Dattawa da Bayi Masu Hidima—Ku Bi Misalin Timoti
A SHEKARAR da ta shige, an naɗa dattawa da kuma bayi masu hidima da yawa a faɗin duniya. Idan kuna cikinsu, babu shakka, kuna farin ciki don wannan gatar da aka ba ku a bautarku ga Jehobah.
Wataƙila kun ɗan damu don wannan gatan da aka ba ku. Wani mai suna Jason da ya zama dattijo ya ce: “Na ji kamar aiki ya yi mini yawa sa’ad da aka naɗa ni dattijo.” A lokacin da Jehobah ya naɗa Musa da Irmiya, suna ganin ba su cancanci samun gatar nan ba. (Fit. 4:10; Irm. 1:6) Idan kuna jin hakan, ta yaya za ku daina damuwa, kuma ku samu ci gaba a hidimarku? Bari mu yi la’akari da misalin wani Kirista mai suna Timoti.—A. M. 16:1-3.
KU YI KOYI DA TIMOTI
A lokacin da manzo Bulus ya soma wa’azi a ƙasashen waje da Timoti, wataƙila Timoti ya kusan kai shekara ashirin ko ya ɗan ɗara hakan. Da yake Timoti matashi ne, wataƙila ya ji ba zai iya yin wannan hidimar ba, kuma ya ɗan yi jinkirin yin wasu ayyuka a hidimarsa. (1 Tim. 4:11, 12; 2 Tim. 1:1, 2, 7) Amma bayan wasu shekaru, Bulus ya gaya wa ikilisiyar da ke Filibi game da Timoti. Ya ce: “Ina sa zuciya cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika Timoti zuwa wurinku ba da daɗewa ba, . . . Ba ni da wani kamarsa.”—Filib. 2:19, 20.
Mene ne ya taimaka wa Timoti ya zama dattijon da mutane suke ƙauna? Bari mu yi la’akari da abubuwa shida da za mu iya koya daga Timoti.
1. Ya damu da mutane. Bulus ya gaya wa ’yan’uwan da ke Filibi cewa: “[Timoti] ya damu da ku sosai.” (Filib. 2:20) Hakika, Timoti ya damu da mutane sosai. Yana so ya taimaka musu su kusaci Jehobah, don haka ya yi iya ƙoƙarinsa don ya tallafa musu.
Bai kamata mu zama kamar direban da ya fi damuwa da kaiwa inda yake so ya je ba, maimakon ya ɗan tsaya ya ɗauki fasinjoji a hanya kuma ya nuna cewa ya damu da su. Wani ɗan’uwa mai suna William da ya zama dattijo fiye da shekaru 20, ya ba wasu ’yan’uwa da aka naɗa ba da daɗewa ba wannan shawarar: “Ku riƙa ƙaunar ’yan’uwa kuma ku damu da zaman lafiyarsu fiye da yadda ake tafiyar da abubuwa a ikilisiya.”
2. Yin wa’azi ya fi muhimmanci a gare shi. Bulus ya nuna bambanci tsakanin Timoti da kuma wasu. Ya ce: “Sauran dai, abin da ya shafi kansu ne kawai sun damu da shi, ba abin da ya shafi Yesu Almasihu ba.” (Filib. 2:21) Bulus ya lura cewa ’yan’uwan da ke Roma, wurin da yake sa’ad da yake rubuta wannan wasiƙar sun fi damuwa da biyan bukatunsu. Ban da haka, ba su da ƙwazo a hidimarsu. Amma Timoti ba ya haka! A duk lokacin da ya sami damar yaɗa bishara, ya nuna irin halin Ishaya da ya ce: “Ga ni nan, ka aike ni!”—Isha. 6:8.
Ta yaya za ka tsara ayyukanka da kuma hidimarka da kyau? Da farko, ka zaɓi abin da ya fi muhimmanci. Bulus ya ce: Ku zaɓi “abin da ya fi kyau.” (Filib. 1:10) Ku sa hidimar Jehobah a kan gaba. Na biyu, ku sauƙaƙa rayuwarku. Ku guje wa abubuwan da suke ɗaukan lokaci kuma suke sa ku gaji ainun. Bulus ya umurci Timoti cewa: “Ka guje wa mugayen sha’awace-sha’awace na matasa, ka sa kai ga neman adalci, da bangaskiya, da ƙauna, da kuma salama.”—2 Tim. 2:22.
Filib. 2:22) Timoti ba mai ƙyuya ba ne. Ya yi aiki tare da Bulus da ƙwazo sosai kuma hakan ya sa sun ƙaunaci juna sosai.
3. Ya kasance da ƙwazo a hidimarsa. Bulus ya gaya wa Filibiyawa cewa: “Ai, kun san yadda Timoti yake, yadda muka yi aikin shelar labari mai daɗi tare kamar ɗa da babansa.” (A yau, aiki daɗa ƙaruwa yake yi a ƙungiyar Jehobah. Ban da haka, wannan aiki ne da yake sa mu sami gamsuwa kuma yana sa mu kusaci ’yan’uwanmu sosai. Don haka, bari ku yi iya ƙoƙarinku don “kullum kuna yalwata cikin aikin Ubangiji.”—1 Kor. 15:58.
4. Ya yi amfani da abin da ya koya. Bulus ya rubuta wa Timoti wasiƙa, ya ce: “Kai kam [ka] riga ka kiyaye koyarwata, da halina, da manufata ta rayuwa, da bangaskiyata, da haƙurina, da ƙaunata, da kuma jimrewata.” (2 Tim. 3:10) Da yake Timoti ya yi amfani da abubuwan da ya koya, hakan ya sa aka ba shi ƙarin aiki.—1 Kor. 4:17.
Kana da abokin da ya manyanta da za ka iya yin koyi da shi? Idan ba ka da shi, zai dace ka samu. Wani ɗan’uwa mai suna Tom da ya yi shekaru da yawa yana hidima a matsayin dattijo, ya ce: “Wani dattijon da ya manyanta ne ya taimaka mini kuma ya horar da ni. Nakan nemi shawara daga wurinsa kuma ina yin abin da ya faɗa. Hakan ya taimaka mini in san yadda zan iya yin aikin da aka ba ni.”
5. Ya ci gaba da horar da kansa. Bulus ya umurci Timoti cewa: Ka “horar da kanka cikin hali irin na Allah.” (1 Tim. 4:7) Alal misali, ko da yake kowane ɗan wasa yana da koci, amma duk da haka, yana bukatar ya riƙa horar da kansa. Shi ya sa Bulus ya umurci Timoti cewa: “Ka ci gaba da karanta Rubutacciyar Maganar Allah wa jama’a, da yin wa’azi, da kuma yin koyarwa. . . . Ka aikata waɗannan abubuwan cikin aikinka, ka miƙa kanka gaba ɗaya gare su, domin kowa ya ga ci gabanka.”—1 Tim. 4:13-15.
Kuna bukatar ku ci gaba da inganta yadda kuke yin aikin da aka ba ku. Kada ku bar dangantakarku da Jehobah ta yi tsami. Maimakon haka, ku riƙa yin nazari sosai don ku san ja-gorancin da ƙungiyar Jehobah take bayarwa. Ƙari ga haka, ku guje wa halin na-san-kome, da kuma nuna cewa za ku iya yin kome ba tare da kun yi bincike sosai ba. Maimakon haka, ku bi misalin Timoti ‘ku lura sosai da kanku da kuma koyarwarku’—1 Tim. 4:16.
6. Ya nemi taimakon ruhun Jehobah. Bulus ya ba wa Timoti shawara game da hidimarsa cewa: “Ta wurin taimakon Ruhu Mai Tsarkin da yake zaune a cikinmu, ka kula da wannan koyarwa ta gaskiyar da aka ba ka amanarta.” (2 Tim. 1:14) Don Timoti ya mai da hankali ga hidimarsa, yana bukatar ya dogara ga ruhun Allah don ya taimaka masa.
Wani ɗan’uwa mai suna Donald da ya yi shekaru da yawa yana hidima a matsayin dattijo, ya ce: “Waɗanda aka naɗa dattawa ko bayi masu hidima suna bukatar su ɗauki dangantakarsu da Jehobah da muhimmanci sosai. Idan suka yi hakan, za su sami ‘ƙarin ƙarfi.’ Ban da haka ma, idan suka yi addu’a don neman taimakon ruhu mai tsarki, za su sami albarka sosai kuma ’yan’uwa za su amfana daga wurinsu.”—Zab. 84:7; 1 Bit. 4:11.
KU DARAJA GATAR DA KUKE DA SHI
Abin ban ƙarfafa ne sosai cewa ’yan’uwa da yawa suna samun ci gaba a hidimarsu ga Jehobah kamar yadda kuke yi. Jason wanda aka ambata ɗazu ya ce: “Shekarun da na yi ina yin hidimar dattijo ya sa na koyi abubuwa da yawa, kuma na ƙara kasancewa da gaba gaɗi. Yanzu ina jin daɗin hidimata kuma gata ce babba!”
Idan kana so ka ci gaba da inganta hidimarka ga Jehobah, zai dace ka yi iya ƙoƙarinka don ka bi misalin Timoti. Idan ka yi hakan, ’yan’uwa za su amfana sosai.