TARIHI
Budurwai Masu Zaman Zuhudu Sun Zama ‘Yan’uwanmu
SHEKARU da yawa da suka shige, ina bayyana wa ƙanwata Araceli wasu abubuwan da nake koya, sai ta yi fushi kuma ta yi mini tsawa. Ta ce: “Ki daina yi min wa’azi. Ba na son in sake jin wani abu game da addininku. Yana ɓata min rai. Na tsane ki!” Na yi baƙin ciki sosai saboda waɗannan kalaman da ta yi. Yanzu shekaru na 91 ne kuma ban manta da waɗannan kalaman ba. Amma kamar yadda Littafin Mai-Wa’azi 7:8 ta ce, “gwamma ƙarshen abu da farkonsa.”—Felisa.
Felisa: An haife ni a ƙasar Sifen kuma iyayena ba masu kuɗi ba ne. Muna bin addinin Katolika a iyalinmu kuma mun riƙe addinin da hannu bibiyu. Dangina guda 13 sun yi hidima a coci a matsayin limamai ko kuma a wani matsayi dabam. Kawuna limami ne kuma malami ne a wata makarantar Katolika. Bayan mutuwarsa, Paparoma John Paul II ya ɗaukaka shi a matsayin tsarkakke. Mahaifina maƙeri ne kuma mahaifiyata tana aiki a gona. Mu yara takwas ne kuma ni ce babba a cikin su.
An soma yaƙin basasa a ƙasar Sifen sa’ad da nake ‘yar shekara sha biyu. Bayan yaƙin, sai aka jefa mahaifina a kurkuku don gwamnatin ƙasar ba ta amince da ra’ayinsa game da siyasa ba. Mahaifiyarmu ta soma shan wahala wajen neman abinci don ta ciyar da mu. Saboda haka, sai ta aika ƙannena mata guda uku, wato Araceli da Lauri da kuma Ramoni zuwa wani gidan zaman zuhudu a birnin Bilbao don su sami isashen abinci.
Araceli: A lokacin, ina ‘yar shekara 14, Lauri tana da shekara 12, Ramoni kuma shekarunta 10 ne. Mun yi kewar iyalinmu sosai. Muna aikin shara a gidan zaman zuhudun. Shekaru biyu bayan haka, matan zuhudun sun tura mu zuwa wani gidan zuhudu inda ake kula da tsofaffi da ke birnin Zaragoza. Muna aiki tuƙuru wajen share kicin kuma hakan ya sa muna gajiya sosai.
Felisa: Sa’ad da aka tura ƙannena mata zuwa gidan zuhudu a birnin Zaragoza, mahaifiyata da kawuna limami sun ce za su tura ni wurin. Suna so su kāre
ni daga wani yaro da ke so na. Na yi ɗokin zama a gidan zuhudu don ina ƙaunar Allah. Ina zuwa coci kullum kuma na soma kasancewa da burin zama mai wa’azin addinin Katolika a ƙasar waje kamar wani ɗan’uwana da ke Afirka.Amma ban sami damar yin abubuwan da nake so a gidan zuhudun ba. Matan zuhudun ba sa son in je wa’azi a ƙasar waje kamar yadda nake fata. Shekara ɗaya bayan haka, sai na koma gida don in kula da kawuna, wanda limami ne. Ina kula da hidimomin gida, kuma muna addu’ar Rosary tare kowace yamma. Ƙari ga haka, ina jin daɗin jera furanni a coci da kuma yi wa siffofin Maryamu da “waliyai” ado.
Araceli: Sa’ad da nake Zaragoza, na ɗauki alkawari na farko na zama ‘yar zuhudu. Bayan haka, matan zuhudun suka raba ni da ‘yan’uwana mata. Sun tura ni zuwa wani gidan zuhudu da ke birnin Madrid kuma suka tura Lauri zuwa gidan zuhudu da ke birnin Valencia. Amma, an bar Ramoni a Zaragoza. A birnin Madrid ne na ɗauki alkawari na biyu na zama ‘yar zuhudu. Mutane da yawa kamar ɗalibai da tsofaffi sukan zo su zauna a gidan zuhudu. Saboda haka, akwai aikin yi da yawa. Na yi aiki a asibitin da ke gidan zuhudun.
Na yi marmarin zama ‘yar zuhudu. Na ɗauka cewa zan sami damar karanta Littafi Mai Tsarki da kuma koyon abin da ke ciki. Amma abin taƙaici shi ne ba wanda yake karanta Littafi Mai Tsarki ko kuma yin magana game da Allah ko Yesu. Na koyi yaren Latin kuma na yi nazari a kan rayuwan “waliyai” da kuma bauta wa Maryamu. Amma a yawancin lokaci, aiki mai wuya muke yi.
Hakan ya sa na soma gajiya da kuma damuwa. Na ga cewa zai fi dacewa in yi aiki don in taimaka wa iyalina a maimakon yin aiki a gidan zuhudu da ke azurtar da mutane. Saboda haka, sai na gaya wa shugaban mata zuhudu game da hakan kuma na ce mata ina son in bar gidan. Amma ta kulle ni a cikin wani ɗaki don ta ɗauka cewa hakan zai sa in canja ra’ayina game da barin gidan.
Matan zuhudun sun fito da ni daga cikin ɗakin, amma sa’ad da suka ga cewa ina son in bar gidan, sai suka sake rufe ni a cikin ɗakin. Da suka yi hakan sau uku, sai suka ce za su bar ni in tafi idan na rubuta cewa ina son in bar gidan zuhudun don na fi so in bauta wa Shaiɗan maimakon Allah. Hakan ya ba ni mamaki. Ko da yake na ƙosa in bar gidan, amma na ƙi in rubuta waɗannan kalaman. A ƙarshe, na nemi izinin yin magana da limami kuma na gaya masa abin da ya faru. Sai ya nemi izini daga wurin babban limami, wato bishop cewa a tura ni zuwa gidan zuhudu da ke Zaragoza, inda nake dā. Bayan na yi wasu watanni a Zaragoza, sai aka bar ni in tafi. Jim kaɗan bayan haka, Lauri da Ramoni ma suka bar gidan zuhudun.
LITTAFIN DA YA RABA MU
Felisa: Bayan haka sai na yi aure kuma muka koma wani yanki da ake kira Cantabria. Ina zuwa coci kullum. Wata ranar Lahadi, limamin ya nuna mana littafin nan Gaskiya Mai Bishe Zuwa Rai Madauwami kuma ya ce: “Kun ga wannan littafin? Idan wani ya ba ku, ku kawo min ko kuma ku yar da shi!”
Ba ni da littafin, amma na so in samu. ‘Yan kwanaki bayan haka, wasu mata biyu Shaidun Jehobah suka zo gidanmu kuma suka ba ni littafin. Na karance littafin a daren. Sa’ad da matan suka dawo, sai suka tambaye ni ko zan so in yi nazarin Littafi Mai Tsarki, sai na amince.
Burina shi ne in yi abin da Allah yake so. Sai na soma koyan gaskiya game da Jehobah kuma hakan ya sa na soma ƙaunarsa sosai. Ina son in gaya wa kowa game da shi. A shekara ta 1973, aka yi min baftisma. Ina yi wa ‘yan gidanmu magana game da gaskiyar da ke cikin Littafin Mai Tsarki a duk lokacin da na sami damar yin haka. Amma suna gani cewa an yaudare ni, musamman ma ƙanwata Araceli.
Araceli: Na tsani addinina saboda yadda aka wulaƙanta ni a gidan zuhudu. Amma hakan bai hana ni zuwa coci ranar Lahadi ba, kuma ina addu’ar Rosary kullum. Har ila, ina son in san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Na yi addu’a Allah ya taimake ni. Sai Felisa ta soma bayyana min abin da ta koya. Tana farin ciki sosai game da abin da ta yi imani da shi, har hakan ya sa na ɗauka cewa ta haukace. Ban gaskata da abin da take gaya min ba.
Daga baya, na koma yin aiki a birnin Madrid kuma na yi aure. A cikin waɗannan shekarun, na lura cewa mutanen da ke zuwa coci ba sa bin koyarwar Yesu. Saboda haka, sai na daina zuwa coci. Na ƙi gaskatawa da “waliyai” da wutar jahannama, kuma na ƙi yarda cewa limami zai iya gafarta zunubai. Ƙari ga haka, na zubar da dukan siffofin addini da nake da su. Ban san ko abin da nake yi ya dace ba. Na soma baƙin ciki amma na ci gaba da yin addu’a ga Allah, cewa: “Ina son in san ka. Ka taimake ni!” Na tuna cewa Shaidun Jehobah sun sha zuwa gidanmu don su yi min wa’azi, amma ban taɓa sauraran su ba. Ban yarda da addini ba.
’Yar’uwata Lauri tana zama a Faransa a lokacin kuma Ramoni tana zama a Sifen. A wajen shekara ta
1980, Shaidun Jehobah suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Na tabbata cewa an yaudare su kamar Felisa kuma ba su san cewa ƙarya ne ake koya musu ba. Daga baya, ni da wata maƙwabciyata mai suna Angelines muka zama abokai na kud da kud. Ita ma Mashaidiyar Jehobah ce. Angelines da maigidanta sun sha gaya min cewa za su so su soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Sun san cewa ina son in san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa duk da cewa na yi watsi da addini. A ƙarshe, sai na amince amma na ce musu: “Zan yarda ku yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni idan har zan yi amfani da Littafi Mai Tsarki da nake da shi!” A lokacin, ina amfani da juyin Littafi Mai Tsarki na Nácar-Colunga.A ƘARSHE LITTAFI MAI TSARKI YA SHIRYA MU
Felisa: Sa’ad da na yi baftisma a shekara ta 1973, Shaidun Jehobah guda 70 ne suke Santander, babban birnin Cantabria. Muna tafiya mai nisa don mu yi wa’azin bishara a ɗarurruwan ƙauyuka da ke yankin. Saboda haka, muna zuwa wa’azi a waɗannan ƙauyukan da bas, daga baya mun yi amfani da ƙaramar mota.
Na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa a cikin waɗannan shekarun, kuma 11 daga cikinsu sun yi baftisma. Yawancin mutanen da nake nazari da su ‘yan Katolika ne. Ina bukata in bi su da haƙuri. Da yake na taɓa samun kai na a yanayinsu, burina shi ne in taimaka musu su san cewa abubuwan da suka yi imani da shi ba daidai ba ne. Na san cewa Littafi Mai Tsarki da ruhun Jehobah ne kawai za su iya canja ra’ayin mutum don ya fahimci gaskiya. (Ibraniyawa 4:12) Maigidana mai suna Bienvenido ɗan sanda ne, amma ya yi baftisma a shekara ta 1979, kuma kafin mahaifiyata ta mutu, an soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ita.
Araceli: Sa’ad da Shaidun Jehobah suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni, na yi shakkar su. Amma da shigewar lokaci, sai na soma yarda da su. Shaidun Jehobah ba sa koyar da Littafi Mai Tsarki kawai, amma suna yin rayuwar da ta jitu da ƙa’idodinsa. Na soma ba da gaskiya ga Jehobah da kuma Littafi Mai Tsarki kuma hakan ya sa ni farin ciki sosai. Wasu maƙwabtana sun lura da hakan kuma suka ce mini, “Araceli, ki ci gaba da bin wannan addinin!”
Na tuna na taɓa yin addu’a cewa: “Na gode maka Jehobah, don ba ka yi watsi da ni ba kuma ka ba ni dama sosai don in sami abin da nake nema, wato gaskiyar Littafi Mai Tsarki.” Na nemi gafara daga wurin Felisa, saboda baƙar magana da na yi mata a dā. Tun daga lokacin, mun daina gardama. A maimakon haka, muna jin daɗin tattaunawa game da Littafi Mai Tsarki. Na yi baftisma a shekara ta 1989, sa’ad da nake shekara 61.
Felisa: Yanzu, shekaruna 91 ne. Maigidana ya mutu, kuma ba ni da ƙarfi kamar dā. Amma har ila, ina karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. Ƙari ga haka, ina zuwa taro da kuma wa’azi a duk lokacin da zan iya yin hakan.
Araceli: Ina son yin wa’azi ga duk limamai da kuma mata masu zaman zuhudu da na haɗu da su, wataƙila don na yi zaman zuhudu a dā ne ya sa nake son yin hakan. Na ji daɗin tattaunawa da wasu daga cikin su, kuma da yawa daga cikin su sun karɓi littattafai da mujallu. Na tuna da wani limami da na yi masa wa’azi. Ya yarda da abin da na faɗa. Amma sai ya ce: “Yanzu na tsufa, ina zan je? Mene ne ‘yan cocina da iyalina za su ce?” Sai na ce: “Mene ne Allah zai ce? Sai ya gane cewa abin da na faɗa gaskiya ne kuma hakan ya ratsa zuciyarsa. Amma kamar dai yana tsoron yin canji don ya soma bauta wa Jehobah.
Ba zan taɓa manta da ranar da maigidana ya gaya min cewa yana so ya halarci taro tare da ni ba. Ya soma halartan taro sa’ad da yake shekara 80 kuma tun daga lokacin, bai fasa zuwa taro. An yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi kuma ya soma fita wa’azi. Na ji daɗin fita wa’azi tare da shi. Ya mutu watanni biyu kafin ranar da zai yi baftisma.
Felisa: Sa’ad da na soma bauta wa Jehobah, ƙannena mata sun yi gāba da ni. Amma daga baya su ma sun soma bauta wa Jehobah. Ina matuƙar godiya saboda wannan abin da ya faru da ni. Bayan haka, muna jin daɗin hira tare kuma mu riƙa tattaunawa game da Allahnmu, Jehobah da kuma Kalmarsa! A ƙarshe, dukanmu, muna bauta wa Jehobah. *
^ sakin layi na 29 Araceli tana da shekara 87, Felisa tana da shekara 91, Ramoni kuma shekara 83. Har yanzu suna bauta wa Jehobah da aminci. Lauri ta mutu a shekara ta 1990, ita ma ta kasance da aminci ga Jehobah.