Abubuwan da Allah Ya Riga Ya Yi
Idan kana so ka san wani sosai, kana bukatar ka san abin da ya yi a dā da kuma ƙalubalen da ya shawo kansu. Haka ma yake da Allah, don ka san shi sosai, kana bukatar ka san abubuwan da ya riga ya yi. Idan ka yi hakan, za ka yi mamakin sanin abubuwa masu kyau da ya yi don mu amfana a yanzu da kuma a nan gaba.
ALLAH YA HALICCI DUKAN ABUBUWA DON MU JI DAƊIN RAYUWA
Jehobah Allah shi ne Mahaliccin kome da kome kuma ana iya gane halayensa ta “abubuwan da aka halitta.” (Romawa 1:20) ‘Allah ne ya yi ƙasa ta wurin ikonsa, ya kafa duniya ta wurin hikimarsa, ya shimfiɗa sammai ta wurin ganewarsa.’ (Irmiya 10:12) Abubuwan da Allah ya halitta sun nuna cewa yana ƙaunar mu sosai.
Jehobah ya halicce mu a wata hanya ta musamman. Ya yi mu cikin “kamanninsa.” (Farawa 1:27) Hakan yana nufin cewa ya halicce mu da wasu daga cikin halayensa masu kyau. Ya yi mu a hanyar da za mu iya fahimtar ra’ayinsa da kuma umurninsa. Idan muka bi shawarwarinsa, za mu ji daɗin rayuwa sosai. Mafi muhimmanci ma, ya ba mu damar kasancewa da dangantaka mai kyau da shi.
Abubuwan da muke gani a duniyar nan suna bayyana mana yadda Allah yake ƙaunar mu. Manzo Bulus ya ce, Allah “bai taɓa barin kansa babu shaida ba, saboda yana yin alherin ba ku ruwan sama da damina mai albarka. Yana ƙosar da ku da abinci a daidai lokaci, yana kuma sa ku yi farin ciki.” (Ayyukan Manzanni 14:17) Allah yana ba mu fiye da abubuwan da muke bukata don mu rayu. Ya halicci abubuwa dabam-dabam don mu ji daɗin rayuwa. Amma waɗannan abubuwan kaɗan ne daga cikin abubuwan da yake so ya yi mana.
Jehobah ya halicci duniyar nan don ’yan Adam su yi rayuwa a cikinta har abada. Littafi Mai Tsarki Zabura 115:16; Ishaya 45:18) Su waye za su zauna a cikinta kuma har tsawon wane lokaci? “Masu adalci za su gāji ƙasar, su zauna a ciki har abada.”—Zabura 37:29.
ya ce: Allah “ya ba ’yan Adam” duniya kuma “bai halicci duniya ta zama wofi ba, ya yi ta domin a zauna a cikinta.” (Jehobah ya halicci mutane na farko, wato Adamu da Hauwa’u kuma ya saka su a cikin aljanna don su “dinga aiki a cikinta suna lura da ita.” (Farawa 2:8, 15) Allah ya ba su aiki guda biyu masu kyau da za su yi, ya ce musu: “Ku yi ta haifuwa sosai ku yalwata, ku ciccika duniya ku kuma sha ƙarfinta.” (Farawa 1:28) Allah ya ba wa Adamu da Hauwa’u damar yin rayuwa har abada a duniya. Abin baƙin ciki shi ne, sun yi wa Allah rashin biyayya kuma suka rasa damar kasancewa cikin “masu adalci” da “za su gāji ƙasar.” Amma kamar yadda za mu koya, halin da suka nuna bai sa Allah ya canja nufinsa ga ’yan Adam da kuma duniya ba. Yanzu, bari mu ƙara bincika wani abu kuma da Allah ya yi.
ALLAH YA YI MANA TANADIN KALMARSA
Ana kiran Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah. Me ya sa Jehobah ya yi mana tanadin Littafi Mai Tsarki? Don yana so mu koya game da shi. (Karin Magana 2:1-5) Littafi Mai Tsarki bai faɗi kome da kome game da Allah ba, kuma babu wani littafin da ya yi hakan. (Mai-Wa’azi 3:11) Amma dukan bayanai da ke Littafi Mai Tsarki suna taimaka mana mu san Allah da kyau. Yadda ya bi da mutane ya nuna mana halayensa. Littafi Mai Tsarki ya nuna mana irin mutanen da yake so da waɗanda ba ya so. (Zabura 15:1-5) A cikin Littafi Mai Tsarki ne muke koyan yadda Allah yake so mu bauta masa, da halayen da yake so mu kasance da su da kuma yadda za mu ɗauki abin duniya. Ƙari ga haka, ya nuna mana yadda halin Jehobah yake ta wurin kalaman Yesu da kuma abubuwan da ya yi.—Yohanna 14:9.
Wani dalili kuma da ya sa Allah ya yi mana tanadin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki shi ne don mu san yadda za mu ji daɗin rayuwa. A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya gaya mana yadda za mu zauna lafiya da iyalanmu, da yadda za mu gamsu da abubuwan da muke da su da kuma yadda za mu rage yawan damuwa. Kamar yadda za a bayyana a mujallar nan, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da amsoshin tambayoyi game da rayuwa kamar: Me ya sa muke shan wahala? Me zai faru da mu a nan gaba? Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da Allah ya yi don ya iya cim ma ainihin nufinsa ga duniyar nan.
Akwai wasu abubuwa da yawa da suka nuna cewa Littafi Mai Tsarki, littafi ne mai muhimmanci da babu kamarsa. An rubuta shi shekaru 1,600 da suka shige kuma mutane 40 ne suka rubuta shi. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da saƙo guda ɗaya mai muhimmanci. Hakan ya faru ne don Allah ne Mawallafinsa. (2 Timoti 3:16) Ba kamar sauran tsofaffin littattafai ba, an yi shekaru dubbai ana amfani da Littafi Mai Tsarki kuma bayanan da ke ciki daidai ne kamar yadda suke a cikin rubuce-rubucen Littafi Mai Tsarki na dā. Ban da haka ma, mutane sun yi ƙoƙarin hana fassara da karanta da kuma rarraba Littafi Mai Tsarki, amma ba su yi nasara ba. A yau, Littafi Mai Tsarki shi ne littafin da aka fi rarrabawa da kuma fassarawa. Dukan waɗannan abubuwan sun nuna mana cewa “maganar Allahnmu tana nan har abada!”—Ishaya 40:8.
ALLAH YA TABBATAR MANA CEWA ZAI CIKA NUFINSA
Wani abu kuma da Allah ya yi shi ne ya ba mu tabbacin cewa nufinsa ga ’yan Adam zai cika. Kamar yadda muka ambata ɗazu, nufin Allah shi ne mutane su rayu har abada a nan duniya. Amma bayan Adamu da Hauwa’u sun yi wa Allah rashin biyayya, su da ’ya’yansu sun rasa damar yin rayuwa har abada. “Kamar yadda zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, zunubin nan kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta bi ta shiga dukan ’yan Adam, gama kowa ya yi zunubi.” (Romawa 5:12) Zunubin da Adamu ya yi yana son ya hana cikar nufin Allah da farko. Mene ne Jehobah ya yi?
Farawa 3:15) Yesu Kristi ne kawai zai iya ceto mu daga zunubi da kuma mutuwa. Mene ne hakan ya ƙunsa?
Abubuwan da Jehobah yake yi suna nuna irin halin da yake da shi. Ya hukunta Adamu da Hauwa’u don zunubin da suka yi amma ya yi tanadi wa ’ya’yan da za su haifa. Saboda Jehobah yana da hikima sosai, ya san yadda zai magance matsalar kuma ya faɗi hakan ba tare da ɓata lokaci ba. (Don Jehobah ya ceto mutane daga sakamakon zunubin Adamu, ya aiko da Yesu duniya don ya koya wa mutane hanyar rai kuma ya “ba da ransa domin ceton mutane da yawa.” a (Matiyu 20:28; Yohanna 14:6) Yesu zai iya biyan fansar domin shi kamili ne. Yesu ya riƙe amincinsa har mutuwa ba kamar Adamu ba. Tun da yake Yesu bai cancanci mutuwa ba, Jehobah ya ta da shi daga mutuwa. Ta hakan, Yesu ya ba wa ’yan Adam rai na har abada, abin da Adamu ya ƙasa ba su. “Kamar yadda mutane da yawa suka zama masu zunubi ta wurin rashin biyayyar mutum ɗaya, haka kuma mutane da yawa za su zama masu adalci ta wurin biyayyar mutum ɗaya.” (Romawa 5:19) Ta wurin fansar Yesu, Allah zai cika alkawarinsa ga mutane na yin rayuwa har abada a duniya.
Yadda Jehobah ya magance matsalolin da zunubin Adamu ya jawo ya koya mana abubuwa da yawa game da shi. Mun koyi cewa babu wani abin da zai iya hana Jehobah cim ma nufinsa domin maganar bakinsa “ba za ta kāsa cika” ba. (Ishaya 55:11) Mun kuma koyi irin ƙaunar da Jehobah yake mana. “Ga yadda Allah ya nuna mana ƙaunarsa. Ya aiko da makaɗaicin ɗansa zuwa cikin duniya domin mu sami rai ta wurinsa. Ga yadda ƙauna ta gaskiya take, wato ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, har ya aiko da Ɗansa domin ya zama hadaya ta ɗaukar alhakin zunubanmu.”—1 Yohanna 4:9, 10.
Allah “kuwa bai hana mana Ɗansa ba, amma ya miƙa shi saboda mu duka,” hakan ya tabbatar mana cewa Allah “zai ba mu duk sauran abubuwa hannu sake.” (Romawa 8:32) Mene ne Allah ya yi alkawarin zai yi mana a nan gaba? Ka ci gaba da karatun.
MENE NE ALLAH YA RIGA YA YI? Jehobah ya halicci mutane don su yi rayuwa har abada a duniya. Ya yi mana tanadin Littafi Mai Tsarki don mu koyi abubuwa game da shi. Ta wurin Yesu Kristi, Jehobah ya tanadar da fansar da za ta sa nufinsa ya cika
a Don samun ƙarin bayani game da fansar Yesu, ka duba darasi na 27 na littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi kuma za ka iya sauƙar da shi a dandalinmu na www.dan124.com/ha.