Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Manzo Bulus ya rubuta cewa Jehobah “ba za ya bari a yi muku jarraba wadda ta fi ƙarfinku ba.” (1 Kor. 10:13) Shin hakan yana nufin cewa Jehobah yana zaɓan jarrabar da za mu fuskanta bayan da ya duba ya gan wadda za mu iya jimrewa?
Ka yi la’akari da yadda irin wannan ra’ayin zai iya shafanmu. Alal misali, yaron wani ɗan’uwa ya kashe kansa kuma abin ya sa ɗan’uwan baƙin ciki sosai: Sai ya kama tunani ko Jehobah ya san cewa shi da matarsa za su iya jimrewa shi ya sa ya bar hakan ya faru. Shin zai dace ne mu gaskata cewa Jehobah ne yake ƙaddara dukan abubuwan da suke faruwa da mu?
Idan mun sake bincika abin da Bulus ya faɗa a littafin 1 Korintiyawa 10:
Da farko, Jehobah ya ba mu ‘yancin yin zaɓi. Yana so mu zaɓi tafarkin da za mu bi a rayuwa. (K. Sha. 30:
Na biyu, Jehobah ba ya kāre mu daga “sa’a, da tsautsayi.” (M. Wa. 9:
Na uku, dukanmu muna bukatar mu riƙe amincinmu ga Jehobah. Shaiɗan ya ce ‘yan Adam suna bauta wa Jehobah ne saboda abin da yake ba su. Ƙari ga haka, ya yi da’awa cewa ba za mu kasance da aminci ba idan muna fuskantar jarraba. (Ayu. 1:
Na huɗu, Jehobah ba ya bukatar ya san kome da yake faruwa da mu ba. Babu shakka, idan Jehobah yana son ya san abin da zai faru a nan gaba, zai iya sani. (Isha. 46:10) Amma Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa ba kowane abin da ya faru ba ne Jehobah yake zaɓan ya sani kafin ya faru. (Far. 18:
Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce: “Allah . . . ba za ya bari a yi muku jarraba wadda ta fi ƙarfinku ba”? Abin da Bulus ya kwatanta shi ne abin da Allah yake yi sa’ad da mutum yake shan wahala ba kafin ya sha wahalar ba. * Kalaman Bulus sun tabbatar mana cewa ko da wane irin matsala muke fuskanta, Jehobah zai taimaka mana idan mun dogara gare shi. (Zab. 55:22) Wannan abu mai ban ƙarfafa da Bulus ya faɗa yana bayyana abubuwa guda biyu masu muhimmanci.
Na farko, jarraba da muke fuskanta irin wanda mutane suka saba fuskanta ne. Saboda haka, duk wata jarraba da ta same mu za mu iya jimrewa idan muka dogara ga Allah. (1 Bit. 5:
Na biyu, “Allah mai-aminci ne.” Yadda Allah ya bi da mutanensa ya nuna cewa yana ƙaunar “masu-ƙaunarsa da masu-kiyaye dokokinsa.” (K. Sha. 7:9) Kalmar Allah ta nuna cewa Allah yana cika alkawarinsa. (Josh. 23:14) Yadda Allah ya nuna aminci a dā ya tabbatar mana da cewa idan muna ƙaunarsa kuma muka yi masa biyayya, zai cika alkawarin da ya yi mana sa’ad da muke shan wahala. Ya ce: (1) Ba zai bar mu mu fuskanci jarraba wadda ta fi ƙarfinmu ba, na (2) ‘za ya yi mana hanyar tsira.’
Ta yaya Jehobah yake yi mana hanyar tsira ko taimaka mana sa’ad da muke fuskantar jarraba? Hakika, Allah zai iya kawar da jarrabar. Amma ka tuna da kalaman Bulus cewa: ‘[Jehobah] za ya yi muku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.’ A yawancin lokaci, yana mana “hanyar tsira” ta wurin tanadar mana da abin da muke bukata don mu iya jimre duk wata matsala da muke fuskanta. Bari mu tattauna wasu hanyoyin da Jehobah yake amfani da su don ya taimaka mana:
-
Yana “mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.” (2 Kor. 1:
3, 4) Jehobah zai iya kwantar mana da hankali ta wajen Kalmarsa da ruhu mai tsarki da kuma koyarwa Littafi Mai Tsarki da ke ƙarfafa bangaskiyarmu da bawan nan mai aminci yake tanadarwa. —Mat. 24:45; Yoh. 14:16; Rom. 15:4. -
Zai iya yi mana ja-gora ta ruhunsa mai tsarki. (Yoh. 14:26) Sa’ad da muke fuskantar matsaloli, ruhu mai tsarki zai iya taimaka mana mu tuna wasu labaran Littafi Mai Tsarki da kuma ƙa’idodin da za su taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau.
-
Zai iya yin amfani da mala’iku su ƙarfafa mu.
—Ibran. 1:14. -
Zai iya yin amfani da ‘yan’uwa da muke ibada tare, su ƙarfafa mu ta kalamansu da kuma ayyuka masu kyau kuma hakan zai “sanyaya mana zuciya.”
—Kol. 4: 11, LMT.
To, mene ne ma’anar furucin da Bulus ya yi a 1 Korintiyawa 10:13? Jehobah ba ya zaɓan jarraba da za mu fuskanta. Amma a lokacin da muke fuskantar jarraba muna da tabbaci cewa idan mun dogara gare shi sosai, ba zai bar jarrabar ta fi ƙarfinmu ba. Kuma a kullum yana mana hanyar tsira ko ya taimaka mana mu iya jimre duk wata matsala da muke fuskanta. Hakan abin ban ƙarfafa ne, ko ba haka ba?
^ sakin layi na 2 A Helenanci kalmar nan “jarraba” tana iya nufin “gwaji.”