Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Me ya sa Yesu ya yi ƙaulin furucin Dauda da ke Zabura 22:1 gab da mutuwarsa?
Gab da mutuwar Yesu, ya yi furucin da ke Matiyu 27:46, ya ce: “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?” Yesu ya cika annabcin da Dauda ya yi a Zabura 22:1, sa’ad da ya yi wannan furucin. (Mar. 15:34) Ba zai dace mu yi tunanin cewa Yesu ya yi wannan furucin ne domin yana fushi da Jehobah ko kuma ya yi rashin bangaskiya na ɗan lokaci ba. Yesu ya san dalilin da ya sa yake bukatar ya mutu, kuma yana shirye ya yi hakan. (Mat. 16:21; 20:28) Ban da haka, ya san cewa a lokacin mutuwarsa, Jehobah ba zai kāre shi ba. (Ayu. 1:10) Jehobah ya ba Yesu damar nuna cewa zai kasance da aminci duk da wahalar da zai sha kafin ya mutu.—Mar. 14:35, 36.
Me ya sa Yesu ya yi furucin da ke zaburar nan? Duk da cewa ba mu san ainihin dalilin yin furucin ba, za mu tattauna wasu dalilai da wataƙila suka sa ya yi furucin. *
Shin ta wajen yin wannan furucin Yesu ya nuna cewa Jehobah ba zai kāre shi sa’ad da ake so a kashe shi ba ne? Yesu yana bukatar ya biya fansa ba tare da taimakon Jehobah ba. Shi ɗan Adam ne kuma yana bukatar ya “mutu saboda kowa.”—Ibran. 2:9.
Ta wajen yin ƙaulin wasu kalmomi a zaburar, Yesu yana so mutane su yi tunani a Zab. 22:7, 8, 15, 16, 18, 24) Ƙari ga haka, a ƙarshen ayoyin zaburar, an yabi Jehobah kuma an bayyana cewa shi ne maɗaukakin sarki.—Zab. 22:27-31.
kan abin da ke zaburar gabaki ɗaya ne? A zamanin Yesu, Yahudawa suna yawan haddace zabura. Sa’ad da suka ji aya guda na zabura, hakan yana sa su yi tunanin dukan zaburar. Idan abin da Yesu yake so ke nan, ya taimaka wa mabiyansa Yahudawa su yi tunanin annabce-annabcen da aka yi game da mutuwarsa. (Shin ta wajen yin ƙaulin furucin Dauda, Yesu yana nufin cewa bai yi laifi ba ne? Kafin a kashe Yesu, Majalisar Yahuduwa ta yi ƙarya a kansa cewa ya yi saɓo. (Mat. 26:65, 66) Majalisar ta yi shari’a da gaggawa daddare, kuma hakan ya saɓa wa doka. (Mat. 26:59; Mar. 14:56-59) Sa’ad da ya yi tambayar nan: “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?” wataƙila yana nufin cewa bai yi laifi ba da zai sa a kashe shi.
Shin Yesu yana tuna wa mutane cewa ko da yake Dauda marubucin wannan zabura ya sha wahala, hakan ba ya nufin cewa Jehobah ya daina amincewa da Dauda? Tambayar da Dauda ya yi ba ta nufin cewa bai yi imani ga Allah ba. Bayan da ya yi wannan tambayar, ya ce yana da tabbaci cewa Jehobah zai ceci mutanensa, kuma Jehobah ya ci gaba da yi wa Dauda albarka. (Zab. 22:23, 24, 27) Hakazalika, ko da yake Yesu “Ɗan Dawuda” ya sha wahala a kan gungumen azaba, hakan ba ya nufin cewa Jehobah bai amince da shi ba.—Mat. 21:9.
Shin Yesu yana nuna baƙin ciki cewa Jehobah ya daina kāre shi domin a jarraba amincinsa? Ba nufin Jehobah ba ne Ɗansa ya sha wahala kuma ya mutu. Zunubin da Adamu da Hauwa’u suka yi ne ya jawo hakan. Yesu bai yi wani laifi ba, amma yana bukatar ya sha wahala kuma ya mutu don ya amsa zargin da Shaiɗan ya yi kuma ya cece mu daga zunubi da mutuwa. (Mar. 8:31; 1 Bit. 2:21-24) Jehobah zai cim ma hakan idan ya ɗan daina kāre Yesu kuma wannan zai zama lokaci na farko da zai yi hakan.
Shin Yesu yana ƙoƙari ya sa mabiyansa su san dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale shi ya mutu a kan gungumen azaba? * Yesu ya san cewa irin wannan mutuwar za ta sa mutane da yawa tuntuɓe. (1 Kor. 1:23) Idan mabiyansa suka mai da hankali ga ainihin dalilin da ya sa ya mutu, hakan zai taimaka musu su fahimci ma’anar mutuwarsa. (Gal. 3:13, 14) Hakan zai sa su ɗauke shi a matsayin mai ceto maimakon wani da ya yi laifi.
Ko da wane dalili ne ya sa Yesu ya yi ƙaulin waɗannan kalmomin, ya fahimci cewa mutuwa a kan gungumen azaba za ta cika nufin Jehobah. Jim kaɗan bayan Yesu ya yi ƙaulin wannan zaburar, sai ya ce: “An gama!” (Yoh. 19:30; Luk. 22:37) Hakika, yadda Jehobah ya daina kāre Yesu na ɗan lokaci, ya sa ya yiwu Yesu ya cim ma abin da ya sa ya zo duniya. Hakan ya ba shi damar cika dukan abubuwan da aka rubuta game da shi “cikin Koyarwar Musa, da littattafan annabawa, da kuma Zabura.”—Luk. 24:44.
^ sakin layi na 2 Ka duba sakin layi na 9 da 10 a talifin nan “Darussa Daga Kalmomin Yesu na Ƙarshe” a fitowar nan.
^ sakin layi na 4 A lokacin da Yesu yake hidima a duniya, a wasu lokuta, yakan faɗi abubuwa ko kuma ya yi tambayoyi da ba su nuna ra’ayinsa ba. Ya yi hakan don ya ba mabiyansa dama su furta ra’ayinsu.—Mar. 7:24-27; Yoh. 6:1-5; ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2010, shafuffuka na 4-5.