Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 20

Yadda Za a Taimaka ma Wadanda Aka Ci Zarafinsu

Yadda Za a Taimaka ma Wadanda Aka Ci Zarafinsu

“Allah wanda yake yi mana kowace irin ta’aziyya . . . yana yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalarmu.”​—2 KOR. 1:​3, 4.

WAƘA TA 134 Yara Amana Ne Daga Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Wane misali ne ya nuna cewa ʼyan Adam suna so a riƙa ƙarfafa su kuma su ma suna iya ƙarfafa mutane? (b) Ta yaya cin zarafi yake shafan yara?

DUKAN ʼyan Adam suna so a riƙa ƙarfafa su kuma su ma suna iya ƙarfafa mutane. Alal misali, idan ƙananan yara sun faɗi sa’ad da suke wasa kuma sun ji rauni, suna yawan zuwa wurin Mamarsu ko Babansu suna kuka. Iyayen ba za su iya warkar da su ba, amma za su iya lallashe su. Suna iya tambayar su abin da ya faru, sai su share musu hawaye, su lallashe su kuma su sa musu magani a ciwon. Ba da daɗewa ba, sai yaran su daina kuka, wasu suna ci gaba da wasa. Bayan ɗan lokaci, sai ciwon ya warke.

2 Amma akwai wasu lokuta da ake ji wa yara raunin da ya fi wannan tsanani. Wasu ana cin zarafinsu ta hanyar jima’i. Ana iya yi musu hakan sau ɗaya kawai ko kuma har tsawon shekaru da yawa. Ko da sau nawa ne aka ci zarafinsu, wannan aukuwar tana yawan tayar musu da hankali sosai. A wasu lokuta ana kama mai laifin kuma a hukunta shi. A wasu kuma, suna kuɓucewa. Amma ko da an kama mai laifin kuma an yanke masa hukunci, laifin yana shafan yaran har zuwa lokacin da suka yi girma.

3. Kamar yadda littafin 2 Korintiyawa 1:​3, 4 ya nuna, mene ne nufin Jehobah, kuma waɗanne tambayoyi ne muke bukatar mu amsa?

3 Ta yaya za mu iya taimaka wa Kiristan da aka ci zarafinsa sa’ad da yake ƙarami kuma har yanzu bai gama warwarewa ba? (Karanta 2 Korintiyawa 1:​3, 4.) Babu shakka, Jehobah yana so a ƙaunaci tumakinsa kuma a ƙarfafa su. Saboda haka, bari mu tattauna tambayoyi uku: (1) Me ya sa mutanen da aka ci zarafinsu suke bukatar ƙarfafa? (2) Su waye ne za su iya ƙarfafa su? (3) Ta yaya za mu iya ƙarfafa su?

ME YA SA MUKE BUKATAR MU ƘARFAFA SU?

4-5. (a) Me ya sa ya kamata mu san cewa yara sun bambanta da manya? (b) Ta yaya cin zarafi zai iya hana yara amincewa da mutane?

4 Ana iya bukatar a ci gaba da ƙarfafa mutanen da aka cin zarafinsu sa’ad da suke ƙanana har bayan shekaru da yawa. Me ya sa? Idan muna so mu san dalilin, muna bukatar mu san cewa yara sun bambanta da manya. Cin zarafi yana shafan yara fiye da manya. Yadda cin zarafi yake shafan yara ya bambanta da yadda yake shafan manya. Ku yi la’akari da wasu misalai.

5 Yara suna bukatar su kusaci mutanen da suke renon su kuma su amince da su. Hakan yana sa su kasance da kwanciyar rai kuma ya sa su amince da mutanen da ke ƙaunar su. (Zab. 22:9) Amma abin baƙin ciki ne cewa a gidan yaran ne ake yawan cin zarafinsu kuma wani a danginsu ko kuma abokan iyayen ne suke yin hakan. Irin wannan cin mutuncin yana hana yara amincewa da mutane har bayan shekaru da yawa.

6. Me ya sa cin zarafin yara yake cutar da su?

6 Yara ba su da ƙarfi kuma cin zarafinsu yana cutar da su sosai. Yin jima’i da yara kafin lokacin da suka yi girma kuma suka yi aure yana shafan su sosai. Cin zarafinsu yana sa su kasance da ra’ayin da bai dace ba game da jima’i, su rena kansu kuma su riƙa nisanta kansu daga mutane.

7. (a) Me ya sa yake da sauƙi a yaudari yara kuma a ci zarafinsu? (b) Mene ne sakamakon ƙaryace-ƙaryacen da ake musu?

7 Yara ba su da wayo, shi ya sa ba sa iya sanin abin da zai cutar da su. (1 Kor. 13:11) Saboda haka, yana da sauƙi masu cin zarafin yara su yaudare su. Masu cin zarafin yara suna ruɗar da su cewa su ne suka jawo matsalar kuma su ce kada su gaya wa kowa. Ƙari ga haka, suna cewa idan sun kai ƙara, ba za a yarda da abin da suka ce ba. Suna gaya musu cewa idan sun yarda su yi jima’i da su, hakan zai nuna cewa suna ƙaunar juna. Irin waɗannan ƙaryace-ƙaryacen suna ruɗar da yara kuma suna sa su yarda da wannan ƙaryar har shekaru da yawa. Hakan yana sa yaran su riƙa yin tunani cewa ba za su iya bauta wa Jehobah ba kuma su ji cewa abin da ya faru laifinsu ne.

8. Me ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah zai ta’azantar da mutanen da ke baƙin ciki?

8 Shi ya sa yaran da aka ci zarafinsu ba sa saurin warwarewa. Wannan mugunta ce sosai kuma ta nuna cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe. Littafi Mai Tsarki ya ce a wannan lokacin, mutane da yawa za su zama “marasa ƙauna” kuma halin “mugayen mutane da masu ruɗu . . . zai yi ta ƙara muni.” (2 Tim. 3:​1-5, 13) Babu shakka, Shaiɗan mugu ne kuma abin baƙin ciki ne idan ʼyan Adam suka yi abin da ke faranta masa rai. Amma Jehobah ya fi Shaiɗan da bayinsa iko. Ya san dabarun Shaiɗan sarai. Ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Jehobah ya san da irin baƙin cikin da mutanen da aka ci zarafinsu suke yi kuma yana a shirye ya ƙarfafa su. Muna hamdala cewa muna bauta wa Allah mai ta’aziyya wanda ke ‘yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalarmu, don mu ma mu yi wa waɗansu ta’aziyya a cikin kowane irin wahalarsu, da wannan ta’aziyyar da muka samu daga wurin Allah.’ (2 Kor. 1:​3, 4) Su waye ne Jehobah yake amfani da su don ya ƙarfafa mu?

SU WAYE NE ZA SU IYA ƘARFAFA SU?

9. Kamar yadda Dauda ya faɗa a Zabura 27:​10, mene ne Jehobah zai yi wa mutanen da iyalinsu suka yi watsi da su?

9 Yaran da iyayensu ba su kāre su ba daga masu cin zarafin yara ko kuma waɗanda wani da suka amince da shi ya ci zarafinsu suna bukatar ta’aziyya sosai. Dauda ya san cewa Jehobah ne ya fi ta’azantar da mu. (Karanta Zabura 27:10.) Dauda yana da tabbaci cewa Jehobah yana taimaka wa mutanen da aka yi watsi da su. Yaya yake yin hakan? Yana yin amfani da bayinsa amintattu. ʼYan’uwanmu maza da mata iyalinmu ne. Alal misali, Yesu ya ce mutanen da ke bauta wa Jehobah sun zama mamarsa da kuma ʼyan’uwansa.​—Mat. 12:​48-50.

10. Ta yaya manzo Bulus ya kwatanta aikinsa a matsayin dattijo?

10 Bari mu tattauna yadda irin wannan dangantakar za ta iya kasancewa a ikilisiyar Kirista. Manzo Bulus dattijo ne mai ƙwazo da kuma aminci. Ya kafa misali mai kyau kuma Allah ya hure shi ya gaya wa ʼyan’uwa cewa su yi koyi da shi yadda yake koyi da Yesu. (1 Kor. 11:1) Ku lura da yadda Bulus ya kwatanta aikinsa a matsayin dattijo. Ya ce: “Yadda mama take renon jaririnta ta kuma lura da shi, haka mun lura da ku cikin sauƙin kai.” (1 Tas. 2:7) Dattawa masu aminci a yau za su iya yin amfani da furuci masu sanyaya zuciya yayin da suke ta’azantar da masu bukatar taimako.

A yawancin lokuta, ’yan’uwa mata da suka manyanta suna iya ba da ƙarfafa sosai (Ka duba sakin layi na 11) *

11. Me ya nuna cewa ba dattawa kaɗai ba ne za su iya ta’azantar da mutane?

11 Dattawa ne kaɗai za su iya ta’azantar da mutanen da aka ci zarafinsu? A’a. Dukanmu muna da hakkin “ƙarfafa juna.” (1 Tas. 4:18) ʼYan’uwa mata da suka manyanta za su iya ƙarfafa masu bukatar taimako. Jehobah ya kwatanta kansa da uwa da take ƙarfafa yaranta. (Isha. 66:13) Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalan mata da suka ta’azantar da mutanen da ke fuskantar matsaloli. (Ayu. 42:11) Babu shakka, Jehobah yana farin cikin ganin ʼyan’uwa mata a yau da suke ta’azantar da mata da suke fama da baƙin ciki! A wasu lokuta, dattawa za su iya gaya wa wata ʼyar’uwa ta taimaka wa wata da ke fuskantar irin wannan matsalar. *

A WACE HANYA CE ZA MU ƘARFAFA SU?

12. Me muke bukatar mu guji yi?

12 Sa’ad da muke ƙoƙarin taimaka ma wani ɗan’uwa ko kuma ’yar’uwa, ya kamata mu mai da hankali don kada mu ta da batu da mutumin ba zai so ya tattauna da mu ba. (1 Tas. 4:11) Amma mene ne za mu iya yi don mu ta’azantar da waɗanda suke bukatar taimako? Bari mu tattauna hanyoyi biyar da za mu iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki don mu taimaka wa mutanen da aka ci zarafinsu.

13. Kamar yadda littafin 1 Sarakuna 19:​5-8 ya nuna, mene ne mala’ikan Jehobah ya yi wa Iliya, kuma ta yaya za mu bi misalinsa?

13 Ka yi abin da zai taimaka wa mutumin da ke cikin matsala. Sa’ad da annabi Iliya yake gudu don kada a kashe shi, ya yi sanyin gwiwa sosai har ya gwammace ya mutu. Jehobah ya tura mala’ika mai ƙarfi don ya ƙarfafa Iliya. Mala’ikan ya kawo masa abinci kuma ya ƙarfafa shi ya ci. (Karanta 1 Sarakuna 19:​5-8.) Mun koyi wani darasi mai muhimmanci daga wannan labarin. A wasu lokuta, wani ɗan abin kirki da muka yi zai iya ƙarfafa mutumin sosai. Wataƙila mu gayyace shi cin abinci ko mu ba shi kyauta, yin hakan zai nuna wa ɗan’uwa ko ’yar’uwa da ta yi sanyi gwiwa cewa mun damu da ita. Idan yana yi mana wuya mu tattauna da mutum game da abin da ke damunsa, muna iya nuna cewa mun damu da shi ta wajen yin waɗannan abubuwan da aka ambata.

14. Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Iliya?

14 Ku sa waɗanda suka karaya su ji za a kāre su da kuma ƙarfafa su. Za mu iya koyan wani darasi kuma daga labarin Iliya. Jehobah ya yi mu’ujiza don ya taimaka wa annabin ya yi tafiya mai nisa zuwa Dutsen Horeb. Wataƙila Iliya ya ji ya sami kāriya a wannan wurin da Jehobah ya yi yarjejeniya da mutanensa shekaru da yawa da suka shige. Wataƙila Iliya ya yi tunani cewa ya yi nesa da mutanen da suke neman su kashe shi. Wane darasi za mu iya koya daga wannan misalin? Idan muna so mu ta’azantar da waɗanda aka ci zarafinsu, da farko muna bukatar mu sa su kasance da kwanciyar hankali. Alal misali, dattawa suna bukatar su tuna cewa ’yar’uwar da aka ci zarafinta za ta saki jiki kuma ta faɗi abin da ya faru idan suka tattauna da ita a gida maimakon a Majami’ar Mulki. Wata kuma wataƙila za ta fi so a tattauna da ita game da batun a Majami’ar Mulki.

Muna iya ƙarfafa mutane ta wajen saurarar su da kyau, yin addu’a tare da su da kuma gaya musu kalmomi masu ban-ƙarfafa (Ka duba sakin layi na 15-20) *

15-16. Mene ne saurarar mutum da kyau ya ƙunsa?

15 Ka saurari mutumin da kyau. Littafi Mai Tsarki ya ba da shawarar nan cewa: “Ya kamata kowa ya kasance mai saurin ji, amma ba mai saurin magana ba.” (Yaƙ. 1:19) Kana saurarar mutum da kyau kuwa? Wataƙila muna tunanin cewa saurarar mutum da kyau yana nufin yin shiru da kuma kallon mutumin sa’ad da yake magana. Amma saurarar mutum da kyau ya ƙunshi yin wasu abubuwa. Alal misali, Iliya ya gaya wa Jehobah dukan abin da ke zuciyarsa, Jehobah ya saurare shi da kyau. Jehobah ya fahimci cewa Iliya yana jin tsoro kuma yana ganin cewa dukan ayyukan da ya yi, a banza ne. Amma Jehobah ya taimaka masa ya daina jin hakan. Jehobah ya nuna cewa ya saurari Iliya da kyau.​—1 Sar. 19:​9-11, 15-18.

16 Sa’ad da muke saurarar ɗan’uwa ko ’yar’uwa, ta yaya za mu nuna cewa mun damu da su? A wasu lokuta, kalaman da suka dace masu sanyaya zuciya za su nuna hakan. Alal misali kana iya cewa: “Ki yi haƙuri don abin da ya faru da ke! Bai kamata a yi wa yara irin wannan abu ba!” Wataƙila kana iya yin tambaya ɗaya ko biyu don ka tabbatar da cewa ka fahimci abin da wadda aka ci zarafinta take faɗa. Kana iya tambaya, “Don Allah za ki iya taimaka mini in fahimci abin da kike nufi?” Ko kuma, “Ga yadda na fahimci abin da kika ce . . . Abin da ya faru ke nan?” Irin kalmomin nan masu sanyaya zuciya za su tabbatar wa mutumin cewa kana saurarar shi da kyau, kuma kana ƙoƙarin ka fahimce shi.​—1 Kor. 13:​4, 7.

17. Me ya sa muke bukatar mu guji “saurin magana”?

17 Ka yi hankali don kada ka zama “mai saurin magana.” Kada ka katse wa mutumin magana domin kana so ka ba shi shawara ko kuma kana so ka daidaita ra’ayinsa. Ka zama mai kamun kai! Sa’ad da Iliya ya gaya wa Jehobah abin da ke zuciyarsa, yana baƙin ciki kuma ya yi amfani da kalaman da suka nuna hakan. Bayan Jehobah ya ƙarfafa shi, Iliya ya sake gaya wa Jehobah dukan abin da ke zuciyarsa. (1 Sar. 19:​9, 10, 13, 14) Wane darasi ne za mu koya? A wasu lokuta, waɗanda ke baƙin ciki sukan faɗa abin da ke damunsu sau da yawa. Kamar Jehobah, muna bukatar mu saurare su da kyau. Maimakon mu soma gaya musu yadda za su magance matsalarsu, muna bukatar mu tausaya musu kuma mu nuna mun damu da su.​—1 Bit. 3:8.

18. Ta yaya addu’armu za ta ƙarfafa waɗanda ke baƙin ciki?

18 Ku yi addu’a tare da waɗanda ke baƙin ciki. Waɗanda ke baƙin ciki suna iya ji ba za su iya yin addu’a ba. Suna iya ji kamar ba su cancanci su kusanci Jehobah ba. Hanya ɗaya da za mu iya ƙarfafa su ita ce ta yin addu’a tare da su kuma mu ambaci sunansu. A addu’ar, muna iya gaya wa Jehobah yadda muke ƙaunar su da kuma yadda ’yan’uwa a ikilisiyar suke ƙaunar su. Muna iya roƙon Jehobah ya taimaka musu kuma ya ƙarfafa su. Irin wannan addu’a tana da ban-ƙarfafa sosai.​—Yaƙ. 5:16.

19. Mene ne zai taimaka mana mu iya ƙarfafa wani?

19 Ka yi amfani da kalmomi masu ban-ƙarfafa. Ka yi tunani kafin ka yi magana. Yin magana ba tare da tunani ba yana iya ci ma mutumin rai. Amma kalami mai daɗi yana iya sanyaya masa zuciya. (K. Mag. 12:18) Don haka, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka yi amfani da kalmomi masu daɗi da kuma ban-ƙarfafa. Ka tuna cewa maganar Jehobah da ke Littafi Mai Tsarki ce ta fi ban-ƙarfafa.​—Ibran. 4:12.

20. Wane irin tunani ne wasu da aka ci zarafinsu suke yi, amma me muke so su sani?

20 Wasu ’yan’uwa da aka taɓa cin zarafinsu suna ganin cewa sun ƙazamtu, ba su da amfani kuma babu wanda zai iya ƙaunar su. Hakan ba gaskiya ba ne! Don haka, ku yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ku nuna musu yadda Jehobah yake daraja su. (Ka duba akwatin nan “ Samun Ƙarfafa Daga Littafi Mai Tsarki.”) Ka tuna yadda mala’ika ya ƙarfafa annabi Daniyel a lokacin da ya karaya kuma yake baƙin ciki. Jehobah yana son Daniyel ya san cewa yana da daraja a gare shi. (Dan. 10:​2, 11, 19) Hakazalika, Jehobah yana daraja ’yan’uwan da ke baƙin ciki!

21. Mene ne zai faru da mugaye da suka ƙi tuba, kuma mene ne muka ƙuduri niyyar yi don mu taimaka ma waɗanda aka ci zarafinsu?

21 Idan muka ƙarfafa mutane, muna tuna musu cewa Jehobah yana ƙaunar su. Ƙari ga haka, kada mu manta cewa Jehobah Allah ne mai son adalci. Ya san dukan waɗanda aka ci zarafinsu ko da babu wanda ya sani. Zai hukunta dukan masu cin zarafin yara idan ba su tuba ba. (L. Ƙid. 14:18) Amma kafin lokacin, mu yi iya ƙoƙarinmu don mu nuna ƙauna ga waɗanda aka ci zarafinsu. Ban da haka, abin farin ciki ne sanin cewa Jehobah zai warkar da dukan waɗanda Shaiɗan da mutanensa suka ci zarafinsu! Nan ba da daɗewa ba, mutane ba za su ƙara tuna wannan mugun abin da ya faru da su ba.​—Isha. 65:17.

WAƘA TA 109 Mu Kasance da Ƙauna ta Gaske

^ sakin layi na 5 Mutanen da aka ci zarafinsu sa’ad da suke yara suna iya fuskantar ƙalubale sosai bayan shekaru da yawa. Wannan talifin zai taimaka mana mu fahimci dalilin. Za mu san irin mutanen da za su iya ƙarfafa su. Za mu kuma tattauna hanyoyin da za mu iya yin hakan.

^ sakin layi na 11 Mutumin da aka ci zarafinsa ne zai yanke shawara ko zai nemi taimako a wurin likita.

^ sakin layi na 76 BAYANI A KAN HOTO: Wata ’yar’uwa da ta manyanta tana ƙarfafa wata da take baƙin ciki.

^ sakin layi na 78 BAYANI A KAN HOTO: Dattawa biyu sun ziyarci ’yar’uwar da ke baƙin ciki. Ta gayyato ’yar’uwar da ta manyanta ta kasance da ita.