Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Zai Yiwu Ka San Allah Kuwa?

Zai Yiwu Ka San Allah Kuwa?

Mutane da yawa suna cewa sun yi imani da Allah. Amma idan ka tambaye su wane ne Allah, za su ba ka amsoshi dabam-dabam. Wasu sun ce Allah mugu ne kuma ya fi mai da hankali ga hukunta mutane don zunubansu. Wasu kuma sun ce Allah yana ƙaunar mutane, yana kuma gafarta musu duk zunubansu. Ƙari ga haka, wasu sun ce Allah yana nesa da mu kuma bai damu da mu ba sam. Irin ra’ayoyin nan sun sa wasu ganin ba zai taɓa yiwuwa mutum ya san Allah ba.

Yana da muhimmanci mutum ya san Allah? Ƙwarai kuwa. Sanin Allah zai taimaka wa mutum ya yi rayuwa mai kyau sosai. (Ayyukan Manzanni 17:​26-28) Allah zai ƙaunace ka sosai kuma ya taimaka maka idan kana kusantar sa. (Yaƙub 4:8) Mafi muhimmanci ma, sanin Allah zai sa ka sami rai na har abada.​—Yohanna 17:3.

Ta yaya za ka san Allah? Ka yi tunani a kan wani amininka. Ta yaya kuka zama aminai? Mai yiwuwa ka fara da sanin sunansa da halayensa da abubuwan da yake so da waɗanda ba ya so da abin da ya yi da kuma wanda zai yi a nan gaba, da dai sauransu. Abubuwan da ka koya game da shi ne suka sa ka zama abokinsa.

Haka ma, za mu san Allah idan muka bincika tambayoyin nan:

An bayyana amsar da Littafi Mai Tsarki ya bayar ga tambayoyin nan a wannan mujallar. Talifofin da suke ciki za su taimaka maka ka san Allah sosai da kuma albarkar da za ka samu a nan gaba idan ka kasance da dangantaka mai kyau da shi.