah kuma hakan zai sa ya ƙi amsa addu’o’inmu.
6. Me ya sa bangaskiya take da muhimmanci? Ta yaya za ka nuna cewa kana da bangaskiya?
6 Idan muna son Jehobah ya amsa addu’armu, wajibi ne mu kasance da bangaskiya gare shi. (Markus 11:24) Manzo Bulus ya ce: “Ba ya kuwa yiwuwa a gamshe shi ba sai tare da bangaskiya: gama mai-zuwa wurin Allah dole ya ba da gaskiya cewan yana da rai, kuma shi mai-sākawa ne ga dukan waɗanda ke biɗarsa.” (Ibraniyawa 11:6) Amma faɗin cewa muna da bangaskiya kawai bai isa ba. Muna bukatar mu nuna hakan ta wurin yin biyayya ga Jehobah a kowace rana.—Karanta Yaƙub 2:26.
7. (a) Me ya sa ya kamata mu kasance da sauƙin kai da kuma ladabi sa’ad da muke addu’a ga Jehobah? (b) Ta yaya za mu nuna cewa muna addu’a daga zuciyarmu?
7 Ya kamata mu kasance da sauƙin kai da kuma ladabi sa’ad da muke addu’a ga Jehobah. Me ya sa? Babu shakka, idan aka gaya mana mu je gaban sarki ko shugaban ƙasa don mu yi masa wata magana, za mu yi hakan da ladabi. Da yake Jehobah Allah Mai Iko Duka ne, ya kamata mu yi masa magana da ladabi da kuma sauƙin kai, ko ba haka ba? (Farawa 17:1; Zabura 138:6) Sa’ad da muke addu’a ga Jehobah, ya kamata mu gaya masa dukan abin da ke zuciyarmu kuma bai kamata mu riƙa maimaita kalmomi iri ɗaya ba. Amma ya kamata mu faɗi ainihin abin da muke bukata.—Matta 6:7, 8.
8. Idan muka yi addu’a game da wani abu, mene ne muke bukatar yi?
8 A ƙarshe, idan muka roƙi Jehobah ya ba mu wani abu, wajibi ne mu yi aiki tuƙuru don mu samu abin da muka roƙa. Alal misali, idan mun yi addu’a cewa Jehobah ya ba mu abincin yini, bai kamata mu zauna mu naɗe hannu muna jiransa ya biya bukatunmu ba, alhalin muna da ƙarfin Matta 6:11; 2 Tasalonikawa 3:10) Ko kuma idan muka yi addu’a cewa Jehobah ya taimaka mana mu daina wani halin da bai da kyau, wajibi ne mu guji duk wani yanayin da zai iya sa mu faɗa cikin jarraba. (Kolosiyawa 3:5) Bari mu bincika wasu tambayoyi game da addu’a.
neman abin. A maimakon haka, zai dace mu yi aiki sosai kuma mu yi duk wani aikin da za mu iya yi. (TAMBAYOYIN DA AKE YAWAN YI GAME DA ADDU’A
9. Ga wane ne ya kamata mu yi addu’a? Mene ne littafin Yohanna 14:6 ya koya mana game da yin addu’a?
9 Ga wane ne ya kamata mu yi addu’a? Yesu ya gaya wa mabiyansa su yi addu’a ga “Ubanmu wanda ke cikin sama.” (Matta 6:9) Ya ƙara da cewa: “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yohanna 14:6) Saboda haka, ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah kaɗai, amma a cikin sunan Yesu. Mene ne yin addu’a cikin sunan Yesu yake nufi? Idan muna son Jehobah ya amsa addu’armu, ya kamata mu daraja aiki na musamman da Jehobah ya ba Yesu. Kamar yadda muka tattauna ɗazu, Yesu ya zo duniya don ya cece mu daga zunubi da kuma mutuwa. (Yohanna 3:16; Romawa 5:12) Ƙari ga haka, Jehobah ya naɗa Yesu Babban Firist da kuma Alƙali.—Yohanna 5:22; Ibraniyawa 6:20.
10. Shin dole ne mu zauna ko durƙusa ko kuma mu tsaya sa’ad da muke addu’a? Ka yi bayani.
10 Shin dole ne mu zauna ko durƙusa ko kuma mu tsaya sa’ad da muke addu’a? A’a, Jehobah bai gaya mana mu durƙusa ko zauna ko kuma mu tsaya ba sa’ad da muke addu’a. Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa yin addu’a da ladabi. (1 Labarbaru 17:16; Nehemiya 8:6; Daniyel 6:10; Markus 11:25) Abin da ya fi muhimmanci ga Jehobah shi ne mu yi masa addu’a da zuciya ɗaya, ba wai mu durƙusa ko tsaya ko kuma mu zauna ba. Za mu iya yin addu’a ga Allah da babbar murya ko kuma a cikin zuciyarmu a ko’ina, a kowane lokaci, ko da rana ne ko kuma da dare. Idan muka yi addu’a ga Jehobah, muna da tabbaci cewa zai ji mu ko da wani bai ji mu ba.—Nehemiya 2:1-6.
11. Mene ne za mu iya roƙa?
11 Mene ne za mu iya roƙa? Za mu iya roƙan kowane abu idan ya yi daidai da nufin Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan mun roƙi kome daidai da nufinsa, yana jinmu.” (1 Yohanna 5:14) Za mu iya roƙan wasu abubuwa da muke so kuwa? Ƙwarai kuwa. Ya kamata addu’armu ga Jehobah ta zama kamar muna tattaunawa da amininmu. Za mu iya gaya wa Jehobah dukan abin da ke zuciyarmu. (Zabura 62:8) Za mu iya roƙan Jehobah ya ba mu ruhunsa mai tsarki don ya taimaka mana mu riƙa yin abin da ya dace. (Luka 11:13) Har ila, za mu iya roƙan Jehobah ya ba mu hikima don tsai da shawarwari masu kyau da kuma ƙarfin jimre matsaloli. (Yaƙub 1:5) Ya kamata mu roƙi Allah ya gafarta zunubanmu. (Afisawa 1:3, 7) Ban da haka ma, ya kamata mu yi addu’a a madadin wasu, wato danginmu da kuma ’yan’uwa maza da mata a ikilisiyarmu.—Ayyukan Manzanni 12:5; Kolosiyawa 4:12.
12. Me ya kamata ya fi muhimmanci a addu’armu?
12 Me ya kamata ya fi muhimmanci a addu’armu? Jehobah da kuma nufinsa. Ya kamata mu gode masa daga zuciyarmu don abubuwan da ya yi mana. (1 Labarbaru 29:10-13) Mun san hakan ne domin a lokacin da Yesu yake duniya, ya koya wa almajiransa yadda za su yi addu’a. (Karanta Matta 6:9-13.) Da farko, ya ce su yi addu’a don a tsarkake sunan Allah ko kuma a ɗauki sunan da tsarki. Bayan haka, Yesu ya ce su yi addu’a don Mulkin Allah ya zo kuma a yi nufin Allah a dukan duniya. Yesu ya fara ce mu yi addu’a a kan waɗannan batutuwa masu muhimmanci sosai kafin ya ce mu roƙi abubuwan da muke bukata. Za mu nuna abin da ya fi muhimmanci a gare mu idan muka saka Jehobah da yin nufinsa farko a addu’armu.
13. Yaya ya kamata tsawon addu’armu ta kasance?
13 Yaya ya kamata tsawon addu’armu ta kasance? Littafi Mai Tsarki bai nuna ba. Addu’armu za ta iya zama gajeriya ko doguwa dangane da yanayinmu. Alal misali, za 1 Sama’ila 1:12, 15) Bai kamata mu yi doguwar addu’a don mu burge mutane ba kamar yadda wasu suka yi a zamanin Yesu. (Luka 20:46, 47) Jehobah ya tsani irin waɗannan addu’o’in. Abin da ya fi muhimmanci ga Jehobah shi ne mu yi masa addu’a da zuciya ɗaya.
mu iya yin gajeruwar addu’a kafin mu ci abinci ko kuma mu yi doguwar addu’a sa’ad da muke gode wa Jehobah ko kuma muke gaya masa damuwarmu. (14. Sau nawa ne ya kamata mu yi addu’a, kuma mene ne wannan ya koya mana game da Jehobah?
14 Sau nawa ne ya kamata mu riƙa yin addu’a? Jehobah ya gaya mana mu riƙa addu’a kullum. Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa yin “addu’a,” mu yi “addu’a ba fasawa,” kuma mu “lizima cikin addu’a.” (Matta 26:41; Romawa 12:12; 1 Tasalonikawa 5:17) A kullum Jehobah yana shirye ya amsa addu’armu. Za mu iya gode masa kowace rana don ƙaunarsa da kuma abubuwan da yake ba mu. Za mu iya roƙan sa ya ja-gorance mu, ya ba mu ƙarfi kuma ya ƙarfafa mu. Idan muka ɗauki gatan yin addu’a da muhimmanci, za mu yi iya ƙoƙarinmu don mu riƙa tattaunawa da shi.
15. Me ya sa muke ce “amin” a ƙarshen addu’a?
15 Me ya sa muke ce “amin” a ƙarshen addu’a? Kalmar nan “amin” tana nufin “hakika” ko kuma “ya zamanto haka.” Faɗin hakan a ƙarshen addu’a yana nufin cewa mun amince da abin da muka roƙa. (Zabura 41:13) Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa ya dace mu ce “amin” da babbar murya ko kuma a cikin zuciyarmu a ƙarshen addu’ar da wani ya yi don mu nuna cewa mun amince da abin da ya faɗa.—1 Labarbaru 16:36; 1 Korintiyawa 14:16.
YADDA ALLAH YAKE AMSA ADDU’O’INMU
16. Jehobah yana amsa addu’o’inmu kuwa? Ka yi bayani.
16 Jehobah yana amsa addu’o’inmu kuwa? Ƙwarai kuwa. Littafi Mai Tsarki ya kira shi “mai jin addu’a.” (Zabura 65:2) Jehobah yana ji da kuma amsa addu’o’in da miliyoyin mutane suke yi da zuciya ɗaya, kuma yana yin hakan a hanyoyi dabam-dabam.
17. Ta yaya Jehobah yake amfani da mala’iku da kuma bayinsa a duniya don ya amsa addu’o’inmu?
17 Jehobah yana amfani da mala’iku da kuma bayinsa a duniya don ya amsa addu’o’inmu. (Ibraniyawa 1:13, 14) Akwai misalai da yawa na mutanen da suka roƙi Allah ya taimake su su fahimci Littafi Mai Tsarki kuma jim kaɗan bayan haka, sai wani Mashaidin Jehobah ya ziyarce su. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mala’iku ma suna yaɗa “bishara” a dukan duniya. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 14:6.) Ƙari ga haka, wasu a cikinmu sun taɓa yin addu’a don suna da wata matsala ko kuma suna bukatar wani abu, sai wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta taimaka musu.—Misalai 12:25; Yaƙub 2:16.
18. Ta yaya Jehobah yake amfani da ruhunsa mai tsarki da kuma Littafi Mai Tsarki don ya amsa addu’o’inmu?
2 Korintiyawa 4:7) Jehobah yana kuma yin amfani da Littafi Mai Tsarki don ya amsa addu’o’inmu kuma ya taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau. Idan muka karanta Littafi Mai Tsarki, za mu samu wasu nassosin da za su iya taimaka mana. Jehobah zai iya sa wani da yake kalami a taro ya faɗi wani abin da zai taimaka mana ko kuma wani dattijo zai iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki don ya ƙarfafa mu.—Galatiyawa 6:1.
18 Jehobah yana amfani da ruhunsa mai tsarki don ya amsa addu’o’inmu. Idan muka yi addu’a don ya taimake mu mu jimre wata matsala, zai iya yin amfani da ruhunsa mai tsarki don ya ja-gorance mu, ya kuma ba mu ƙarfin jimrewa. (19. Me ya sa za mu iya ji kamar Jehobah bai amsa addu’o’inmu ba?
19 A wani lokaci za mu iya tunani, ‘Me ya sa Jehobah bai amsa addu’o’ina har yanzu ba?’ Ya kamata mu tuna cewa Jehobah ya san lokaci da kuma yadda zai amsa addu’o’inmu. Ya san abin da muke bukata. A wasu lokuta, zai dace mu yi roƙo a kai a kai don mu nuna cewa muna bukatar abun sosai. Ƙari ga haka, muna yin hakan don mu nuna cewa mun ba da gaskiya gare shi. (Luka 11:5-10) A wasu lokuta, Jehobah yakan amsa addu’o’inmu a hanyoyin da ba mu yi tsammani ba. Alal misali, za mu iya yin addu’a don muna fuskantar wata matsala, amma maimakon Jehobah ya kawar da matsalar, sai ya ba mu ƙarfin jimrewa.—Karanta Filibiyawa 4:13.
20. Me ya sa ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah a koyaushe?
20 A gaskiya, yin addu’a ga Jehobah babbar gata ce, ko ba haka ba? Mun tabbata cewa zai amsa addu’o’in da muke yi. (Zabura 145:18) Idan muna yin addu’a ga Jehobah a koyaushe kuma da zuciya ɗaya, dangantakarmu da shi za ta yi ƙarfi sosai.