‘Ku Ji Horarwa Don Ku Zama Masu Hikima’
“’Ya’yana, . . . ku ji horarwata, ku zama masu hikima.”—MIS. 8:32, 33, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.
1. Me zai taimaka mana mu zama masu hikima, kuma wane sakamako za mu samu?
JEHOBAH, Allah ne mafi hikima kuma yana sa mu zama masu hikima. Littafin Yaƙub 1:5 ya ce: “Idan kowane a cikinku ya rasa hikima, bari ya yi roƙo ga Allah, wanda yake bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma.” Abu ɗaya da zai taimaka mana mu zama masu hikima shi ne amincewa da horon Jehobah. Kasancewa da hikima zai taimaka mana mu guji yin abubuwan da za su ɓata wa Jehobah rai kuma hakan na sa mu ci gaba da kusantar sa. (Mis. 2:10-12) Yin hakan zai sa mu ‘tsare kanmu cikin ƙaunar Allah, . . . zuwa rai na har abada.’—Yahu. 21.
2. Me zai taimaka mana mu so horon Allah?
2 Yana mana wuya a wasu lokuta mu amince da horo, wataƙila don ajizancinmu ko kuma yadda aka yi renon mu. Amma ganin amfanin horarwar Allah a rayuwarmu yana sa mu ga cewa yana ƙaunar mu sosai. Shi ya sa littafin Misalai 3:11, 12 ya ce: “Ɗana kada ka rena koyarwar Ubangiji . . . gama wanda Ubangiji yake ƙauna shi yake tsauta wa.” Babu shakka, ya kamata mu riƙa tuna cewa Jehobah yana ƙaunar mu sosai. (Karanta Ibraniyawa 12:5-11.) Horarwar da yake mana tana dacewa sosai da mu kuma ba ta wuce kima domin ya san mu da kyau. Yanzu, bari mu tattauna fasaloli huɗu na horo: (1) horar da kanmu, (2) horarwar da iyaye suke wa ’ya’yansu, (3) horarwa a cikin ikilisiya, da kuma (4) mummunan sakamakon ƙin amincewa da horo.
HORAR DA KANMU ZAI TAIMAKA MANA
3. Ta yaya yara suke koyon horar da kansu? Ka ba da misali.
3 Idan muna horar da kanmu, za mu iya kiyaye tunaninmu da ayyukanmu. Ba a haife mu da wannan halin ba amma za mu iya koyon sa. Alal misali: Idan yaro ya soma koyon tuƙa keke, iyayensa suna yawan riƙe masa keken. Da zarar ya fara iya keken, sai su riƙa sakin sa a wasu lokuta. Amma idan ya iya sosai, sai su daina riƙe masa keken. Hakazalika, idan iyaye suka ci gaba da koyar da yaransu cikin “horon Ubangiji da gargaɗinsa,” suna koya musu su riƙa horar da kansu kuma su zama masu hikima.—Afis. 6:4.
4, 5. (a) Me ya sa horar da kanmu yake da muhimmanci sosai idan muna so mu koyi nuna “sabon” hali? (b) Me ya sa bai kamata mu yi sanyin gwiwa ba idan muka yi kuskure?
4 Haka ma yake da mutanen da suka koyi gaskiya bayan sun yi girma. Ko da yake wataƙila sun riga sun horar da kansu, amma ba su manyanta ba a bautar su ga Jehobah. Idan suka soma “yafa sabon” hali, kuma suka kasance da halayen Kristi, za su manyanta sosai. (Afis. 4:23, 24) Horar da kanmu yana taimaka mana mu “ƙi rashin bin Allah da mugayen sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi zamanmu a duniyan nan da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah.”—Tit. 2:12, Littafi Mai Tsarki.
5 Amma dukanmu ajizai ne. (M. Wa. 7:20) Saboda haka, idan muka yi kuskure, kada mu ga kamar ba mu iya horar da kanmu ba. Littafin Misalai 24:16 ya ce: “Mai-adalci yakan fāɗi sau bakwai, ya sake tashi kuma.” Mene ne zai taimaka mana mu sake tashi idan muka yi kuskure? Ruhun Allah ne zai taimaka mana, ba ƙarfinmu ba. (Karanta 2 Korintiyawa 4:7.) Kamewa na cikin ’yar ruhun Allah, kuma wannan halin kusan ɗaya ne da horar da kai.
6. Me zai taimaka mana mu kyautata yadda muke nazarin Kalmar Allah? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.)
6 Yin addu’a da nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini za su taimaka mana mu horar da kanmu. Amma idan yana mana wuya mu yi nazarin Kalmar Allah ko kuma ba ma jin daɗin yin nazari kuma fa? Ka san cewa Jehobah zai taimaka maka idan ba ka karaya ba. Zai sa ka “yi marmarin” Kalmarsa. (1 Bit. 2:2) Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka riƙa yin nazarin Kalmarsa. Bayan haka, ka ɗauki mataki ta wajen yin nazari ƙila na ’yan mintoci. Da shigewar lokaci, yin nazari zai yi maka sauƙi kuma za ka jin daɗin lokacin da kake keɓewa don yin bimbini a kan Kalmar Jehobah.—1 Tim. 4:15.
7. Ta yaya horar da kanmu zai taimaka mana mu cim ma maƙasudanmu a hidimar Jehobah?
7 Horar da kanmu zai taimaka mana mu cim ma maƙasudanmu a hidimar Jehobah. Alal misali, akwai wani mahaifi da ya lura cewa ya soma sanyi a hidimarsa. Sai ya kafa maƙasudi cewa zai zama majagaba na kullum. Bayan haka, sai ya soma karanta talifofi game da hidimar majagaba kuma ya yi addu’a a kan batun. Hakan ya ƙarfafa shi kuma ya farfaɗo da ƙwazonsa. Yakan yi hidimar majagaba na ɗan lokaci sa’ad da ya sami zarafi. Wane sakamako ne ya
samu? Duk da ƙalubalen da ya fuskanta, ya ci gaba da biɗan maƙasudinsa a hidimar Jehobah har ya zama majagaba na kullum.KU RIƘA KOYAR DA YARANKU GAME DA JEHOBAH
8-10. Mene ne zai taimaka wa iyaye su yi nasara sa’ad da suke renon yaransu? Ka ba da misali.
8 Iyaye Kiristoci suna da gata na musamman, wato gatan koya wa yaransu “horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afis. 6:4) Hakan ba ƙaramin aiki ba ne musamman a wannan mugun zamanin. (2 Tim. 3:1-5) Yara ba sa sanin bambanci tsakanin abu mai kyau da marar kyau sa’ad da aka haife su don ba a horar da lamirinsu ba. Suna bukatar a koya musu hakan. (Rom. 2:14, 15) Wani manazarcin Littafi Mai Tsarki Bahelane ya ce furucin nan “horo” yana iya nufin “rayar da yara.”
9 Idan iyaye suka horar da yaransu yadda ya dace, yaran za su san cewa iyayensu suna ƙaunar su. Yaran za su san cewa akwai abubuwan da bai kamata su yi ba, kuma kome da suka yi yana da sakamako. Saboda haka, yana da muhimmanci iyaye su bi ja-gorancin Jehobah sa’ad da suke horar da yaransu. Ya kamata su riƙa tuna cewa yadda ake koyar da yara ya dangana da inda suke zama kuma koyarwar tana canjawa a kai a kai. Amma, idan iyaye suka nemi taimakon Allah, za su san yadda ya kamata su horar da yaransu.
10 Alal misali, Nuhu bai san yadda ake gina jirgi ba sa’ad da Jehobah ya gaya masa ya yi hakan. Amma ya dogara ga Allah kuma ya bi umurnin da aka ba shi. (Far. 6:22) Hakan ya sa Nuhu ya ceci ransa da na iyalinsa. Ƙari ga haka, ya yi nasara sa’ad da yake renon yaransa domin ya dogara ga Allah. Nuhu ya koyar da yaransa da kyau kuma ya kafa musu misali mai kyau ko da yake hakan bai da sauƙi a zamaninsa.—Far. 6:5.
11. Me ya sa yake da muhimmanci iyaye su yi iya ƙoƙarinsu su koyar da yaransu?
11 Ta yaya iyaye za su yi nasara wajen renon yaransu? Ya kamata ku bi umurnin Jehobah don ya yi amfani da Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa wajen koya muku yin hakan. Da shigewar lokaci, yaranku za su gode muku don yadda kuka rene su! Wani ɗan’uwa ya ce: “Ina godiya ga iyayena don yadda suka rene ni. Sun yi iya ƙoƙarinsu don su ratsa zuciyata. Iyayena ne suka taimaka mini in sami ci gaba a bautata ga Jehobah.” Hakika, wasu yara sukan daina bauta wa Jehobah duk da ƙoƙarin da iyayensu suka yi don su koyar da su. Duk da haka, iyayen da suka yi iya ƙoƙarinsu za su iya kasancewa da lamiri mai kyau kuma su sa rai
cewa wata rana yaronsu zai iya komo ga Jehobah.12, 13. (a) Ta yaya iyaye za su nuna suna yin biyayya ga Allah idan an yi wa yaransu yankan zumunci? (b) Ta yaya wasu ma’aurata suka amfana don sun yi biyayya ga Jehobah?
12 Ba ya yi wa iyaye sauƙi su yi wa Jehobah biyayya idan aka yi wa yaransu yankan zumunci. Wata ’yar’uwa da aka yi wa ’yarta yankan zumunci kuma ’yar ta bar gida ta ce: “Na nemi hujja a littattafanmu da zai ba ni damar yin magana da ’yata da kuma ’yar da ta haifa. Amma, maigidana ya taimaka min in san cewa ’yarmu ta isa ta ba da lissafin kanta ga Jehobah kuma ya kamata mu riƙe amincinmu ga Jehobah.”
13 Bayan wasu shekaru, ’yarsu ta dawo ƙungiyar Jehobah. Sai mahaifiyar ta ce: “Yanzu tana kira ko tura mini saƙo a waya kusan kowace rana. Ban da haka, tana daraja mu don ta san cewa mun yi wa Jehobah biyayya kuma dangantakarmu da ita ta yi ƙarfi sosai.” Idan an yi wa yaronka yankan zumunci, za ka ‘dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kuma ka ƙi jingina ga naka fahimi’? (Mis. 3:5, 6) Ka tuna cewa yadda Jehobah yake horar da mu ya dace kuma hakan ya nuna yana ƙaunarmu. Kada ka manta cewa ya ba da Ɗansa a madadinmu kuma ba ya son a halaka kowa. (Karanta 2 Bitrus 3:9.) Saboda haka, iyaye ku ci gaba da amincewa da ja-gorancin Jehobah har ma a lokacin da yin hakan bai da sauƙi. Ku riƙa bin horarwar da Allah yake mana, kada ku ƙi ta.
A CIKIN IKILISIYA
14. Ta yaya muke amfana daga koyarwar Jehobah ta wurin “amintaccen wakili”?
14 Jehobah ya yi alkawari cewa zai riƙa kula da mu kuma ya kāre mu. Ban da haka, zai riƙa koyar da mu, kuma yana hakan a hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, Jehobah ya ba Yesu hakkin kula da ikilisiya, Yesu kuma ya sa “amintaccen wakilin” nan ya riƙa mana tanadin abin da zai taimaka mana mu riƙe amincinmu. (Luk. 12:42) Wannan wakilin yana koyar da mu a hanyar da ta dace. Ka tambayi kanka, ‘Na taɓa jin wani jawabi ko karanta wani talifi da ya sa na canja ra’ayina ko halina?’ Babu shakka, za ka yi farin ciki idan ka yi hakan, domin zai nuna cewa kana barin Jehobah ya horar da kai.—Mis. 2:1-5.
15, 16. (a) Ta yaya za mu amfana daga aikin da dattawa suke yi? (b) Ta yaya za mu sa dattawa su ji daɗin aikinsu?
15 Kristi ya ba dattawa hakkin kula da ikilisiya. (Afis. 4:8, 11-13) Ta yaya za mu amfana daga aikin dattawa? Hanya ɗaya ita ce yin koyi da bangaskiyarsu da kuma bin misalinsu. Wata hanya kuma ita ce bin gargaɗin su. (Karanta Ibraniyawa 13:7, 17.) Dattawa suna ƙaunar mu kuma suna so mu kusaci Allah. Alal misali, suna taimaka mana da zarar sun lura cewa ba ma zuwa taro a kai a kai ko kuma mun daina ƙwazo kamar yadda muke yi a dā. Za su saurare mu kuma su yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen ƙarfafa mu. Shin kana ganin cewa Jehobah yana ƙaunar ka sa’ad da dattawa suka taimaka maka?
16 Ka tuna cewa ba ya yi wa dattawa sauƙi su yi mana gargaɗi. Kana ganin ya yi wa annabi Nathan sauƙi ya yi wa Sarki Dauda gargaɗi sa’ad da Dauda ya so ya ɓoye zunubinsa? (2 Sam. 12:1-14) Hakazalika, bai yi wa manzo Bulus sauƙi ya yi wa Bitrus gargaɗi sa’ad da Bitrus ya nuna ya fi son Yahudawa ba. (Gal. 2:11-14) Saboda haka, ta yaya za ka sa aikin dattawa ya yi musu sauƙi? Ka zama mai tawali’u da sauƙin hali kuma ka riƙa gode musu. Ka san cewa Jehobah yana ƙaunar ka shi ya sa ya yi amfani da dattawa don su taimaka maka. Hakan zai amfane ka kuma dattawa za su ji daɗin aikinsu.
17. Ta yaya wata ’yar’uwa ta amfana daga taimakon dattawa?
17 Ya yi ma wata ’yar’uwa wuya ta riƙa ƙaunar Jehobah don abubuwan da ta yi a dā. Ta ce: “Sa’ad da na soma sanyin gwiwa don abubuwan da na yi a dā da kuma wasu matsalolin da nake fuskanta, sai na san cewa ya kamata in yi magana da dattawa. Ba su kushe ni ba kuma ba su zage ni ba, amma sun ƙarfafa ni. Bayan kowane taro, wani daga cikinsu yakan zo ya tambaye ni yadda nake ji duk da cewa suna da ayyuka da yawa. Nakan ji kamar Allah ba zai taɓa ƙaunata ba don abubuwan da na yi a dā. Amma, Jehobah ya yi amfani da ’yan’uwa da kuma dattawa don ya nuna yana ƙaunata. Ina roƙon Jehobah ya taimaka mini in ci gaba da bauta masa.”
MUMMUNAN SAKAMAKON ƘIN AMINCEWA DA HORO
18, 19. Wane mummunan sakamako ne ƙin amincewa da horo yake jawowa? Ka ba da misali.
18 Duk da cewa mukan yi baƙin ciki sa’ad da aka mana horo, amma ƙin amincewa da horon Allah yana jawo mummunan sakamako sosai. (Ibran. 12:11) Ka yi la’akari da misalin Kayinu da Sarki Zedekiya. Sa’ad da Allah ya ga cewa Kayinu ya tsani ƙanensa, ya yi masa gargaɗi. Ya ce: “Me ya sa ka fusata, me kuma ya sa har tsikar jikinka ta tashi? In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi.” (Far. 4:6, 7, LMT) Kayinu ya ƙi ya ji gargaɗin Allah kuma ya kashe ƙanensa. Hakan ya jawo masa mummunan sakamako! (Far. 4:11, 12) Da a ce Kayinu ya saurari Allah, da ba zai fuskanci wannan sakamakon ba.
19 Sarki Zedekiya mugu ne kuma mutanen Urushalima sun sha wahala sosai sa’ad da yake sarauta. Annabi Irmiya ya ja wa Zedekiya kunne sau da sau amma bai ji ba. Hakan ya jawo masa mummunan sakamako. (Irm. 52:8-11) Jehobah ba ya son mu sha irin wannan wahalar!—Karanta Ishaya 48:17, 18.
20. Mene ne zai faru da waɗanda suka amince da horarwar Allah da kuma waɗanda suka ƙi amincewa da ita?
20 A yau mutane ba sa son horo, kuma sukan yi wa mutumin da ke horar da kansa ba’a. Amma, nan ba da daɗewa ba, duk wanda ya ƙi horon Allah zai fuskanci mummunan sakamako. (Mis. 1:24-31) Saboda haka, bari mu ‘ji horarwa, mu zama masu hikima.’ Misalai 4:13 ta ce: Ka “riƙe koyarwar nan da ƙarfi, kada ka rabu da ita, kiyaye ta da kyau, gama rai ce a gare ka.” (Juyi Mai Fitar da Ma’ana)