Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

‘Yana Ba da Karfi ga Masu Kasala’

‘Yana Ba da Karfi ga Masu Kasala’

Jigonmu na shekara ta 2018: Za a sabunta ƙarfin waɗanda suke dogara ga Jehobah.​—ISHA. 40:31.

WAƘOƘI: 3, 47

1. Me muke fama da su a yau, amma me ya sa Jehobah yake farin ciki da bayinsa masu aminci? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

RAYUWA a wannan zamani tana cike da matsaloli. Jehobah ya san cewa ’yan’uwa da yawa suna fama da rashin lafiya mai tsanani. Wasu kuma suna kula da danginsu da suka tsufa ko da yake su ma da kansu sun tsufa. Har ila, wasu suna ƙoƙari su biya bukatun iyalinsu. Ƙari ga haka, ’yan’uwa da yawa suna fama da dukan waɗannan matsaloli! Yin waɗannan ayyukan yana ɗaukan lokaci sosai, yana gajiyarwa kuma yana cinye musu kuɗi. Amma, Jehobah zai yi farin ciki sosai idan ka tabbatar da cewa zai cika dukan alkawuransa, kuma ka yi imani cewa za ka ji daɗin rayuwa a nan gaba!

2. Ta yaya littafin Ishaya 40:29 yake ƙarfafa mu, amma wane kuskure ne za mu iya yi?

2 A wasu lokuta kana ganin cewa ka gaji da rayuwa don matsalolin da kake fuskanta? Idan haka ne, ba kai kaɗai kake jin haka ba. Domin a cikin Littafi Mai Tsarki, an ambata bayin Jehobah masu aminci da suke ganin ba za su iya jimrewa da matsaloli ba. (1 Sar. 19:4; Ayu. 7:7) Amma sun dogara ga Jehobah maimakon su kasala, kuma Allah ya taimaka musu don yana “ba da ƙarfi ga masu-kasala.” (Isha. 40:29) Abin baƙin ciki shi ne, wasu a cikin bayin Allah sun daina bauta masa don suna ganin hakan ne zai taimaka musu su jimre da matsalolin rayuwa. Sun ɗauka cewa yin ayyukan ibada yana taƙura musu maimakon ya sa su sami albarka. Saboda haka sun daina karanta Kalmar Allah da halartan taro da kuma yin wa’azi. Kuma abin da Shaiɗan yake son su yi ke nan.

3. (a) Me za mu iya yi don kada Shaiɗan ya sa mu karaya? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Iblis ya san cewa za mu sami ƙarfafa idan mun shagala da yin ayyukan ibada, kuma ba ya son mu yi hakan. Saboda haka, idan ka gaji ainun, kada ka daina bauta wa Jehobah. Ka kusace shi sosai don ya ‘kafa ka, ya ƙarfafa ka kuma.’ (1 Bit. 5:10; Yaƙ. 4:8) A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa biyu da za su iya sa mu yi sanyin gwiwa a hidimarmu ga Allah da kuma yadda bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu jimre da matsaloli. Amma bari mu fara tattauna yadda Jehobah zai iya ƙarfafa mu kamar yadda aka nuna a littafin Ishaya 40:​26-31.

ZA A SABUNTA ƘARFIN WAƊANDA SUKE DOGARA GA JEHOBAH

4. Wane darasi ne za mu iya koya daga abin da ke Ishaya 40:26?

4 Karanta Ishaya 40:26. Babu wanda zai iya ƙirga dukan taurarin da ke sama. Ko masanan kimiyya ma sun gaskata cewa damin tauraro da ake kira Milky Way galaxy yana ɗauke da taurari kusan biliyan 400. Duk da haka, Jehobah ya ba kowannensu suna. Mene ne hakan ya koya mana? Idan Jehobah yana kula da abubuwan da ba su da rai, babu shakka ya damu da mu. Muna bauta masa ba don an tilasta mana ba, amma don muna ƙaunarsa! (Zab. 19:​1, 3, 14) Jehobah ya san ku ciki da waje, don “har da gasussuwan kanku dukansu an ƙididdige su.” (Mat. 10:30) Ƙari ga haka, wani marubucin zabura ya tabbatar mana da cewa: “Ubangiji ya san kwanakin kamilai.” (Zab. 37:18) Hakika, yana ganin matsalolin da kake fuskanta, kuma zai ƙarfafa ka ka jimre da kowace matsala da kake fuskanta.

5. Me ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah zai iya ƙarfafa mu?

5 Karanta Ishaya 40:28. Jehobah yana da iko sosai da babu irinsa. Alal misali, ka yi la’akari da ƙarfin da Jehobah ya saka a rana. Wani masanin kimiyya mai suna David Bodanis ya ce: “A kowace daƙiƙa, rana tana fid da zafi da ya yi daidai da na biliyoyin bama-bamai na atam.” Wani ɗan bincike ya ce rana tana “fid da zafi . . . a kowace daƙiƙa da zai iya biyan bukatun ’yan Adam har shekaru 200,000”! Babu shakka, da yake Jehobah ne ya yi rana haka, zai iya ƙarfafa mu mu jimre da duk wata matsalar da muke fuskanta.

6. A wace hanya ce karkiyar Yesu take da sauƙi, kuma ta yaya sanin hakan zai taimaka mana?

6 Karanta Ishaya 40:29. Bauta wa Jehobah yana sa mu farin ciki sosai. Shi ya sa Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: “Ku ɗaukar wa kanku karkiyata.” Ya daɗa cewa: “Za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma marar-nauyi.” (Mat. 11:​28-30) Hakan gaskiya ne! A wasu lokuta, mukan gaji sa’ad da muka bar gida don mu halarci taro ko kuma fita wa’azi. Amma yaya kake ji idan ka dawo? Sai ka ga ka daɗa samun ƙarfin bi da matsalolin rayuwa. Babu shakka, karkiyar Yesu tana da sauƙi!

7. Ka ba da labarin da ya nuna cewa abin da ke cikin Matta 11:​28-30 gaskiya ne.

7 Wata ’yar’uwa mai suna Kayla ta yi fama da kasala da baƙin ciki da kuma ciwon kai mai tsanani. Kuma a wasu lokuta hakan yana hana ta halartar taro. Amma, sa’ad da ta yi ƙoƙari ta halarci wani taro, sai ta ce: “Jawabin da aka yi a taron game da sanyin gwiwa ne. Ya sosa zuciyata har na soma zub da hawaye. Ya tuna mini cewa ina bukatar in riƙa halartar taro duk da yanayina.” Ta yi farin ciki sosai cewa ta halarci taron!

8, 9. Mene ne manzo Bulus yake nufi sa’ad da ya ce: “Sa’ad da ina rashin ƙarfi, sa’an nan mai ƙarfi nake”?

8 Karanta Ishaya 40:30. Ko da mun ƙware a yin wani abu, ba abin da za mu iya cim ma da ƙarfinmu. Alal misali, ko da yake manzo Bulus ya ƙware, duk da haka, bai iya yin wasu abubuwan da yake so ya yi ba. Amma sa’ad da ya gaya wa Allah matsalolinsa, Jehobah ya gaya masa: “Cikin kumamanci ikona yake cika.” Bulus ya fahimci abin da Jehobah yake nufi, shi ya sa ya ce: “Sa’ad da ina rashin ƙarfi, sa’an nan mai ƙarfi nake.” (2 Kor. 12:​7-10) Me Bulus yake nufi da hakan?

9 Bulus ya fahimci cewa Jehobah ne yake ba shi ƙarfin yin dukan abubuwan da yake yi. Ruhun Allah ne ke taimaka ma Bulus ya yi ayyukan da ba zai taɓa yi da ƙarfinsa ba. Haka ma yake da mu a yau. Za mu zama masu ƙarfi idan Jehobah yana ƙarfafa mu mu yi wasu ayyuka!

10. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Dauda ya jimre da matsalolin da ya fuskanta?

10 Ruhun Allah ya taimaka wa Dauda sosai, shi ya sa ya ce: “Da ikonka na fāɗa ma taron yaƙi; da ikon Allahna ni ke tsallake ganuwa.” (Zab. 18:29) Akwai wasu ganuwa, wato matsaloli da ba za mu iya magancewa da kanmu ba sai da taimakon Jehobah.

11. Yaya ruhu mai tsarki yake taimaka mana mu jimre da matsalolinmu?

11 Karanta Ishaya 40:31. Gaggafa ba za ta iya firewa zuwa wasu wurare masu nisa da ƙarfinta ba. Iska mai ɗumi ne ke ba ta ƙarfin tashiwa sama kuma hakan yana taimaka mata kada ta yi amfani da dukan ƙarfinta. Saboda haka, idan kana fama da wata matsala da kake ganin ta fi ƙarfinka, ka tuna da gaggafa. Ka roƙi Jehobah ya ba ka “ruhu mai-tsarki” don ya taimaka maka. (Yoh. 14:26) Abin farin ciki shi ne cewa, muna iya samun wannan taimakon a kowane lokaci. Za mu bukaci wannan taimakon sosai sa’ad da wani ɗan’uwa a cikin ikilisiya ya ɓata mana rai. Amma me ya sa hakan yake faruwa?

12, 13. (a) Me ya sa Kiristoci suke samun saɓani a tsakaninsu? (b) Mene ne labarin Yusufu ya koya mana game da Jehobah?

12 Da yake dukanmu ajizai ne, mukan samu saɓani da ’yan’uwa. Don haka, akwai wasu lokuta da za mu iya yin fushi don abin da wani ɗan’uwa ya faɗa ko ya yi. Ƙari ga haka, ayyukanmu ko furucinmu na iya ɓata ma wasu rai. Hakan yana iya jawo matsala sosai. Amma kamar yadda yake da wasu jarabobi da muke fuskanta, Jehobah yana so mu nuna mu masu aminci ne. Yana so mu yi hakan ta wajen yin abubuwan da za su sa ’yan’uwa haɗin kai tun da Jehobah yana ƙaunarsu duk da ajizancinsu.

Jehobah bai manta da Yusufu ba; kuma ba zai yashe ka ba (Ka duba sakin layi na 13)

13 Labarin Yusufu ya nuna cewa Jehobah yakan bar bayinsa su fuskanci matsaloli a wasu lokuta. ’Yan’uwan Yusufu sun sayar da shi ya zama bawa sa’ad da yake matashi kuma aka kai shi ƙasar Masar. (Far. 37:28) Babu shakka cewa Jehobah ya yi baƙin ciki da yadda aka wulaƙanta abokinsa Yusufu. Duk da haka, bai ɗauki mataki ba. Daga baya, an yi wa Yusufu sharrin cewa ya so ya yi wa matar Fotifar fyaɗe, kuma aka saka shi a fursuna. Har ila, Jehobah bai ɗauki wani mataki ba. Amma Jehobah ya manta da Yusufu ne? A’a, ya ci gaba da yi wa Yusufu ‘albarka.’​—Far. 39:​21-23.

14. Ta yaya za mu amfana idan muka “daina” fushi?

14 Wani misali kuma da za mu tattauna shi ne na Dauda. An wulaƙanta shi sosai, duk da haka bai bar ƙiyayya ta shawo kansa ba. Maimakon haka, ya ce: ‘Ka daina yin fushi, ka rabu da hasala: kada ka dami ranka, wannan ba ya kawo kome sai mugunta.’ (Zab. 37:8) Ainihin abin da ya sa ya kamata mu “daina” fushi shi ne don muna koyi da Jehobah wanda ‘ba ya aika mana gwargwadon zunubanmu.’ (Zab. 103:10) Ƙari ga haka, za mu amfana sosai idan muka daina yin fushi. Yin fushi zai iya jawo mana hawan jini da kuma ciwon huhu da hanta kuma zai iya shafan abin da ke narkar da abinci a jikinmu. Ban da haka ma, fushi zai iya sa mu wawan tunani. Ƙari ga haka, yakan jawo yin baƙin ciki na dogon lokaci. Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Natsatsiyar zuciya rai ce ga jiki.” (Mis. 14:30) Ta yaya za mu magance duk wani saɓani da muka samu da ’yan’uwanmu? Bin shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana.

SA’AD DA ’YAN’UWANMU SUKA ƁATA MANA RAI

15, 16. Ta yaya ya kamata mu tattauna da wanda ya ɓata mana rai?

15 Karanta Afisawa 4:26. Ba ma yin mamaki idan mutanen duniya suka ɓata mana rai. Amma idan wani ɗan’uwa ko wani a iyalinmu ya faɗa ko ya yi wani abu da ya ɓata mana rai sosai, mukan yi baƙin ciki sosai. Idan muka riƙe mutumin a zuciya, za mu ci gaba da fushi har shekaru da yawa, ko ba haka ba? Zai dace mu bi shawarar da ke Littafi Mai Tsarki da ya ce mu sasanta matsala nan da nan. Ba za mu iya sasanta da ɗan’uwanmu ba idan muka ƙi tattauna batun da shi.

16 A ce wani ɗan’uwa ya ɓata maka rai kuma ka riƙe shi a zuciya. Waɗanne matakai ne za ka ɗauka don ku sasanta? Na farko, ka yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka maka ka tattauna batun da shi cikin kwanciyar hankali. Ka tuna cewa ɗan’uwanka yana ɗaya daga cikin abokan Jehobah. (Zab. 25:​14, Littafi Mai Tsarki) Allah yana ƙaunarsa. Kuma da yake Allah yana wa abokansa alheri, yana so mu ma mu yi koyi da shi. (Mis. 15:23; Mat. 7:12; Kol. 4:6) Na biyu kuma, ka yi tunani sosai a kan abin da kake son ka tattauna da ɗan’uwanka. Kada ka ɗauka cewa ɗan’uwan ya so ne ya ɓata maka rai da gangan; ka yi ƙoƙari ka fahimci dalilin da ya sa wataƙila ya yi hakan. Ƙari ga haka, wataƙila kai ma ka yi wani abu da ya sa kuka samu saɓani. Kana iya soma da cewa, “Wataƙila ina saurin fushi, amma sa’ad da ka yi mini magana jiya, sai na ji kamar . . . ” Idan hakan bai taimaka maka ba, ka nemi wani zarafi don ku sasanta. Kafin wannan lokacin, ka yi addu’a a madadin ɗan’uwanka kuma ka ce Jehobah ya albarkace shi. Ban da haka ma, ka roƙi Allah ya taimaka maka ka riƙa mai da hankali ga halaye masu kyau na ɗan’uwanka. Ko da mene ne ya faru, ka tabbatar da cewa Jehobah zai yi farin ciki don ka yi iya ƙoƙarinka ka sasanta da ɗan’uwanka da yake shi ma abokin Allah ne.

SA’AD DA ABIN DA MUKA YI DĀ YAKE DAMUNMU

17. Ta yaya Jehobah zai taimaka mana mu farfaɗo daga zunubin da muka yi, kuma me ya sa ya dace mu yi amfani da wannan tanadin?

17 Wasu suna ganin ba su cancanci su bauta wa Jehobah ba domin zunubi da suka yi a dā. Zunubin da mutum ya yi a dā zai iya ci gaba da damunsa. Sarki Dauda ma ya taɓa fama da alhakin zunubin da ya yi, shi ya sa ya ce: “Lokacin da na yi shuru, ƙasusuwana suka tsufa domin kukana da na yini ina yi. Gama dare da rana hannunka yana da nauyi a bisana.” Amma Dauda ya bi da yanayin yadda ya dace domin shi mutum ne mai ibada sosai. Ya ce: “Na ɗauki zunubina a gabanka . . . kai ma ka gafarta muguntar zunubina.” (Zab. 32:​3-5) Jehobah yana shirye ya taimaka maka ka farfaɗo idan ka yi zunubi mai tsanani. Amma, kana bukatar ka nemi taimako da yake bayarwa a ikilisiya. (Mis. 24:16; Yaƙ. 5:​13-15) Kada ka ɓata lokaci don haka zai iya hana ka samun rai na har abada. Amma wane mataki za ka ɗauka idan zuciyarka tana damunka bayan an gafarta maka?

18. Ta yaya misalin Bulus zai iya taimaka ma waɗanda suke ganin ba su cancanci bauta wa Jehobah ba?

18 Akwai wasu lokuta da manzo Bulus ya damu game da abubuwan da ya yi a dā. Ya ce: “Ni ne mafi ƙanƙanta cikin manzanni, ban ma isa a ce da ni manzo ba, saboda na tsananta wa ikilisiyar Allah.” Duk da haka Bulus ya ce: ‘Amma saboda alherin Allah na zama yadda nake.’ (1 Kor. 15:​9, 10, LMT) Jehobah ya amince da Bulus duk da zunubin da ya yi a dā, kuma yana son Bulus ya gaskata da hakan. Idan ka tuba da gaske kuma ka gaya wa dattawa in zunubi mai tsanani ne, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai nuna maka jinƙai. Saboda haka, ka gaskata da abin da Jehobah ya faɗa cewa ya gafarta maka!​—Isha. 55:​6, 7.

19. Mene ne jigon shekara ta 2018, kuma me ya sa ya dace?

19 Yayin da ƙarshen wannan zamanin ya kusa, ya kamata mu san cewa matsaloli za su ƙaru. Amma, ka kasance da tabbaci cewa wanda yake “ba da ƙarfi ga masu-kasala: ga wanda ba shi da iko” zai iya ba ka duk abin da kake bukata don ka ci gaba da jimrewa. (Isha. 40:29; Zab. 55:22; 68:19) Za mu riƙa tuna da gaskiyar nan a duk lokacin da muka halarci taro a Majami’ar Mulki kuma muka ga jigonmu na shekara ta 2018: Za a sabunta ƙarfin waɗanda suke dogara ga Jehobah.​Isha. 40:31.