Sabon Memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu
A SAFIYAR ranar Laraba, 24 ga Janairu, 2018, an sanar wa ’yan’uwa da ke hidima a Bethel da ke Amirka da kuma Kanada cewa an naɗa Ɗan’uwa Kenneth Cook Jr., a matsayin memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah.
An haifi Ɗan’uwa Cook a kudancin jihar Pennsylvania da ke Amirka, kuma ya yi girma a wurin. Ya koyi gaskiya daga wani ɗan ajinsu kafin ya sauke karatu daga makarantar sakandare kuma ya yi baftisma a ranar 7 ga Yuni, 1980. Ya soma hidimar majagaba na kullum a ranar 1 ga Satumba, 1982. Kuma bayan ya yi hidimar majagaba na shekara biyu, sai ya soma hidima a Bethel da ke Wallkill a Amirka a ranar 12 ga Oktoba, 1984.
Ɗan’uwa Cook ya yi hidima a sashe dabam-dabam, hakan ya ƙunshi Sashen Buga Littattafai da kuma Sashen da Ke Kula da Ma’aikatan Bethel. Ya auri matarsa Jamie a shekara ta 1996, kuma ta soma hidima tare da shi a Wallkill. Ɗan’uwa Cook da matarsa sun koma Cibiyar Koyarwa da ke Patterson a Amirka a watan Disamba 2009. Ya yi aiki a Sashen Amsa Tambayoyin Masu Karatu a wurin. A watan Afrilu, 2016 bayan ya ɗan koma Bethel da ke Wallkill, Ɗan’uwa Cook da matarsa sun koma Bethel da ke Brooklyn. Bayan watanni biyar sai suka koma hedkwatarmu da ke Warwick a Amirka. Ɗan’uwa Cook ya soma hidima a matsayin mataimakin Kwamitin Rubuce-Rubuce na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah a watan Janairu 2017.