Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TAMBAYA TA 10

Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Taimaka Mini?

Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Taimaka Mini?

ABIN DA YA SA HAKAN YAKE DA MUHIMMANCI

Littafi Mai Tsarki ya ce, “kowane nassi hurarre daga wurin Allah” ne. (2 Timotawus 3:16) Idan hakan gaskiya ne, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka a lokacin da kake bukatar ja-gora.

MENE NE ZA KA YI?

Ka yi tunanin wannan yanayin: David yana tuƙi a wani wurin da bai taɓa zuwa ba. Duk alamun da ya gani sun nuna cewa har yanzu bai kai inda yake so ya je ba. Hakan ya sa David ya san cewa ya ɓace. Ya bi hanyar da bai kamata ya bi ba.

Idan kai ne David, me za ka yi?

KA DAKATA KA YI TUNANI!

Kana da zaɓi da yawa:

  1. Kana iya tambayar wani ya nuna maka hanya.

  2. Kana iya yin amfani da taswira ko kuma na’aurar GPS.

  3. Kana iya ci gaba da tafiya, da fatan cewa za ka ga hanyar da ya kamata ka bi.

Hakika, Zaɓi na 3 ba zai taimake ka ba.

Zaɓi na 2 ya fi na farkon amfani sosai. Domin za ka kasance da taswirar ko na’aurar GPS ɗin yayin da kake tafiya kuma za ta ja-gorance ka ka san hanyar da za ka bi.

Littafi Mai Tsarki yana kama da wannan taswirar da kuma na’aurar GPS!

Wannan littafin da aka fi sayarwa zai iya taimaka maka

  • ka san yadda za ka bi da matsalolin rayuwa

  • ka san kanka da kyau da kuma yadda za ka kasance da halayen kirki

  • ka san yadda za ka yi rayuwa mai ma’ana sosai

INDA ZA KA SAMI AMSOSHIN MUHIMMAN TAMBAYOYI GAME DA RAYUWA

Muna tambayoyi da zarar mun fara magana.

  • Me ya sa sama yake da haske?

  • Da me aka yi taurari?

Daga baya, sai mu soma yin tambayoyi game da abubuwan da muke gani.

Idan amsoshin suna cikin Littafi Mai Tsarki tun dā can fa?

Mutane da yawa sun ce Littafi Mai Tsarki yana cike ne da tatsuniya, sun ce tsohon yayi ne, ko kuma yana da wuyar fahimta. Shin Littafi Mai Tsarki ne matsalar, ko kuma abin da mutane suka ji game da Littafi Mai Tsarki ne ba daidai ba?

Alal misali, mutane sun ɗauka Littafi Mai Tsarki ya ce duniyar nan tana ƙarƙashin ikon Allah. Amma hakan ba gaskiya ba ce. Duniya ta taɓarɓare! Tana cike da baƙin ciki da wahala da rashin lafiya da mutuwa da talauci da kuma bala’i. Yaya Allah mai ƙauna zai jawo hakan?

Za ka so ka san amsar? Wataƙila abin da Littafi Mai Tsarki ya ce zai ba ka mamaki!

Mai yiwuwa ka lura cewa an ɗauko shawarwarin da aka bayar a ƙasidar nan daga cikin Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah sun gaskata cewa Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da tabbatattun shawarwari game da rayuwa. Littafi Mai Tsarki “hurarre” ne daga wurin Allah, kuma “mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa.” (2 Timotawus 3:16, 17) Kana bukatar ka bincika wannan littafin dā da yake taimaka wa mutane a yau!