Ka Tuna?
Ka ji daɗin karanta talifofin Hasumiyar Tsaro na kwanan bayan nan kuwa? Ka ga ko za ka iya amsa tambayoyi na gaba:
Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah yana tausaya mana?
Sa’ad da Isra’ilawa a zamanin dā suke zaman bauta a Masar, Allah ya san suna shan wahala kuma ya tausaya musu. (Fit. 3:7; Isha. 63:9) Allah ya halicce mu a kamanninsa, saboda haka mu ma muna jin tausayin mutane. Allah yana jin tausayinmu ko a lokacin da muke ganin ba mu cancanci ya ƙaunace mu ba.—wp18.3, shafuffuka na 8-9.
Ta yaya koyarwar Yesu ta taimaka wa mutane su daina nuna wariya?
Yahudawa da yawa a zamanin Yesu suna nuna wariya. Kristi ya nuna cewa yana da muhimmanci mu zama masu tawali’u kuma ya hana mu nuna kishin ƙasa. Ya ƙarfafa mabiyansa su ɗauki juna a matsayin ’yan’uwa.—w18.06, shafuffuka na 9-10.
Me muka koya daga dalilin da ya sa Allah ya hana Musa shiga Ƙasar Alkawari?
Musa ya ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah. (M. Sha. 34:10) Kusan ƙarshen shekara 40 da Isra’ilawa suka yi a jeji, sun yi gunaguni a ƙaro na biyu game da rashin ruwa. Allah ya gaya wa Musa ya yi wa dutsen magana, amma Musa ya bugi dutsen. Wataƙila Jehobah ya yi fushi da Musa don bai bi umurninsa ba ko kuma bai ɗaukaka shi sa’ad da ya yi mu’ujizar ba. (L. Ƙid. 20:6-12) Ya kamata hakan ya koya mana cewa yana da muhimmanci mu riƙa yi wa Jehobah biyayya kuma mu ɗaukaka shi.—w18.07, shafuffuka na 13-14.
Me ya sa bai dace ba mu riƙa shari’anta mutane bisa abin da muka gani?
Akwai wurare uku da abin da mutane suka gani yake shafansu. Abubuwan su ne launin fata da arziki da kuma shekaru. Yana da muhimmanci mu riƙa yin koyi da Allahn da ba ya nuna wariya! (A. M. 10:34, 35)—w18.08, shafuffuka na 8-12.
A waɗanne hanyoyi ne tsofaffi za su iya taimaka ma wasu?
Allah yana daraja tsofaffin da ba sa iya yin hidimar da suke yi a dā kuma za su iya yin iya ƙoƙarinsu don su riƙa taimaka ma wasu. Suna iya taimaka wa ma’aurata da ɗaya a cikinsu ba ya bauta wa Jehobah da waɗanda suka daina halartan taro. Za su iya yin nazarin Littafi Mai Tsarki da wani kuma su faɗaɗa hidimarsu.—w18.09, shafuffuka na 8-11.
Waɗanne abubuwa ne ke cikin Kayan Aiki don Koyarwa da za mu iya yin amfani da su?
Muna da katin JW da takardun gayyata da warƙoƙi guda takwas da aka tsara da kyau da kuma Hasumiyar Tsaro da Awake! Ƙari ga haka, muna da wasu ƙasidu da littattafai guda biyu da muke nazari da su da kuma bidiyoyi huɗu masu ƙayatarwa, hakan ya ƙunshi bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki?—w18.10, shafi na 16.
Ta yaya za mu iya ‘sayan gaskiya,’ kamar yadda aka ambata a Karin Magana 23:23?
Ba ma biyan kuɗi don mu koyi gaskiya. Amma muna bukatar mu keɓe lokaci don mu koyi gaskiya kuma mu ƙoƙarta sosai domin mu same ta.—w18.11, shafi na 4.
Wane darasi ne muka koya daga Hosiya a yadda ya bi da matarsa?
Matarsa ta yi zina sau da sau, amma Hosiya ya gafarta mata kuma ya ci gaba da zama da ita. Idan mutum mai aure ya yi zina, mijin ko matar za ta iya gafartawa. Kuma idan wanda ya gafarta ya soma yin jima’i da mai laifin, ba zai sake samun izinin kashe auren ba.—w18.12, shafi na 13.