HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI fabrairu 2017

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 3-30 ga Afrilu, 2017.

Jehobah Zai Cika Nufinsa!

Me ya sa Allah ya halicci duniya da kuma mutane? Ta yaya abubuwa suka lalace haka? Me ya sa fansar da Yesu ya yi ne zai iya sa a cika nufin Allah game da duniya?

Fansa “Cikakkiyar Kyauta” Ce Daga Jehobah

Wannan tanadin da Allah ya yi zai sa mutane su sami albarka kuma su fahimci wasu batutuwa masu muhimmanci.

TARIHI

Allah Ya Yi Mana Alheri Sosai

Allah ya yi wa Douglas da Mary Guest alheri, sun yi hidimar majagaba a Kanada da kuma Brazil da Portugal a matsayin masu wa’azi a kasar waje.

Jehobah Yana Ja-gorar Mutanensa

A dā Jehobah ya yi amfani da mutane don ya ja-goranci mutanensa. Wane tabbaci muke da shi cewa Jehobah ne ya mara musu baya?

Su Wa Suke Yi wa Mutanen Allah Ja-gora a Yau?

Yesu ya yi alkawari cewa zai kasance tare da almajiransa har karshen zamani. Ta yaya yake taimaka wa mutanen Allah a yau?

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Manzo Bulus ya rubuta cewa Jehobah “ba za ya bari a yi muku jarraba wadda ta fi karfinku ba.” Shin hakan yana nufin cewa Jehobah ya san jarrabar da za mu iya jimrewa bayan haka sai ya zaɓa wadda da za mu fuskanta?

DAGA TARIHINMU

“Ba Abin da Zai Iya Hana Mu Yin Wa’azi”

Kafin shekara ta 1929, majagaba masu kwazo sun shiga kauyukan Ostareliya suna wa’azi a birane da garuruwan kasar.