Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Tarihi

Jehobah Ya Yi Mana “Alheri Sosai”

Jehobah Ya Yi Mana “Alheri Sosai”

NI DA matata Danièle mun shiga wani masauki ke nan sai wani ma’aikaci a wurin ya ce mini, “Malam, don Allah ka kira ’yan sandan!” Hakan ya faru ne jim kaɗan bayan mun iso ƙasar Gabon da ke Afirka, kuma a ƙasar an saka wa aikinmu taƙunƙumi bayan shekara ta 1970.

Da yake matata mai hattara ce sosai, nan da nan ta gane abin da ke faruwa kuma da sauri ta gaya mini a kunne cewa, “Kada ka kira ’yan sandar, sun riga sun iso!” Sai wata mota ta faka a gaban masaukin. Bayan wasu mintoci, sai aka tsare mu. Amma da yake matata ta gargaɗe ni, hakan ya taimaka mini in ba wani ɗan’uwa takardun da nake riƙe da su.

Sa’ad da muke hanyar zuwa ofishin ’yan sandar, na yi farin ciki cewa na auri mata mai ƙarfin hali da take son ƙungiyar Jehobah sosai. Wannan ba shi ne lokaci na farko da muke yin abu da haɗin kai ba. Barin in gaya muku abin da ya sa muka ziyarci ƙasashen da aka saka wa aikinmu taƙunƙumi.

JEHOBAH YA TAIMAKA MIN IN KOYI GASKIYA

Iyayena ’yan Katolika ne kuma an haife ni a shekara ta 1930 a Croix, wani ƙaramin gari da ke arewaci Faransa. Iyalinmu tana zuwa coci kowane mako kuma mahaifina yana da wasu ayyuka a cocin. Amma da na kusan kai shekara 14, wani aukuwa ya sa na ga cewa ana munafunci sosai a cocin.

Ƙasar Jamus ce ke mulkan Faransa a lokacin da ake Yaƙin Duniya na Biyu. Sa’ad da firist ɗin cocinmu yake wa’azi, yana yawan ƙarfafa mu mu goyi bayan gwamnatin Vichy da ’yan Jamus suka kafa. Abin da ya faɗa ya ba mu mamaki sosai. Mukan saurari labarai daga rundunar haɗin gwiwa ta tashar rediyo na BBC a asirce kuma haka mutane da yawa ke yi a Faransa a lokacin. Ba da daɗewa ba, sai firist ɗin ya daina goyon bayan ’yan Jamus kuma ya shirya taro don a gode wa Allah saboda nasarar da aka ci a kan ’yan Jamus a watan Satumba, 1944. Munafuncin nan ya ba ni mamaki sosai kuma ya sa na daina amincewa da malaman.

Ba da daɗewa ba bayan an daina yaƙin, sai mahaifina ya rasu. Da yake yayata ta riga ta yi aure kuma tana zama a ƙasar Belgium, hakan ya sa na ga cewa ina bukatar in kula da mahaifiyata. Sai na soma aiki a wani kamfani. Shugaban aikina da ɗansa ’yan Katolika ne. Ko da yake da akwai abubuwa da yawa da zan iya cim ma a kamfanin, amma ba da daɗewa ba zan fuskanci jarrabawa.

A shekara ta 1953, ’yar’uwata mai suna Simone da ta zama Mashaidiyar Jehobah ta ziyarce mu. Ta nuna min a Littafi Mai Tsarki cewa koyarwar Katolika, kamar wutan jahannama da Allah-uku-cikin-ɗaya da kuma cewa kurwa ba ta mutuwa ba daidai ba ne. Da farko, na yi mūsu cewa ba ta yin amfani da Littafi Mai Tsarki na Katolika, amma ba da daɗewa ba sai na fahimci cewa abin da take gaya mini gaskiya ne. Bayan haka, sai ta kawo mini wasu tsofaffin talifofin Hasumiyar Tsaro kuma na karance su daddare. Nan da nan, na fahimci cewa wannan shi ne gaskiya, amma na ji tsoro domin idan mutane suka san cewa ni Mashaidin Jehobah ne, za a kore ni daga wurin aiki.

Na yi ’yan watanni ina yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma talifofin Hasumiyar Tsaro ni kaɗai. A ƙarshe sai na yanke shawarar zuwa Majami’ar Mulki. Yadda mutane a wurin ke nuna ƙauna ya ratsa zuciyata sosai. Wani ɗan’uwa da ya manyanta ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni, kuma bayan wata shida, sai na yi baftisma a watan Satumba 1954. Ba da daɗewa ba sai mahaifiyata da kuma ƙanwata suka zama Shaidun Jehobah, hakan ya sa ni farin ciki sosai.

MUN DOGARA GA JEHOBAH A HIDIMARMU

Abin baƙin ciki, mahaifiyata ta rasu kafin taron ƙasashen da aka yi a birnin New York a 1958, amma na sami gatar halartan taron. Da na dawo gida, babu wanda zan kula da shi. Don haka, sai na yi murabus daga wurin aikina kuma na soma hidimar majagaba. Amma kafin nan, na yi wa wata mai suna Danièle Delie alkawarin aure, kuma tana hidimar majagaba da ƙwazo sosai. Sai muka yi aure a watan Mayu 1959.

Matata ta soma hidima ta cikakken lokaci a karkara da ke yankin Brittany, kuma wurin yana da nisa daga garinsu. Tana bukatar ta kasance da gaba gaɗi don ta yi wa’azi a wannan yanki da yawanci mazaunan ’yan Katolika ne kuma takan je wannan yankin a keke. Mun sa ƙwazo sosai a yin wa’azi don ƙarshen wannan zamanin ya kusa sosai. (Mat. 25:13) Halin Danièle na son taimaka wa mutane ya sa mun ci gaba a hidimarmu.

’Yan kwanaki bayan da muka yi aure, sai aka tura mu hidimar kula da da’ira. Mun sauƙaƙa salon rayuwarmu sosai. Masu shela 14 ne kaɗai suke ikilisiya ta farko da muka kai wa ziyara, kuma ’yan’uwan talakawa ne sosai. Saboda haka, ba mu sauƙa a gidansu ba, amma mun kwana a kan tabarma a saman dakalin magana a Majami’ar Mulki. Ko da yake wurin ba tsararre ba ne, amma abin da Jehobah ya yi mana tanadinsa ke nan!

Mun ziyarci ikilisiyoyi a ƙaramar motarmu

Duk da cewa mukan shagala da aiki, matata Danièle ta saba da wannan hidimar sosai. Sau da yawa, takan jira ni a motarmu sa’ad da muke taro da ba mu shirya yi ba da dattawa, amma ba ta taɓa yin gunaguni ba. Mun yi shekara biyu kaɗai a hidimar kula da da’ira. A lokacin, mun koyi cewa yana da muhimmanci ma’aurata su riƙa tattaunawa da juna kuma su riƙa aiki da haɗin kai.​—M. Wa. 4:9.

MUN SOMA WATA HIDIMA

A shekara ta 1962, an gayyace mu mu halarci aji na 37 na Makarantar Gilead a birnin Brooklyn da ke jihar New York. Da akwai ɗalibai 100 a ajin kuma 26 cikinsu suna da aure. Saboda haka, gata ne sosai a gare mu da muka halarci makarantar. Har ila, nakan tuna da cuɗanyar da muka yi da ’yan’uwa masu bangaskiya sosai kamar Ɗan’uwa Frederick Franz da Ulysses Glass da kuma Alexander H. Macmillan.

Mun yi farin cikin halartar Makaranta Gilead!

A makarantar, an ƙarfafa mu mu riƙa mai da hankali don mu lura da abubuwa sosai. A wasu ranakun Asabar da rana mukan je birnin New York don yawon buɗe ido. Kuma mun san cewa za mu rubuta jarabawa a ranar Litinin don mu bayyana abubuwan da muka gani. Mukan gaji sosai sa’ad da muka dawo da yamma a ranar Asabar. Ƙari ga haka, ɗan’uwa da ke Bethel da ya kai mu zagaya yakan yi mana tambayoyi don ya taimaka mana su tuna da abubuwan da muka gani. Wata ranar Asabar mun zagaya birnin sosai. Mun ziyarci wani ginin da ake koyon abubuwa game da taurari. A wani ma’adanar kayayyakin tarihi da ke American Museum of Natural History, mun koyi game da kadoji dabam-dabam. Da muka koma Bethel, ɗan’uwa da ya kai mu zagaya ya tambaye mu, “Mene ne bambanci tsakanin tauraro mai wutsiya da kuma tauraro da ke faɗowa duniya da ake kiran Meteorites?” Matata ta gaji tikis kuma ta amsa, “Meteorites yana da dogayen haƙora!”

Mun ji daɗin ziyartar ’yan’uwa a Afirka

An tura mu yin hidima a ofishinmu da ke ƙasar Faransa kuma mun yi fiye da shekara 53 muna hidima a wurin. A shekara ta 1976, an naɗa ni mai tsara ayyukan Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah. Bayan haka, aka tura ni ziyartar wasu ƙasashen da aka saka wa aikinmu taƙunƙumi a Afirka da kuma a Gabas ta Tsakiya. Wannan ne ya sa muka je ƙasar Gabon da na ambata ɗazu. A gaskiya, a wasu lokuta na ji kamar ban cancanci yin waɗannan hidimomi ba, amma matata ta goyi bayana kuma na sami damar cim ma kowace irin hidima.

Ina fassara jawabin Ɗan’uwa Theodore Jaracz a taron yankin “Divine Justice” a 1988 a birnin Faris

MUN JIMRE DA WATA MATSALA

Tun daga farko, muna son yin hidima a Bethel. A cikin watanni biyar kafin mu halarci Makarantar Gilead, matata Danièle ta koyi Turanci kuma ta ƙware a fassara littattafanmu. Mun ji daɗin hidimar da muke yi a Bethel sosai, amma ayyukan da muke yi a ikilisiyarmu ta fi sa mu farin ciki. Na tuna ranar da ni da Danièle muka shiga jirgin ƙasa daddare. Duk da cewa mun gaji, mun yi farin ciki domin mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗalibanmu da ke samun ci gaba. Abin taƙaici, matata ta soma rashin lafiyar da ya hana ta yin abubuwa kamar yadda take yi a dā.

A shekara ta 1993, an gano cewa matata tana da cutar kansa ta mama. Yin jinyar wannan cuta bai yi mata sauƙi ba domin ta ƙunshi tiyata da kuma chemotherapy, wato shan ƙwayoyi masu ƙarfi don warkar da cutar. Bayan shekara goma sha biyar, an sake ganowa tana da kansar da ta fi na farkon tsanani. Matata tana son aikinta na fassara sosai, don haka tana zuwa aiki a duk lokacin da ta ɗan samu sauƙi.

Duk da cewa matata tana rashin lafiya mai tsanani, ba mu taɓa yin tunanin barin Bethel ba. Yin hidima a Bethel sa’ad da mutum yake rashin lafiya bai da sauƙi, musamman ma idan mutane ba sun cewa rashin lafiyar na da tsanani ba. (K. Mag. 14:13) Duk da cewa Danièle ta kusan shekara 80, mutum ba zai taɓa ganewa cewa tana rashin lafiya sosai ba. Matata ba ta mai da hankali ga matsalarta, a maimakon haka, ta mai da hankali ga taimaka wa mutane ta wajen saurarar su. (K. Mag. 17:17) Ta yi amfani da abubuwan da ta fuskanta wajen taimaka ma wasu ’yan’uwa mata don kada su riƙa jin tsoron ciwon kansa.

Ƙari ga haka, mun jimre da wasu matsalolin da suka taso. A lokacin da matata ta daina yin aiki kullum, ta yi ƙoƙari don ta taimaka mini a wasu hanyoyi. Ta yi iya ƙoƙarinta don abubuwa su yi mini sauƙi kuma hakan ya taimaka mini na yi shekaru 37 ina hidima a matsayin mai tsara ayyukan Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah. Alal misali, tana shirya abin da za mu ci da rana a ɗakinmu kuma mu ɗan huta kowace rana.​—K. Mag. 18:22.

YADDA MUKE JIMREWA DA ALHINI KULLUM

Matata ta kasance da ra’ayi mai kyau game da rayuwa. Amma an sake ganowa cewa tana da ciwon kansa. Hakan ya sa mu sanyin gwiwa. Shan ƙwayoyi masu ƙarfi sosai da kuma kasancewa a cikin na’urar gashi don warkar da cutar ya rage ƙarfinta har a wasu lokuta, ba ta iya yin tafiya. Ganin yadda yin magana yake yi wa matata wadda ta ƙware a aikin fassara wuya, ya sa ni baƙin ciki sosai.

Duk da cewa ba mu san abin da za mu yi ba, mun ci gaba da yin addu’a kuma mun kasance da tabbaci cewa Jehobah ba zai taɓa barin mu mu fuskanci abin da ba za mu iya jimrewa ba. (1 Kor. 10:13) Mun yi iya ƙoƙarinmu don mu nuna godiya ga Jehobah a yadda ya yi amfani da Kalmarsa da ’yan’uwan da ke aiki a sashen jinya a Bethel da kuma ’yan’uwanmu maza da mata don ya ƙarfafa mu.

Mukan nemi taimakon Jehobah don mu san irin jinyar da za mu amince da ita. Akwai wani lokaci da babu likitan da ke son ya kula da matata. Likitan da ya yi shekaru 23 yana taimaka mata ya kasa bayyana mana dalilin da ya sa take sumewa a duk lokacin da aka ba ta ƙwayoyi, kuma bai san maganin da zai ce ta riƙa sha ba. Hakan ya sa ba mu san abin da za mu yi ba kuma ba mu san abin da zai faru ba. Sai wani likitan da ke warkar da ciwon kansa ya aminci ya kula da ita. Kamar dai Jehobah ya taimaka mana mu daina yin alhini ne.

Muna mai da hankali ga matsalar da muke fuskanta kowace rana ba wacce za mu fuskanta a nan gaba ba. Yesu ya ce “wahalolin yau sun ishe ku domin yau.” (Mat. 6:34) Wani abu kuma da ya taimaka mana shi ne kasancewa da fara’a. Alal misali, da akwai wani lokaci da matata ta yi wata biyu ba tare da shan magunguna ba, sai ta ce mini da murmushi, “Yanzu na ji garau!” (K. Mag. 17:22) Duk da cewa tana rashin lafiya sosai, tana son rera waƙoƙinmu da babbar murya da kuma gaba gaɗi.

Ra’ayi mai kyau da matata take da shi ya taimaka mini na bi da kasawata. A gaskiya, a shekaru 57 da muka yi a aurenmu, matata ta kula da ni sosai. Har ma ba ta koya mini yadda ake soya ƙwai ba! Don haka, a lokacin da ba ta iya yin wasu abubuwa ba, na koyi yin wanke-wanke da wanki da kuma dafa wasu abinci masu sauƙi. Duk da cewa sa’ad da nake waɗannan abubuwan na fasa wasu kofin, amma na yi farin cikin domin ina kula da matata. *

MUNA GODIYA DON ALHERIN JEHOBAH

Na koyi darussa sosai daga rashin lafiyar matata da kuma tsufa. Na farko, kada mu bari yawan aiki ya hana mu nuna wa matarmu ko kuma mijinmu cewa muna ƙaunar su. Muna bukatar mu yi amfani da lokacin ƙuruciyarmu domin mu kula da masoyanmu. (M. Wa. 9:9) Na biyu, kada mu riƙa damuwa ainun a kan abin da bai taka-kara-ya-ƙarya ba, domin yin hakan zai hana mu ganin yadda Jehobah yake yi mana albarka a kowace rana.​—K. Mag. 15:15.

Idan na yi tunani a kan shekarun da muka yi muna yin hidima ta cikakken lokaci, ina da tabbaci cewa Jehobah ya yi mana albarka fiye da kima. Hakan ya sa na kasance da irin ra’ayin wani marubucin Zabura da ya ce, Jehobah ya yi mini “alheri sosai.”​—Zab. 116:7.

^ sakin layi na 32 ’Yar’uwa Danièle Bockaert ta rasu yayin da ake shirya wannan talifin. Tana ’yar shekara 78.