Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Taron Tuna da Mutuwar Yesu na Kawo Hadin Kai

Taron Tuna da Mutuwar Yesu na Kawo Hadin Kai

“Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma, ga jama’ar Allah su zauna tare kamar ’yan’uwa!”​—ZAB. 133:​1, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 18, 14

1, 2. Wane taro ne za a yi a shekara ta 2018 da zai sa mutane haɗin kai, kuma me ya sa? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

A RANAR 31 ga Maris 2018, miliyoyin mutane a faɗin duniya za su yi wani taro da ake yi sau ɗaya a kowace shekara. Bayan faɗuwar rana, Shaidun Jehobah da wasu mutane za su taru don su Tuna da Mutuwar Yesu. A kowace shekara, wannan taron ne ya fi sa mutane a faɗin duniya kasancewa da haɗin kai!

2 Babu shakka, Jehobah da Yesu suna farin ciki sosai idan suka ga yadda miliyoyin mutane a faɗin duniya suke halartar wannan taron. An yi annabci a Littafi Mai Tsarki cewa “taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga cikin kowane iri, da dukan kabilai da al’ummai da harsuna” za su yi ihu su ce: “Ceto ga Allahnmu ne wanda ya zauna bisa kursiyin, ga Ɗan ragon kuma.” (R. Yoh. 7:​9, 10) Muna girmama Jehobah da kuma Yesu sosai idan muka halarci wannan taron!

3. Waɗanne tambayoyi ne za a ba da amsarsu a wannan talifin?

3 Za mu amsa wasu tambayoyi a wannan talifin. (1) Ta yaya za mu yi shiri don taron Tuna da Mutuwar Yesu kuma me za mu yi don mu amfana? (2) Ta yaya taron Tuna da Mutuwar Yesu yake sa bayin Allah haɗin kai? (3) Ta yaya kowannenmu zai sa a kasance da haɗin kai? (4) Akwai lokacin da za a yi taron Tuna da mutuwar Yesu na ƙarshe kuwa? Idan akwai, yaushe ne za a yi hakan?

YADDA ZA MU YI SHIRI DON MU AMFANA DAGA TARON

4. Me ya sa bai kamata mu bar wani abu ya hana mu halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu ba?

4 Ka yi tunani sosai a kan muhimmancin halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu. Kuma kada ka manta cewa Jehobah ya umurce mu mu riƙa halartan taron ikilisiya. Don haka, Jehobah da Yesu suna lura da waɗanda suke iya ƙoƙarinsu don su halarci wannan taro mafi muhimmanci da ake yi a kowace shekara. Muna son mu nuna musu cewa ciwo ko wani yanayi da ya fi ƙarfinmu ne kaɗai zai iya hana mu halartan taron nan mai muhimmanci. Idan muna nuna cewa halartan taro yana da muhimmanci sosai, hakan zai sa Jehobah ya rubuta sunanmu a “littafin tunawa,” wato “littafin rai.” A wannan littafin ne ake rubuta sunayen waɗanda za su sami rai na har abada.​—Mal. 3:16; R. Yoh. 20:15.

5. Ta yaya za mu ‘gwada kanmu ko muna cikin imani’ kafin taron Tuna da Mutuwar Yesu?

5 ʼYan kwanaki kafin taron, ya kamata mu nemi lokaci don mu yi addu’a kuma mu bincika kanmu ko muna da dangantaka mai kyau da Jehobah. (Karanta 2 Korintiyawa 13:5.) Ta yaya za mu yi hakan? Za mu iya yin hakan ta wajen ‘gwada kanmu ko muna cikin imani.’ Kafin mu yi hakan, muna bukatar mu tambayi kanmu: ‘Shin na gaskata cewa ina cikin ƙungiyar da Jehobah ya amince da ita da take yin nufinsa? Ina iya ƙoƙarina in yi wa’azi kuma in koyar da mutane game da Mulkin Allah? Shin ayyukana suna nuna cewa na gaskata muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe kuma ƙarshen mulkin Shaiɗan ya kusa? Har ila ina gaskata da Jehobah da Yesu yadda nake yi sa’ad da na soma bauta wa Jehobah?’ (Mat. 24:14; 2 Tim. 3:1; Ibran. 3:14) Yin tunani a kan amsoshin waɗannan tambayoyin zai sa mu san ko har yanzu muna da imani.

6. (a) Wace hanya ɗaya tak ce za ta sa mu sami rai na har abada? (b) Waɗanne shirye-shirye ne wani ɗan’uwa yake yi kowace shekara don Tuna da Mutuwar Yesu, kuma ta yaya za ka yi koyi da shi?

6 Ka karanta talifofin da suka tattauna muhimmancin Tunawa da Mutuwar Yesu kuma ka yi bimbini a kansu. (Karanta Yohanna 3:16; 17:3.) Hanya ɗaya tak da za ta sa mutum ya sami rai na har abada ya ƙunshi ‘sanin’ Jehobah da kuma “ba da gaskiya” ga Ɗansa Yesu. Don ka yi shirin halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu, zai dace ka zaɓi wasu abubuwan da za ka yi nazarinsu don ka kusaci Jehobah da Yesu. Ka yi la’akari da abin da wani dattijo da ya daɗe yana hidima yake yi. Ɗan’uwan ya yi shekaru yana ajiye talifofin Hasumiyar Tsaro da suka tattauna abin da ya sa taron Tuna da Mutuwar Yesu yake da muhimmanci da kuma ƙaunar da Jehobah da Yesu suka nuna mana. ʼYan makonni kafin taron, yana sake karanta talifofin kuma ya yi bimbini a kan muhimmancin wannan taron. A wasu lokuta yana ƙara talifi ɗaya ko biyu ga talifofin da yake da su. Wannan dattijon ya ga cewa sake karanta waɗannan talifofin da surorin da ake karantawa a lokacin da kuma yin bimbini sosai yana sa ya koya sabbin abubuwa a kowace shekara. Ban da haka ma, yana ganin yadda ƙaunar da yake yi wa Jehobah da Yesu yake daɗa ƙarfi a kowace shekara. Irin wannan tsarin nazarin zai sa kai ma ka ƙaunaci Jehobah da Yesu sosai. Ƙari ga haka, zai sa ka amfana sosai daga taron Tuna da Mutuwar Yesu.

TARON YANA SA MU HAƊIN KAI

7. (a) Wace addu’a ce Yesu ya yi a daren da ya soma Jibin Maraice na Ubangiji? (b) Me ya nuna cewa Jehobah ya amsa addu’ar Yesu?

7 A daren farko da aka soma Jibin Maraice na Ubangiji, Yesu ya yi addu’a a madadin almajiransa don su kasance da haɗin kai kamar yadda shi da Ubansa suke da haɗin kai. (Karanta Yohanna 17:​20, 21.) Jehobah ya amsa wannan addu’ar da Yesu ya yi kuma yanzu miliyoyin mutane sun gaskata cewa Jehobah ne ya aiko Yesu. Taron Tuna da Mutuwar Yesu ya fi kowane taro da mutanen Allah suke yi muhimmanci kuma yana nuna cewa Shaidun Jehobah suna da haɗin kai. Mutane daga wurare dabam-dabam suna haɗuwa a majami’u a faɗin duniya don su yi wannan taron. A wasu wurare, mutanen ƙabilu dabam-dabam da kuma maza da mata ba sa yin ibada tare, amma ba haka yake da Shaidun Jehobah ba. Shi ya sa Jehobah da Yesu suna farin ciki don irin haɗin kai da muke da shi!

8. Wane saƙo ne Jehobah ya ba Ezekiyel game da haɗin kai?

8 Ba ma mamaki don haɗin kan da muke da shi da yake mu bayin Jehobah ne. Jehobah da kansa ya ce hakan zai faru. Ka yi la’akari da saƙon da ya ba Ezekiyel game da sanduna biyu da aka haɗa, wato sandar “Yahuda” da kuma sandar “Yusufu.” (Karanta Ezekiyel 37:​15-17.) Talifin nan “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke Hasumiyar Tsaro ta Yuli 2016, ya ce: “Ta bakin annabi Ezekiyel, Jehobah ya gaya wa mutanensa cewa za su koma Ƙasar Alkawari kuma za su sāke kasancewa da haɗin kai a matsayinsu na al’umma ɗaya. Ƙari ga haka, wannan saƙon ya nuna haɗin kan da zai kasance tsakanin mutanen Allah a kwanaki na ƙarshe.”

9. Ta yaya annabcin Ezekiyel yake cika a kowace shekara sa’ad da ake tuna da Mutuwar Yesu?

9 Daga shekara ta 1919, Jehobah ya fara tsara waɗanda za su je sama kuma ya sa su kasance da haɗin kai. Waɗannan su ne sandar “Yahuda” a alamance. Bayan haka, mutane da yawa da suke da begen zama a duniya, wato sandar “Yusufu” a alamance, sun haɗa kai da waɗanda za su je sama. Shi ya sa rukuni biyun suka zama “garke ɗaya.” (Yoh. 10:16; Zak. 8:23) Jehobah ya yi alkawari cewa zai haɗa sanduna biyun su zama sanda ɗaya a hannunsa. (Ezek. 37:19) Yanzu rukuni biyun suna ibada da haɗin kai tare, kuma Yesu, Sarkin da Littafi Mai Tsarki ya kira ‘Dauda bawan’ Allah ne yake musu ja-goranci. (Ezek. 37:​24, 25) Ana ganin wannan haɗin kan da aka kwatanta a annabcin Ezekiyel a kowace shekara sa’ad da shafaffu da suka rage a duniya da kuma “waɗansu tumaki” suka haɗu don su tuna da Mutuwar Yesu! Mene ne kowannenmu zai yi don mu ci gaba da kasancewa da wannan haɗin kai?

YADDA KOWANNENMU ZAI SA A KASANCE DA HAƊIN KAI

10. Ta yaya za mu sa mutanen Allah su ci gaba da kasancewa da haɗin kai?

10 Hanya ɗaya da za mu sa mutanen Allah su ci gaba da haɗin kai ita ce kasancewa da tawali’u. A lokacin da Yesu yake duniya, ya gaya wa almajiransa su riƙa kasancewa da tawali’u. (Mat. 23:12) Idan muna da tawali’u, ba za mu zama masu girman kai kamar mutanen duniya ba. A maimakon haka, tawali’u zai taimaka mana mu riƙa bin shawarar waɗanda suke ja-goranci don hakan zai sa mu kasance da haɗin kai a ikilisiya. Idan muka kasance da tawali’u, za mu faranta ran Jehobah don “yana tsayayya da masu-girman kai, amma yana ba da alheri ga masu-tawali’u.”​—1 Bit. 5:5.

11. Ta yaya yin bimbini a kan abin da gurasa da kuma ruwan anab suke wakilta zai sa mu kasance da haɗin kai?

11 Hanya ta biyu da za mu sa mutanen Allah su ci gaba da haɗin kai ita ce yin bimbini a kan ma’anar gurasa da ruwan anab da ake amfani da su a taron. Zai dace mu yi tunani sosai a kan ma’anar gurasar da ruwan anab kafin a yi wannan taro mai muhimmanci da kuma a lokacin da ake taron. (1 Kor. 11:​23-25) Wannan gurasar tana wakiltar jiki marar zunubi na Yesu da ya bayar a matsayin hadaya. Ruwan anab ɗin kuma yana wakiltar jinin Yesu da ya zubar domin mu. Amma sanin ma’anar kawai ba shi ke nan ba. Zai dace mu riƙa tuna cewa ƙauna ce ta sa Allah ya ba da Ɗansa a madadinmu. Yesu ma yana ƙaunar mu shi ya sa ya ba da ransa don zunubanmu. Idan muka yi tunani sosai a kan ƙaunar da suka nuna mana, hakan zai sa mu riƙa ƙaunarsu sosai. Kuma ƙaunar da muke yi wa Jehobah da kuma ’yan’uwanmu tana sa mu kasance da haɗin kai.

Idan muna gafarta wa mutane, muna sa a kasance da haɗin kai (Ka duba sakin layi na 12, 13)

12. A kwatancin Yesu na wani Sarki da bayinsa, ta yaya Yesu ya nuna cewa Jehobah yana so mu riƙa gafarta wa juna?

12 Hanya ta uku da za mu sa a kasance da haɗin kai ita ce ta wurin gafarta wa mutane. Idan muka gafarta ma waɗanda suka yi mana laifi, muna nuna cewa muna godiya da hadayar da Kristi ya yi don ta hakan ne zai sa a gafarta zunubanmu. Ka yi la’akari da kwatancin da Yesu ya yi da ke Matta 18:​23-34. Ka tambayi kanka: ‘Shin ina son in bi shawarar da Yesu ya bayar? Ina haƙuri da ’yan’uwa? Ina shirye in gafarta ma waɗanda suka yi mini laifi?’ Da yake mu ajizai ne, akwai wasu zunubai da laifuffuka da suke da wuya mu gafarta wa ’yan’uwanmu. Duk da haka, wannan kwatancin ya nuna mana matakin da Jehobah yake son mu ɗauka. (Karanta Matta 18:35.) Yesu ya koya mana cewa Jehobah ba zai gafarta mana ba idan ba mu gafarta wa ’yan’uwanmu da suka tuba da gaske. Ya kamata mu yi tunani sosai a kan wannan batun, ko ba haka ba? Muna ƙarfafa zumuncin da ke tsakaninmu idan muka gafarta wa ’yan’uwanmu kamar yadda Yesu ya ce mu yi.

13. Ta yaya zaman lafiya zai sa a ci gaba da kasancewa da haɗin kai?

13 Idan muka gafarta wa mutane, muna nuna cewa muna son zaman lafiya. Ka yi la’akari da shawarar da Yesu ya bayar cewa mu yi ‘ƙwazo mu kiyaye ɗayantuwar ruhu cikin ɗaurin salama.’ (Afis. 4:3) A lokacin da za a yi taron Tuna da Mutuwar Yesu musamman a daren da za a yi taron, zai dace ka yi tunani sosai a kan yadda kake bi da wasu. Ka tambayi kanka: ‘Halina yana nuna cewa ba na riƙe mutane a zuci? An san ni da yin sadaukarwa don in sa ’yan’uwa su kasance da zumunci da kuma haɗin kai?’ Zai dace mu yi tunani a kan tambayoyin nan a lokacin tuna da Mutuwar Yesu na wannan shekarar.

14. Ta yaya za mu nuna cewa ‘muna haƙuri da junanmu cikin ƙauna’?

14 Hanya ta huɗu da za mu sa a kasance da haɗin kai ita ce ta wurin yin koyi da halin Jehobah na nuna ƙauna. (1 Yoh. 4:8) Bai kamata mu ce, “Ina bukatar in ƙaunaci ’yan’uwana Kiristoci, amma ba lallai sai jininmu ya haɗu ba!” Yin irin wannan tunanin zai saɓa da shawarar Bulus cewa ‘muna haƙuri da junanmu cikin ƙauna.’ (Afis. 4:2) Ka lura cewa Yesu bai ce mu riƙa ‘haƙuri da junanmu’ kawai ba. Amma ya ƙara da cewa zai dace mu yi hakan ‘cikin ƙauna.’ Akwai bambanci sosai tsakanin furuci biyun. A ikilisiyoyinmu, akwai mutane dabam-dabam da Jehobah ya kawo ƙungiyarsa don su bauta masa. (Yoh. 6:44) Da yake Jehobah ya kawo su ƙungiyarsa, wajibi ne ya riƙa ƙaunar su. Idan haka ne, ba zai dace mu ce ba za mu ƙaunace su ba. Bai kamata mu ƙi nuna wannan ƙaunar da Jehobah ya ce mu riƙa nunawa ba!​—1 Yoh. 4:​20, 21.

YAUSHE NE ZA A YI TARON TUNA DA MUTUWAR YESU NA ƘARSHE?

15. Ta yaya muka sani cewa za a yi taron tuna da Mutuwar Yesu na ƙarshe?

15 Wata rana za a yi taron Tuna da Mutuwar Yesu na ƙarshe. Ta yaya muka san da hakan? A wasiƙa ta farko da Bulus ya rubuta wa Kiristoci shafaffu da ke Koranti, ya ce ta wurin tuna da mutuwar Yesu kowace shekara, suna ‘shelar mutuwar Ubangiji har ya zo.’ (1 Kor. 11:26) Kalmar nan “zo” da Bulus ya yi amfani da ita tana nufin “zuwa” da Yesu ya ambata a annabcinsa game da kwanaki na ƙarshe. Game da ƙunci mai girma da ke nan tafe, Yesu ya ce: ‘Sa’an nan alama ta Ɗan mutum za ta bayyana a sama: sa’annan kuma dukan ƙabilan duniya za su yi baƙin ciki, za su kuwa ga Ɗan mutum yana zuwa a bisa gizagizai na sama tare da iko da ɗaukaka mai-girma. Kuma [Yesu] za ya aika mala’ikunsa da babbar ƙara ta ƙaho, su kuma za su tattara zaɓaɓɓunsa daga ƙusurwoyi huɗu, daga wancan iyakar sama zuwa wannan.’ (Mat. 24:​29-31) ‘Tattara zaɓaɓu’ da za a yi yana nufin lokacin da dukan shafaffun da suka rage a duniya za su sami ladarsu na zuwa sama. Hakan zai faru ne bayan an soma ƙunci mai girma amma kafin yaƙin Armageddon. A lokacin, Yesu da shafaffu 144,000 za su yi yaƙi da sarakunan duniya kuma za su yi nasara a kansu. (R. Yoh. 17:​12-14) Taron Tuna da Mutuwar Yesu da za a yi kafin a tattara shafaffu zuwa sama shi ne zai zama na ƙarshe domin a lokacin, Yesu ya riga ya “zo.”

16. Me ya sa ka kuɗiri aniyar halartan taron tuna da Mutuwar Yesu na wannan shekarar?

16 Bari mu ƙudura niyya cewa za mu halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu a ranar 31 ga Maris, 2018. Ban da haka ma, bari mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu ci gaba da sa a kasance da haɗin kai a ikilisiya! (Karanta Zabura 133:1.) Ka tuna cewa wata rana, za a yi taron Tuna da Mutuwar Yesu na ƙarshe. Kafin lokacin, bari mu yi iya ƙoƙarinmu mu riƙa halartar taron kuma mu riƙa nuna cewa mun daraja wannan haɗin kan da muke samu a lokacin taron tuna da Mutuwar Yesu.