Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Matasa, Za Ku Iya Yin Rayuwa Mai Gamsarwa

Matasa, Za Ku Iya Yin Rayuwa Mai Gamsarwa

“Kana nuna mini hanya, hanyar da za ta kai ga rai.”​—ZAB. 16:11.

WAƘOƘI: 133, 89

1, 2. Ta yaya labarin ɗalibin nan ya nuna cewa za mu iya yin canji a rayuwa?

AKWAI wani yaro mai suna Tony da ya girma ba tare da mahaifinsa ba, kuma ba ya son zuwa makaranta. Bugu da ƙari, yana tunanin barin makaranta. A ƙarshen mako, yana yawan kallon fina-finai da kuma yin cuɗanya da abokansa. Tony ba mugu ba ne kuma ba ya shan ƙwayoyi. Matsalarsa ita ce bai san manufar rayuwa ba. Ƙari ga haka, yana shakka cewa Allah yana wanzuwa. Wata rana ya haɗu da wasu Shaidun Jehobah ma’aurata, ya tattauna da su game da abubuwan da suke sa shi shakka kuma ya yi musu tambayoyi. Sun ba shi ƙasidu guda biyu masu jigo The Origin of Life​—Five Questions Worth Asking da kuma Was Life Created?

2 Da ma’auratan suka sake ziyarta Tony, ra’ayinsa ya canja. Ya yi nazarin ƙasidun sosai har ƙasidun sun yanƙwane. Ya ce, “Babu shakka akwai Allah.” Tony ya amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi kuma a sannu-a-hankali ya canja ra’ayinsa game da rayuwa. Ƙari ga haka, kafin Tony ya soma nazari, ba ya ƙoƙari a makaranta. Amma sa’ad da ya soma nazari, sai ya soma ƙoƙari sosai har ya zama ɗaya cikin ɗaliban da malamai ke alfahari da su. Shugaban makarantar ya yi mamaki kuma ya ce: “Halinka ya canja sosai kuma kana ƙoƙari a makaranta yanzu. Yin cuɗanya da Shaidun Jehobah ne ya taimaka maka?” Tony ya ce E, kuma ya yi wa shugaban makarantarsu wa’azi. Tony ya sauke karatu kuma a yau yana yin hidimar majagaba na kullum. Ban da haka, shi bawa mai hidima ne, kuma yana farin ciki cewa yanzu yana da Uba nagari, wato Jehobah.​—Zab. 68:5.

ZA KU YI NASARA IDAN KUKA YI BIYAYYA GA JEHOBAH

3. Wace shawara ce Jehobah ya ba matasa?

3 Labarin Tony ya tuna mana cewa Jehobah ya damu da matasa sosai. Yana so ku yi nasara kuma ku samu gamsuwa a rayuwa. Don haka ya shawarce ku cewa: ‘Ku tuna da Mahaliccinku a kwanakin kuruciyarku.’ (M. Wa. 12:1) A yau yin hakan bai da sauƙi, amma za ku iya yin hakan. Da taimakon Allah za ku iya yin nasara yanzu da kuke matasa da kuma sa’ad da kuka girma. Yanzu, bari mu tattauna abin da ya taimaka wa Isra’ilawa su shiga Ƙasar Alkawari da kuma abin da ya taimaka wa Dauda ya yi nasara a kan Goliath.

4, 5. Wane darasi ne muka koya daga labarin nasarar da Isra’ilawa suka yi a kan Kan’aniyawa da kuma yadda Dauda ya yi nasara a kan Goliath? (Ka duba hotunan da ke shafi na 24.)

4 A lokacin da Isra’ilawa suka kusan shiga Ƙasar Alkawari, Allah bai umurce su su zama ƙwararrun sojoji ba ko kuma su koyi yin yaƙi. (M. Sha. 28:​1, 2) A maimakon haka, ya gaya musu cewa suna bukatar su bi umurninsa kuma su dogara gare shi. (Yosh. 1:​7-9) A ra’ayin ’yan Adam, wannan shawarar ba ta dace ba! Amma shawarar ta dace sosai domin Jehobah ya taimaka wa mutanensa su yi nasara a kan Kan’aniyawa. (Yosh. 24:​11-13) Babu shakka, muna bukatar bangaskiya domin mu bi umurnin Allah, kuma kasancewa da bangaskiya yana sa mu yi nasara a kowanne lokaci. Hakan ya faru a zamanin dā kuma yana faruwa a yau.

5 Goliath jarumi ne wanda tsayinsa ya kai wajen ƙafa tara da rabi kuma yana ɗauke da makamai. (1 Sam. 17:​4-7) Amma bangaskiya ga Jehobah da kuma majajjawa ne kawai Dauda yake da su. Mutanen da ba su da bangaskiya suna ganin cewa Dauda wawa ne. Amma a gaskiya, Goliath ne wawa.​—1 Sam. 17:​48-51.

6. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

6 A talifin da ya gabata, mun tattauna abubuwa guda huɗu da za su sa mu farin ciki da kuma samun gamsuwa a rayuwa. Waɗannan abubuwan su ne ƙulla dangantaka mai kyau da Allah da neman abokan kirki da kafa maƙasudai masu kyau da kuma daraja ’yancinmu. A wannan talifin, za mu tattauna wasu hanyoyi da za mu amfana idan muka yi waɗannan abubuwan. Yin la’akari da wasu ƙa’idodin da ke littafin Zabura ta 16 zai taimaka mana.

KU ƘARFAFA DANGANTAKARKU DA JEHOBAH

7. (a) Ta yaya za ka kwatanta mutumin da ke da dangantaka mai kyau da Allah? (b) Mene ne Dauda yake “da shi” kuma ta yaya hakan ya shafe shi?

7 Mutumin da ke da dangantaka mai kyau da Allah yana ƙoƙarin kasancewa da ra’ayin Allah. Yana barin Jehobah ya yi masa ja-goranci kuma yana masa biyayya. (1 Kor. 2:​12, 13) Dauda ya kafa misali mai kyau a wannan batun. Ya ce: “Ya Yahweh, Kai ne abin da nake da shi, kai ne kwaf na biyan bukatata.” (Zab. 16:5) Abin da Dauda yake da shi ya ƙunshi dangantakarsa da Allah kuma hakan ya sa ya dogara gare shi. (Zab. 16:1) Wane sakamako ne Dauda ya samu? Ya rubuta cewa: “Zuciyata tana murna.” Babu abin da ya fi sa Dauda farin ciki kamar dangantakarsa da Allah.​—Karanta Zabura 16:​9, 11.

8. Waɗanne abubuwa ne za su sa mutum ya sami gamsuwa a rayuwa?

8 Mutanen da suke mai da hankali ga biɗan kayan duniya ba za su taɓa yin farin ciki kamar Dauda ba. (1 Tim. 6:​9, 10) Wani ɗan’uwa a Kanada ya ce: “Abubuwan da muke da su ba za su sa mu sami gamsuwa a rayuwa ba, amma abubuwan da muke ba Jehobah Wanda ya ba mu rai su ne za mu sa mu sami gamsuwa.” (Yaƙ. 1:17) Kasancewa da bangaskiya ga Jehobah da kuma bauta masa ne za su sa rayuwarku ta kasance da ma’ana kuma ku sami gamsuwa. Mene ne zai ƙarfafa bangaskiyarku? Kuna bukatar karanta Kalmar Allah, ku lura da abubuwan da ya halitta kuma ku yi tunani a kan halayensa, har da yadda yake ƙaunar ku.​—Rom. 1:20; 5:8.

9. Kamar Dauda, ta yaya za ka bar Kalmar Allah ta riƙa sarrafa tunaninka?

9 Kamar yadda mahaifi yake yi wa yaransa gyara, Allah yana nuna mana cewa yana ƙaunar mu ta wajen yi mana gyara idan mun yi kuskure. Dauda ya so irin wannan gyaran, shi ya sa ya ce: Zan “yabi Yahweh wanda yake bi da ni, ko da dare zuciyata tana yi mini gargaɗi.” (Zab. 16:7) Dauda ya yi tunani sosai a kan ra’ayin Allah, kuma ya yi ƙoƙarin kasancewa da irin wannan ra’ayin. Ya bar ra’ayin Allah ya gyara halayensa. Idan ka yi hakan, ƙaunarka ga Allah za ta yi ƙarfi kuma za ka so yin abin da zai riƙa faranta masa rai. Ban da haka, za ka manyanta. Wata ’yar’uwa mai suna Christin ta ce: “Idan na yi bincike kuma na yi tunani sosai a kan abin da na karanta, ina ji kamar Jehobah ya sa a rubuta shi domin ni!”

10. Kamar yadda littafin Ishaya 26:3 ya ce, ta yaya ƙulla dangantaka mai kyau da Allah zai taimaka muku?

10 Idan kuna mai da hankali ga ibadarku ga Jehobah, za ku ɗauki duniyar nan yadda Allah yake ɗaukan ta. Jehobah ya ba ku ilimi da kuma hikima na yin hakan. Me ya sa Allah ya ba ku irin wannan ilimi da kuma hikima? Yana so ku kafa maƙasudai masu kyau, ku tsai da shawarwarin da suka dace kuma ku kasance da bege game da nan gaba! (Karanta Ishaya 26:3.) Wani ɗan’uwa a Amirka mai suna Joshua ya ce: “Idan mutum ya kusaci Jehobah, zai san abubuwan da suke da muhimmanci da kuma waɗanda ba su da muhimmanci.” Hakan gaskiya ne, kuma yana kawo gamsuwa a rayuwa!

KU NEMI ABOKAN KIRKI

11. Mene ne ya taimaki Dauda ya zaɓi abokan kirki?

11 Karanta Zabura 16:3. Dauda ya san yadda zai nemi abokan kirki. Ya zaɓi yin abokantaka da mutanen da ke ƙaunar Jehobah kuma yin hakan ya “faranta” masa rai. Ya ce abokansa ‘amintattun jama’a’ ne domin suna da ɗabi’a mai kyau. Wani marubucin Zabura ma ya kasance da irin wannan ra’ayin, ya ce: “Ni abokin dukan masu tsoronka ne, abokin dukan masu kiyaye ƙa’idodinka.” (Zab. 119:63) Kamar yadda muka tattauna a talifin da ya gabata, kuna iya samun abokan kirki a cikin mutanen da suke bauta wa Jehobah kuma suke yi masa biyayya. Hakan yana nufin cewa ba tsararku kaɗai ba ne za su zama abokanku ba.

12. Mene ne ya taimaka wa Dauda da Jonathan su zama abokai?

12 Dauda bai yi abokantaka da tsararsa kaɗai ba. Za ka iya tuna sunan wani abokin Dauda na kud da kud? Sunansa Jonathan ne, kuma abokantakarsa da Dauda yana cikin abokantaka mafi kyau da aka ambata a Littafi Mai Tsarki. Amma kun sani cewa Jonathan ya girme Dauda da wajen shekaru 30? Mene ne ya taimaka musu su ci gaba da zama abokai? Bangaskiyarsu ga Allah ce da daraja juna da kuma gaba gaɗin da suka nuna yayin da suke yaƙan maƙiyan Allah ne.​—1 Sam. 13:3; 14:13; 17:​48-50; 18:1.

13. Ta yaya za ku sami ƙarin abokai? Ku ba da misali.

13 Kamar Dauda da Jonathan, idan kuka ƙulla abokantaka da mutanen da ke ƙaunar Jehobah kuma suke da bangaskiya, hakan zai “faranta” muku rai. Wata mai suna Kiera da ta daɗe tana bauta wa Jehobah ta ce: “Na ƙulla abokantaka da mutane da yawa a faɗin duniya, mutane daga wurare dabam-dabam da kuma al’adu dabam.” Idan kuka yi hakan, za ku ga yadda Littafi Mai Tsarki da kuma ruhu mai tsarki suke taimaka mana mu kasance da haɗin kai.

KU KAFA MAƘASUDAI MASU KYAU

14. (a) Mene ne zai taimaka muku ku kafa maƙasudai masu kyau? (b) Mene ne wasu matasa suka ce game da kafa maƙasudai?

14 Karanta Zabura 16:8. Dauda ya ɗauki bauta wa Jehobah da muhimmanci sosai. Za ku yi farin ciki kuma ku sami gamsuwa idan kuka ɗauki bautarku ga Jehobah da muhimmanci kuma kuka kafa maƙasudai. Wani ɗan’uwa mai suna Steven ya ce: “Idan na yi tunani a kan maƙasudai da na kafa kuma na cim ma, hakan na sa ni farin ciki.” Wani ɗan’uwa daga Jamus da yanzu yake hidima a wata ƙasa ya ce: “A lokacin da na tsufa ba na so in ga cewa dukan maƙasudai da na kafa domin in faranta wa kaina rai ne kawai.” Kuna jin hakan kuwa? Idan haka ne, ku yi amfani da baiwarku don ku ɗaukaka Allah kuma ku taimaka wa mutane. (Gal. 6:10) Ku kafa maƙasudai a hidimarku ga Jehobah kuma ku roƙe shi ya taimaka muku ku cim ma hakan. Jehobah yana farin cikin amsa irin waɗannan addu’o’i.​—1 Yoh. 3:22; 5:​14, 15.

15. Waɗanne maƙasudai ne za ku iya kafa wa kanku? (Ka duba akwatin nan “ Wasu Maƙasudai da Za Ku Iya Kafa wa Kanku.”)

15 Waɗanne irin maƙasudai ne za ku kafa wa kanku? Za ku iya kafa maƙasudan yin kalami a taro da yin hidimar majagaba da kuma yin hidima a Bethel. Ƙari ga haka, kuna iya koyan wani yare don ku yi wa’azi a yankin da ake yaren. Wani matashi mai suna Barak da yake yin hidima ta cikakken lokaci ya ce: “A kowace rana ina farin ciki domin na san cewa ina amfani da ƙarfina don in yi wa Jehobah hidima.”

KU RIƘA DARAJA ’YANCINKU

16. Ta yaya Dauda ya ɗauki ƙa’idodin Jehobah kuma me ya sa?

16 Karanta Zabura 16:​2, 4Kamar yadda muka tattauna a talifin da ya gabata, idan kuna yin rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Allah da dokokinsa, za ku sami ’yanci na gaske. Ƙari ga haka, za su taimaka muku ku so abubuwa masu kyau kuma ku guji abubuwa marasa kyau. (Amos 5:15) Dauda ya ce ba shi da wani “abu mai daraja” sai Jehobah. Kalmar asali a Littafi Mai Tsarki da aka fassara zuwa “abu mai daraja” tana kuma nufin nagarta. Dauda ya yi ƙoƙarin yin koyi da Allahnsa kuma ya so abubuwan da Jehobah ke so. Ƙari ga haka, ya yi ƙoƙarin guje wa abubuwan da Jehobah ba ya so. Hakan ya ƙunshi bautar gumaka, abin da ke ƙazantar da ’yan Adam kuma yake hana mu ɗaukaka Jehobah.​—Isha. 2:​8, 9; R. Yar. 4:11.

17, 18. (a) Wane sakamako ne Dauda ya ce bin addinin ƙarya ke jawowa? (b) Mene ne yake sa mutane a yau su jawo wa “kansu wahala sosai”?

17 A zamanin dā, bautar gumaka ta ƙunshi yin lalata. (Hos. 4:​13, 14) Mutane da yawa suna jin daɗin bautar ƙarya domin suna son lalata. Amma hakan ba ya sa mutanen farin ciki. A maimakon haka, Dauda ya ce suna “jawo wa kansu wahala.” Ban da haka, waɗannan mutanen suna ba da yaransu hadaya ga allolin ƙarya. (Isha. 57:5) Jehobah ya tsani irin wannan muguntar! (Irm. 7:31) Da a ce kuna raye a zamanin, babu shakka da kun yi farin ciki cewa iyayenku suna bauta wa Jehobah kuma suna biyayya gare shi.

18 A yau, yin lalata da luwaɗi a addinin ƙarya ba laifi ba ne. Hakan yana iya sa mutane tunanin cewa suna da ’yanci, amma a gaske suna jawo wa kansu wahala ne kawai. (1 Kor. 6:​18, 19) Shin ka lura da hakan kuwa? Idan haka ne, matasa, kuna bukatar ku saurari Ubanmu da ke sama. Ku kasance da tabbaci cewa yin biyayya gare shi zai amfane ku. Ku san cewa sakamako marar kyau na yin munanan ayyuka yana da muni sosai. (Gal. 6:8) Joshua wanda aka ambata ɗazu ya ce: “Muna iya yin amfani da ’yancinmu yadda muke so, amma yin amfani da shi yadda muka ga dama ba zai sa mu sami gamsuwa ba.”

19, 20. Wace albarka ce matasa da suke da bangaskiya ga Jehobah kuma suke yi masa biyayya za su samu?

19 Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “In dai kun ci gaba da riƙe koyarwata, ku almajiraina ne na gaske. Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ba ku ’yanci.” (Yoh. 8:​31, 32) Wannan ’yancin ya ƙunshi ’yanci daga addinin ƙarya da rashin sani da kuma camfi. Ban da haka, ya ƙunshi wasu abubuwa dabam. Kamar yadda muka tattauna, ta ƙunshi “ ’yancin nan na ɗaukakar da za a yi wa ’ya’yan Allah.” (Rom. 8:21) A yau, kuna iya amfana daga wannan ’yanci idan kuka ‘ci gaba da riƙe koyarwar’ Yesu. Za ‘ku san gaskiya’ kuma za ku yi rayuwar da ta jitu da ita.

20 Matasa, ku riƙa daraja ’yancin da Allah ya ba ku. Ku yi amfani da shi yadda ya dace. Hakan zai taimaka muku ku riƙa tsai da shawarwarin da suka dace yanzu kuma zai amfane ku a nan gaba. Wani ɗan’uwa matashi ya ce: “Idan kana amfani da ’yancinka yadda ya dace yanzu da kake matashi, hakan zai taimaka maka idan a nan gaba ka bukaci tsai da shawara mai muhimmanci. Shawarwari kamar neman aiki ko yin aure ko kuma jimawa kafin ka yi aure.”

21. Me zai taimaka muku ku sami “ainihin rai”?

21 A wannan zamanin, abubuwan da mutane ke ganin cewa jin daɗi ne ba ya jimawa. Babu wanda ya san abin da zai faru a nan gaba. (Yaƙ. 4:​13, 14) Abin da kuke bukatar ku yi shi ne tsai da shawarwarin da za su taimaka muku ku sami “ainihin rai,” wato rai na har abada da Allah ya yi mana alkawarinsa. (1 Tim. 6:19) Babu shakka, Jehobah ba ya tilasta mana mu bauta masa. Mu ne za mu zaɓi abin da za mu yi. Don haka, ku riƙa daraja “abubuwa masu kyau” da Jehobah ya ba ku. (Zab. 103:5) Ku kasance da bangaskiya cewa zai sa ku yi “farin ciki” sosai kuma ku ‘ji daɗi . . . har abada.’​—Zab. 16:11.