Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Ban da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, mene ne kuma ya nuna cewa a dā, Isra’ilawa bayi ne a Masar?

Littafi Mai Tsarki ya ambata cewa bayan da Midiyanawa suka kai Yusufu ƙasar Masar, Yakubu da iyalinsa sun ƙaura daga Kan’ana zuwa Masar. Sun sauƙa a yankin da ake kira Goshen kusa da kogin Nilu. (Far. 47:​1, 6) Isra’ilawa sun “ƙaru har jama’arsu ta yi ƙarfi.” Hakan ya sa Masarawa suka soma jin tsoron Isra’ilawa kuma suka sa su zama bayi.​—Fit. 1:​7-14.

Wasu masu sūkar Littafi Mai Tsarki sun ce wannan labarin ƙage ne. Duk da haka, akwai abubuwa da suka nuna cewa ʼyan Semite * sun yi zaman bayi a Masar a dā.

Alal misali, masu tone-tonen ƙasa sun gano wani yanki a arewacin Masar da mutane suke zama a dā. Wani mai suna Dokta John Bimson ya ce alamomi sun nuna cewa akwai yankuna 20 ko fiye da hakan inda mutanen Semite suke zama a arewacin Masar. Bugu da ƙari, wani ɗan Tarihin Masar mai suna James K. Hoffmeier ya ce: “Daga wajen shekara ta 1800 zuwa 1540 kafin haihuwar Yesu, Masar wuri ne da mutanen Semite da ke yammacin Asiya suke zuwa.” Ya ƙara da cewa: “Wannan lokacin ya yi daidai da lokacin da su Ibrahim da Ishaƙu da kuma Yakubu suka yi rayuwa kuma ya jitu da yanayin da aka bayyana a littafin Farawa.”

Akwai wasu ƙarin tabbaci kuma da aka samo a kudancin Masar. Wata takardar ganye da aka samo wadda aka rubuta a (wajen shekara ta 2000–1600 K.H.Y.) tana ɗauke da sunayen bayin da suka yi aiki a kudancin Masar. A cikin sunayen, fiye da 40 na ʼyan Semite ne. James K. Hoffmeier ya ce: “Tun da yake fiye da ʼyan Semite arba’in ne suke aiki a wannan gidan a Thebaid [kudancin Masar], da alama cewa adadinsu a ƙasar baƙi ɗaya, musamman kusa da kogin Nilu na da yawa sosai.”

Wani mai tone-tonen ƙasa mai suna David Rohl ya ce sunayen wasu bayi da ke takardar “sun jitu da waɗanda aka ambata a Littafi Mai Tsarki.” Alal misali, takardar tana ɗauke da sunaye kamar su Issakar da Asher da kuma Shifra. (Fit. 1:​3, 4, 15) Rohl ya kammala da cewa: “Wannan ya nuna cewa akwai lokacin da Isra’ilawa suke ƙasar Masar.”

Dokta Bimson ya ce: “Labaran da ke Littafi Mai Tsarki game da lokacin da Isra’ilawa suka yi zaman bauta a Masar da kuma lokacin da suka sami ’yanci gaskiya ne.”

^ sakin layi na 4 An samo sunan nan Semite daga ɗan Nuhu na uku mai suna Shem. Wataƙila zuriyar Shem ne ʼyan Elim da Assuriyawa da Kaldiyawa na dā da Ibraniyawa da ʼyan Suriya da ƙabilun Larabawa dabam-dabam.