Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 18

Yadda Ake Nuna Kauna da Adalci a Cikin Ikilisiya

Yadda Ake Nuna Kauna da Adalci a Cikin Ikilisiya

“Ku taimaki juna ta wajen ɗaukar wahalar juna. Ta haka ne za ku cika koyarwar Almasihu.”​—GAL. 6:2.

WAƘA TA 12 Jehobah Allah Mai Iko Duka

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Waɗanne abubuwa biyu ne muka tabbatar da su?

JEHOBAH ALLAH yana ƙaunar bayinsa. Yana yin hakan a koyaushe kuma zai ci gaba da yin hakan. Ƙari ga haka, yana so a riƙa nuna adalci. (Zab. 33:5) Don haka, muna bukatar mu tabbata da abubuwa biyu: (1) Jehobah ba ya farin ciki idan aka wulaƙanta bayinsa. (2) Zai tabbatar da cewa an yi adalci. A talifi na farko a wannan jerin talifofin, * mun koyi cewa ƙauna ce ta sa Allah ya kafa Dokar da ya ba da ta hannun Musa. Dokar ta sa a nuna wa mutane adalci musamman ma marasa ƙarfi. (M. Sha. 10:18) Wannan dokar ta nuna mana cewa Jehobah ya damu da bayinsa sosai.

2. Waɗanne tambayoyi ne za mu amsa?

2 An daina bin Dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa a shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu sa’ad da aka kafa ikilisiyar Kirista. Da yake Kiristoci sun daina bin dokar, za su sami kāriya kuwa? Ƙwarai kuwa! An kafa wa Kiristoci sabuwar doka, wato dokar Kristi. A wannan talifin, za mu fara tattauna abin da wannan dokar take nufi. Bayan haka, za mu amsa waɗannan tambayoyin: Me ya sa muka ce ƙauna ce ta sa aka kafa wannan dokar? Me ya sa muka ce dokar ta sa a riƙa yin adalci? Ta yaya dokar za ta taimaka wa dattawa da magidanta a yadda suke bi da mutane?

MECE CE DOKAR KRISTI?

3. Mece ce dokar Kristi da aka ambata a Galatiyawa 6:2 ta ƙunsa?

3 Karanta Galatiyawa 6:2. Kiristoci suna bin koyarwa ko kuma dokar Kristi. Yesu bai rubuta jerin dokoki da mabiyansa za su riƙa bi ba, amma ya ba su umurnai da kuma ƙa’idodin da za su riƙa yin amfani da su a rayuwarsu. Dokar Kristi ta ƙunshi dukan abubuwan da Yesu ya koyar. Don mu fahimci hakan da kyau, ka yi la’akari da wannan.

4-5. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya koyar da mutane, kuma a wane lokaci ne ya yi hakan?

4 A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya koyar da mutane? Na farko, ya yi hakan ta abubuwan da ya faɗa. Abin da ya faɗa ya ratsa zuciyar mutane domin ya koyar da gaskiya game da Allah da kuma abin da ya sa Allah ya halicci mutane. Ƙari ga haka, Yesu ya bayyana cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance dukan wahalolin ’yan Adam. (Luk. 24:19) Yesu ya koyar da mutane ta wajen kafa musu misali mai kyau. Kuma ta salon rayuwarsa, ya nuna wa mabiyansa yadda ya kamata su yi rayuwa.​—Yoh. 13:15.

5 A wane lokaci ne Yesu ya koyar da mutane? Ya yi hakan sa’ad da yake hidima a duniya. (Mat. 4:23) Ƙari ga haka, ya koyar da mabiyansa jim kaɗan bayan ya tashi daga mutuwa. Alal misali, ya bayyana ga almajiransa fiye da 500 kuma ya umurce su su sa mutane su ‘zama almajiransa.’ (Mat. 28:​19, 20; 1 Kor. 15:6) Da yake Yesu ne shugaban ikilisiya, bayan ya koma sama, ya ci gaba da ba almajiransa umurni. Alal misali, a wajen shekara ta 96, ya ja-goranci manzo Yohanna ya ƙarfafa Kiristoci shafaffu kuma ya ba su shawara.​—Kol. 1:18; R. Yar. 1:1.

6-7. (a) A ina ne za mu sami koyarwar Yesu? (b) Ta yaya za mu bi dokar Kristi?

6 A ina ne za mu sami koyarwar Yesu? Littafin Matiyu da Markus da Luka da kuma Yohanna suna ɗauke da abubuwa da yawa da Yesu ya faɗa da kuma ayyukansa sa’ad da yake duniya. Ruhu mai tsarki ya hure mutane masu ‘tunani’ kamar Kristi su rubuta sauran Nassosin Helenanci na Kirista domin su taimaka mana mu san ra’ayin Yesu.​—1 Kor. 2:16.

7 Darussa: Abubuwan da Yesu ya koyar za su iya taimaka mana a dukan abubuwan da muke yi a rayuwa. Sun ƙunshi abin da muke yi a gida da wurin aiki da makaranta da kuma ikilisiya. Za mu koyi hakan idan muka karanta littattafan Helenanci na Kirista kuma muka yi bimbini a kansu. Idan muna so mu nuna muna bin wannan dokar, muna bukatar mu yi rayuwar da ta jitu da umurnai da dokoki da kuma ƙa’idodin da ke littattafan. Idan muka yi biyayya ga dokar Kristi, muna yin biyayya ne ga Allahnmu mai ƙauna, wato Jehobah wanda shi ne Tushen dukan abubuwan da Yesu ya koyar.​—Yoh. 8:28.

ƘAUNA CE TA SA AKA KAFA DOKAR

8. Mene ne tushen dokar Kristi?

8 Idan mutum yana zama a gidan da ke da tushe mai ƙarfi, hankalinsa zai kwanta. Hakazalika, dokar da aka kafa bisa ƙa’idodi masu kyau za ta sa waɗanda ke bin ta su sami kwanciyar rai. An kafa dokar Kristi bisa tushe mafi kyau, wato ƙauna. Me ya sa muka ce hakan?

Idan muka nuna wa mutane ƙauna, muna bin “dokar Kristi” (Ka duba sakin layi na 9-14) *

9-10. Waɗanne misalai ne ya nuna cewa ƙauna ce ta sa Yesu ya taimaka wa mutane, kuma ta yaya za mu yi koyi da shi?

9 Na farko, Yesu ya nuna ƙauna a dukan abubuwan da ya yi. Ƙauna ta ƙunshi nuna tausayi. Yesu ya nuna irin wannan tausayin, hakan ya sa ya koyar da jama’a, ya warkar da marasa lafiya, ya ciyar da mayunwata kuma ya ta da matattu. (Mat. 14:14; 15:​32-38; Mar. 6:34; Luk. 7:​11-15) Duk da cewa yin waɗannan abubuwan sun ɗauki lokacinsa da kuma kuzarinsa, Yesu ya biya bukatun mutane kafin nasa. Ban da haka, ya nuna ƙauna ta wajen ba da ransa domin ya ceci mutane.​—Yoh. 15:13.

10 Darussa: Za mu iya yin koyi da Yesu ta wajen mai da hankali ga bukatun mutane kafin namu. Ban da haka, za mu iya yin koyi da Yesu ta wajen jin tausayin mutanen da ke yankinmu. Idan tausayi ya sa muka yi wa’azi da kuma koyarwa, muna bin dokar Kristi.

11-12. (a) Mene ne ya nuna cewa Jehobah ya damu da mu sosai? (b) Ta yaya za mu nuna ƙauna kamar Jehobah?

11 Na biyu, Yesu ya nuna cewa Ubansa mai ƙauna ne. A lokacin da Yesu yake duniya, ya nuna yadda Jehobah yake ƙaunar bayinsa. Ƙari ga abubuwan da Yesu ya koyar, ya koyar cewa kowannenmu yana da tamani da kuma daraja sosai a wurin Ubanmu da ke sama. (Mat. 10:31) Jehobah yana ɗokin marabtar mutumin da ya tuba kuma ya komo ikilisiya. (Luk. 15:​7, 10) Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar mu ta wajen aiko da Ɗansa ya ba da ransa a madadinmu.​—Yoh. 3:16.

12 Darussa: Ta yaya za mu nuna ƙauna kamar Jehobah? (Afis. 5:​1, 2) Ta wajen ɗaukan ’yan’uwa da tamani da daraja su da kuma marabtar “tunkiyar da ta ɓace,” amma ta sake komo ga Jehobah da zuciya ɗaya. (Zab. 119:176) Za mu nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu ta wajen taimaka musu, musamman sa’ad da suke fuskantar matsaloli. (1 Yoh. 3:17) Idan muka nuna wa mutane ƙauna, muna bin dokar Kristi.

13-14. (a) Kamar yadda Yohanna 13:​34, 35 ta nuna, mene ne Yesu ya umurce mabiyansa su yi, kuma me ya sa wannan dokar sabuwa ce? (b) Ta yaya muke bin sabuwar dokar?

13 Na uku, Yesu ya umurci mabiyansa su yi koyi da shi a nuna ƙauna. (Karanta Yohanna 13:​34, 35.) Dokar Kristi sabuwa ce domin ta ce mutane su riƙa nuna ƙauna irin wadda ba a ambata a Dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa ba. Hakan yana nufin cewa muna bukatar mu saka bukatun mutane gaba da tamu. Muna bukatar mu ƙaunaci ’yan’uwanmu fiye da yadda muke ƙaunar kanmu. Muna bukatar mu nuna cewa za mu iya ba da ranmu a madadinsu domin muna ƙaunar su yadda Yesu ya ƙaunace mu.

14 Darussa: Ta yaya za mu bi sabuwar dokar nan? A taƙaice, ta wajen yin sadaukarwa don ’yan’uwanmu. Don muna ƙaunar su, a shirye muke mu sadaukar da ranmu a madadinsu. Ban da haka, za mu iya sadaukar da abubuwan da ba na musamman ba dominsu. Alal misali, muna bin dokar Kristi idan muka ɗauki tsofaffi zuwa taro, idan muka sadaukar da abin da muke so don ’yan’uwanmu da kuma sa’ad da muka nemi izini daga wurin aiki don mu taimaka wajen ba da agaji. Ƙari ga haka, muna bin dokar idan muna sa kowa a ikilisiya ya sami kwanciyar rai.

DOKAR DA KE ƊAUKAKA YIN ADALCI

15-17. (a) Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana son adalci? (b) Ta yaya za mu iya yin koyi da Yesu?

15 Kalmar nan “adalci” da aka yi amfani da ita a Littafi Mai Tsarki, tana nufin yin abin da Allah yake so ba tare da son kai ba. Me ya sa bin dokar Kristi za ta sa mu riƙa yin adalci?

Yesu ya daraja mata kuma ya tausaya musu, har da waɗanda aka rena (Ka duba sakin layi na 16) *

16 Na ɗaya, bari mu duba yadda ayyukan Yesu suka nuna cewa shi mai adalci ne. A zamanin Yesu, malaman addinin Yahudawa sun ƙi jinin mutanen da ba Yahudawa ba, da kuma Yahudawan da ba su je makarantar addinin Yahudawa ba, kuma sun rena mata. Amma Yesu bai nuna son kai ba. Ya amince da mutanen da ba Yahudawa ba da suka yi imani da shi. (Mat. 8:​5-10, 13) Ya yi wa’azi ga masu arziki da talakawa ba tare da nuna bambanci ba. (Mat. 11:5; Luk. 19:​2, 9) Bai taɓa zagin mata ko ya zalunce su ba. Amma ya daraja su kuma ya tausaya musu, har da waɗanda ake ganin ba su da amfani.​—Luk. 7:​37-39, 44-50.

17 Darussa: Za mu yi koyi da Yesu idan muka guji nuna bambanci. Idan muka fita wa’azi, mu yi wa’azi ga kowa, talakawa da masu kuɗi, ko da wane irin addini ne suke bi. ’Yan’uwa maza suna bin wannan misalin Yesu ta wajen daraja mata. Idan muka yi hakan muna bin dokar Kristi.

18-19. Mene ne Yesu ya koyar game da adalci, kuma waɗanne darussa ne muka koya daga koyarwarsa?

18 Na biyu, ka yi la’akari da abin da Yesu ya koyar game da yin adalci. Ya koyar da ƙa’idodin da za su taimaka wa mabiyansa su riƙa tausaya wa mutane. Ka yi tunani a kan ƙa’idar da ke littafin Matiyu 7:12. Dukanmu muna so a riƙa nuna mana adalci. Saboda haka, ya kamata mu riƙa bi da mutane haka ma. Idan muka yi hakan, su ma za su riƙa nuna mana adalci. Amma, idan aka yi mana rashin adalci kuma fa? Yesu ya koya wa mabiyansa cewa Jehobah zai ‘biya wa mutanen da ya zaɓa, waɗanda suke masa kuka dare da rana hakkinsu.’ (Luk. 18:​6, 7) Wannan furucin alkawari ne. Allah ya san dukan matsalolin da muke fuskanta a wannan kwanaki na ƙarshe, kuma zai tabbatar da cewa an nuna mana adalci a lokacin da ya dace.​—2 Tas. 1:6.

19 Darussa: Idan muka bi ƙa’idar da ya Yesu ya koyar, za mu riƙa tausaya wa mutane. Idan an taɓa yi mana rashin adalci, sanin cewa Jehobah zai sa a yi mana adalci zai ƙarfafa mu sosai.

YADDA YA KAMATA DATTAWA DA MAGIDANTA SU BI DA MUTANE

20-21. (a) Yaya ya kamata dattawa da magidanta su bi da mutane? (b) Yaya miji zai iya nuna ƙaunar da babu son kai, kuma ta yaya mahaifi zai bi da yaransa?

20 Ta yaya wannan dokar za ta taimaka wa dattawa da magidanta su bi da mutane? Da yake ƙauna ita ce tushen wannan dokar, dattawa da magidanta suna bukatar su riƙa daraja da kuma ƙaunar waɗanda suke wa ja-goranci. Suna bukatar su tuna cewa Yesu yana so mu riƙa nuna ƙauna a kowane lokaci.

21 A iyali. Miji yana bukatar ya riƙa ƙaunar matarsa “kamar yadda Almasihu ya ƙaunaci” ikilisiya. (Afis. 5:​25, 28, 29) Yana bukatar ya yi koyi da ƙauna marar son kai da Yesu ya nuna ta wajen biyan bukatun matarsa kafin nasa. Hakan yana iya yi wa wasu maza wuya, wataƙila don an yi renonsu a wurin da mutane ba sa nuna ƙauna da kuma daraja mutane. Yana iya yi musu wuya su canja wannan hali, amma wajibi ne su yi canji idan suna so su bi dokar Kristi. Mace za ta riƙa daraja mijin da ke ƙaunar ta sosai. Mahaifin da ke ƙaunar yaransa ba zai taɓa zaluntar su ta furucinsa ko ayyukansa ba. (Afis. 4:31) A maimakon haka, yana nuna wa yaran cewa yana ƙaunar su kuma ya amince da su, hakan zai sa su sami kwanciyar rai. Yara za su ƙaunaci mahaifin da ke yin hakan kuma za su amince da shi.

22. Kamar yadda 1 Bitrus 5:​1-3 ta nuna, waye ne ke da ‘tumakin’ da dattawa suke kula da su, kuma yaya ya kamata su bi da su?

22 A ikilisiya. Dattawa suna bukatar su tuna cewa ‘tumakin’ da suke kula da su ba nasu ba ne. (Yoh. 10:16; karanta 1 Bitrus 5:​1-3.) Kalmar nan “garken Allah” da kuma “mutanen da Allah ya ba ku,” suna tuna wa dattawa cewa tumakin da suke kula da su na Jehobah ne. Jehobah yana so a riƙa kula da tumakinsa kuma a ƙaunace su. (1 Tas. 2:​7, 8) Dattawan da suke nuna ƙauna sa’ad da suke yin aikin da Jehobah ya ba su za su sami amincewarsa. Ƙari ga haka, ’yan’uwa za su ƙaunace su kuma su daraja su.

23-24. (a) Wane mataki ne dattawa suke ɗauka sa’ad da wani ya yi zunubi mai tsanani? (b) Me ya kamata dattawa su yi la’akari da shi sa’ad da wani ya yi zunubi mai tsanani?

23 Mene ne dattawan ikilisiya suke yi sa’ad da wani ya yi zunubi mai tsanani? Matakin da suke ɗauka ya bambanta da wanda alƙalai da kuma dattawa suke ɗauka a zamanin Isra’ilawa. A zamanin, suna shari’a a kan batutuwan da suka shafi bautar Jehobah da kuma waɗanda ba su shafi bautarsa ba. A yanzu da ake bin dokar Kristi, dattawa suna yin shari’a ne a batutuwan da suka shafi bautarmu ga Jehobah. Sun san cewa hukuma ce ke da hakkin yanke hukunci a kan laifofin da ba su shafi bautarmu ga Jehobah ba. Hakan ya ƙunshi ci wa mutum tara ko kuma saka shi a kurkuku.​—Rom. 13:​1-4.

24 Wane mataki ne dattawa suke ɗauka idan wani ya yi zunubi mai tsanani? Suna yin amfani da Littafi Mai Tsarki don su bincika batun kuma su yanke hukunci. Suna tuna cewa ƙauna ce tushen dokar Kristi. Ƙauna tana sa dattawa su tambayi kansu: Mene ne za mu yi don mu taimaka wa waɗanda zunubin ya shafa? Ƙauna tana kuma taimaka wa dattawa su bincika ko mai laifin ya tuba da gaske. Za a iya taimaka masa ya sake ƙulla dangantaka da Jehobah kuwa?

25. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

25 Muna farin ciki sosai cewa muna bin dokar Kristi! Idan dukanmu muka yi ƙoƙarin bin dokar, ikilisiyarmu za ta zama wurin da kowa zai sami kāriya, ya ji ana ƙaunar sa da kuma daraja shi. Duk da haka, muna rayuwa a zamanin da halin “mugayen mutane” yake “ƙara muni” sosai. (2 Tim. 3:13) Muna bukatar mu kasance a faɗake. Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su nuna adalci kamar Jehobah sa’ad da wani ya ci zarafin yara? Za mu amsa wannan tambayar a talifi na gaba.

WAƘA TA 15 Mu Yabi Ɗan Allah!

^ sakin layi na 5 Wannan talifin da kuma biyu da za su biyo bayansa, suna cikin jerin talifofin da suka nuna dalilin da ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah Allah ne mai ƙauna da kuma adalci. Yana son a riƙa nuna wa bayinsa adalci kuma yana ƙarfafa waɗanda aka yi musu rashin adalci a wannan muguwar duniyar.

^ sakin layi na 1 Ka duba talifin nan “Dokoki Game da Nuna Ƙauna da Adalci a Isra’ila ta Dā” a Hasumiyar Tsaro ta Fabrairu 2019.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTO: Yesu yana kallon wata gwauruwar da ɗanta tilo ya mutu. Tausayi ya sa Yesu ya ta da saurayin daga mutuwa.

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTO: Yesu ya ci abinci a gidan wani Ba-farisi mai suna Siman. Wata mata, da wataƙila ƙaruwa ce, ta wanke ƙafafun Yesu da hawayenta, ta share da gashinta kuma ta zuba māi a ƙafafunsa. Siman bai ji daɗin abin da matar ta yi ba, amma Yesu ya goyi bayanta.