Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 22

Mene Ne Ake Yi a Ofishin Reshe?

Mene Ne Ake Yi a Ofishin Reshe?

Solomon Islands

Kyanada

Afirka ta Kudu

Waɗanda suke hidima a Bethel suna aiki ne a sassa dabam-dabam, kuma suna kula da aikin wa’azin da ake yi a ƙasarsu ko a wasu ƙasashe da dama. Wasu suna aiki a inda ake fassara, wasu suna buga mujallu ko littattafai, wasu suna tattara littattafai kuma su tura su zuwa wuraren da za a yi amfani da su, wasu suna aiki a inda ake shirya faifai na bidiyo ko kaset, wasu kuma suna kula da ayyukan da suka shafi yankin.

Kwamitin da ke Kula da Ofishin Reshe na Shaidun Jehobah. Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta ɗaura nauyin gudanar da aiki a kowane ofishin reshe a kan Kwamitin da ke Kula da Ofishin Reshe, wanda ya ƙunshi ƙwararrun dattawa uku ko sama da haka. Kwamitin da ke kula da ofishin reshe yana sanar da Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah game da ci gaban da ake samu a kowace ƙasar da ke ƙarƙashinsa da kuma matsalolin da suka taso. Irin waɗannan rahotannin suna taimaka wa Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta tsai da shawara a kan batutuwan da ya kamata a tattauna a littattafanmu, a taron ikilisiya da kuma manyan taro a nan gaba. Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana da wakilai da suke ziyartar ofisoshin reshe kuma suna ba Kwamitin da ke Kula da Ofishin Reshe shawara a kan yadda za su gudanar da ayyukansu. (Misalai 11:14) Wakilin hedkwatan yana ba da jawabi na musamman don ya ƙarfafa waɗanda suke reshen.

Ana yi wa ikilisiyoyin da ke yankin ja-gora. Akwai ’yan’uwa maza a ofishin reshe da aka ba hakkin amincewa da sababbin ikilisiyoyin da ake son a kafa. Suna kuma kula da ayyukan majagaba da masu wa’azi a ƙasashen waje da kuma masu kula da da’ira da ke hidima a yankin reshen. Suna shirya manyan taro da taron gunduma, suna kuma kula da aikin gina sababbin Majami’un Mulki, tare da tabbatar da cewa an aika littattafai zuwa ikilisiyoyin da suke bukatar su. Duk wani aikin da ake yi a ofishin reshe yana sa a cim ma aikin wa’azin da ake yi cikin tsari.—1 Korintiyawa 14:33, 40.

  • Ta yaya Kwamitin da ke Kula da Ofishin Reshe na Shaidun Jehobah yake taimaka wa Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah?

  • Wane irin ayyuka ne ake yi a ofishin reshe?