Iyaye, Kuna Taimaka wa Yaranku Su Yi Baftisma?
“Don me kake jinkiri? Ka tashi, a yi maka baftisma.”—A. M. 22:16.
1. Mene ne iyaye Kiristoci suke so su tabbatar kafin yaransu su yi baftisma?
WATA mai suna Blossom Brandt ta bayyana abin da ya faru kafin ta yi baftisma. Ta ce: “Na yi watanni da yawa ina damun mahaifina da mahaifiyata cewa ina so in yi baftisma. Amma suna so su tabbatar da cewa na san abin da yin baftisma yake nufi. A ranar 31 ga Disamba, 1934, na shaida wannan rana mai muhimmanci a rayuwata.” A yau, iyaye Kiristoci suna so su taimaka wa yaransu su yanke shawara mai kyau. Ɗage ranar yin baftisma ko kuma jinkirta yin baftisma ba gaira ba dalili na iya ɓata dangantakar yara da Jehobah. (Yaƙ. 4:17) Duk da haka, iyaye suna so su tabbatar da cewa kafin yaransu su yi baftisma, sun shirya su zama mabiyan Kristi.
2. (a) Wace matsala ce wasu masu kula da da’ira suka lura da ita? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
2 Wasu masu kula da da’ira sun lura cewa matasa da yawa da ba su kai shekara 20 ba, har da wasu kuma da suka wuce shekara 20 waɗanda iyayensu Shaidu ne ba su yi baftisma ba tukun. A yawancin lokuta, waɗannan matasan suna halartan taro kuma suna yin wa’azi. Ƙari ga haka, suna ɗaukan kansu
a matsayin Shaidun Jehobah. Amma saboda wasu dalilai, waɗannan matasan sun ƙi yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma. Mene ne yake jawo hakan? A wasu lokuta, iyayen waɗannan matasan ne suke ƙarfafa su cewa su ɗan jinkirta yin baftisma. Shi ya sa a wannan talifin, za mu tattauna abubuwa huɗu da suke hana iyaye Kiristoci taimaka wa yaransu su yi baftisma.ƊANA YA ISA YIN BAFTISMA KUWA?
3. Mene ne ya sa iyayen Blossom Brandt suka damu?
3 Iyayen Blossom Brandt da muka ambata a sakin layi na ɗaya sun damu sa’ad da ’yarsu take so ta yi baftisma. Sun yi haka ne domin ba su san ko ’yarsu ta fahimci abin da yin baftisma yake nufi ba. Ta yaya iyaye za su iya sani ko yaransu sun isa yin baftisma?
4. Ta yaya umurnin Yesu da ke Matta 28:19, 20 zai taimaka wa iyaye su koyar da yaransu?
4 Karanta Matta 28:19, 20. Kamar yadda muka ambata a talifi na farko, Littafi Mai Tsarki bai faɗi shekarun da mutum zai kai kafin ya yi baftisma ba. Amma ya kamata iyaye su yi tunani a kan abin da furucin nan ‘almajirtarwa’ yake nufi. A Helenanci, kalmar nan “ku almajirtar” da ke littafin Matta 28:19 tana nufin koyar da mutum domin ya zama ɗalibi ko kuma almajiri. Almajiri mutumi ne da ya yi nazarin koyarwar Yesu, ya san koyarwar sosai kuma yana a shirye ya bi su. Saboda haka, ya kamata dukan iyaye Kiristoci su kafa maƙasudin koyar da yaransu tun suna ƙanana su zama almajiran Yesu ta wajen yin baftisma. Ko da yake jarirai ba za su iya yin baftisma ba. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ƙananan yara za su iya fahimtar gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma su yi abin da suka koya.
5, 6. (a) Mene ne yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Timotawus ya nuna game da lokacin da ya yi baftisma? (b) Ta yaya iyaye masu basira za su taimaka wa yaransu?
5 Timotawus almajiri ne da ya san gaskiya tun yana ƙarami. Manzo Bulus ya ce Timotawus ya koyi gaskiyar da ke cikin Nassosi tun yana jariri. Ko da yake mahaifin Timotawus ba Kirista ba ne, amma mahaifiyarsa Afiniki wadda Bayahudiya ce da kuma kakarsa Loyis, sun taimaka masa ya san gaskiya. A sakamakon haka, Timotawus ya zama mai bangaskiya sosai. (2 Tim. 1:5; 3:14, 15) A lokacin da Timotawus ya kusan shekara 20 ko kuma ya ɗan fi shekara 20, ya cancanci samun gatan yin wasu ayyuka a cikin ikilisiya.—A. M. 16:1-3.
6 Babu shakka, kowane yaro yana da irin nasa baiwa. Wasu suna saurin girma da kuma manyanta. Wasu yara suna saurin fahimtar gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma su yanke shawarar yin baftisma. Wasu kuma ba sa saurin yanke shawarar yin baftisma har sai sun yi girma. Saboda haka, iyaye masu basira ba sa tilasta wa yaransu su yi baftisma. A maimakon haka, suna taimaka wa yaran su fahimci gaskiya sosai dangane da shekarunsu. Iyaye za su yi farin ciki idan yaransu sun bi shawarar da ke cikin littafin Misalai 27:11. (Karanta.) Amma duk da haka, ya kamata su riƙa tuna cewa maƙasudinsu shi ne taimaka wa yaransu su zama almajiran Kristi. Hakan zai sa iyaye su yi wa kansu waɗannan tambayoyin, ‘Yarona ya san gaskiya sosai da har zai yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ya yi baftisma kuwa?’
SHIN ƊANA YA SAN GASKIYA SOSAI KUWA?
7. Shin ɗalibi yana bukatar ya san kome da kome kafin ya yi baftisma? Ka bayyana.
7 Yayin da iyaye suke koyar da yaransu, ya kamata su ƙoƙarta don yaran su san gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki sosai don su yanke shawarar yin baftisma. Amma hakan ba ya nufin cewa suna bukatar su san kome da kome da ke cikin Littafi Mai Tsarki kafin su yi baftisma. Wajibi ne kowane almajirin Yesu ya ci gaba da koyo game da Allah bayan ya yi baftisma. (Karanta Kolosiyawa 1:9, 10.) Saboda haka, me ya kamata ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya sani kafin ya yi baftisma?
8, 9. Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Bulus da kuma mai tsaron kurkuku?
8 Labarin wata iyali a ƙarni na farko zai iya taimaka wa iyaye a yau. (A. M. 16:25-33) Manzo Bulus ya je birnin Filibi sa’ad da ya je wa’azi a ƙasashen waje a ƙaro na biyu a wajen shekara ta 50. Da suke wurin, sai aka yi wa Bulus da abokinsa Sila sharri kuma aka jefa su cikin kurkuku. Da dare ya yi, sai girgizar ƙasa ta auku kuma ƙofar kurkukun ta buɗe. Sa’ad da mai tsaron kurkukun ya tashi ya ga ƙofar a buɗe, ya so ya kashe kansa domin yana tunanin cewa fursunonin sun gudu. Amma Bulus ya hana shi kashe kansa. Bayan haka, Bulus da Sila suka yi wa mai tsaron kurkukun da iyalinsa wa’azi game da Yesu. Sun gaskata da abin da suka koya kuma hakan ya motsa su su yi baftisma ba tare da ɓata lokaci ba. Wane darasi ne za mu iya koya daga wannan labarin?
9 Wataƙila wannan mutumin da ke tsaron kurkuku sojan Roma ne da ya yi ritaya. Bai san abubuwan da ke cikin Kalmar Allah ba. Saboda haka, kafin ya san gaskiya game da Allah, wajibi ne ya san dokokin Allah, ya san abin da zama bawan Allah yake nufi kuma ya ƙuduri niyyar bin koyarwar Yesu. Abubuwan da mai tsaron kurkukun ya koya a wannan ɗan ƙanƙanin lokaci ya taimaka masa ya yanke shawarar yin baftisma. Babu shakka, ya ci gaba da yin nazari game da Allah bayan ya yi baftisma. Ta yaya wannan misalin zai taimaka wa iyaye sa’ad da yaransu suka ce suna so su yi baftisma domin sun fahimci gaskiyar da suke koya daga Littafi Mai Tsarki? Za ku iya gaya musu cewa su tuntuɓi dattawa a ikilisiya don su san ko sun cancanci yin baftisma. * Hakika, yaran suna kamar wasu mutane da suka yi baftisma domin za su riƙa koyo game da Jehobah muddar ransa kuma za su ci gaba da yin hakan har abada.—Rom. 11:33, 34.
YARONA YANA KOYAN ABIN DA ZAI AMFANA SHI KUWA?
10, 11. (a) Mene ne wasu iyaye suke tunani? (b) Mene ne zai fi taimaka wa yara?
10 Wasu iyaye suna ganin cewa zai fi dacewa yaronsu ya sauke karatu kuma ya sami aiki mai kyau kafin ya yi baftisma. Wataƙila iyayen suna da dalilai masu kyau na yin wannan tunanin, amma ya kamata su tambayi kansu: ‘Shin hakan zai taimaka wa yarona ya yi nasara? Hakan ya jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuwa? Yaya Jehobah yake so mu yi amfani da rayuwarmu?’—Karanta Mai-Wa’azi 12:1.
11 Ya kamata mu tuna cewa muguwar Yaƙ. 4:7, 8; 1 Yoh. 2:15-17; 5:19) Kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah ne zai taimaka wa yaranku su kāre kansu daga Shaiɗan da muguwar duniyarsa da kuma ra’ayoyinta. Idan iyaye suka ce yaransu su kammala makaranta kuma su sami aiki mai kyau kafin su yi baftisma, hakan zai sa su yi tunanin cewa waɗannan abubuwan ne suka fi muhimmanci a rayuwa. Babu shakka, iyaye ba za su so duniyar nan ta rinjayi yaransu ba. Saka hidimar Jehobah a kan gaba a rayuwarmu ne kaɗai zai sa mu yi nasara sosai.—Karanta Zabura 1:2, 3.
duniyar nan da dukan ayyukanta ba su jitu da abin da Jehobah yake so da kuma tunani ba. (IDAN ƊANA YA YI ZUNUBI KUMA FA?
12. Me ya sa wasu iyaye ba sa barin yaransu su yi baftisma da sauri?
12 Wata ’yar’uwa ta faɗi dalilin da ya sa ba ta yarda ’yarta ta yi baftisma ba. Ta ce, “Ina kunyar faɗin cewa ban yarda ’yata ta yi baftisma ba domin ba na so a yi mata yankan zumunci.” Wasu iyaye ma suna tunanin cewa zai fi dacewa su hana yaransu yin baftisma har sai sun yi wayo sosai. (Far. 8:21; Mis. 22:15) Suna iya ganin cewa idan yaransu ba su yi baftisma ba, ba za a iya yi musu yankan zumunci ba. Amma me ya sa irin wannan tunanin bai dace ba?—Yaƙ. 1:22.
13. Shin ƙin yin baftisma yana kāre mutum daga ɗaukan nauyin laifofinsa? Ka bayyana.
13 Gaskiya ne cewa iyaye Kiristoci ba za su so yaransu su yi baftisma idan yaran ba su fahimci muhimmancin yin baftisma ba. Amma, bai kamata mu yi tunanin cewa idan yaro bai yi baftisma ba, ba zai ɗauki nauyin laifofinsa ba. Me ya sa? Domin mutum zai ɗauki nauyin laifofinsa ko da bai yi baftisma ba. Da zarar yaro ya san bambanci tsakanin abu mai kyau da marar kyau, to zai ɗauki nauyin laifofinsa. (Karanta Yaƙub 4:17.) Saboda haka, iyaye masu basira ba sa hana yaransu yin baftisma. Maimakon haka, suna kafa musu misali mai kyau. Suna koya musu su so dokokin Jehobah kuma su tsani abubuwan da Jehobah ba ya so tun suna ƙanana. (Luk. 6:40) Hakan zai sa yaron ya guji yin abin da bai dace ba domin yana ƙaunar Jehobah sosai.—Isha. 35:8.
WASU ZA SU IYA TAIMAKA
14. Ta yaya dattawa za su iya tallafa wa iyaye yayin da suke ƙoƙarin taimaka wa yaransu?
14 Dattawa za su iya tallafa wa iyaye yayin da suke ƙoƙarin taimaka wa yaransu. Za su iya yin hakan ta wajen ƙarfafa su su kafa maƙasudai a hidimar Jehobah. Wata ’yar’uwa ta tuna tattaunawar da ita da Ɗan’uwa Russell suka yi sa’ad da take ’yar shekara 6. Ta ce: “Ya ɗau minti 15 don ya tattauna da ni game da maƙasudaina a hidimar Jehobah.” A sakamakon haka, ta soma hidimar majagaba kuma ta yi sama da shekaru 70 tana hidimar. Babu shakka, ƙarfafawa tana shafan rayuwar mutane sosai. (Mis. 25:11) Dattawa za su kuma iya ba iyaye da yaransu ayyuka a Majami’ar Mulki. Za su iya ba yaran ayyukan da za su iya yi dangane da shekarunsu.
15. A waɗanne hanyoyi ne wasu a cikin ikilisiya za su iya ƙarfafa yara da matasa?
15 Sauran ’yan’uwa a ikilisiya ma za su iya taimaka ta wajen nuna cewa sun damu da yara da kuma matasa. Za ku iya lura cewa wani yaro a cikin ikilisiya yana ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah. Alal misali, wataƙila ya yi kalamai masu ban ƙarfafa a taro ko kuma ya yi aiki a taron Zab. 35:18.
tsakiyar mako. Ko ya fuskanci jarrabawa amma ya magance su. Ko ya yi wa’azi a makaranta sa’ad da ya sami zarafin yin hakan. Idan kun lura da haka, kada ku yi jinkirin yaba musu! Zai dace mu riƙa tattaunawa da yara da kuma matasa kafin a soma taro da kuma bayan an idar da taron. Idan muna yin hakan, yara za su ji cewa su ma suna cikin “babbar” ikilisiya.—KA TAIMAKA WA YARANKA SU YI BAFTISMA
16, 17. (a) Me ya sa yake da muhimmanci yara su yi baftisma? (b) Me ke sa iyaye Kiristoci farin ciki? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.)
16 Koya wa yara su riƙa ƙaunar Jehobah ɗaya ne cikin gata mafi girma da iyaye Kiristoci suke da ita. (Afis. 6:4; Zab. 127:3) A zamanin dā, Jehobah ya zaɓi Isra’ilawa a matsayin mutanensa. Saboda haka, duk yaron da aka haifa zaɓaɓɓe ne. Amma ba haka yake da yaranmu a yau ba. Yin ƙaunar Allah da kuma sanin gaskiya ba abu ne da yara suke gāda daga iyayensu ba. Daga ranar da aka haifi yara, wajibi ne iyayensu su taimaka musu su zama almajiran Yesu. Wannan ne abu mafi muhimmanci. Domin yin alkawarin bauta wa Allah da yin baftisma da kuma riƙe aminci ne zai taimaka wa mutum ya tsira a lokacin ƙunci mai girma.—Mat. 24:13.
17 Sa’ad da Blossom Brandt da muka ambata a sakin layi na ɗaya ta yanke shawarar yin baftisma, iyayenta sun so su tabbatar da cewa ta san ma’anar yin baftisma. Da suka tabbatar da haka, sun goyi bayan ta. Saboda haka, a dare na ƙarshe kafin ta yi baftisma, mahaifinta ya yi wani abu mai ban sha’awa. Blossom ta ce: “Mahaifina ya ce dukanmu mu durƙusa, sai ya yi addu’a. Ya gaya wa Jehobah cewa yana murna sosai cewa ’yarsa ta yanke shawarar bauta masa!” Bayan sama da shekara 60 yanzu, Blossom ta ce ba za ta taɓa mantawa da abin da ya faru a daren nan ba. Muna fatan cewa dukanku iyaye za ku yi farin cikin ganin yaranku sun yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma sun yi baftisma.
^ sakin layi na 9 Iyaye za su iya tattauna bayanan da ke talifin nan mai jigo: Yara da Matasa, Ta Yaya Za Ku Yi Shirin Yin Baftisma? A shafuffuka na 12-17 na Hasumiyar Tsaro ta Maris, 2016. Ku kuma duba “Tambayoyin Masu Shela” a Hidimarmu ta Mulki ta Afrilu 2011, shafi na 2.