Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 50

Ta Yaya Za A Ta da Matattu?

Ta Yaya Za A Ta da Matattu?

“Ke, mutuwa, ina nasararki? Ke, mutuwa, ina dafinki?”​—1 KOR. 15:55.

WAƘA TA 141 Rai, Kyauta Ce Daga Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Me ya sa ya kamata dukan Kiristoci su sani game da tashin matattu zuwa sama da za a yi?

YAWANCIN mutanen da ke bauta wa Jehobah a yau suna da begen yin rayuwa har abada a duniya. Za a ta da shafaffu da suka rage a duniya zuwa sama. Waɗannan shafaffun suna so su san yadda rayuwa a sama a nan gaba za ta kasance. Me ya sa waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya ma suke bukatar su san abin da zai faru a sama? Kamar yadda za mu gani, tashin matattu da za a yi zuwa sama zai sa waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya su sami albarka. Saboda haka, ko da muna da begen yin rayuwa a sama ko a duniya, ya kamata mu so sanin yadda za a ta da matattu zuwa sama.

2 Allah ya hure wasu cikin almajiran Yesu a ƙarni na farko su rubuta abubuwa game da tashin matattu zuwa sama. Manzo Yohanna ya ce: “Yanzu mu ʼya’yan Allah ne. Ba a bayyana mana abin da za mu zama nan gaba ba tukuna. Amma mun sani cewa in Almasihu ya bayyana, za mu zama kamarsa.” (1 Yoh. 3:2) Saboda haka, shafaffun Kiristoci ba su san irin rayuwar da za su yi ba a lokacin da aka ta da su zuwa sama da jiki na ruhu. Amma za su ga Jehobah sa’ad da aka ba su ladarsu. Littafi Mai Tsarki bai bayyana dukan abin da zai faru sa’ad da aka ta da shafaffu zuwa sama ba, amma manzo Bulus ya ba da ɗan ƙarin haske game da abin da zai faru. Shafaffu za su kasance tare da Yesu sa’ad da ya “kawar da dukan masu mulki, da mulki, da iko.” Wannan ya ƙunshi “abokiyar gāba ta ƙarshe,” wato “mutuwa.” A ƙarshe, Yesu da abokan sarautarsa za su miƙa kansu da kuma kome-da-kome ga Jehobah. (1 Kor. 15:​24-28) Wannan zai zama lokaci mai ban al’ajabi! *

3. Kamar yadda 1 Korintiyawa 15:​30-32 suka nuna, mene ne begen tashin matattu da Bulus yake da shi ya taimaka masa ya yi?

3 Begen tashin matattu da Bulus yake da shi ya taimaka masa ya jimre matsaloli. (Karanta 1 Korintiyawa 15:​30-32.) Ya gaya wa Kiristocin da ke Korinti cewa: “Ina [fuskantar] mutuwa kullum.” Ya ƙara cewa: “Na yi kokawa da namomin daji a Afisa.” Wataƙila yana nufin yadda ya yi faɗa da namomin daji a babban filin wasan Afisa. (2 Kor. 1:8; 4:10; 11:23) Ko kuma wataƙila yana magana ne game da Yahudawa da wasu mutane masu halaye kamar “namomin daji.” (A. M. 19:​26-34; 1 Kor. 16:9) Ko da mene ne ya faru, Bulus ya fuskanci matsaloli sosai. Duk da haka, ya ci gaba da kasancewa da ra’ayi mai kyau game da nan gaba.​—2 Kor. 4:​16-18.

Wata iyali da ke zama a ƙasar da aka saka wa aikinmu takunkumi, sun ci gaba da bauta wa Jehobah cike da imani cewa zai taimaka musu (Ka duba sakin layi na 4)

4. Ta yaya begen tashin matattu zai ƙarfafa Kiristoci a yau? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

4 Muna rayuwa a mawuyacin lokaci. Wasu ’yan’uwanmu sun fuskanci zalunci. Wasu kuma suna zama a wuraren da ake yaƙi kuma babu kāriya. A wasu wurare, an saka wa aikinmu taƙunƙumi, kuma duk da cewa za a iya saka bayin Jehobah a kurkuku, sun ci gaba da bauta masa. ’Yan’uwan nan sun kafa misali mai kyau da ya kamata mu yi koyi da shi. Ba sa jin tsoro domin sun san cewa idan sun mutu, Jehobah zai sa su yi rayuwa mafi kyau a nan gaba.

5. Wane ra’ayi da bai dace ba ne zai iya raunana bangaskiyarmu?

5 Bulus ya gaya wa ’yan’uwansa su guji ra’ayin da bai dace ba da wasu suke da shi. Ya ce: “Idan dai har ba za a tā da matattu ba, ‘Ba sai mu yi ta ci da sha ba, tun da gobe za mu mutu?’ ” Wasu mutane suna da wannan ra’ayin a zamanin Bulus. Wataƙila Bulus ya yi ƙaulin Ishaya 22:13 da ya yi magana game da halin Isra’ilawa. Maimakon su kusaci Allah, sun fi mai da hankali ga jin daɗin rayuwa. A taƙaice dai Isra’ilawa suna ganin cewa zai fi dacewa su ji daɗin rayuwa domin gobe za su iya mutuwa. Mutane da yawa a yau suna da wannan ra’ayin. Littafi Mai Tsarki ya bayyana sakamakon da Isra’ilawa suka samu domin suna da wannan ra’ayin da bai dace ba.​—2 Tar. 36:​15-20.

6. Ta yaya begen tashin matattu zai taimaka mana mu zaɓi abokan kirki?

6 Ya kamata sanin cewa Jehobah zai ta da matattu ya shafi irin mutanen da muke abokantaka da su. Kiristocin da ke Korinti sun bukaci guje wa yin abokantaka da mutanen da ba su amince da tashin matattu ba. A yau, muna iya koyan darasi daga abin da suka yi: Idan kana yawan tarayya da mutanen da suka fi sa jin daɗin rayuwa a gaba, za su ɓata halinka mai kyau. Hakan yana iya sa ka soma yin abubuwan da Allah ba ya so. Saboda haka, Bulus ya yi gargaɗi cewa: “Ku dawo cikin tunani mai kyau, ku daina yin zunubi. Gama waɗansunku ba su san Allah ba. Na faɗa wannan ne domin ku ji kunya.”​—1 Kor. 15:​33, 34.

DA WANE IRIN JIKI NE ZA A TA DA SU?

7. Kamar yadda 1 Korintiyawa 15:​35-38 suka nuna, wace tambaya ce wataƙila wasu suka yi game da tashin matattu?

7 Karanta 1 Korintiyawa 15:​35-38. Wani da ke so ya sa mutane su yi shakkar tashin matattu zai iya cewa: “Ta yaya za a ta da matattu?” Zai dace mu yi tunani a kan amsar da Bulus ya ba da, domin a yau mutane da yawa suna da ra’ayi dabam-dabam game da abin da zai faru da mutum idan ya mutu. Amma mene ne Littafi Mai Tsarki ya koyar?

Bulus ya yi amfani da shuki don ya bayyana cewa Allah zai iya ba waɗanda aka ta da su daga matattu jikin da ya dace (Ka duba sakin layi na 8)

8. Wane kwatanci ne zai iya taimaka mana mu fahimci tashin matattu zuwa sama da za a yi?

8 Sa’ad da mutum ya mutu, jikinsa yana ruɓewa. Amma Allah da ya halicci sama da duniya zai iya ta da mutum daga matattu kuma ya ba shi irin jikin da ya dace da shi. (Far. 1:1; 2:7) Bulus ya yi amfani da kwatancin da ya nuna cewa Allah ba ya bukatar ya mai da wa mutum jikin da yake da shi a dā. Ka yi tunanin iri da aka shuka. Irin zai iya tsira ya soma girma. Kuma tsiron zai bambanta da hatsin da aka shuka. Bulus ya yi amfani da wannan kwatancin don ya nuna cewa Mahaliccinmu zai iya ba mutum “jiki yadda ya nufa.”

9. Wane ire-iren jiki ne 1 Korintiyawa 15:​39-41 suka ambata?

9 Karanta 1 Korintiyawa 15:​39-41. Bulus ya ambata cewa Jehobah ya halicci jiki iri-iri. Alal misali, jikin shanu da tsuntsaye da kuma kifaye sun bambanta. Ya ce muna ganin bambancin da ke tsakanin rana da taurari. Kuma ya daɗa cewa “wani tauraro yakan zama dabam da wani wajen ɗaukaka.” Ko da yake ba za mu iya ganin wannan bambanci da ido ba, ’yan kimiyya sun ce akwai ire-iren taurari. Wasu manya ne, wasu ƙanana, wasu farare, wasu jajaye, wasu kuma suna da launin ruwan ɗorawa, kamar rana. Bulus ya daɗa cewa “akwai halitta irin ta sama, akwai kuma irin ta ƙasa.” Mene ne Bulus yake nufi? Halittun da ke duniya suna da jiki na nama da jini, amma na sama kuma jiki na ruhu kamar mala’iku.

10. Wane irin jiki ne waɗanda aka ta da zuwa sama za su samu?

10 Ka yi la’akari da abin da Bulus ya sake faɗa, ya ce: “Haka kuma yake game da tashin matattu. Abin da aka shuka yana da halin ruɓa, abin da aka tā da shi kuma ba shi da halin ruɓa.” Mun san cewa idan mutum ya mutu, jikinsa zai ruɓe kuma ya zama ƙurar ƙasa. (Far. 3:19) Ta yaya za a ta da mutum ba a “halin ruɓa” ba? Bulus ba ya nufin mutanen da Iliya da Elisha da kuma Yesu suka ta da a nan duniya ba. Yana magana ne game da mutumin da aka ta da shi da jikin yin rayuwa a sama wato “jiki na ruhu.”​—1 Kor. 15:​42-44.

11-12. Mene ne ya faru da Yesu sa’ad da aka ta da shi, kuma mene ne zai faru da shafaffu idan an ta da su?

11 A lokacin da Yesu yake duniya, yana da jikin ’yan Adam. Amma sa’ad da aka ta da shi, ya zama ‘ruhu mai ba da rai’ kuma ya koma sama. Hakazalika, za a ta da shafaffu da jiki na ruhu. Bulus ya bayyana cewa: “Kamar yadda muka ɗauki kamanni na ƙurar nan, haka kuma za mu ɗauki kamanni na mutumin saman nan.”​—1 Kor. 15:​45-49.

12 Da Bulus yake kammala tattaunawa game da yadda za a ta da matattu, ya faɗi cewa ba a ta da Yesu da jikin ɗan Adam ba. Bulus ya ce: “Ba zai yiwu jikinmu na nama da jini ya sami gādo a mulkin Allah” a sama ba. (1 Kor. 15:50) Ba za a ta da manzanni da shafaffu zuwa sama da jiki na ’yan Adam da zai iya ruɓa ba. A wane lokaci ne za a ta da su? Bulus ya ce za a yi hakan a nan gaba, ba nan da nan bayan sun mutu ba. A lokacin da Bulus ya rubuta littafin Korintiyawa na ɗaya, wasu mabiyan Yesu kamar su manzo Yaƙub, sun riga “sun yi barci,” wato sun mutu. (A. M. 12:​1, 2) Bayan haka, sauran manzannin da kuma wasu shafaffu ma sun mutu.​—1 Kor. 15:6.

ZA A KAWAR DA MUTUWA

13. Mene ne zai faru a lokacin bayyanuwar Yesu?

13 Yesu da manzo Bulus sun yi annabci game da wani lokaci mai muhimmanci wato bayyanuwar Kristi. A lokacin, za a riƙa yin yaƙe-yaƙe da girgizar ƙasa da cututtuka kuma wasu mutane za su riƙa yin mugayen ayyuka a duniya. Muna ganin cikar wannan annabcin tun daga shekara ta 1914. Akwai wani sashe mafi muhimmanci na wannan annabcin da zai cika. Yesu ya ce za a yi shela ga dukan al’umma cewa Mulkin Allah yana sarauta ‘sa’an nan ƙarshen [zai] zo.’ (Mat. 24:​3, 7-14) Bulus ya ce a lokacin bayyanuwar Yesu, za a ta da Kiristoci shafaffu “waɗanda suka mutu.”​—1 Tas. 4:​14-16; 1 Kor. 15:23.

14. Mene ne zai faru da shafaffu da suka mutu a lokacin bayyanuwar Kristi?

14 A yau, ana ta da shafaffun da suka mutu nan da nan zuwa sama. Abin da Bulus ya faɗa a 1 Korintiyawa 15:​51, 52, ya tabbatar da hakan. Ya ce: “Ba dukanmu ne za mu mutu ba, amma dukanmu za a canja kamanninmu, farat ɗaya, da ƙyiftawar ido, da jin ƙarar ƙaho na ƙarshe.” Wannan furucin Bulus yana cika yanzu! Bayan an ta da shafaffu, za su yi farin ciki sosai kuma za su “kasance tare da Ubangiji har abada.”​—1 Tas. 4:17.

Waɗanda za a ta da su “farat ɗaya, da ƙyiftawar ido” za su yaƙi mugaye tare da Yesu (Ka duba sakin layi na 15)

15. Wane aiki ne waɗanda za a ta da su “farat ɗaya, da ƙyiftawar ido” za su yi?

15 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana aikin da waɗanda za a ta da su “farat ɗaya, da ƙyiftawar ido” za su yi a sama. Yesu ya gaya musu cewa: “Duka wanda ya ci nasara, ya kuma ci gaba da yin abin da nake so har ƙarshe, zan ba shi iko ya yi mulki a kan al’ummai. Zai yi mulki a kansu da sandan ƙarfe, zai farfashe su kamar tukwanen laka.” (R. Yar. 2:​26, 27) Su da shugabansu Yesu Kristi za su yi mulki a kan al’ummai da sandan ƙarfe.​—R. Yar. 19:​11-15.

16. Ta yaya mutane da yawa za su yi nasara a kan mutuwa?

16 Babu shakka, shafaffu za su yi nasara a kan mutuwa. (1 Kor. 15:​54-57) Tashinsu da za a yi daga matattu zai sa su cire mugunta daga duniya a lokacin yaƙin Armageddon. Miliyoyin Kiristoci maza da mata za su “fito daga azabar nan mai zafi,” wato ƙunci mai girma kuma za su shiga sabuwar duniya. (R. Yar. 7:14) Waɗanda suka tsira za su ga sa’ad da aka ta da biliyoyin mutanen da suka rasu. Hakan zai zama babban nasara a kan mutuwa! (A. M. 24:15) Kuma dukan waɗanda suka kasance da aminci ga Jehobah za su yi nasara a kan mutuwar da muka gāda daga Adamu. Za su yi rayuwa har abada.

17. Kamar yadda 1 Korintiyawa 15:58 ta nuna, me muke bukatar mu yi yanzu?

17 Kowane Kirista da ke raye yana bukatar ya nuna godiya don wasiƙa mai ban ƙarfafa game da tashin matattu da Bulus ya tura wa ’yan’uwan da ke Korinti. Muna da dalilai da yawa da za su sa mu bi umurnin da Bulus ya ba da cewa mu yi iya ƙoƙarinmu a “aikin Ubangiji.” (Karanta 1 Korintiyawa 15:58.) Idan muna yin wannan aikin da zuciya ɗaya, za mu yi farin ciki a nan gaba. Za mu kasance a irin yanayin da ba mu taɓa shaida ba a rayuwarmu. Wannan zai tabbatar mana da cewa hidimar da muka yi ba a banza ba ne.

WAƘA TA 140 Za Mu Yi Rayuwa Har Abada!

^ sakin layi na 5 Sashe na biyu na littafin Korintiyawa na 1 sura 15 yana ɗauke da bayanai game da yadda za a ta da matattu, musamman ma shafaffun Kiristoci. Amma abin da Bulus ya rubuta yana da muhimmanci ga waɗansu tumaki. Wannan talifi zai nuna yadda begen tashin matattu zai shafe mu yanzu da kuma yadda zai taimaka mana mu yi farin ciki a nan gaba.

^ sakin layi na 2 A “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke fitowar nan, an tattauna abin da Bulus ya faɗa a 1 Korintiyawa 15:29.