TALIFIN NAZARI NA 9
Dokoki Game da Nuna Kauna da Adalci a Isra’ila ta Dā
“Yahweh yana son adalci da gaskiya, ƙaunarsa marar canjawa ta cika duniya.”—ZAB. 33:5.
WAƘA TA 3 Jehobah Ne Ƙarfinmu, Begenmu da Kuma Makiyayinmu
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1-2. (a) Mene ne dukanmu muke so? (b) Wane tabbaci ne muke bukatar mu kasance da shi?
DUKANMU muna so a riƙa nuna mana ƙauna kuma a yi mana adalci. Idan aka ƙi nuna mana ƙauna da adalci a kai a kai, hakan yana iya rage mutuncinmu kuma ya sa mu ji ba mu da bege.
2 Jehobah ya san cewa muna so a ƙaunace mu kuma a nuna mana adalci. (Zab. 33:5) Muna bukatar mu kasance da tabbaci cewa Allahnmu yana ƙaunar mu kuma yana so a riƙa nuna mana adalci. Muna iya ganin hakan idan muka bincika dokar da Jehobah ya ba al’ummar Isra’ila. Idan kana baƙin ciki domin mutane ba su nuna maka ƙauna da adalci ba, ka yi la’akari da yadda Dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa * ta nuna cewa Jehobah ya damu da mutanensa.
3. (a) Kamar yadda Romawa 13:8-10 ya nuna, me za mu koya idan muka yi nazarin Dokar Musa? (b) Waɗanne tambayoyi ne za a amsa a wannan talifin?
3 Idan muka yi nazarin Dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa, za mu ga cewa Jehobah yana ƙaunar mu sosai. (Karanta Romawa 13:8-10.) A wannan talifin, za mu tattauna kaɗan daga cikin dokokin da aka ba Isra’ilawa, kuma za mu amsa waɗannan tambayoyin: Me ya sa za mu iya cewa ƙauna ce ta sa aka ba da Dokar? Me ya sa muka ce Dokar ta ɗaukaka nuna adalci? Ta yaya aka bukaci waɗanda suke shugabanci su bi Dokar? Kuma su waye ne suka amfana daga Dokar? Amsoshin waɗannan tambayoyin za su ƙarfafa mu sosai kuma su sa mu kasance da bege. Ƙari ga haka, za su sa mu kusaci Jehobah Ubanmu mai ƙauna.—A. M. 17:27; Rom. 15:4.
ƘAUNA CE TA SA AKA KAFA DOKAR
4. (a) Me ya sa za mu iya cewa ƙauna ce ta sa aka ba da Dokar Musa? (b) Kamar yadda Matiyu 22:36-40 ya nuna, waɗanne dokoki ne Yesu ya ambata?
4 Muna iya cewa ƙauna ce ta sa Allah ya ba da Dokar, domin ita ce take motsa Jehobah ya yi dukan abubuwan da yake yi. (1 Yoh. 4:8) Abubuwa biyu ne suka sa Jehobah ya kafa dukan dokokin nan, wato mu ƙaunaci Allah da kuma maƙwabtanmu. (L. Fir. 19:18; M. Sha. 6:5; karanta Matiyu 22:36-40.) Don haka, muna iya cewa kowace cikin sama da umurni 600 da ke cikin Dokar tana koya mana game da ƙaunar Jehobah ga mutane. Bari mu tattauna wasu misalai.
5-6. Mene ne Jehobah yake son ma’aurata su yi, kuma me yake lura? Ka ba da misali.
5 Ma’aurata, ku kasance da aminci ga juna kuma ku kula da yaranku. Jehobah yana so ma’aurata su ƙaunaci juna muddar ransu. (Far. 2:24; Mat. 19:3-6) Zina tana cikin laifuffuka mafi tsanani. Saboda haka, doka ta bakwai a cikin dokoki goma da aka ba Musa ta haramta yin zina. (M. Sha. 5:18) Yin zina “zunubi” ne ga Allah da kuma cin amanar abokin aure ko abokiyar aure. (Far. 39:7-9) Mace ko namijin da aka ci amanarsa ta wannan hanyar yana iya ɗaukan shekaru yana baƙin ciki.
6 Jehobah yana ganin yadda ma’aurata suke bi da juna. Yana so Isra’ilawa magidanta su riƙa bi da matansu yadda ya dace. Mijin da ke daraja Dokar zai ƙaunaci matarsa, kuma ba zai kashe aurensu don dalilin da bai taka-kara-ya-ƙarya ba. (M. Sha. 24:1-4; Mat. 19:3, 8) Amma idan sun sami matsala mai tsanani kuma suka kashe aurensu, mijin zai ba matar takardar saki. Wannan takardar za ta kāre matar idan aka yi mata zargin yin zina. Ƙari ga haka, kafin mijin ya ba ta takardar, yana bukatar ya nemi shawarar dattawa. Dattawan za su yi amfani da wannan damar don su yi ƙoƙarin sulhunta su. Ba a kowane lokaci ba ne Jehobah yake ɗaukan mataki idan Ba’isra’ile ya kashe aurensa ba tare da wani ƙwaƙƙwarar dalili ba. Duk da haka, Jehobah yana ganin yadda mijin ya sa matar ta sha wahala, kuma hakan na sa shi baƙin ciki.—Mal. 2:13-16.
7-8. (a) Mene ne Jehobah ya umurci iyaye su yi? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.) (b) Wane darasi ne muka koya?
7 Ban da haka, Dokar ta nuna cewa Jehobah yana so a kāre yara kuma su riƙa farin ciki. Ya umurci iyaye su riƙa biyan bukatun yaransu kuma su taimaka musu su ƙulla dangantaka mai kyau da shi. Iyayen suna bukatar su yi amfani da dukan damar da suka samu don su taimaka wa yaransu su fahimci Dokar Allah kuma su riƙa daraja ta. (M. Sha. 6:6-9; 7:13) Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa Allah ya hukunta Isra’ilawa shi ne domin sun wulaƙanta wasu cikin ’ya’yansu. (Irm. 7:31, 33) Bai kamata iyaye su riƙa wulaƙanta yaransu ba, amma ya kamata su ɗauki yaran a matsayin kyauta daga Jehobah kuma su daraja su.—Zab. 127:3.
8 Darussa: Jehobah yana lura da yadda ma’aurata suke bi da juna. Yana so iyaye su riƙa ƙaunar yaransu, kuma zai shari’anta iyaye idan suka wulaƙanta yaransu.
9-11. Me ya sa Jehobah ya ba da dokar da ta hana yin kwaɗayin kayan wani?
9 Kada ka yi kwaɗayin kayan wani. Doka ta ƙarshe a cikin dokoki goma da aka M. Sha. 5:21; Rom. 7:7) Jehobah ya ba da wannan dokar ne don ya koya wa mutanensa darasi mai muhimmanci. Wane darasi ke nan? Mutanensa suna bukatar su kāre zuciyarsu da kuma tunaninsu. Jehobah ya san cewa muna yawan aikata mugun tunanin da muka yi. (K. Mag. 4:23) Idan Ba’isra’ile ya soma tunani marar kyau, hakan yana iya sa ya soma bi da mutane yadda bai dace ba. Alal misali, Sarki Dauda ya yi wannan kuskuren. Shi mutumin kirki ne, amma akwai lokacin da ya soma sha’awar matar wani, kuma hakan ya sa ya yi zunubi. (Yaƙ. 1:14, 15) Dauda ya yi zina kuma ya yi ƙoƙarin ya ruɗi mijin matar, bayan haka, sai ya kashe shi.—2 Sam. 11:2-4; 12:7-11.
ba Isra’ilawa ta haramta yin kwaɗayi ko kuma yin sha’awar kayan wani. (10 Da yake Jehobah yana ganin abin da ke zuciyar mutum, ya sani a duk lokacin da Ba’isra’ile ya soma kwaɗayin kayan wani. (1 Tar. 28:9) Dokar da Allah ya ba da game da kwaɗayin kayan wani ta bayyana wa Isra’ilawa cewa suna bukatar su guji dukan abin da zai sa su kasance da halin da bai dace ba. Hakika, Jehobah Uba ne mai ƙauna da kuma hikima!
11 Darussa: Jehobah ya san yadda muke ji da kuma abubuwan da muke tunani a kai. Ya san dukan abin da ke cikin zuciyarmu. (1 Sam. 16:7) Ba za mu iya ɓoye masa tunaninmu ko yadda muke ji ko kuma ayyukanmu ba. Idan ya lura da halayenmu masu kyau, yana ƙarfafa mu mu ci gaba da hakan. Amma yana so mu bincika kanmu kuma mu kawar da tunanin banza kafin hakan ya sa mu yi zunubi.—2 Tar. 16:9; Mat. 5:27-30.
DOKOKIN DA KE ƊAUKAKA NUNA ADALCI
12. Mene ne Dokar Jehobah ta nanata?
12 Dokar ta nanata cewa Jehobah yana son adalci. (Zab. 37:28; Isha. 61:8) Jehobah ya kafa misali mai kyau na nuna wa mutane adalci. Sa’ad da Isra’ilawa suka bi dokokin da Jehobah ya ba su, ya yi musu albarka. Amma da suka ƙi bin dokokinsa na adalci sun sha wahala. Ka yi la’akari da dokoki biyu daga Dokoki Goma da Jehobah ya ba Musa.
13-14. Mene ne doka ta farko da ta biyu ta ce Isra’ilawa su yi, kuma ta yaya za su amfana da a ce sun yi biyayya?
13 Ku bauta wa Jehobah kaɗai. A doka ta farko da ta biyu cikin Dokoki Goma da Allah ya bayar, ya umurci Isra’ilawa su bauta masa kaɗai. Jehobah ya yi musu kashedi cewa kada su bauta wa gumaka. (Fit. 20:3-6) Waɗannan dokokin ba za su amfane Jehobah ba. A maimakon haka, mutanen ne za su amfana. Sa’ad da mutanensa suka kasance da aminci, sun ji daɗi. Amma da suka soma bauta wa gumaka, sun sha wahala.
14 Ka yi tunanin Kan’aniyawa da ke bauta wa allolin ƙarya maimakon Allah na gaskiya. Da yake suna bauta ta ƙarya hakan ya sa sun zub da darajarsu. (Zab. 115:4-8) Bautarsu ta ƙunshi yin lalata da kuma ba da yaransu hadaya. Sa’ad da Isra’ilawa suka ƙi yin biyayya ga Jehobah kuma suka soma bauta wa gumaka, sun zub da mutuncinsu kuma suka jawo ma iyalinsu baƙin ciki. (2 Tar. 28:1-4) Waɗanda suke shugabanci sun daina bin dokoki na adalci da Jehobah ya kafa musu. Sun soma amfani da ikonsu a hanyar da ba ta dace ba kuma suka soma cin zarafin marasa ƙarfi. (Ezek. 34:1-4) Jehobah ya gargaɗi Isra’ilawa cewa zai hukunta su idan suka ci zarafin mata da yara marasa ƙarfi. (M. Sha. 10:17, 18; 27:19) A lokacin da mutanensa suke da aminci kuma suka nuna wa juna adalci, Jehobah ya yi musu albarka.—1 Sar. 10:4-9.
15. Mene ne muka koya game da Jehobah?
Isha. 49:15) Ko da yake ba zai ɗau mataki nan da nan ba, amma zai hukunta mutanen da suke cutar da wasu.
15 Darussa: Bai kamata mu ɗora wa Jehobah laifi ba sa’ad da mutanen da ke da’awar bauta masa suka ƙi bin ƙa’idodinsa kuma suka cutar da wasu. Jehobah yana ƙaunar mu kuma yana gani sa’ad da aka yi mana rashin adalci. Yana baƙin ciki idan muna shan wahala fiye da yadda mahaifiya take ji idan yaranta suna shan wahala. (YADDA YA KAMATA A BI DOKAR
16-18. Ta yaya Dokar Allah ta shafi rayuwar Isra’ilawa, kuma wane darasi ne hakan ya koya mana?
16 Dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa ta shafi abubuwa da yawa a rayuwar Ba’isra’ile. Shi ya sa yake da muhimmanci dattawan su yi shari’a da adalci. Dattawan suna yin shari’a a kan batutuwa dabam-dabam, ba batun da ya shafi bautar Jehobah kaɗai ba. Suna yin hakan sa’ad da mutanen suka sami saɓani ko kuma suka aikata laifi. Ka yi la’akari da wasu misalai.
17 Ana shari’anta Ba’isra’ile da ya kashe wani kuma ba a gafarta masa haka kawai. Dattawan birnin za su yi bincike don su san abin da ya jawo kisan. Bayan haka, sai su tsai da shawara ko hukuncin kisa ne ya dace a yanke wa mai laifin. (M. Sha. 19:2-7, 11-13) Ƙari ga haka, suna yin shari’a a batutuwa dabam-dabam har da batun gādo da kuma matsala tsakanin ma’aurata. (Fit. 21:35; M. Sha. 22:13-19) Sa’ad da dattawan suka yi shari’a da adalci kuma Isra’ilawa suka bi Dokar Allah, kowa ya amfana kuma al’ummar ta daraja Jehobah.—L. Fir. 20:7, 8; Isha. 48:17, 18.
18 Darussa: Dukan abubuwan da muke yi a rayuwa suna da muhimmanci ga Jehobah. Yana so mu riƙa nuna ƙauna da adalci sa’ad da muke sha’ani da mutane. Ƙari ga haka, yana jin furucinmu, yana ganin ayyukanmu ko da muna yin hakan sa’ad da babu kowa.—Ibran. 4:13.
19-21. (a) Yaya ya kamata dattawa da kuma alƙalai su bi da mutanen Allah? (b) Ta yaya Dokar Allah ta kāre mutane, kuma wane darasi ne hakan ya koya mana?
19 Jehobah ya so ya kāre mutanensa domin kada al’ummar da ke kewaye da su su rinjaye su. Don haka, ya bukaci dattawan da kuma alƙalai su riƙa hukunci da kuma kafa doka ba tare da son kai ba. Ƙari ga haka, bai kamata waɗanda suke yin shari’a su yi hakan a hanyar da ba ta dace ba. A maimakon haka, suna bukatar su riƙa nuna adalci.—M. Sha. 1:13-17; 16:18-20.
20 Jehobah yana tausaya wa mutanensa sosai, shi ya sa ya kafa dokokin da za su hana su yin rashin adalci. Alal misali, Dokar ta hana zargin mutumin da bai aikata laifi ba. Ban da haka, mutum da ake zargin shi da aikata laifi yana da ’yancin sanin wanda yake zargin sa. (M. Sha. 19:16-19; 25:1) Kafin a ɗauki mataki, wajibi ne sai shaidu aƙalla guda biyu sun tabbatar da cewa ya aikata laifin. (M. Sha. 17:6; 19:15) Me zai faru idan mutum ɗaya ne kaɗai ya shaida laifin da wani Ba’isra’ile ya yi? Kada ya yi tunanin cewa ba za a hukunta shi don laifin da ya yi ba. Jehobah ya ga abin da ya yi. A cikin iyali, magidanta suna da iko, amma ikon yana da iyaka. Dattawan birnin suna da hakkin sasanta wasu matsaloli da iyalai ke fuskanta kuma su yanke hukunci.—M. Sha. 21:18-21.
21 Darussa: Jehobah ya kafa misali mafi kyau domin yana yin adalci a dukan ayyukansa. (Zab. 9:7) Yana yi ma waɗanda suke bin ƙa’idodinsa albarka, amma yana hukunta waɗanda suke amfani da ikonsu don cutar da wasu. (2 Sam. 22:21-23; Ezek. 9:9, 10) Wasu sun aikata laifi kuma suna tunanin cewa babu abin da zai faru, amma Jehobah zai tabbatar da cewa ya hukunta su a lokacin da ya dace. (K. Mag. 28:13) Idan ba su tuba ba, za su fahimci cewa abin ‘ban tsoro ne mutum ya fāɗa cikin hannuwan Allah Mai Rai.’—Ibran. 10:30, 31.
SU WAYE NE SUKA AMFANA DAGA DOKAR?
22-24. (a) Su waye ne Dokar ta kāre, kuma mene ne muka koya game da Jehobah? (b) Wane gargaɗi ne ke littafin Fitowa 22:22-24?
22 Dokar ta kāre marasa ƙarfi, kamar su marayu da gwauraye da kuma baƙi. An umurci alƙalai a Isra’ila cewa: ‘Ba za ku jujjuye gaskiyar da take hakkin baƙo ko na maraya ba, ko kuwa ku ɗauki rigar matar da M. Sha. 24:17) Jehobah ya nuna cewa ya damu da marasa ƙarfi a cikin al’ummar. Ban da haka, ya hukunta waɗanda suka nuna musu rashin adalci.—Karanta Fitowa 22:22-24.
mijinta ya mutu a kan jingina ba.’ (23 Dokar ta kuma kāre iyalai domin ta haramta Isra’ilawa yin jima’i da danginsu. (L. Fir. 18:6-30) Al’ummai da ke kewaye da Isra’ilawa ba sa ɗaukan yin jima’i tsakanin dangi a matsayin laifi. Amma Jehobah ya umurci Isra’ilawa cewa su tsani yin hakan yadda shi ma ya tsane shi.
24 Darussa: Jehobah yana so waɗanda ya ba hakkin kula da mutanensa su nuna cewa sun damu da su. Ya tsani cin zarafin mutane ta hanyar lalata. Yana so kowa har da marasa ƙarfi su sami kāriya kuma a nuna musu adalci.
DOKAR TANA NUNA “ABUBUWA MASU KYAU” DA ZA SU FARU
25-26. (a) Me ya sa za mu iya cewa ƙauna da adalci suna kama da rai da kuma numfashi? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba a jerin talifofin nan?
25 Ƙauna da adalci suna kama da rai da kuma numfashi. Sai da rai ake yin numfashi, kuma sai da numfashi ake samun rai. Ɗaya ba zai iya wanzuwa ba tare da ɗayan ba. Idan muka gaskata cewa Jehobah yana mana adalci, hakan zai sa mu daɗa ƙaunar sa. Idan muna ƙaunar Allah kuma muna son ƙa’idodinsa, za mu ƙaunaci mutane kuma mu riƙa nuna musu adalci.
26 Wannan Dokar ta taimaka wa Isra’ilawa su ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah. Amma mutanen Allah a yau ba sa bukatar su bi Dokar domin Yesu ya sauya ta da wadda ta fi kyau. (Rom. 10:4) Manzo Bulus ya ce Dokar tana nuna “abubuwa masu kyau waɗanda suke a gaba.” (Ibran. 10:1) A talifi na gaba cikin jerin talifofin nan, za a tattauna wasu daga cikin abubuwan nan masu kyau da kuma dalilin da ya sa ƙauna da adalci suke da muhimmanci a cikin ikilisiya.
WAƘA TA 109 Mu Kasance da Ƙauna ta Gaske
^ sakin layi na 5 Wannan talifin shi ne na farko a cikin jerin talifofi guda huɗu da za su nuna dalilin da ya sa muke bukatar mu kasance da tabbaci cewa Jehobah ya damu da mu. Talifofi guda uku da suka rage za su fito ne a Hasumiyar Tsaro ta watan Mayu 2019. Jigon talifofin su ne, “Yadda Ake Nuna Ƙauna da Adalci a Cikin Ikilisiya” da “Yadda Ake Nuna Ƙauna da Adalci Sa’ad da Aka Ci Zarafin Yara” da kuma “Yadda Za a Taimaka ma Waɗanda Aka Ci Zarafinsu.”
^ sakin layi na 2 MA’ANAR WASU KALMOMI: Ana kiran dokoki ɗari shida da Jehobah ya ba Isra’ilawa “Dokar Musa” ko “Dokar” ko kuma “Dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa.” Ƙari ga haka, ana yawan kira littattafai biyar na Littafi Mai Tsarki (Farawa zuwa Maimaitawar Shari’a) Dokar. A wasu lokuta, hakan yana nufin Nassosin Ibrananci.
^ sakin layi na 60 HOTON DA KE BANGON GABA: Jehobah yana so iyaye su yi renon yaransu kuma su koyar da su a cikin yanayi mai kyau.
BAYANI A KAN HOTUNA: Sa’ad da wata mahaifiya Ba’isra’iliya take dafa abinci, tana jin daɗin hirar da take yi da yaranta. Mahaifin kuma yana koya wa yaronsa yadda ake kiwon tumaki.
^ sakin layi na 64 BAYANI A KAN HOTUNA: Dattawan birnin suna taimaka ma wata gwauruwa da ɗanta sa’ad da wani ɗan kasuwa ya nuna musu rashin adalci.