TALIFIN NAZARI NA 3
Ta Yaya Za Ka Iya Kiyaye Zuciyarka?
Ka “kiyaye zuciyarka da dukan iyakacin ƙoƙari.”—K. MAG. 4:23.
WAƘA TA 36 Muna Kāre Zuciyarmu
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1-3. (a) Me ya sa Jehobah ya ƙaunaci Sulemanu, kuma ta yaya ya albarkace shi? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa a wannan talifin?
SULEMANU ya zama sarkin Isra’ila sa’ad da yake matashi. A lokacin da ya fara sarauta, Jehobah ya bayyana masa a mafarki, ya ce masa: “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.” Sai Sulemanu ya ce: “Ni ɗan yaro ne da ban san dama ko hagu ba. . . . Saboda haka, ka ba ni, ni bawanka, zuciya mai hikima.” (1 Sar. 3:5-10) Sulemanu ya ce Allah ya ba shi “zuciya mai hikima.” Babu shakka, shi mai sauƙin kai ne sosai shi ya sa Jehobah ya ƙaunace shi! (2 Sam. 12:24) Jehobah ya yi farin ciki sosai don abin da Sulemanu ya roƙa kuma ya ba shi “zuciya mai hikima da ganewa.”—1 Sar. 3:12.
2 Sulemanu ya sami albarka sosai sa’ad da yake da aminci ga Allah. Ya sami gatan gina haikali “domin a girmama sunan Yahweh Allahn Isra’ila.” (1 Sar. 8:20) Ya zama sananne saboda hikimar da Allah ya ba shi. Kuma abubuwan da Allah ya hure shi ya rubuta suna cikin littattafai uku a Littafi Mai Tsarki. Ɗaya cikinsu shi ne littafin Karin Magana.
3 An ambata kalmar nan zuciya a juyin New World Translation wajen sau ɗari a littafin Karin Magana. Alal misali, Karin Magana 4:23, ya ce: Ka “kiyaye zuciyarka da dukan iyakacin ƙoƙari.” Mene ne “zuciyar” da aka ambata a wannan ayar take nufi? Za mu amsa tambayar a wannan talifin. Ƙari ga haka, za mu amsa tambayoyin nan biyu: Ta yaya Shaiɗan yake nema ya gurɓata zuciyarmu? Kuma mene ne za mu iya yi don mu kiyaye zuciyarmu? Idan muna so mu riƙe aminci ga Allah, muna bukatar mu san amsoshin tambayoyin nan.
MECE CE KALMAR NAN “ZUCIYARKA” TAKE NUFI?
4-5. (a) Ta yaya Zabura 51:6 ta taimaka mana mu fahimci ma’anar kalmar nan zuciya? (b) Wane misali ne ya nuna muhimmancin kiyaye zuciyarmu?
4 Kalmar nan zuciya da ke littafin Karin Magana 4:23 tana nufin abin da ke ciki-cikin zuciyarmu. (Karanta Zabura 51:6.) Zuciya tana kuma nufin tunaninmu da yadda muke ji da kuma muradinmu. Tana nufin abin da ke cikin zuciyarmu, ba abin da mutane suke gani ba, wato siffarmu.
5 Ka yi la’akari da yadda lafiyar jikinmu take nuna abin da ke cikin jikinmu. Da farko, idan muna so mu kasance da ƙoshin lafiya, wajibi ne mu riƙa cin abinci mai kyau kuma mu riƙa motsa jiki a kai a kai. Hakazalika, idan muna so mu kyautata abotarmu da Allah, dole ne mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu a kai a kai kuma mu nuna cewa muna da bangaskiya. Za mu nuna bangaskiyarmu ta wajen aikata abubuwan da muka koya da kuma yin shelar bangaskiyarmu. (Rom. 10:8-10; Yaƙ. 2:26) Na biyu, muna iya ganin jikinmu kuma mu yi tsammani cewa muna da ƙoshin lafiya, alhali cikin jikinmu bai da lafiya. Hakazalika, za mu iya riƙa yin ayyukan ibada kuma hakan zai iya sa mu yi tsammanin cewa muna da bangaskiya sosai, amma zai yiwu cewa muna tunanin banza a cikin zuciyarmu. (1 Kor. 10:12; Yaƙ. 1:14, 15) Wajibi ne mu tuna cewa Shaiɗan yana so mu kasance da irin ra’ayinsa. A wace hanya ce yake yin hakan? Kuma ta yaya za mu iya kāre kanmu?
YADDA SHAIƊAN YAKE NEMA YA GURƁATA ZUCIYARMU
6. Mene ne Shaiɗan yake so ya cim ma, kuma wace dabara ce yake yin amfani da ita?
6 Shaiɗan yana so mu zama ’yan tawaye kamar shi, wato mu daina bin ƙa’idodin Jehobah kuma mu riƙa nuna son kai. Amma ba zai iya tilasta mana mu yi koyi da shi ba. Saboda haka, yana yin amfani da wasu dabaru don ya cim ma burinsa. Alal misali, ya kewaye mu da mutanen da ya riga ya yaudara. (1 Yoh. 5:19) Yana so mu riƙa yin cuɗanya da su duk da yake mun san cewa “zama da mugaye yakan ɓata halayen kirki.” (1 Kor. 15:33) Abin da ya yi wa Sarki Sulemanu ke nan kuma ya yi nasara. Sulemanu ya auri mata da yawa da ba sa bauta wa Jehobah. A hankali, matan suka rinjaye shi kuma “suka juya masa zuciya” daga bin Jehobah.—1 Sar. 11:3.
7. Wane abu ne kuma Shaiɗan yake yin amfani da shi wajen fifita ra’ayinsa, kuma me ya sa ya kamata mu yi hattara?
7 Shaiɗan yana yin amfani da fina-finai da kuma shirye-shiryen talabijin wajen fifita ra’ayinsa. Ya san cewa labarai suna iya rinjayar tunaninmu da yadda muke ji da kuma ayyukanmu. Yesu ya yi amfani da wannan dabarar a koyarwarsa. Alal misali, ya ba da labarin wani Basamaren da ɓarayi suka kusan kashe shi da kuma na wani ɗa mubazzari. (Mat. 13:34; Luk. 10:29-37; 15:11-32) Amma mutanen da Shaiɗan ya riga ya ɓata za su iya yin amfani da labarai wajen ɓata mu. Gaskiya ne cewa za mu iya jin daɗin kallon fina-finai da shirye-shiryen talabijin kuma za su iya ilimantar da mu ba tare da sun ɓata tunaninmu ba. Amma ya kamata mu yi hankali. Sa’ad da muke zaɓan nishaɗin da za mu yi, ya kamata mu yi wa kanmu tambayar nan, ‘Shin wannan fim ko shirye-shiryen talabijin yana koya mini cewa yin lalata ba laifi ba ne?’ (Gal. 5:19-21; Afis. 2:1-3) Me ya kamata ka yi idan ka lura cewa ana fifita ra’ayin Shaiɗan a fim da kake kallo? Ka guje shi yadda za ka guje wa annoba!
8. Ta yaya iyaye za su iya taimaka wa yaransu su kāre zuciyarsu?
8 Iyaye, ya kamata ku yi tsayin daka wajen tabbatar da cewa kun kāre yaranku daga ra’ayin Shaiɗan. Babu shakka, kuna yin iya ƙoƙarinku wajen kāre yaranku daga kamuwa da cuta. Kuna tsabtace gidanku kuma kuna jefar da duk abin da kuka san cewa zai iya sa yaranku kamuwa da cuta. Hakazalika, ya kamata ku kāre yaranku daga fina-finai da shirye-shiryen talabijin K. Mag. 1:8; Afis. 6:1, 4) Saboda haka, kada ku yi jinkirin kafa dokokin da za su kāre iyalinku. Ku gaya wa yaranku fina-finan da za su iya kalla, kuma ku gaya musu dalilan hakan. (Mat. 5:37) Yayin da suke girma, ku taimaka musu su yi amfani da ƙa’idodin Jehobah wajen zaɓan abin da ya dace da kuma ƙin wanda bai dace ba. (Ibran. 5:14) Ku tuna cewa yaranku za su fi yin koyi da misalinku.—M. Sha. 6:6, 7; Rom. 2:21.
da wasannin bidiyo da kuma dandalin Intane da za su iya cusa musu ra’ayin Shaiɗan. Jehobah ya ba ku hakkin taimaka wa yaranku su ƙulla abota da shi. (9. Wane ra’ayi ne Shaiɗan yake fifitawa, kuma me ya sa yake da haɗari sosai?
9 Shaiɗan yana kuma neman ya ɓata mu ta wajen sa mu bi ra’ayin ’yan Adam, maimakon na Jehobah. (Kol. 2:8) Alal misali, yana sa mutane su gaskata cewa biɗan kayan duniya shi ne abu mafi muhimmanci a rayuwa. Mutanen da ke da wannan ra’ayin suna iya yin wadata ko kuma a’a. Wannan ra’ayin ba shi da kyau. Me ya sa? Domin suna iya mai da hankali ga yin wadata har su sadaukar da lafiyarsu da iyalinsu da kuma dangantakarsu da Allah don su cim ma burinsu. (1 Tim. 6:10) Muna farin ciki sosai cewa Jehobah yana taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi.—M. Wa. 7:12; Luk. 12:15.
TA YAYA ZA MU IYA KIYAYE ZUCIYARMU?
10-11. (a) Me ya kamata mu yi don mu kāre kanmu? (b) Mene ne masu-tsaro suke yi a zamanin dā, kuma ta yaya lamirinmu zai iya zama kamar mai-tsaro?
10 Idan muna so mu yi nasara wajen kiyaye zuciyarmu, wajibi ne mu san abubuwan da za su jawo mana haɗari kuma mu ɗauki mataki nan da nan don mu kāre kanmu. Kalmar nan “kiyaye” a littafin Karin Magana 4:23 ta tuna mana da aikin da mai-tsaro yake yi. A zamanin Sarki Sulemanu, masu gadi suna tsayawa a ganuwar birni kuma idan suka hango maƙiya suna zuwa, suna sanar da mazaunan birnin. Wannan kwatancin ya taimaka mana mu san abin da muke bukatar mu yi don mu hana Shaiɗan ɓata tunaninmu.
11 A zamanin dā, masu-tsaro suna aiki tare da masu kula da ƙofar birnin. (2 Sam. 18:24-26) Suna aiki tare wajen tabbatar da cewa an rufe ƙofar birnin a duk lokacin da maƙiya suka zo. (Neh. 7:1-3) Lamiri mai kyau * zai iya faɗakar da mu kamar wannan mai-tsaron a duk lokacin da Shaiɗan yake neman ya ɓata tunaninmu da muradinmu da sha’awoyinmu da kuma yadda muke ji. A duk lokacin da lamirinmu ya faɗakar da mu, ya kamata mu saurare shi kuma mu rufe zuciyarmu yadda ake rufe ƙofar birni.
12-13. Mene ne za a iya jarraba mu mu yi, kuma mene ne za mu yi?
12 Ka yi la’akari da wani misalin da zai iya taimaka mana mu kāre kanmu don kada Shaiɗan ya rinjaye mu. Jehobah ya gaya mana cewa ‘kada ma a ko ambaci iskanci da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninmu.’ (Afis. 5:3) Amma mene ne za mu yi idan yara a makaranta ko kuma mutane a wurin aiki suka soma yin maganganun banza? Ya kamata mu guji “rayuwa marar halin Allah, da sha’awace-sha’awacen duniya.” (Tit. 2:12) Kuma lamirinmu wato mai-tsaro, zai iya yi mana kashedi. (Rom. 2:15) Amma za mu saurari kashedin kuwa? Zuciyarmu na iya rinjayar mu mu saurare su ko kuma mu kalli hotunan da suke kallo. Amma muna bukatar mu guji yin hakan ta wajen canja batun ko kuma ficewa daga wurin.
13 Muna bukatar gaba gaɗi don mu iya guje wa matsi daga abokanmu na yin tunani ko kuma yin abubuwa yadda suke yi. Mu kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ganin ƙoƙarin da muke yi kuma zai ba mu ƙarfin yin tsayayya da Shaiɗan. (2 Tar. 16:9; Isha. 40:29; Yaƙ. 1:5) Ta yaya za mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu kāre zuciyarmu?
KU KASANCE A FAƊAKE
14-15. (a) Mene ne ya kamata mu riƙa tunani a kai, kuma ta yaya za mu yi hakan? (b) Ta yaya Karin Magana 4:20-22 zai taimaka mana mu amfana daga karatun Littafi Mai Tsarki? (Ka duba akwatin nan “ Yadda Za Mu Riƙa Yin Bimbini.”)
14 Muna bukatar mu guji tunanin banza idan muna so mu kāre zuciyarmu, amma muna bukatar mu riƙa yin tunanin da ya dace. Ka sake yin tunanin a kan birnin da ke da ganuwa. Mai gadi yana rufe ƙofar birnin don kada maƙiya su kawo musu hari, amma a wasu lokuta, yana buɗe ƙofar birnin domin a kawo musu abinci da kuma wasu abubuwa. Idan ba a buɗe ƙofar birnin ba, mazaunan birnin za su mutu domin rashin abinci. Hakazalika, muna bukatar mu riƙa buɗe zuciyarmu don mu kasance da ra’ayin Jehobah.
15 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ra’ayin Jehobah. Don haka, a duk lokacin da muka karanta shi, muna barin ra’ayin Jehobah ya shafi yadda muke tunani da kuma yadda muke yin abubuwa. Ta yaya za mu amfana daga karanta Littafi Mai Tsarki? Yin addu’a yana da muhimmanci sosai. Wata ’yar’uwa ta ce: “Kafin in soma karanta Littafi Mai Tsarki, ina addu’a ga Jehobah kuma na roƙe shi ya taimaka mini na ga ‘abubuwa masu ban mamaki’ da ke cikin Kalmarsa.” (Zab. 119:18) Ƙari ga haka, muna bukatar mu riƙa yin bimbini a kan abin da muka karanta. Idan muka yi addu’a da karatu da kuma bimbini, hakan zai sa Kalmar Allah ta kasance a ‘cikin zuciyarmu.’—Karanta Karin Magana 4:20-22; Zab. 119:97.
16. Ta yaya mutane da yawa suka amfana daga kallon shirye-shiryen tashar JW?
16 Wata hanya kuma da za mu iya barin ra’ayin Allah ya shafe mu ita ce ta wajen kallon shirye-shiryen da ke Tashar JW®. Wasu ma’aurata sun ce: “Jehobah ya amsa addu’armu ta wajen tanadar mana da wannan tashar!” Shirye-shiryen suna ƙarfafa mu a duk lokacin da muka karaya ko kuma muka kaɗaita. Ban da haka ma, muna yawan saka waƙoƙin shirye-shiryen a gidanmu. Muna sauraron su sa’ad da muke dafa abinci ko share-share ko kuma sa’ad da muke hutawa.” Waɗannan shirye-shiryen suna taimaka mana mu kiyaye zuciyarmu. Ƙari ga haka, suna koya mana ra’ayin Jehobah kuma suna taimaka mana mu guji ra’ayin Shaiɗan.
17-18. (a) Mene ne zai faru idan muka yi amfani da abubuwan da Jehobah ke koya mana, kamar yadda 1 Sar. 8:61 ya nuna? (b) Mene ne za mu iya koya daga labarin Sarki Hezekiya? (c) Kamar yadda Zabura 139:23, 24 ta nuna, mene ne za mu iya yin addu’a a kai?
17 A duk lokacin da muka ga yadda mutane ke amfana domin suna yin abin da ya dace, hakan yana daɗa ƙarfafa bangaskiyarmu. (Yaƙ. 1:2, 3) Ƙari ga haka, muna murna domin mun sa Jehobah farin ciki kuma yana alfahari da mu, hakan yana sa mu so yin abubuwan da ke faranta masa rai. (K. Mag. 27:11) Kowace jarrabawa da muka fuskanta, tana ba mu damar nuna cewa muna so mu bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya. (Zab. 119:113) Za mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarmu kuma muna a shirye mu bi dokokinsa kuma mu yi nufinsa.—Karanta 1 Sarakuna 8:61.
18 Za mu iya yin kuskure kuwa? E, domin mu ajizai ne. Amma idan muka yi kuskure, mu tuna misalin Sarki Hezekiya. Ya yi kuskure, amma ya tuba kuma ya ci gaba da bauta wa Jehobah da ‘dukan zuciyarsa.’ (Isha. 38:3-6; 2 Tar. 29:1, 2; 32:25, 26) Bari mu yi iya ƙoƙarinmu don kada mu kasance da ra’ayin Shaiɗan. Mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu kasance da “zuciya mai hikima.” (1 Sar. 3:9; karanta Zabura 139:23, 24.) Za mu iya kasancewa da aminci ga Jehobah idan muka kiyaye zuciyarmu fiye da kowane abu.
WAƘA TA 54 ‘Wannan Ita Ce Hanyar Rai’
^ sakin layi na 5 Za mu riƙe aminci ga Jehobah kuwa ko za mu yarda Shaiɗan ya yaudare mu? Amsar tambayar nan ba ta dangana ga irin jarrabawar da muke fuskanta ba, amma ta dangana da yadda muke kiyaye zuciyarmu. Mene ne kalmar nan “zuciya” take nufi? Ta yaya Shaiɗan yake nema ya gurɓata zuciyarmu? Kuma ta yaya za mu iya kiyaye ta? Za a amsa tambayoyin nan a wannan talifin.
^ sakin layi na 11 MA’ANAR WASU KALMOMI: Jehobah ya ba mu zarafin bincika tunaninmu da yadda muke ji da kuma ayyukanmu kuma mu hukunta kanmu. A Littafi Mai Tsarki, ana kiransa lamiri. (Rom. 2:15; 9:1) Lamiri mai kyau yana sa mutum ya yi amfani da ƙa’idodin Jehobah da ke Littafi Mai Tsarki don ya yanke shawara ko abin na da kyau ko a’a.
^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa yana kallon talabijin sai aka soma nuna batsa. Yana bukatar ya tsai da shawarar abin da zai yi.
^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTUNA: Mai-tsaro a zamanin dā ya hango maƙiya. Sai ya sanar da masu kula da ƙofar birnin, su kuma suka ɗauki mataki nan da nan ta wajen rufe ƙofar birnin.