Ku Ci-gaba da “Kaunar ‘Yan’uwa” da Anniya!
Ku ci gaba da “ƙaunar ‘yan’uwa.”—IBRANIYAWA 13:1.
WAƘOƘI: 72, 119
1, 2. Me ya sa Bulus ya rubuta wasiƙa ga Kiristoci Ibraniyawa?
A SHEKARA ta 61 bayan haihuwar Yesu, ikilisiyoyin da ke faɗin ƙasar Isra’ila suna zaman lafiya. Ko da yake manzo Bulus ya sami kansa a cikin kurkuku a ƙasar Roma, ya sa rai cewa za a sake shi ba da daɗewa ba. An sake abokin tafiyarsa Timotawus daga kurkuku kuma suna sa rai za su kai ziyara ga ‘yan’uwa da ke Yahudiya. (Ibraniyawa 13:23) A cikin shekara biyar, Kiristoci da ke Yahudiya, musamman waɗanda suke Urushalima suna bukatar su ɗauki mataki nan da nan. Me ya sa? Shekaru da suka shige, Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa suna bukatar su gudu su bar Urushalima da zarar sun ga sojoji sun kewaye ta.—Luka 21:20-24.
2 Shekaru 28 sun shige da Yesu ya yi wannan gargaɗin ga mabiyansa. A wannan lokacin, Kiristocin da ke Isra’ila sun kasance da aminci duk da hamayya da kuma gwaji da suka fuskanta. (Ibraniyawa 10:32-34) Amma Bulus yana so ya shirya su domin abin da zai faru a nan gaba. Nan ba da daɗewa ba, za su fuskanci gwaji da ba su taɓa fuskanta ba a rayuwarsu. (Matta 24:20, 21; Ibraniyawa 12:4) Suna bukatar haƙuri da kuma bangaskiya sosai don su bi umurnin Yesu cewa su gudu su bar Urushalima. Ta yin hakan ne za su sami ceto. (Karanta Ibraniyawa 10:36-39.) Shi ya sa Jehobah ya ja-goranci Bulus ya rubuta wa waɗannan ƙaunatattun ‘yan’uwa wasiƙa. An rubuta wannan wasiƙar, wadda yanzu ake kira littafin Ibraniyawa don a ƙarfafa su saboda abin da zai faru.
3. Me ya sa ya kamata mu yi marmarin bincika littafin Ibraniyawa?
3 A matsayinmu na bayin Allah a yau, ya kamata mu yi marmarin bincika littafin Ibraniyawa. Me ya sa? Domin muna cikin irin yanayin da Kiristoci da ke Yahudiya suka sami kansu a ciki. Muna rayuwa ne a “miyagun zamani,” kuma mutane da yawa sun jimre da gwaji ko kuma hamayya mai tsanani. (2 Timotawus 3:1, 12) Amma yawancinmu muna da kwanciyar hankali kuma ba ma fuskantar hamayya kai tsaye. Saboda haka, muna bukatar mu yi hattara kamar Kiristoci a zamanin Bulus. Me ya sa? Nan ba da daɗewa ba, za mu fuskanci gwaji da ba mu taɓa fuskanta a rayuwarmu ba!—Karanta Luka 21:34-36.
4. Mene ne jigon shekara ta 2016 kuma me ya sa hakan ya dace?
4 Mene ne zai taimaka mana mu kasance a shirye saboda wannan abin da zai faru a nan gaba? Bulus ya ambaci abubuwa da yawa a cikin littafin Ibraniyawa da za su taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Wani abu mai muhimmanci shi ne abin da aka ambata a littafin Ibraniyawa 13:1 cewa: Ku ci gaba da “ƙaunar ‘yan’uwa.” An ɗauko jigon shekara ta 2016 daga wannan ayar.
Jigonmu na shekara ta 2016 shi ne: Ku ci gaba da “ƙaunar ‘yan’uwa.”—Ibraniyawa 13:1
MECE CE ƘAUNAR YAN’UWA TAKE NUFI?
5. Mece ce ƙaunar ‘yan’uwa take nufi?
5 Mece ce ƙaunar ‘yan’uwa take nufi? Ƙauna ce da ke tsakanin iyali ko kuma abokai na kud da kud. (Yohanna 11:36) Mu ‘yan’uwan juna ne ƙwarai da gaske, ba cika baki muke yi ba. (Matta 23:8) Bulus ya ce: “Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ‘yan’uwa; kuna gabatar da juna cikin bangirma.” (Romawa 12:10) Waɗannan kalaman sun nuna cewa muna ƙaunar ‘yan’uwanmu sosai. Wannan ƙaunar da kuma ƙauna da ke tsakanin Kiristoci suna taimaka mana mu zama abokai na kud da kud kuma mu kasance da haɗin kai.
6. Kiristoci na gaskiya suna nuna ƙauna ga su wane ne, kuma me ya sa?
6 Ana yawan amfani da wannan kalmar “ƙaunar ‘yan’uwa” a cikin littattafanmu. Ga Yahudawa a dā, wannan kalmar “ɗan’uwa” tana nufin ɗan dangi ko kuma wani Bayahude dabam. Amma hakan bai haɗa da wanda ba Bayahude ba. Amma, a matsayinmu na Kiristoci na gaskiya, kowane Kirista na gaskiya “ɗan’uwa” ne a gare mu, ko da a wace ƙasa ya fito. (Romawa 10:12) Jehobah ya koya mana mu ƙaunaci juna kamar ‘yan’uwa. (1 Tasalonikawa 4:9) Me ya sa yake da muhimmanci mu ƙaunaci ‘yan’uwanmu?
ME YA SA YAKE DA MUHIMMANCI MU CI GABA DA ƘAUNAR ‘YAN’UWANMU?
7. (a) Wane dalili mafi muhimmanci ne zai sa mu ƙaunaci ‘yan’uwanmu? (b) Ka ba da wani dalilin da ya sa yake da muhimmanci mu ƙara ƙaunar juna.
7 Dalili mafi muhimmanci da ya sa ya kamata mu ci gaba da ƙaunar ‘yan’uwanmu shi ne cewa Jehobah ya umurce mu 1 Yohanna 4:7, 20, 21) Wani dalilin da ya sa muke ƙaunar ‘yan’uwanmu shi ne, muna bukatar juna musamman ma a mawuyacin lokaci. Sa’ad da Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa ga Kiristoci Ibraniyawa, ya san cewa nan ba da daɗewa ba za su bar gidajensu da kuma abubuwan da suka mallaka. Yesu ya kwatanta yadda wannan mawuyacin lokaci zai kasance. (Markus 13:14-18; Luka 21:21-23) Saboda haka, kafin wannan lokacin, waɗannan Kiristoci suna bukata su ƙara ƙaunar juna.—Romawa 12:9.
mu yi hakan. Ba za mu iya ƙaunar Jehobah ba idan ba ma ƙaunar ‘yan’uwanmu. (Muna bukatar mu ƙarfafa ƙaunar da muke yi wa ‘yan’uwanmu yanzu domin hakan zai taimaka mana mu jimre kowane gwajin da za mu fuskanta a nan gaba
8. Mene ne muke bukata mu yi kafin a soma ƙunci mai girma?
8 Nan ba da daɗewa ba, za a soma ƙunci mai girma. (Markus 13:19; Ru’ya ta Yohanna 7:1-3) Muna bukatar mu bi wannan umurni cewa: “Ku zo, mutanena, ku shiga cikin ɗakunanku, ku rufe ma kanku ƙofofi: ku ɓuya kaɗan, har fushin ya wuce.” (Ishaya 26:20) Waɗannan “ɗakunan” suna iya nufin ikilisiyoyinmu. A wajen ne muke bauta wa Jehobah tare da ‘yan’uwanmu. Amma muna bukatar mu yi wasu abubuwa ba halarta taro kawai ba. Bulus ya tuna wa Kiristoci Ibraniyawa cewa su ƙarfafa juna, su ƙaunaci juna kuma su riƙa yi wa juna alheri. (Ibraniyawa 10:24, 25) Muna bukatar mu ƙarfafa ƙaunar da muke yi wa ‘yan’uwanmu yanzu domin hakan zai taimaka mana mu jimre kowane gwajin da za mu fuskanta a nan gaba.
9. (a) Wane zarafi ne muke da shi a yau na nuna cewa muna ƙaunar ‘yan’uwanmu? (b) Ka ba da misalan da suka nuna yadda mutanen Jehobah suke ƙaunar ‘yan’uwansu.
9 Kafin a soma ƙunci mai girma, muna da zarafi da yawa na nuna cewa muna ƙaunar ‘yan’uwanmu. ‘Yan’uwanmu da yawa suna shan wahala saboda girgizar ƙasa da rigyawa da mahaukaciyar guguwa da tsunami ko kuma wasu bala’i. Wasu ‘yan’uwa suna fuskantar hamayya. (Matta 24:6-9) Ƙari ga haka, ana fama da matsalar tattalin arziki saboda wannan duniya da muke ciki. (Ru’ya ta Yohanna 6:5, 6) Hakika, matsalolin da ‘yan’uwanmu suke fuskanta suna ba mu zarafin nuna musu cewa muna ƙaunar su sosai. Ko da yake mutane a wannan duniyar ba sa ƙaunar juna, muna bukata mu ci gaba da ƙaunar ‘yan’uwanmu. (Matta 24:12) [1]—Ka duba ƙarin bayani.
TA YAYA ZA MU CI GABA DA ƘAUNAR ‘YAN’UWANMU?
10. Mene ne za mu tattauna yanzu?
10 Ta yaya za mu iya ci gaba da ƙaunar ‘yan’uwanmu duk da matsalolin da muke fuskanta? Ta yaya za mu iya nuna cewa muna da irin wannan ƙaunar ga ‘yan’uwanmu? Bayan manzo Bulus ya ce ku
ci gaba da “ƙaunar ‘yan’uwa,” ya faɗi abubuwan da za su taimaka wa Kiristoci su yi hakan. Yanzu, bari mu tattauna abubuwa guda shida daga cikin su.11, 12. Mene ake nufin da nuna karimci? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)
11 “Kada a manta a nuna ƙauna ga baƙi.” (Karanta Ibraniyawa 13:2.) Wataƙila wannan furucin ya tuna mana Ibrahim da kuma Lutu. Waɗannan maza biyu su nuna alheri ga baƙi da ba su san su ba. Daga baya, Ibrahim da Lutu sun gano cewa waɗannan baƙi mala’iku ne. (Farawa 18:2-5; 19:1-3) Waɗannan misalan sun ƙarfafa Kiristoci Ibraniyawa su riƙa nuna karimci ga ‘yan’uwa.
12 Ta yaya za mu iya nuna karimci ga wasu? Muna iya gayyatar ‘yan’uwanmu su zo gidanmu don mu ci abinci tare ko kuma mu ƙarfafa juna. Sa’ad da mai kula da da’ira ya zo ikilisiyarmu, muna iya gayyatar sa da matarsa zuwa gidanmu ko da ba mu san su sosai ba. (3 Yohanna 5-8) Ba ma bukatar mu dafa abinci da yawa ko kuma mu kashe kuɗi sosai. Manufarmu ita ce mu ƙarfafa ‘yan’uwanmu, ba wai mu burge su ba. Bai dace mu gayyaci waɗanda za su so su yi mana alheri a nan gaba kawai ba. (Luka 10:42; 14:12-14) Abu mafi muhimmanci shi ne kada mu bar harkokinmu su sa mu manta da nuna karimci!
13, 14. Ta yaya za mu “riƙa tunawa da waɗanda ke kurkuku”?
13 “Ku riƙa tunawa da waɗanda ke kurkuku.” (Ibraniyawa 13:3, Littafi Mai Tsarki.) Sa’ad da Bulus yake rubuta wannan wasiƙar, yana magana ne game da ‘yan’uwan da suke cikin kurkuku saboda imaninsu. Bulus ya yaba wa ikilisiyar domin sun “yi juyayin waɗanda ke cikin sarƙa.” (Ibraniyawa 10:34) A shekara huɗu da Bulus ya yi a kurkuku, wasu ‘yan’uwa sun taimaka masa. Amma inda wasu suke zama, ya yi nisa daga inda yake. Shin ta yaya waɗannan za su taimaka wa Bulus? Suna iya yin addu’a sosai a madadinsa.—Filibiyawa 1:12-14; Ibraniyawa 13:18, 19.
Muna iya yin addu’a wa ‘yan’uwa maza da mata har da yara da suke cikin kurkuku a ƙasar Eritrea
14 A yau, akwai Shaidun Jehobah da yawa da suke kurkuku saboda imaninsu. ‘Yan’uwa maza da mata da suke zama kusa da su suna iya taimaka musu da abubuwan da suke bukata. Amma yawancinmu mun yi nesa da su. Ta yaya za mu iya taimaka musu kuma kada mu manta da su? Ƙaunar da muke yi wa ‘yan’uwa za ta motsa mu mu yi addu’a a madadinsu. Alal misali, muna iya yin addu’a wa ‘yan’uwa maza da mata har da yara da suke cikin kurkuku a ƙasar Eritrea. Ƙari ga haka, muna iya yin addu’a a madadin ‘yan’uwa Paulos Eyassu da Isaac Mogos da kuma Negede Teklemariam, da suka yi sama da shekara 20 yanzu a cikin kurkuku.
15. Ta yaya za mu daraja aurenmu?
15 “Aure shi zama abin darajantuwa a wajen dukan mutane.” (Karanta Ibraniyawa 13:4.) Muna iya nuna cewa muna ƙaunar ‘yan’uwanmu ta guje wa yin lalata. (1 Timotawus 5:1, 2) Alal misali, idan muka yi zina da ‘yar’uwa ko kuma ɗan’uwa, muna saka mutumin da kuma iyalinsa cikin haɗari. Ƙari ga haka, ‘yan’uwanmu ba za su ƙara amincewa da mu ba. (1 Tasalonikawa 4:3-8) Ka yi tunanin yadda matan aure za ta ji idan ta gano cewa mijinta yana kallon hotunan batsa. Shin za ta ji cewa mijinta yana ƙaunarta kuma yana daraja tsarin da Allah ya kafa na aure kuwa?—Matta 5:28.
16. Ta yaya haƙura da abin da muke da shi zai taimaka mana mu ƙaunaci ‘yan’uwanmu?
16 “Ku haƙura da abin da kuke da shi.” (Karanta Ibraniyawa 13:5.) Idan muka dogara ga Jehobah, hakan zai taimaka mana mu haƙura da abin da muke da shi. Ta yaya hakan yake taimaka mana mu ƙaunaci ‘yan’uwanmu? Idan muka haƙura da abin da muke da shi, za mu tuna cewa ‘yan’uwanmu sun fi kuɗi da abin duniya muhimmanci. (1 Timotawus 6:6-8) Ba za mu riƙa yin gunaguni game da ‘yan’uwanmu ko kuma yanayinmu ba. Ƙari ga haka, ba za mu yi kishin ‘yan’uwanmu ko kuma mu riƙa yin haɗama ba. A maimakon hakan, za mu haƙura da abin da muke da shi kuma mu riƙa bayarwa.—1 Timotawus 6:17-19.
17. Ta yaya kasancewa da “gaba gaɗi” zai taimaka mana mu ƙaunaci ‘yan’uwanmu?
17 Ku kasance da “gaba gaɗi.” (Karanta Ibraniyawa 13:6.) Idan mun dogara ga Jehobah, za mu kasance da gaba gaɗi kuma mu jimre da matsaloli. Wannan gaba gaɗin zai sa mu kasance da ra’ayin da ya dace. Ƙari ga haka, idan muna da ra’ayin da ya dace, za mu ƙaunaci ‘yan’uwanmu ta wajen ƙarfafa su da kuma yi musu ta’aziyya. (1 Tasalonikawa ) Za mu iya kasancewa da gaba gaɗi ko a lokacin ƙunci mai girma, domin mun san cewa cetonmu ya kusa.— 5:14, 15Luka 21:25-28.
Za mu iya kasancewa da gaba gaɗi don mun san cewa cetonmu ya kusa
18. Ta yaya za mu daɗa ƙaunar dattawa?
18 “Ku tuna da waɗanda suke ja-gora.” (Karanta Ibraniyawa 13:7, 17, NW.) Dattawa a ikilisiyarmu suna amfani da lokacinsu don su yi aiki tuƙuru a madadinmu. Muna matuƙar ƙaunar su da kuma nuna godiya sa’ad da muka tuna da abubuwan da suke yi. Ba ma so su daina farin ciki saboda abin da muka yi. A maimakon haka, muna so mu yi biyayya da yardar rai. Ta hakan, muna ganin “kwarjininsu ƙwarai da gaske cikin ƙauna sabili da aikinsu.”—1 Tasalonikawa 5:13.
KU CI GADA DA ƘAUNAR JUNA SOSAI
19, 20. Ta yaya za mu ci gaba da ƙaunar ‘yan’uwa sosai?
19 An san mutanen Jehobah a faɗin duniya da ƙaunar ‘yan’uwa. Haka yake a zamanin Bulus. Amma Bulus ya ƙarfafa ‘yan’uwa su riƙa nuna ƙauna sosai. Ya ce: su “ƙara yin haka ƙwarai da gaske.” (1 Tasalonikawa 4:9, 10, LMT) Hakika, akwai hanyoyi da yawa da za mu iya nuna cewa muna ƙaunar ‘yan’uwanmu!
20 Saboda haka, a wannan shekara, yayin da muka shiga cikin Majami’ar Mulkin kuma muka ga jigon shekara a bango, bari mu riƙa yin bimbini a kan waɗannan tambayoyin: Shin zan iya daɗa zama mai ƙaunar baƙi ko kuma mai karimci? Ta yaya zan taimaka wa ‘yan’uwanmu da ke kurkuku? Shin ina daraja tsarin aure da Allah ya kafa? Mene ne zai taimaka mini in kasance da wadar zuci? Ta yaya zan ƙara dogara ga Jehobah? Ta yaya zan ƙara zama mai biyayya ga waɗanda suke ja-gora? Idan muka kyautata yadda muke abubuwa a waɗannan wurare shida, jigon shekara ba zai zama rubutu da ke jikin bango kawai a garemu ba, amma zai riƙa tuna mana mu bi shawarar Bulus sa’ad da ya ce: Ku ci gaba da “ƙaunar ‘yan’uwa.”—Ibraniyawa 13:1.
^ [1] (sakin layi na 9) Don ƙarin bayani game da yadda Shaidun Jehobah suke nuna ƙauna ga ‘yan’uwa a lokacin bala’i, ka duba babi na 20 na littafin nan, Mulkin Allah Yana Sarauta!