Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 21

Jehobah Zai Karfafa Ka

Jehobah Zai Karfafa Ka

“Sa’ad da ina da rashin ƙarfi, a lokacin ne nake da ƙarfi.”​—2 KOR. 12:10.

WAƘA TA 73 Ka Ba Mu Ƙarfin Zuciya

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Waɗanne matsaloli ne Kiristoci da yawa suke fuskanta?

MANZO Bulus ya ƙarfafa Timoti da kuma dukan Kiristoci su yi iya ƙoƙarinsu a bautarsu ga Jehobah. (2 Tim. 4:5) Ya kamata dukanmu mu bi shawarar Bulus ta wajen yin iya ƙoƙarinmu a bautarmu ga Jehobah. Amma a wasu lokuta, yin hakan yana da wuya. ’Yan’uwanmu da yawa sukan ji tsoron yin wa’azi. (2 Tim. 4:2) Alal misali, ka yi tunanin ’yan’uwanmu da suke zama a ƙasashen da aka saka wa aikinmu takunkumi. Suna wa’azi duk da cewa za a iya saka su a kurkuku!

2 Mutanen Jehobah da yawa suna jimre matsaloli dabam-dabam da za su iya sa su sanyin gwiwa. Alal misali, ’yan’uwanmu da yawa suna aiki tuƙuru don su biya bukatun iyalinsu. Suna so su yi wa’azi sosai, amma sukan gaji a ƙarshen mako. Wasu kuma ba sa yin wa’azi sosai domin suna rashin lafiya mai tsanani ko sun tsufa ko kuma ba sa iya fita daga gida. Ban da haka, wasu suna ganin cewa ba su da amfani ga Jehobah. Wata ’yar’uwa mai suna Mary, * ta ce: “A duk lokacin da na yi sanyin gwiwa, nakan yi ƙoƙari sosai don kada in riƙa yin tunanin da bai dace ba, kuma hakan yakan gajiyar da ni. Sai in ji kamar na yi laifi domin ba na samun lokaci da kuma ƙarfin yin wa’azi.”

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Jehobah zai iya ba mu ƙarfin da muke bukata don mu yi iya ƙoƙarinmu mu ci gaba da bauta masa ko da wace irin matsala ce muke fuskanta. Kafin mu tattauna yadda Jehobah zai iya taimaka mana, bari mu bincika yadda ya ƙarfafa Bulus da Timoti su riƙa bauta masa duk da matsalolinsu.

JEHOBAH YANA ƘARFAFA MU MU CI GABA DA YIN WA’AZI

4. Waɗanne matsaloli ne Bulus ya fuskanta?

4 Bulus ya fuskanci matsaloli da yawa. Ya bukaci taimakon Jehobah sa’ad da abokan gābansa suka yi masa dūka, suka saka shi a kurkuku kuma suka yi ƙoƙari su kashe shi. (2 Kor. 11:​23-25) Bulus bai ji kunyar faɗin cewa a wasu lokuta ya yi fama da sanyin gwiwa ba. (Rom. 7:​18, 19, 24) Ƙari ga haka, ya yi fama da rashin lafiya da ke kama da “ƙaya a jiki,” kuma ya so Jehobah ya cire masa ƙayar nan.​—2 Kor. 12:​7, 8.

Mene ne ya taimaka wa Bulus ya cika hidimarsa? (Ka duba sakin layi na 5-7) *

5. Mene ne Bulus ya cim ma duk da matsalolin da ya fuskanta?

5 Jehobah ya ba Bulus ƙarfi don ya ci gaba da hidimarsa duk da matsalolin da ya fuskanta. Ka yi la’akari da abubuwan da Bulus ya cim ma. Alal misali, sa’ad da aka tsare shi a cikin gida a Roma, ya yi wa mutane da yawa wa’azi da ƙwazo, har da ma’aikatan gwamnati. (A. M. 28:17; Filib. 4:​21, 22) Ƙari ga haka, ya yi wa’azi ga sojojin gidan sarki, da kuma dukan waɗanda suka ziyarce shi. (A. M. 28:​30, 31; Filib. 1:13) A wannan lokacin, Allah ya yi hure Bulus ya rubuta wasiƙu da suka taimaka wa Kiristoci na gaskiya a dā, kuma suna taimaka mana a yau. Ban da haka, misalin Bulus ya ƙarfafa ikilisiyar da ke Roma, kuma hakan ya sa ’yan’uwansa su kasance da “ƙarfin hali su yi shaidar Kalmar Allah ba tare da jin tsoro ba.” (Filib. 1:14) Ko da yake Bulus bai yi wa’azi yadda yake so ba, ya yi iya ƙoƙarinsa a yanayin da yake, kuma hakan “ya ƙara sa labari mai daɗi ya yaɗu.”​—Filib. 1:12.

6. Kamar yadda aka nuna a 2 Korintiyawa 12:​9, 10, me ya taimaka wa Bulus ya cika hidimarsa?

6 Bulus ya fahimci cewa Jehobah ne ya ba shi ƙarfin yin dukan abubuwan da ya yi a hidimarsa. Ya ce ta wajen kasawarsa ne ‘ake ganin cikakken’ ikon Allah. (Karanta 2 Korintiyawa 12:​9, 10.) Ta yin amfani da ruhu mai tsarki, Jehobah ya ba Bulus ƙarfin cika hidimarsa duk da cewa an tsananta masa, an saka shi a kurkuku kuma ya fuskanci wasu matsaloli.

Mene ne ya taimaka wa Timoti ya cika hidimarsa? (Ka duba sakin layi na 7) *

7. Waɗanne matsaloli ne za su iya sa ya yi wa Timoti wuya ya yi hidimarsa?

Timoti, abokin wa’azin Bulus, ya dogara ga ikon Allah don ya cim ma hidimarsa. Timoti ya bi Bulus zuwa ƙasashen waje don yin wa’azi. Ban da haka, Bulus ya tura shi ya ziyarci ikilisiyoyi don ya ƙarfafa su. (1 Kor. 4:17) Mai yiwuwa Timoti yana ganin bai cancanci yin wannan hidimar ba, shi ya sa Bulus ya gaya masa cewa: “Kada ka bar wani ya rena ƙuruciyarka.” (1 Tim. 4:12) A wannan lokacin, Timoti yana “yawan rashin lafiya” kuma hakan yana kama da ƙaya a jikinsa. (1 Tim. 5:23) Amma Timoti ya san cewa ruhun Jehobah zai ba shi ƙarfin yin wa’azi da kuma yi wa ’yan’uwansa hidima.​—2 Tim. 1:7.

JEHOBAH YANA ƘARFAFA MU DUK DA MATSALOLINMU

8. Ta yaya Jehobah yake ƙarfafa mutanensa a yau?

8 A yau, Jehobah yana ba mutanensa ‘cikakken iko’ don su ci gaba da bauta masa da aminci. (2 Kor. 4:7) Bari mu tattauna abubuwa huɗu da Jehobah ke tanadar mana don ya ƙarfafa mu kuma ya taimaka mana mu kasance da aminci a gare shi. Waɗannan abubuwan su ne addu’a da Littafi Mai Tsarki da ’yan’uwa masu bi da kuma hidimarmu.

Jehobah yana ƙarfafa mu ta wurin addu’a (Ka duba sakin layi na 9)

9. Ta yaya addu’a za ta taimaka mana?

Samun ƙarfafa ta addu’a. Kamar yadda aka ambata a Afisawa 6:​18, Bulus ya ƙarfafa mu mu riƙa addu’a “kullum.” Allah zai amsa addu’armu ta wajen taimaka mana. Wani ɗan’uwa mai suna Jonnie da yake zama a Bolibiya, ya ga cewa Jehobah ya taimaka masa sa’ad da ya fuskanci matsaloli dabam-dabam. Matarsa da iyayensa sun soma rashin lafiya mai tsanani a lokaci ɗaya. Bai yi wa Jonnie sauki ya kula da dukansu uku ba. Sai mahaifiyarsa ta rasu, kuma ya ɗauki dogon lokaci kafin matarsa da mahaifinsa su warke. Sa’ad da Jonnie yake magana a kan abin da ya faru, ya ce: “A lokacin da nake damuwa, yin addu’a ga Jehobah da kuma gaya masa yadda nake ji, yana taimaka mini sosai.” Jehobah ya ba Jonnie ƙarfin da yake bukata don ya jimre. Wani dattijo a Bolibiya mai suna Ronald ya sami labari cewa mahaifiyarsa tana da cutar kansa, kuma bayan wata guda, sai ta mutu. Mene ne ya taimaka masa a wannan lokacin? Ya ce: “Sa’ad da nake addu’a ga Jehobah, na gaya masa yadda nake ji. Na san ya fahimce ni fiye da kowa, har fiye da yadda na fahimci kaina.” A wasu lokuta, muna iya ganin kamar ba za mu iya jimre matsalolinmu ba, ko kuma ba mu san abin da za mu yi addu’a a kai ba. Amma, Jehobah ya ce mu yi addu’a, ko da yana mana wuya mu bayyana yadda muke ji.​—Rom. 8:​26, 27.

Jehobah yana ƙarfafa mu ta wurin Littafi Mai Tsarki (Ka duba sakin layi na 10)

10. Kamar yadda aka nuna a Ibraniyawa 4:​12, me ya sa karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini yake da muhimmanci sosai?

10 Samun ƙarfafa ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki. Bulus ya karanta Nassosi don ya samu ƙarfafa, mu ma muna bukatar mu yi hakan. (Rom. 15:4) Yayin da muke karanta Kalmar Allah da kuma yin bimbini a kai, Jehobah zai iya yin amfani da ruhunsa don ya taimaka mana mu fahimci yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana a yanayinmu. (Karanta Ibraniyawa 4:12.) Ronald da aka ambata ɗazu ya ce: “Na gode Allah cewa a lokacin na iya na karanta wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki kowace rana. Nakan yi bimbini sosai game da halayen Jehobah da kuma yadda yake kula da mutanensa. Hakan yana ƙarfafa ni sosai.”

11. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa wata ’yar’uwa da take baƙin ciki?

11 Idan muka yi bimbini a kan Kalmar Allah, za mu kasance da ra’ayin da ya dace game da matsalolinmu. Ga yadda Littafi Mai Tsarki ya taimaki wata gwauruwa da ke makoki. Wani dattijo ya gaya mata cewa karanta littafin Ayuba zai taimaka mata. Da farko, ta yi tunani cewa ra’ayin Ayuba bai dace ba. A zuciyarta, tana yi wa Ayuba gargaɗi cewa: “Ka daina tunanin matsalolinka kawai!” Amma daga baya, sai ta fahimci cewa halinta ɗaya ne da na Ayuba. Hakan ya taimaka mata ta daidaita ra’ayinta kuma ta iya jimre mutuwar mijinta.

Jehobah yana ƙarfafa mu ta wurin ’yan’uwa (Ka duba sakin layi na 12)

12. Ta yaya Jehobah yake amfani da ’yan’uwanmu don ya ƙarfafa mu?

12 Samun ƙarfafa ta yin cuɗanya da ’yan’uwa. Wata hanya kuma da Jehobah yake ƙarfafa Kiristoci ita ce ta wajen yin amfani da ’yan’uwansu masu bi. Bulus ya ce yana marmarin haɗuwa da ’yan’uwansa don su “ƙarfafa juna.” (Rom. 1:​11, 12) Mary da aka ambata ɗazu tana jin daɗin kasancewa tare da ’yan’uwa. Ta ce: “Jehobah ya yi amfani da ’yan’uwa da ba su ma san matsalolina ba. Sukan faɗi abin ban ƙarfafa ko su turo mini wasiƙa, kuma abin da nake bukata ke nan. Ƙari ga haka, dattawa suna taimaka mini in ga cewa ’yan’uwa a ikilisiya suna ƙaunata.”

13. Ta yaya za mu ƙarfafa juna a taron ikilisiya?

13 Wuri mafi kyau na ƙarfafa juna shi ne taro. A duk lokacin da ka halarci taro, ka ƙarfafa ’yan’uwa ta wajen gaya musu cewa kana ƙaunar su kuma kana godiya don abubuwan da suke yi. Alal misali, kafin a soma taro, wani dattijo mai suna Peter ya gaya wa wata ’yar’uwa da mijinta ba ya bauta wa Jehobah cewa: “Ganin ki a taro yana ƙarfafa mu sosai. A kowane lokaci kina shirya yaranki shida su halarci taro kuma su yi kalami.” Ta yi farin ciki sosai kuma ta ce: “Ba ka san yadda furucinka ya ƙarfafa ni ba.”

Jehobah yana ƙarfafa mu ta wurin yin wa’azi (Ka duba sakin layi na 14)

14. Ta yaya yin wa’azi yake taimaka mana?

14 Samun ƙarfafa ta wurin yin wa’azi. Mukan yi farin ciki sa’ad da muka yi wa mutane wa’azi ko da sun saurara ko ba su saurara ba. (K. Mag. 11:25) Wata ’yar’uwa mai suna Stacy ta ga cewa yin wa’azi yana da ban ƙarfafa. Sa’ad da aka yi wa wani a iyalinsu yankan zumunci, ta ji kamar akwai abin da ya kamata ta yi don ta taimaka da ba ta yi ba. Ya yi wa Stacy wuya ta daina tunani game da matsalar. Mene ne ya taimaka mata ta jimre wannan yanayin? Yin wa’azi ya taimaka mata, domin yayin da take wa’azi tana mai da hankali ga mutane da ke yankin da ke bukatar taimakonta. Ta ce: “A wannan lokacin, Jehobah ya sa na sami ɗaliba da ta sami ci gaba sosai. Hakan ya ƙarfafa ni sosai. Abin da ya fi taimaka mini shi ne yin wa’azi.”

15. Me ka koya daga abin da Mary ta ce?

15 Wasu suna ganin ba sa iya yin wa’azi sosai domin yanayinsu. Idan kana jin hakan, ka tuna cewa Jehobah yana farin ciki sa’ad da kake iya ƙoƙarinka. Ka sake yin la’akari da misalin Mary. Tana ganin ba ta da amfani sa’ad da ta ƙaura zuwa wani yanki da ake wani yare. Ta ce: “Abin da nake yi kawai shi ne in yi ɗan kalami ko in karanta wata ayar Littafi Mai Tsarki ko kuma in ba da warƙa sa’ad da nake wa’azi.” Sai ta soma ganin kamar ba ta kai mutanen da suka iya yaren amfani ba. Amma ta canja ra’ayinta kuma ta soma ganin cewa Jehobah zai iya yin amfani da ita duk da cewa ba ta iya yaren sosai ba. Ta ce “koyarwar Littafi Mai Tsarki yana da sauƙi, kuma wannan koyarwar za ta iya gyara rayuwar mutane.”

16. Me zai taimaka wa waɗanda ba sa iya fita daga gidansu?

16 Jehobah ya san cewa wasu daga cikinmu suna so su yi wa’azi amma ba sa iya fita daga gidansu. Zai iya buɗe mana hanyar yin wa’azi ga mutane da ke kula da mu ko kuma ma’aikatan kiwon lafiya. Muna iya yin sanyin gwiwa idan muka gwada abin da muke yi yanzu da abin da muka yi a dā. Amma idan muka fahimci yadda Jehobah yake taimaka mana a yanzu, za mu sami ƙarfin da muke bukata don mu ci gaba da jimre jarrabawa da farin ciki.

17. Kamar yadda Mai-Wa’azi 11:6 ta nuna, me ya sa za mu ci gaba da wa’azi ko da ba ma samun sakamako mai kyau nan da nan?

17 Ba mu san wanne ne cikin irin da muka shuka zai yi jijiya kuma ya soma girma ba. (Karanta Mai-Wa’azi 11:6.) Alal misali, akwai wata ’yar’uwa mai suna Barbara da ta ba shekaru 80 baya, tana wa’azi da waya da kuma rubuta wasiƙu. A ɗaya daga cikin wasiƙunta, ta saka Hasumiyar Tsaro na 1 ga Maris, 2014 mai jigo “Alherin da Allah Ya Yi Maka.” Ba ta san cewa ta tura wasiƙar ga ma’aurata da aka yi wa yankan zumunci ba. Ma’auratan sun karanta mujallar sau da yawa. Maigidan ɗauka cewa Jehobah ne yake masa magana kai tsaye. Sai suka soma halartan taro kuma daga baya suka soma bauta wa Jehobah, bayan sun daina yin hakan fiye da shekara 27. Barbara ta samu ƙarfafa sosai don yadda wasiƙa guda ɗaya ya kawo sakamako mai kyau!

Jehobah yana ƙarfafa mu ta wurin (1) addu’a, (2) Littafi Mai Tsarki, (3) ’yan’uwa, da (4) yin wa’azi (Ka duba sakin layi na 9-10, 12, 14)

18. Mene ne ya kamata mu yi don Jehobah ya ƙarfafa mu?

18 Jehobah ya ba mu zarafin samun ƙarfafa daga wurinsa. Ya yi mana tanadin abubuwa da yawa da za su ƙarfafa mu kamar addu’a da Littafi Mai Tsarki da ’yan’uwanmu da kuma wa’azi. Idan muka yi amfani da waɗannan abubuwan, hakan zai nuna cewa mun tabbata cewa Jehobah zai iya taimaka mana kuma yana so ya yi hakan. Saboda haka, ya kamata mu riƙa dogara ga Ubanmu da ke sama, wanda yake so “ya ƙarfafa waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya.”​—2 Tar. 16:9.

WAƘA TA 61 Bayin Jehobah, Kar Mu Gaji!

^ sakin layi na 5 Muna rayuwa a mawuyacin lokaci, amma Jehobah yana taimaka mana mu jimre. A wannan talifin, za mu tattauna yadda Jehobah ya taimaka wa manzo Bulus da Timoti su ci gaba da bauta masa duk da matsalolinsu. Za mu ga abubuwa huɗu da Jehobah ya tanadar don ya taimaka mana mu jimre a yau.

^ sakin layi na 2 An canja sunan.

^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTUNA: Sa’ad da aka tsare Bulus a gida a Roma, ya rubuta wasiƙu zuwa ga ikilisiyoyi da yawa kuma ya yi wa’azi ga dukan waɗanda suka ziyarce shi.

^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTUNA: Timoti yana ƙarfafa ’yan’uwa sa’ad da ya ziyarci ikilisiyoyi.