Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 3

Ta Yaya Aka Sake Gano Gaskiyar da ke Cikin Littafi Mai Tsarki?

Ta Yaya Aka Sake Gano Gaskiyar da ke Cikin Littafi Mai Tsarki?

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki, a shekara ta 1870 zuwa 1879

Fitar fari ta Hasumiyar Tsaro, a shekara ta 1879

Hasumiyar Tsaro a yau

Littafi Mai Tsarki ya yi annabci cewa bayan mutuwar Kristi, malaman ƙarya za su taso a tsakanin Kiristoci na farko kuma su gurɓata gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (Ayyukan Manzanni 20:29, 30) Hakan ya faru da shigewar lokaci. Sun haɗa koyarwar Yesu da ra’ayoyin arna, kuma hakan ya haifar da Kiristanci na ƙarya. (2 Timotawus 4:3, 4) Ta yaya za mu kasance da tabbaci cewa mun san ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa a yau?

Lokaci ya yi da Jehobah zai bayyana gaskiya. Jehobah ya annabta cewa a ‘kwanakin ƙarshe, ilimi na gaskiya za ya ƙaru.’ (Daniyel 12:4) A shekara ta 1870, wasu masu neman gaskiya sun fahimci cewa yawancin abubuwan da ake koyarwa a coci ba sa cikin Nassi. Sai suka soma bincike don su fahimci ainihin abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa, kuma da taimakon Jehobah, sun fahimci gaskiyar.

Mutane masu son gaskiya sun bincika Littafi Mai Tsarki sosai. Waɗannan ɗalibai na Littafi Mai Tsarki da suka gabace mu sun yi amfani ne da tsarin nazari da muke bi a yau. Sun tattauna batutuwan da ke cikin Littafi Mai Tsarki bi da bi. Idan suka ga wani fanni na Littafi Mai Tsarki mai wuyar fahimta, sai su bincika wasu ayoyi don su ƙara fahimtar batun. Sa’ad da suka tabbatar da cewa abin da suka gano ya jitu da sauran Nassi, sai su rubuta hakan. Ta wajen bincika Littafi Mai Tsarki sosai, sun sake gano gaskiya game da sunan Allah da Mulkinsa da nufinsa ga ’yan Adam da duniya da yanayin matattu, da kuma begen tashin matattu. Binciken da suka yi ya ’yantar da su daga koyarwar ƙarya da kuma ayyuka marar kyau.—Yohanna 8:31, 32.

A shekara ta 1879, Ɗalibai na Littafi Mai Tsarki sun fahimci cewa lokaci ya yi da ya kamata su sanar da gaskiyar nan a faɗin duniya. Saboda haka, a shekarar nan, sun soma wallafa mujallar Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah, wadda har yanzu muna wallafa ta. A yau, muna gaya wa mutane gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki a ƙasashe 240 da kuma a harsuna wajen 750. Ba a taɓa yaɗa cikakken ilimi na gaskiya kamar yadda ake yaɗa shi a yau ba!

  • Me ya faru da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki bayan mutuwar Kristi?

  • Ta yaya muka sake gano gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah?