Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 42

“Masu Albarka ne Masu Bin Hanyar Gaskiya” ta Jehobah

“Masu Albarka ne Masu Bin Hanyar Gaskiya” ta Jehobah

“Masu albarka ne masu bin hanyar gaskiya a zuci, masu tafiya cikin Koyarwar Yahweh.”​—ZAB. 119:1.

WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

Wasu ’yan’uwanmu da suka taɓa zama a kurkuku ko suke kurkuku a yanzu domin amincinsu ga Jehobah (Ka duba sakin layi na 1-2)

1-2. (a) Waɗanne matakai ne gwamnatocin ꞌyan Adam suka ɗauka domin suna gāba da Jehobah da kuma mutanensa, amma mene ne bayin Allah suka yi? (b) Ta yaya za mu iya yin farin ciki ko da ana tsananta mana? (Ka kuma yi kalamai a kan hoton da ke shafin farko.)

 A YANZU haka, an dakatar da wasu sashe na ayyukanmu ko kuma an dakatar da shi gabaki ɗaya a ƙasashe 30 a faɗin duniya. A wasu daga cikin ƙasashen nan, hukumomi sun saka ꞌyanꞌuwanmu a cikin kurkuku. Wane laifi ne suka yi? Ba su yi wani abu da ya taka dokar Jehobah ba. Abin da suka yi kawai shi ne karanta da nazarin Littafi Mai Tsarki da gaya ma wasu game da imaninsu da kuma halartar taro tare da ꞌyanꞌuwansu. Ƙari ga haka, ba sa saka hannu a harkokin siyasa. Duk da tsanantawa da ake musu, waɗannan bayin Allah sun ci gaba da bin hanyar gaskiya b ta Jehobah, wato sun ci gaba da bauta ma Jehobah babu fashi. Kuma yin hakan yana sa su farin ciki!

2 Mai yiwuwa ka taɓa ganin ꞌyanꞌuwan nan da suke nuna ƙarfin zuciya kuma ka ga yadda suke faraꞌa. Suna farin ciki ne domin sun san cewa Jehobah yana alfahari da su don sun ci gaba da bin hanyarsa ta gaskiya. (1 Tar. 29:17a) Yesu ya ce: “Masu albarka ne masu shan tsanani saboda adalci, . . . Ku yi murna da farin ciki sosai, domin za ku sami lada mai yawa.”​—Mat. 5:​10-12.

GA MISALI DA ZA MU IYA YIN KOYI DA SHI

Bitrus da Yohanna sun kafa misali mai kyau ma Kiristoci a zamaninmu da suke zuwa kotu don su kāre imaninsu (Ka duba sakin layi na 3-4)

3. Bisa ga Ayyukan Manzanni 4:​19, 20, mene ne manzannin Yesu suka yi sa’ad da ake tsananta musu a ƙarni na farko, kuma me ya sa suka yi hakan?

3 ꞌYanꞌuwanmu Kiristoci suna fuskantar irin yanayin da manzannin Yesu suka fuskanta a ƙarni na farko, saꞌad da aka tsananta musu domin suna waꞌazi game da Yesu. Sau da yawa, alƙalan babban kotun Yahudawa sun ja musu kunne “kada su kuskura su yi wa kowa magana, ko su ƙara koyarwa cikin sunan Yesu.” (A. M. 4:18; 5:​27, 28, 40) Mene ne manzannin suka yi? (Karanta Ayyukan Manzanni 4:​19, 20.) Sun san cewa wanda ya fi alƙalan iko ya ‘umarce su su yi wa mutane wa’azi, su kuma yi shaida’ game da Yesu Kristi. (A. M. 10:42) Don haka, manzo Bitrus da Yohanna sun yi magana da ƙarfin zuciya a madadin sauran manzannin kuma sun ce za su yi biyayya ga Allah maimakon su yi biyayya ga alƙalan, kuma sun ce ba za su daina wa’azi game da Yesu ba. Kamar dai suna tambayar alƙalan ne cewa, ‘Kuna ganin ya kamata mutane su yi muku biyayya maimakon Allah?’

4. Bisa ga Ayyukan Manzanni 5:​27-29, wane misali mai kyau ne manzannin suka kafa wa dukan Kiristoci, kuma ta yaya za mu yi koyi da su?

4 Manzannin sun kafa misali mai kyau da dukan Kiristoci suke bi tun daga lokacin, wato “yi wa Allah biyayya fiye da mu yi wa mutum.” (Karanta Ayyukan Manzanni 5:​27-29.) Bayan an yi wa manzannin dūka domin sun ci gaba da bin hanyar gaskiya ta Jehobah, manzannin sun bar kotun “suna farin ciki a kan an ga sun isa su sha wulaƙanci saboda sunan Yesu.” Kuma suka ci gaba da yin wa’azi.​—A. M. 5:​40-42.

5. Waɗanne tambayoyi ne muke bukatar mu amsa?

5 Misali da manzannin suka kafa mana ya tayar da wasu tambayoyi. Alal misali, ta yaya manzannin za su yi biyayya ga Allah maimakon ’yan Adam, kuma su bi abin da Kalmar Allah ta faɗa cewa su “yi biyayya ga shugabannin gwamnati” ? (Rom. 13:1) Ta yaya za mu yi biyayya ga “shugabannin gwamnati” kamar yadda manzo Bulus ya faɗa kuma mu ci gaba da bin hanyar gaskiya ta Jehobah wanda shi ne mai iko duka?​—Tit. 3:1.

“SHUGABANNIN GWAMNATI”

6. (a) Su wane ne shugabannin da aka ambata a Romawa 13:1 kuma mene ne aka umurce mu mu yi musu? (b) Wane alaƙa ne ke tsakanin dukan gwamnatocin ’yan Adam?

6 Karanta Romawa 13:1. A wannan ayar, “shugabannin gwamnati” suna nufin ’yan Adam da suke da iko kuma suke mulki a kan wasu. Dole ne Kiristoci su yi biyayya ga waɗannan shugabannin. Shugabannin sukan sa al’umma ta zauna lafiya, su sa mutane su bi dokoki kuma a wasu lokuta, sukan kāre bayin Jehobah. (R. Yar. 12:16) Don haka, an umurce mu mu ba su abubuwan da suke bukata, kamar haraji da ban girma, kuma mu ji tsoron su idan sun bukaci hakan. (Rom. 13:7) Amma Jehobah ne ya ƙyale shugabannin gwamnatin su kasance da ikon da suke da shi. Yesu ya nuna hakan a lokacin da gwamnan Roma mai suna Bilatus ya yi masa tambayoyi. Shi ya sa da Bilatus ya gaya wa Yesu cewa yana da ikon sake shi ko ya sa a kashe shi, Yesu ya gaya masa cewa: “Ikon da kake da shi a kaina iko wanda Allah ya ba ka ne kawai.” (Yoh. 19:11) Kamar yadda ikon Bilatus yake da iyaka, ikon da shugabannin gwamnati suke da shi a yau ma yana da iyaka.

7. A waɗanne yanayoyi ne bai kamata mu yi biyayya ga shugabannin gwamnati ba, kuma me ya kamata shugabannin su tuna?

7 Kiristoci suna yin biyayya ga shugabannin gwamnati idan dokokinsu bai taka dokar Allah ba. Amma ba ma yin biyayya ga shugabannin gwamnati idan sun ce mu yi abin da ya taka dokar Allah ko kuma idan sun ce kada mu yi abin da Allah ya ce mu yi. Za su iya umurci matasa su yi yaƙi a madadin ƙasar. c Ko kuma za su iya hana mu karanta Littafi Mai Tsarki ko littattafanmu ko su hana mu yin wa’azi ko bauta ma Jehobah tare. Idan shugabannin gwamnati sun yi amfani da ikonsu a hanyar da bai dace ba, kamar tsananta wa mabiyan Yesu, za su gamu da fushin Allah. Jehobah yana ganin abin da suke yi!​—M. Wa. 5:8.

8. Wane bambanci ne yake tsakanin Jehobah da shugabannin gwamnati kuma me ya sa muke bukatar mu san da hakan?

8 Hukumomin gwamnati suna da iko, amma ba su ne mafi iko ba. Jehobah ne mafi iko duka. A cikin Littafi Mai Tsarki, an kira shi “Mafi Ɗaukaka” a wurare da yaya.​—Dan. 7:​18, 22, 25, 27.

“MAFI ƊAUKAKA”

9. Mene ne annabi Daniyel ya ga a wahayi?

9 Annabi Daniyel ya ga wahayin da ya tabbatar mana cewa Jehobah yana da iko fiye da dukan gwamnatoci a duniya. Daniyel ya ga manyan dabbobi guda huɗu da ke wakiltar gwamnatoci mafi iko a duniya da suka wuce da wanda yake mulki a yanzu. Gwamnatocin su ne Babila da gwamnatin Midiya da Fasiya da Girka da Roma da kuma wanda take a zamaninmu, wato gwamnatin Birtaniya da Amirka. (Dan. 7:​1-3, 17) Sa’an nan Daniyel ya ga Jehobah yana zaune a kan kursiyinsa a sama inda yake yin shari’a. (Dan. 7:​9, 10) Abin da annabin ya gani bayan hakan, ya kamata ya zama gargaɗi ga shugabannin gwamnati a yau.

10. Bisa ga Daniyel 7:​13, 14, 27, su waye ne Allah zai ba wa mulkin duniya, kuma mene ne hakan ya nuna game da shi?

10 Karanta Dan. 7:​13, 14, 27. Allah zai ɗauke ikon da shugabannin gwamnati suke da shi kuma ya ba ma waɗansu da suka fi cancanta kuma suka fi iko. Su waye ke nan? Su ne “wani mai kamannin Ɗan mutum,” wato Yesu Kristi, da kuma “tsarkaka na Mafi Ɗaukaka,” wato shafaffu 144,000 da za su yi mulki “har abada abadin.” (Dan. 7:18) Babu shakka, Jehobah ne “Mafi Ɗaukaka” domin shi kaɗai ne zai iya ɗaukan irin matakin nan.

11. Mene ne kuma Daniyel ya rubuta da ya nuna cewa Jehobah ne Mafi Ɗaukaka?

11 Abin da Daniyel ya gani a wahayin ya jitu da abin da ya faɗa kafin wannan lokacin. Daniyel ya ce: “Allah na Sama . . .  yakan tuɓe sarakuna, ya kuma naɗa waɗansu.” Ya kuma ƙara da cewa: “Mafi Ɗaukaka shi ne yana mulki a kan dukan ’yan Adam. Shi ne yakan ba da mulki ga wanda ya ga dama.” (Dan. 2:​19-21; 4:17) Akwai lokutan da Jehobah ya taɓa cire sarakuna kuma ya naɗa wasu? Ƙwarai kuwa!

Jehobah ya karɓi mulkin Belshazzar daga hannunsa kuma ya ba da shi ga Midiya da Fasiya (Ka duba sakin layi na 12)

12. Ka ba da misalin da ya nuna yadda Jehobah ya tuɓe sarakuna a zamanin dā. (Ka duba hoton.)

12 Jehobah ya nuna a bayyane cewa shi ne Mafi Ɗaukaka. Ka yi la’akari da misalai uku da suka nuna hakan. Fir’auna sarkin Masar, ya mai da mutanen Jehobah bayi, kuma ya ƙi ya sake su. Amma Jehobah ya hallaka shi a Jar Teku. (Fit. 14:​26-28; Zab. 136:15) Sarki Belshazzar na Babila, ya yi biki kuma ya “nuna wa Ubangijin sama girman kai.” Ƙari ga haka, ya yabi “gumakan zinariya da na azurfa,” maimakon Jehobah. (Dan. 5:​22, 23) Amma Allah ya ƙasƙantar da wannan mutum mai taurin kai. “A daren nan” an kashe Belshazzar, kuma an ba da mulkinsa ga mutanen Midiya da Fasiya. (Dan. 5:​28, 30, 31) Sarki Hirudus Agaribas na ɗaya na ƙasar Falasɗinu, ya sa an kashe Yakubu, kuma ya sa Bitrus a kurkuku da niyar kashe shi. Amma Jehobah bai bar Hiridus ya yi abin da yake so ya yi ba. “Mala’ikan Ubangiji ya buge shi” kuma ya mutu.​—A. M. 12:​1-5, 21-23.

13. Ka ba da misalin yadda Jehobah ya hallaka ƙasashen da suka yi haɗin gwiwa.

13 Jehobah ya kuma nuna cewa shi ne mafi ɗaukaka ga ƙasashe da suka yi haɗin gwiwa. Ya yi faɗa a madadin Isra’ilawa, kuma ya taimaka musu su hallaka sarakuna 31 na Kan’aniyawa, hakan ya sa sun iya mamaye yawancin Ƙasar Alkawari. (Yosh. 11:​4-6, 20; 12:​1, 7, 24) Jehobah ya kuma taimaka ma Isra’ilawa su ci nasara a kan Sarki Ben-hadad da kuma wasu sarakuna 32 na ƙasar Siriya waɗanda suka yi yaƙi da Isra’ila.​—1 Sar. 20:​1, 26-29.

14-15. (a) Mene ne Sarki Nebuchadnezzar da Sarki Darius suka faɗa game da ikon Jehobah? (b) Mene ne marubucin Zabura ya faɗa game da Jehobah da kuma al’ummarsa?

14 Sau da dama, Jehobah ya nuna cewa shi ne Mafi Ɗaukaka! Sa’ad da Sarki Nebuchadnezzar na Babila ya buga kirji don ya nuna ‘ƙarfin ikonsa,’ da darajarsa da ɗaukakarsa, maimakon ya nuna cewa Jehobah ne ya cancanci yabo, Allah ya sa shi ya haukace. Bayan Nebuchadnezzar ya warke, ya “girmama Mafi Ɗaukaka” kuma ya amince cewa mulkin Jehobah “mulki ne na har abada.” Ya kuma ƙara da cewa: “Ba mai hana shi.” (Dan. 4:​30, 33-35) Bayan an gwada amincin Daniyel kuma Jehobah ya kāre shi a ramin zakuna, Sarki Darius ya ba da umurni cewa: “Kowa ya yi rawar jiki, ya kuma ji tsoron Allah na Daniyel. “Gama shi ne Allah Mai Rai, shi wanda yake na har abada ne! Mulkinsa ba za a taɓa halakar da shi ba, ikon mulkinsa na har abada ne.”​—Dan. 6:​7-10, 19-22, 26, 27.

15 Marubucin Zabura ya rubuta cewa: “Yahweh yakan lalatar da shirin al’ummai, yakan ɓata dabarar kabilu.” Ya kuma ƙara da cewa: “Mai albarka ce al’ummar da Yahweh shi ne Allahnta, jama’ar da ya zaɓa su zama gādonsa!” (Zab. 33:​10, 12) Wannan dalili ne mai kyau da ya sa ya kamata mu ci gaba da bin hanyar gaskiya ta Jehobah!

YAƘI NA ƘARSHE

Ba zai yi wa malaꞌikun Jehobah wuya su hallaka ƙasashe da suka yi haɗin gwiwa kuma suke gāba da shi da mutanensa ba (Ka duba sakin layi na 16-17)

16. Mene ne za mu iya tabbatarwa a lokacin ƙunci mai girma, kuma me ya sa? (Ka duba hoton.)

16 Mun karanta abin da Jehobah ya yi a zamanin dā. Don haka, mene ne za mu sa rai cewa zai faru a nan gaba? Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai kāre bayinsa masu aminci a lokacin ƙunci mai girma ko kuma “azaba mai zafi.” (Mat. 24:21; Dan. 12:1) Zai yi hakan a lokacin da haɗin gwiwa na ƙasashe da ake kira Gog na Magog za su kai wa bayin Allah hari a duk faɗin duniya. Ko da dukan ƙasashe 193 na Majalisar Ɗinkin Duniya, suna cikin haɗin gwiwar, ba za su iya yin faɗa da Mafi Ɗaukaka da kuma mala’ikunsa ba! Jehobah ya yi alkawari cewa: “Zan bayyana girmana da tsarkina in kuma sanar da kaina a fili ga al’ummai da yawa. Sa’an nan za su sani cewa ni ne Yahweh.”​—Ezek. 38:​14-16, 23; Zab. 46:10.

17. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce zai faru da sarakunan duniya da kuma masu gaskiya a zuci?

17 Harin da Gog zai kawo, zai jawo yaƙi na ƙarshe a Armageddon, kuma a lokacin Jehobah zai hallaka “dukan sarakunan duniya.” (R. Yar. 16:​14, 16; 19:​19-21) Amma akasin haka, “mai gaskiya a zuci zai zauna a ƙasar, marar laifi ne zai kasance a cikinta.”​—K. Mag. 2:21.

DOLE NE MU BI HANYAR GASKIYA

18. Mene ne Kiristoci da yawa suka ƙudiri niyyar yi, kuma me ya sa? (Daniyel 3:28)

18 A duk tarihi, Kiristoci da yawa sun sadaukar da ꞌyancinsu da kuma ransu domin Jehobah, wanda shi ne Mafi Ɗaukaka. Ba su fasa bin hanyar gaskiya ba, sun ƙudiri niyyar ci gaba da bin hanyar gaskiya. Suna kamar Yahudawa guda uku da suka ci gaba da bauta wa Mafi Ɗaukaka wanda ya cece su daga cikin wuta.​—Karanta Daniyel 3:28.

19. Wane dalili ne zai sa Jehobah ya yi wa mutanensa shari’a, kuma mene ne ya zama wajibi mu yi yanzu?

19 Dauda marubucin Zabura ya rubuta muhimmancin ci gaba da bin hanyar gaskiya ta Jehobah, ya ce: “Yahweh, kai ne mai hukunta kabilu. Ya Yahweh, ka yi mini shari’a bisa ga adalcina, gama ka sani ba ni da laifi.” (Zab. 7:8) Dauda ya sake rubuta cewa: “Bari mutunci da gaskiya su kiyaye ni.” (Zab. 25:21) Abu mafi muhimmanci shi ne mu ci gaba da kasancewa da amincinmu, kuma kada mu daina bin hanyar gaskiya ko da mene ne zai faru! Idan mun yi hakan, mu ma za mu yi farin ciki kamar marubucin Zabura da ya ce: “Masu albarka ne masu bin hanyar gaskiya a zuci, masu tafiya cikin Koyarwar Yahweh!”​—Zab. 119:1.

WAƘA TA 122 Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!

a Littafi Mai Tsarki ya gaya wa Kiristoci su yi biyayya ga hukumomin gwamnati na wannan duniyar. Amma wasu gwamnatoci ba sa son Jehobah da kuma bayinsa. Ta yaya za mu yi biyayya ga gwamnatocin ’yan Adam kuma mu ci gaba da bin hanyar gaskiya ta Jehobah?

b MA’ANAR WASU KALMOMI: Bin hanyar gaskiya yana nufin kasancewa da aminci ga Jehobah ko da yin hakan zai yi mana wuya.