BABI NA BAKWAI
Za a Ta da Matattu!
1-3. Me ya sa dukanmu muke kamar waɗanda suke cikin kurkuku, kuma ta yaya Jehobah zai ceto mu?
A CE wani ya yi maka sharri, sai aka yi maka ɗaurin rai da rai. Kuma babu yadda za a fitar da kai daga kurkukun. Ba ka da wani mafita kuma babu abin da za ka iya yi. Sai ka sami labari cewa akwai wani da ke da ikon fitar da kai kuma ya yi alkawari cewa zai yi hakan! Yaya za ka ji?
2 Mutuwa ta sa dukanmu mun zama kamar muna kurkuku. Ba mu da mafita, kome ƙoƙarin da muka yi. Amma Jehobah yana da iko ya cece mu daga mutuwa. Kuma ya yi alkawari cewa maƙiyiya ta ‘ƙarshe da za a kawar, mutuwa ce.’—1 Korintiyawa 15:26.
3 Ka yi tunanin irin farin cikin da za ka yi idan aka kawar da mutuwa! Amma ba mutuwa ce kaɗai Jehobah zai kawar ba, zai ta da waɗanda suka mutu. Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance a lokacin. Allah ya yi alkawari cewa zai ta da “matattu.” (Ishaya 26:19) Wannan ne abin da Littafi Mai Tsarki ya kira tashin matattu.
IDAN WANI YA RASU
4. (a) Me zai iya ta’azantar da mu a lokacin da ɗan’uwanmu ko abokinmu ya rasu? (b) Ka faɗi sunayen wasu abokan Yesu?
4 Muna baƙin ciki sosai sa’ad da wani danginmu ko abokinmu ya rasu. Kuma ba mu da wani abin da za mu iya yi don mu ta da shi. Amma Littafi Mai Tsarki yana ta’azantar da mu. (Karanta 2 Korintiyawa .) Bari mu tattauna wani misali ɗaya da ya nuna yadda Jehobah da Yesu suke marmarin ta da waɗanda suka rasu. Sa’ad da Yesu yake duniya, yakan ziyarci Li’azaru da ’yan’uwansa, Marta da Maryamu. Dukansu abokan Yesu ne. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Yesu kuwa na ƙaunar Marta da ’yar’uwarta, da kuma Li’azaru.’ Amma wata rana, sai Li’azaru ya rasu.— 1:3, 4Yohanna 11:3-5.
5, 6. (a) Mene ne Yesu ya yi sa’ad da ya ga dangin Li’azaru da abokansa suna kuka? (b) Ta yaya yadda Yesu ya ji game da matattu yake ƙarfafa mu a yau?
5 Yesu ya je ya ta’azantar da Marta da Maryamu. Sa’ad da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita daga birnin don ta same shi a hanya. Hankalinta ya kwanta da ta ga Yesu, amma ta ce: “Da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.” Marta ta ga kamar Yesu bai zo da wuri ba. A lokacin da Yesu ya ga Maryamu, ’yar’uwar Marta tana kuka, sai ya damu ƙwarai kuma ya zub da hawaye. (Yohanna 11:21, 33, 35) Ya ji baƙin ciki da mutane suke yi sa’ad da aka musu rasuwa.
6 Sanin cewa Yesu yana jin yadda muke ji sa’ad da aka mana rasuwa abin ƙarfafa ne a gare mu. Kuma Yesu yana da irin halayen Ubansa. (Yohanna 14:9) Jehobah yana da ikon hana mutuwa har abada kuma wannan shi ne abin da zai yi nan ba da daɗewa ba.
“LI’AZARU, KA FITO”!
7, 8. Me ya sa Marta ba ta so a cire dutsen daga kabarin Li’azaru ba, amma mene ne Yesu ya yi?
7 A lokacin da Yesu ya iso wurin da aka binne Li’azaru, an riga an rufe kabarin da babban dutse. Yesu Yohanna 11:39) Ba ta san abin da Yesu yake so ya yi wa ɗan’uwanta ba.
ya ce: “Ku kawar da dutsen.” Amma Marta ba ta so a yi hakan domin Li’azaru ya riga ya yi kwana huɗu a kabari. (8 Yesu ya ce: “Li’azaru, ka fito”! Abin da Marta da Maryamu suka gani ya ba su mamaki sosai. “Shi wanda ya mutu ya fito, ɗaurarre hannu da ƙafa da likkafani.” (Yohanna 11:43, 44) An ta da Li’azaru daga mutuwa. Sai ya ga ’yan’uwansa da abokansa. Za su iya riƙe shi, su taɓa shi kuma su yi magana da shi. Hakika, wannan abin mamaki ne domin Yesu ya ta da Li’azaru daga mutuwa.
“YARINYA, INA CE MAKI, KI TASHI”!
9, 10. (a) Wa ya ba Yesu ikon ta da matattu? (b) Me ya sa karanta labaran tashin matattu zai taimaka mana?
9 Yesu ya ta da mutane da ikonsa ne? A’a. Yesu ya yi addu’a don ya sami ikon ta da Li’azaru daga mutuwa kuma Jehobah ya ba shi ikon yin hakan. (Karanta Yohanna 11:41, 42.) Ba Li’azaru kaɗai aka taɓa ta da daga mutuwa ba. Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin wata ’yar shekara 12 da ta yi ciwo mai tsanani. Mahaifinta Yayirus ya damu ƙwarai, don haka, ya roƙi Yesu ya warƙar da ita. Ita kaɗai ce ’yarsa. Sa’ad da yake cikin magana da Yesu, sai wasu mutane suka zo suka ce masa: “Ɗiyarka ta mutu: don me kake wahalar da Malam”? Da ganin haka, sai Yesu ya ce wa Yayirus: “Kada ka ji tsoro, sai dai ka ba da gaskiya.” Sai suka tafi gidan Yayirus. Da suka yi kusa da gidan, Yesu ya ji kukan mutane sai ya ce musu: “Kada ku yi kuka; gama ba matacciya ba ce, amma barci take yi.” Iyayen yarinyar ba su gane abin da Yesu yake nufi ba. Yesu ya ce shi da iyayenta kaɗai su shiga ɗakin da aka ajiye gawar. Da suka yi hakan, Yesu ya kama hannunta ya ce: “Yarinya, ki tashi.” Babu shakka, iyayenta sun yi farin ciki sosai sa’ad da suka ga ’yarsu ta tashi tana tafiya. Yesu ya ta da ’yarsu. (Markus 5:22-24, 35-42; Luka 8:49-56) Daga ranar, a duk lokacin da suka ga ’yarsu, suna tuna da yadda Jehobah ya yi amfani da Yesu don ya taimake su. *
10 Mutanen da Yesu ya tayar sun sake mutuwa. Amma abin da muka karanta game da waɗannan mutanen yana da ban ƙarfafa domin yana sa mu kasance da bege. Jehobah yana marmarin ta da matattu kuma tabbas, zai yi hakan.
DARUSSA DAGA LABARAN WAƊANDA AKA TA DA DAGA MUTUWA
11. Mene ne Littafin Mai-Wa’azi 9:5 ya koya mana game da Li’azaru?
11 Littafi Mai Tsarki ya faɗa dalla-dalla cewa “matattu ba su san kome ba.” Haka ne yanayin Li’azaru yake sa’ad da ya mutu. (Mai-Wa’azi 9:5) Yesu ya ce Li’azaru yana kamar mutumin da ke barci, kuma hakan gaskiya ne. (Yohanna 11:11) Li’azaru bai “san kome ba” sa’ad da yake kabari.
12. Mene ne ya tabbatar mana cewa an ta da Li’azaru daga mutuwa?
12 Mutane da yawa sun ga lokacin da Yesu ya ta da Yohanna 11:47) Ƙari ga haka, mutane da yawa sun ziyarci Li’azaru kuma wannan ya sa sun gaskata cewa Allah ne ya aiko Yesu. Magabtan Yesu ba su so hakan ba, shi ya sa suka shirya su kashe Yesu da kuma Li’azaru.—Yohanna 11:53; 12:9-11.
Li’azaru. Magabtan Yesu ma sun san cewa shi ya yi wannan abu mai ban al’ajabi. Ganin Li’azaru a raye ya tabbatar da cewa an ta da shi da gaske. (13. Me ya sa muka tabbata cewa Jehobah zai ta da matattu?
13 Yesu ya ce za a ta da ‘dukan waɗanda suke cikin kabarbaru.’ (Yohanna 5:28) Wannan yana nufin cewa akwai matattun da Jehobah zai tayar da su. Amma sai Jehobah ya tuna da kome game da mutumin kafin ya ta da shi. Shin zai iya yin haka? Akwai biliyoyin taurari a sararin sama. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ya san sunan kowannensu. (Karanta Ishaya 40:26.) In har zai iya tuna da sunan kowane tauraro, babu shakka, zai iya tuna da kome game da mutanen da suka mutu kuma ya ta da su. Mafi muhimmanci ma, Jehobah ne ya halicci kome, don haka, mun san cewa yana da ikon ta da matattu.
14, 15. Mene ne za mu iya koya daga kalaman Ayuba game da tashin matattu?
14 Ayuba mutum mai aminci ya gaskata da tashin matattu. Shi ya sa ya yi wannan tambayar: “Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa?” Sai ya ce ma Jehobah: “Za ka yi kira, ni ma in amsa maka: Za ka yi marmarin aikin hannuwanka.” Hakika, Ayuba ya san cewa Jehobah yana so ya ta da mutanen da suka mutu.—Ayuba 14:14, 15.
15 Yaya kake ji game da begen tashin matattu? Za
ka iya yin tunani, ‘Za a ta da ’yan’uwana da kuma abokaina da suka mutu kuwa?’ Sanin cewa Jehobah yana marmarin ta da mutanen da suka mutu yana ƙarfafa mu. Bari mu tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da inda za su zauna bayan an ta da su da kuma irin mutanen da za a ta da daga mutuwa.‘ZA SU JI MURYARSA KUMA SU FITO’
16. Wace irin rayuwa ce mutanen da za a ta da su daga mutuwa za su yi?
16 Waɗanda aka ta da a dā sun sake haɗuwa da ’yan’uwansu da kuma abokansu a nan duniya. Za a yi tashin matattu wanda zai fi wannan a nan gaba. Me ya sa? Domin mutanen da aka ta da a nan duniya za su yi rayuwa har abada kuma ba za su sake mutuwa ba. Za a canja yanayin duniyar nan gabaki ɗaya. Ba za a riƙa yin yaƙi da mugunta da kuma ciwo ba.
17. Su waye ne za a ta da daga mutuwa?
17 Su waye ne za a ta da daga mutuwa? Yesu ya ce ‘dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryarsa, su fito.’ (Yohanna 5:28, 29) Littafin Ru’ya ta Yohanna 20:13 ya ce: “Teku kuma ya ba da matattun da ke cikinsa; mutuwa da Hades kuma suka ba da matattun da ke cikinsu.” Hakika, za a ta da biliyoyin mutanen da suka mutu. Manzo Bulus ya kuma ce za a ta da ‘masu adalci da marasa adalci.’ (Karanta Ayyukan Manzanni 24:15.) Mene ne hakan yake nufi?
18. Su waye ne “masu adalci” da za a ta da daga mutuwa?
18 “Masu adalci” sun ƙunshi bayin Jehobah masu Ibraniyawa sura 11. To, bayin Jehobah da suka mutu a zamaninmu kuma fa? Su ma “masu adalci” ne, don haka, za a ta da su.
aminci da suka yi rayuwa kafin Yesu ya zo duniya. Mutane kamar su Nuhu da Ibrahim da Saratu da Musa da Ruth da kuma Esther ne za a ta da a nan duniya. Za ka iya karanta labarin wasu cikin su a littafin19. Su waye ne “marasa adalci”? Wace dama ce Jehobah zai ba su?
19 “Marasa adalci” su ne biliyoyin mutanen da ba su sami zarafin sanin Jehobah ba. Ko da yake sun mutu, Jehobah bai manta da su ba. Zai ta da su, ya kuma ba su damar sanin sa da kuma bauta masa.
20. Me ya sa ba za a tayar da dukan matattu ba?
20 Wannan yana nuna cewa za a ta da dukan mutanen da suka mutu ne? A’a. Yesu ya ce ba dukan mutane za a tayar daga mutuwa ba. (Luka 12:5) Wane ne zai tsai da shawara a kan mutanen da za a tayar da waɗanda ba za a tayar ba? Jehobah ne babban Alƙali, kuma ya sa Yesu ya zama “mai-shari’a na masu-rai da matattu.” (Ayyukan Manzanni 10:42) Ba za a tayar da mugayen mutanen da suka ƙi canja halayensu ba.—Ka duba Ƙarin bayani na 19.
WAƊANDA ZA A TAYAR ZUWA SAMA
21, 22. (a) Mene ne tayar da matattu zuwa sama yake nufi? (b) Wane ne mutumi na farko da aka tayar zuwa sama?
21 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa wasu mutane za su je sama. Idan aka ta da wani zuwa sama, ba za a ta da shi da irin jikin mutane ba. Zai kasance da jiki irin na ruhu a sama.
22 Yesu ne aka fara tayarwa daga mutuwa da irin wannan jikin. (Yohanna 3:13) Jehobah ya tayar da Yesu bayan kwana uku da aka kashe shi. (Zabura 16:10; Ayyukan Manzanni 13:34, 35) Ba a ta da Yesu da jiki irin na mutane ba. Manzo Bitrus ya ce an kashe Yesu “cikin jiki, amma an rayar da shi cikin ruhu.” (1 Bitrus 3:18) An rayar da Yesu da jiki na ruhu kuma ya zama mai iko sosai. (1 Korintiyawa 15:3-6) Amma Littafi Mai Tsarki ya ce ba shi kaɗai za a yi wa irin wannan tashin matattu ba.
23, 24. Su waye ne “ƙaramin garke” da Yesu ya ambata, kuma su nawa ne?
23 Kafin Yesu ya mutu, ya gaya wa almajiransa masu aminci cewa: “Zan tafi garin in shirya muku wuri.” (Yohanna 14:2) Hakan yana nufin cewa za a tayar da wasu mabiyansa zuwa sama don su kasance tare da shi. Su nawa ne? Yesu ya ce su “ƙaramin garke” ne, wato ba su da yawa. (Luka 12:32) Manzo Yohanna ya ambata adadinsu sa’ad da ya ga Yesu ‘tsaye bisa dutsen Sihiyona [na sama], tare da shi kuma mutum dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu.’—Ru’ya ta Yohanna 14:1.
24 Yaushe ne za a ta da waɗannan mutane dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu zuwa sama? Littafi Mai Tsarki ya ce za a yi hakan bayan Kristi ya soma sarauta a sama. (1 Korintiyawa 15:23) Muna rayuwa ne a wannan zamanin kuma an riga an ta da yawancin waɗannan mutane dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu zuwa sama. Za a ta da duk wani cikinsu da ya mutu a zamaninmu zuwa sama nan take. Amma yawancin mutanen da za a ta da, za su yi rayuwa a Aljanna a nan duniyar.
25. Mene ne za mu koya a babi na gaba?
25 Nan ba daɗewa ba, Jehobah zai ceci ’yan Adam daga mutuwa kuma zai kawar da mutuwa har abada! (Karanta Ishaya 25:8.) Mene ne waɗanda za su je sama za su yi a can? Littafi Mai Tsarki ya ce za su yi sarauta tare da Yesu a Mulkin Allah. Za mu sami ƙarin bayani game da wannan mulkin a babi na gaba.
^ sakin layi na 9 Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin wasu da aka ta da daga mutuwa da suka haɗa da yara da tsofaffi da maza da mata da Isra’ilawa da kuma waɗanda ba Isra’ilawa ba. Za ka iya karanta labarin a 1 Sarakuna 17:17-24; 2 Sarakuna 4:32-37; 13:20, 21; Matta 28:5-7; Markus 5:22-24, 35-42; Luka 7:11-17 da kuma Ayyukan Manzanni 9:36-42; 20:7-12.