Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mu “Kara” Kwazo Wajen Karfafa Juna

Mu “Kara” Kwazo Wajen Karfafa Juna

“Mu lura da juna . . . , mu dinga ƙarfafa juna, mu kuma ƙara yin haka yayin da kuke ganin cewa Ranar nan tana matsowa kusa.”​—IBRAN. 10:​24, 25.

WAƘOƘI: 90, 87

1. Me ya sa manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci Ibraniyawa cewa su “ƙara” ƙwazo wajen ƙarfafa juna?

ME YA sa muke bukatar mu ƙara ƙwazo wajen ƙarfafa mutane? Manzo Bulus ya faɗi dalilin a wasiƙar da ya rubuta wa Kiristoci Ibraniyawa. Ya ce musu: ‘Mu lura da juna ta yadda za mu iza juna ga nuna ƙauna da yin aikin nagarta. Kada mu bar yin taron sujada, kamar yadda waɗansu sun saba yi. A maimakon haka mu dinga ƙarfafa juna, mu kuma ƙara yin haka yayin da kuke ganin cewa Ranar nan tana matsowa kusa.’ (Ibran. 10:​24, 25) Bulus ya yi wannan furucin domin shekara biyar ce ta rage kafin “ranar” Jehobah ta zo a lokacin. Kiristocin da ke Urushalima za su ga alamun da Yesu ya faɗa cewa idan sun gani, su gudu daga birnin. (A. M. 2:​19, 20; Luk. 21:​20-22) Wannan “ranar” Jehobah ta zo a shekara ta 70 sa’ad da Romawa suka zartar da hukuncin Jehobah a kan Urushalima da mazaunanta.

2. Me ya sa muke bukatar mu riƙa ƙarfafa juna?

2 A yau, akwai alamu da yawa da suka nuna cewa “rana . . .  mai ba da tsoro sosai” na Jehobah ta kusa. (Yow. 2:11) Annabi Zafaniya ya ce: “Babbar Ranar Yahweh ta yi kusa, ta yi kurkusa, tana zuwa da sauri.” (Zaf. 1:14) Wannan gargaɗin ya shafe mu ma a yau. Da yake ranar Jehobah ta yi kusa sosai, Bulus ya ce mu “lura da juna ta yadda za mu iza juna ga nuna ƙauna da yin aikin nagarta.” (Ibran. 10:24) Saboda haka, muna bukatar mu riƙa lura da ’yan’uwanmu sosai don mu sami damar ƙarfafa su idan da bukata.

SU WAYE NE SUKE BUKATAR ƘARFAFA?

3. Mene ne manzo Bulus ya faɗa game da ƙarfafa? (Ka duba hoton da ke shafi na 20.)

3 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Damuwa a zuciya takan hana mutum sakewa, amma kalmar ƙarfafawa takan faranta rai.” (K. Mag. 12:25) Dukanmu a yau muna bukatar ƙarfafa a wasu lokuta. Manzo Bulus ya nuna cewa har mutanen da ke da hakkin ƙarfafa wasu suna bukatar ƙarfafa. Ya gaya wa Kiristocin da ke ƙasar Roma cewa: “Ina marmarin in gan ku domin in ba ku wata kyauta ta ruhu wadda za ta ƙarfafa ku. Nufina shi ne, ni da ku mu ƙarfafa juna, wato in ƙarfafa ku da bangaskiyata, ku kuma ku ƙarfafa ni da taku.” (Rom. 1:​11, 12) Babu shakka, manzo Bulus da ke ƙarfafa mutane sosai, ya bukaci ƙarfafa a wasu lokuta.​—Karanta Romawa 15:​30-32.

4, 5. Su waye ne za mu iya ƙarfafawa a yau, kuma me ya sa?

4 A yau, ’yan’uwa maza da mata da suke yin sadaukarwa suna bukatar a yaba musu. Wasu cikinsu su ne majagaba masu aminci. Da yawa daga cikinsu sun yi sadaukarwa sosai don su yi wannan hidimar. Haka ma yake da masu wa’azi a ƙasashen waje da masu hidima a Bethel da masu kula da da’ira da matansu, da masu hidima a ofisoshin fassara. Dukansu suna yin sadaukarwa sosai don su yi hidimar Jehobah. Saboda haka, muna bukatar mu riƙa ƙarfafa su. Ya kamata mu riƙa ƙarfafa dukan ’yan’uwan da suka so su ci gaba da hidimar majagaba, amma yanayinsu bai ƙyale su ba.

5 Ƙari ga haka, akwai ’yan’uwa da yawa da ba su yi aure ba domin suna so su bi shawarar nan da ta ce mu auri “mai bin Ubangiji.” (1 Kor. 7:39) Hakazalika, matan aure masu ƙwazo suna farin ciki sosai idan maigidansu ya yaba musu. (K. Mag. 31:​28, 31) Bugu da ƙari, Kiristocin da suka jimre sa’ad da ake tsananta musu ko sa’ad da suke ciwo, suna bukatar ƙarfafa. (2 Tas. 1:​3-5) Jehobah da kuma Yesu suna ƙarfafa dukan waɗannan ’yan’uwa masu aminci.​—Karanta 2 Tasalonikawa 2:​16, 17.

DATTAWA SUNA ƘARFAFA MU

6. Wane aiki ne dattawan da aka ambata a Ishaya 32:​1, 2 suke yi?

6 Karanta Ishaya 32:​1, 2Muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe kuma muna yawan yin sanyin gwiwa. Saboda haka, Yesu Kristi ya naɗa dattawa shafaffu, da waɗanda su waɗansu tumaki ne da Littafi Mai Tsarki ya kira “shugabanni.” Yana yin amfani da su wajen ƙarfafa mu da kuma yi mana ja-goranci. Dattawan nan ba sa nuna ‘iko a kan bangaskiyar’ ’yan’uwa a ikilisiya, amma suna “aiki ne tare” da su don su yi farin ciki.​—2 Kor. 1:24.

7, 8. Ta yaya dattawa za su iya ƙarfafa wasu da furucinsu da kuma ayyukansu?

7 Manzo Bulus ya kafa wa dattawa misali mai kyau. Ya rubuta wa Kiristocin da ake tsananta musu a Tasalonika cewa: “Muna ƙaunarku ƙwarai, shi ya sa muka ji daɗin yi muku wa’azin labari mai daɗi na Allah, ba wa’azi kaɗai ba, amma mun ji daɗin ba da rayukanmu saboda kun shiga ranmu sosai.”​—1 Tas. 2:8.

8 Bai kamata dattawa su riƙa ƙarfafa mutane da baƙi kawai ba. Bulus ya gaya wa dattawa a Afisa cewa: “Dole ku yi aiki haka don mu taimaka wa marasa ƙarfi. Kuna tuna kuma da kalmar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Ya fi albarka a bayar da a karɓa.’” (A. M. 20:35) Bulus yana a shirye ya ‘kashe duk abin da yake da shi’ don ya ƙarfafa ’yan’uwansa. (2 Kor. 12:15) Hakazalika, ya kamata dattawa su riƙa ƙarfafa da kuma ta’azantar da wasu da furucinsu da kuma ayyukansu. Hakan yana nuna cewa suna kula da mu sosai.​—1 Kor. 14:3.

9. Ta yaya dattawa za su iya yin gargaɗi yadda ya dace?

9 A wasu lokuta, ƙarfafa wasu yana bukatar yi musu gargaɗi. Amma dattawa za su iya koyan yadda za su yi hakan cikin ƙauna daga Littafi Mai Tsarki. Bayan Yesu ya tashi daga mutuwa, ya kafa misali mai kyau a wannan batun. Ya yi wa wasu ikilisiyoyi a Asiya Ƙarama gargaɗi sosai, amma ka lura yadda ya yi hakan. Yesu ya fara yaba wa ikilisiyoyin da ke Afisa da Birgamum da kuma Tiyatira, kafin ya yi musu gargaɗi. (R. Yar. 2:​1-5, 12, 13, 18, 19) Ya gaya wa ikilisiyar da ke Lawudikiya cewa: “Nakan tsawata in kuma hori waɗanda nake ƙauna. Saboda haka sai ka yi ƙwazo ka kuma tuba.” (R. Yar. 3:19) Zai dace dattawa su yi koyi da misalin Yesu sa’ad da suke yi wa wani gargaɗi.

WASU MA ZA SU IYA BA DA ƘARFAFA

Iyaye, ku koya wa yaranku su riƙa ƙarfafa wasu (Ka duba sakin layi na 10)

10. Ta yaya dukanmu za mu iya ƙarfafa juna?

10 Ba dattawa kaɗai ba ne suke da hakkin ƙarfafa wasu ba. Bulus ya gaya wa dukan Kiristoci cewa furucinsu ya zama mai ‘amfani domin ƙarfafawar juna bisa ga bukatarsu. Ta hakan maganarsu za ta zama da amfani ga’ wasu. (Afis. 4:29) Ya kamata dukanmu mu riƙa lura don mu san ‘bukatun’ wasu. Bulus ya gargaɗi Kiristoci Ibraniyawa cewa: ‘Ku miƙe hannuwan da suka gaji, ku kuma ƙarfafa gwiwoyin marasa ƙarfi. Ku miƙe hanyoyi domin ƙafafunku, domin kada mai ciwon ƙafa ya sami damuwa, maimakon warkewa.’ (Ibran. 12:​12, 13) Dukanmu har da matasa za mu iya ƙarfafa wasu da furucinmu.

11. Ta yaya aka ƙarfafa Marthe sa’ad da take baƙin ciki?

11 Wata ’yar’uwa mai suna Marthe * ta taɓa samun kanta tana baƙin ciki sosai. Ta ce: “Wata rana da na yi addu’a don neman ƙarfafa, sai wata ’yar’uwa da ta tsufa ta nuna mini ta damu da ni kuma tana ƙauna ta. Abin da nake bukata a lokacin ke nan. Ban da haka ma, ta gaya mini cewa ta taɓa fuskantar irin matsalar da nake ciki. Hakan ya sa in san cewa wasu suna fuskantar irin matsala ta.” Wataƙila wannan ’yar’uwa ba ta san cewa abin da ta faɗa ya ƙarfafa Marthe sosai ba.

12, 13. Ta yaya za mu bi shawarar da ke Filibiyawa 2:​1-4?

12 Bulus ya ba ’yan’uwan da ke ikilisiyar Filibi wannan shawarar. Ya ce: “Kuna samun ƙarfafawa saboda ku na Almasihu ne? Ko kuna samun ta’aziyya ta wurin ƙaunarsa? Ko kuna da zumunci cikin ruhu? Ko kuma kuna da ƙauna da tausayi a zuciyarku? To, in kuna da waɗannan, ina roƙonku ku sa farin cikina ya cika ta wurin kasancewarku da tunani ɗaya, da ƙauna ɗaya, da nufi ɗaya. Kada ku yi kome da son kai ko girman kai, sai dai da sauƙin kai. Amma cikin sauƙin kai kuma bari kowa ya ɗauka ɗan’uwansa da muhimmanci fiye da kansa. Kada ku kula da kanku kaɗai, amma ku kula da waɗansu kuma.”​—Filib. 2:​1-4.

13 Babu shakka, dukanmu muna bukatar mu riƙa taimaka wa juna. Ta yaya za mu iya yin hakan? Ta wajen ‘ta’azantar’ da juna da kasancewa da “zumunci cikin ruhu” da kuma nuna “ƙauna da tausayi.” Idan muna yin hakan, za mu ƙarfafa ’yan’uwanmu.

HANYOYIN ƘARFAFA MUTANE

14. A wace hanya ce za mu iya ƙarfafa mutum?

14 Kamar manzo Yohanna, muna farin ciki sosai idan muka ji cewa mutanen da muka taimaka musu a dā suna bauta wa Jehobah. Manzon ya ce: “Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna bin gaskiya.” (3 Yoh. 4) Majagaba da yawa suna farin ciki sa’ad da suka ji cewa mutanen da suka yi nazari da su shekaru da yawa da suka shige, suna bauta wa Jehobah da aminci, wataƙila ma suna hidimar majagaba. Don haka, idan wani majagaba yana baƙin ciki, muna iya tuna masa yadda ya taimaka wa mutane su san Jehobah.

15. A wace hanya ce za mu iya ƙarfafa waɗanda suke yin hidima da aminci?

15 Masu kula da da’ira da yawa da matansu, suna yawan cewa saƙon godiya da aka turo musu don ziyarar da suka kai wa ikilisiya yana ƙarfafa su. Hakazalika, dattawa da masu wa’azi a ƙasashen waje da masu hidima a Bethel, suna samun ƙarfafa idan aka yaba musu don hidimar da suke yi da aminci duk da ƙalubale.

DUKANMU ZA MU IYA BA DA ƘARFAFA

16. Me za mu iya yi don mu ƙarfafa wani?

16 Ba zai dace mu yi tunani cewa ba za mu iya ƙarfafa wasu ba, domin mu ba masu yawan magana ba ne. Ƙarfafa mutane ba abu mai wuya ba ne. Yin murmushi sa’ad da muke gaisuwa zai iya ƙarfafa mutum. Idan muka yi wa wani murmushi amma ya ƙi yin murmushi, wataƙila yana cikin wata damuwa ne. Idan muka saurare shi sosai sa’ad da yake magana, hakan zai iya ƙarfafa mutumin.​—Yaƙ. 1:19.

17. Ta yaya wani matashi ya sami ƙarfafa sa’ad da yake baƙin ciki?

17 Wani matashi mai suna Henri ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da danginsa, har ma da mahaifinsa wanda dattijo ne suka daina bauta wa Jehobah. Wani mai kula da da’ira ya lura da hakan kuma ya fita da Henri shan shayi. Abin da ya yi ya sa Henri ya faɗi yadda yake ji. Henri ya fahimci cewa idan yana so ya taimaka wa iyalinsa su komo ga Jehobah, yana bukatar ya ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci. Ƙari ga haka, karanta littafin Zabura 46; Zafaniya 3:17; da kuma Markus 10:​29, 30, sun ƙarfafa shi sosai.

Dukanmu za mu iya ƙarfafa juna (Ka duba sakin layi na 18)

18. (a) Mene ne Sarki Sulemanu ya ce? (b) Wace shawara ce manzo Bulus ya bayar?

18 Mene ne za mu iya koya daga misalin Marthe da Henri? Dukanmu za mu iya ƙarfafa wasu. Sarki Sulemanu ya ce: “Abu mai kyau ne magana ta fita a daidai lokaci. Murmushi yana sa mutum ya yi murna, labari mai daɗi yakan kawo lafiyar jiki.” (K. Mag. 15:​23, 30) Ƙari ga haka, karanta Hasumiyar Tsaro ko kuma wasu talifofi a dandalinmu yana iya ƙarfafa mutumin da ke baƙin ciki. Ban da haka, Bulus ya nuna cewa rera waƙoƙinmu tare da mai baƙin ciki zai iya ƙarfafa shi. Bulus ya ce: “Kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, kuna rera waƙoƙin zabura da na yabon Allah, kuna rera waƙoƙin da Ruhu ya kirkiro, kuna rerawa da godiya a zuciyarku.”​—Kol. 3:16; A. M. 16:25.

19. Me ya sa ƙarfafa mutane zai zama da muhimmanci sosai nan ba da daɗewa ba, kuma me za mu yi?

19 Yanzu da ranar Jehobah take “matsowa kusa,” yana da muhimmanci mu riƙa ƙarfafa juna. (Ibran. 10:25) Bulus ya gaya wa Kiristoci a zamaninsa cewa su ci gaba da ‘ƙarfafa juna, su yi ta gina juna, kamar dai yadda suke yi yanzu.’ Ya kamata mu ma mu bi wannan shawarar.​—1 Tas. 5:11.

^ sakin layi na 11 An canja sunayen.