TALIFIN NAZARI NA 29
Ka Goyi Bayan Shugabanmu Yesu
“An ba ni dukan iko a sama da kuma nan duniya.”—MAT. 28:18.
WAƘA TA 13 Mu Riƙa Bin Misalin Yesu
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. Mene ne Jehobah yake so mu yi a yau?
A YAU, Allah yana so mu yi wa’azin Mulkinsa a duk faɗin duniya. (Mar. 13:10; 1 Tim. 2:3, 4) Aikin da Jehobah ya ba mu ke nan, kuma aikin yana da muhimmanci shi ya sa ya zaɓi Ɗansa da yake ƙauna ya ja-goranci aikin. Mun san cewa a ƙarƙashin ja-gorancin Yesu, za mu yi aikin da Jehobah ya ba mu kafin ƙarshe ya zo.—Mat. 24:14.
2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
2 A wannan talifin, za mu ga yadda Yesu yake amfani da “bawan nan mai aminci, mai hikima” don ya yi wa mabiyansa tanadin abubuwan da za su ƙarfafa bangaskiyarsu, kuma ya tsara su don wa’azi mafi girma a tarihin ʼyan Adam. (Mat. 24:45) Kuma za mu ga abin da kowannenmu zai iya yi don ya goyi bayan bawan nan mai aminci.
YESU YANA MANA JA-GORANCI A WA’AZI
3. Wane iko ne aka ba Yesu?
3 Yesu ne yake mana ja-goranci a wa’azi. Ta yaya muka san hakan? Jim kaɗan kafin ya koma sama, Yesu ya yi taro da mabiyansa masu aminci a kan wani tudu a Galili. Ya gaya musu cewa: “An ba ni dukan iko a sama da kuma nan duniya.” Ku lura da abin da ya faɗa bayan hakan, ya ce: “Ku je ku faɗa wa dukan al’umman duniya su bi ni, ku sa su zama almajiraina.” (Mat. 28:18, 19) Saboda haka, ɗaya daga cikin abubuwan da aka ba Yesu shi ne ikon yin ja-goranci a wa’azin Mulkin Allah.
4. Ta yaya za mu kasance da tabbaci cewa Yesu ne yake yin ja-goranci a wa’azi har a yau?
4 Yesu ya ce za a yi wa’azin Mulkin Allah da kuma almajirtar da mutane a duk faɗin duniya, kuma zai kasance da mabiyansa “kullum har ƙarshen zamani.” (Mat. 28:20) Wannan furucin ya nuna cewa Yesu ne zai ci gaba da yin ja-goranci a wa’azi har zuwa zamaninmu.
5. Ta yaya muke sa annabcin da ke Zabura 110:3 ya cika?
5 Yesu bai ji tsoro cewa za a yi ƙarancin ma’aikata a ƙarshen zamani ba don ya san cewa abin da wani marubucin zabura ya annabta zai cika. Annabcin ya ce: “Da yardar rai, mutanenka za su miƙa kansu, a ranar da ka bi da sojojinka.” (Zab. 110:3) Idan kana yin wa’azin Mulkin Allah, kana goyon bayan Yesu da bawan nan mai aminci ne kuma kana taimakawa a cika wannan annabcin. Aikin yana ci gaba, amma akwai ƙalubale.
6. Wane ƙalubale ne masu shela suke fuskanta a yau?
6 Wani ƙalubale da masu shela suke fuskanta shi ne hamayya. ʼYan ridda da malaman addinai da kuma ʼyan siyasa sun sa mutane su kasance da ra’ayin da bai dace ba game da wa’azin da muke yi. Idan danginmu da abokan aikinmu da kuma wasu mutane sun yarda da ƙaryace-ƙaryacen nan, suna iya matsa mana mu daina bauta wa Jehobah da kuma yin wa’azi. A wasu ƙasashe, maƙiyanmu suna yi mana barazana da kuma kai mana hari, har ma da saka wasu ʼyan’uwa a kurkuku. Hakan ba ya ba mu mamaki domin Yesu ya ce: “Duniya duk za ta ƙi ku saboda sunana.” (Mat. 24:9) Da yake mutane suna tsananta mana, hakan ya nuna cewa Jehobah ya amince da mu. (Mat. 5:11, 12) Shaiɗan ne yake sa su yi hakan. Amma Yesu ya fi ƙarfinsa! Da taimakon Yesu, muna yi wa mutane a duk faɗin duniya wa’azi.
7. Wane tabbaci ne muke da shi cewa abin da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:6, 7 yana cika?
7 Wata matsala kuma da muke fuskanta sa’ad da muke wa’azi ita ce mutane da yawa ba sa jin yarenmu. A Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna, Yesu ya annabta cewa za a shawo kan wannan matsalar a zamaninmu. (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:6, 7.) Ta yaya? Muna ba wa mutane damar saurarar saƙon Mulkin Allah. A yau, mutane a faɗin duniya suna iya karanta littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki a shafinmu na jw.org domin yana ɗauke da bayanai a yaruka fiye da 1,000! An ba da izinin fassara littafin da muke amfani da shi don nazari da mutane, wato Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! a yaruka fiye da 700! Ƙari ga haka, ana wallafa bidiyoyi don kurame da kuma littattafai don makafi. Muna ganin yadda annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suke cika. Mutane “daga kowane yare na kowace al’umma” suna koyan “tsabtacciyar magana,” wato gaskiyar da ke Kalmar Allah. (Zak. 8:23; Zaf. 3:9) Ana cim ma hakan ne domin ja-goranci mai kyau da Yesu Kristi yake yi mana.
8. Wane sakamako ne ake samu don wa’azin da muke yi?
8 A yau, mutane fiye da 8,000,000 a ƙasashe 240 suna cikin ƙungiyar Jehobah, kuma a kowace shekara, ana yi wa dubban mutane baftisma! Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne halaye masu kyau da waɗannan sabbin Kiristoci suke nunawa, wato “sabon halin nan.” (Kol. 3:8-10) Da yawa sun daina lalata, da zalunci, da nuna bambanci da kuma kishin ƙasa. Annabcin da ke Ishaya 2:4 yana cika. Wurin ya ce: “Al’umma ba za ta . . . ƙara koyon dabarar yaƙi kuma ba.” Yayin da muke ƙoƙari mu ɗau sabon hali, muna taimaka wa mutane su shigo ƙungiyar Jehobah kuma muna nuna cewa muna bin ja-gorancin Yesu. (Yoh. 13:35; 1 Bit. 2:12) Abubuwan nan suna faruwa ne domin Yesu ne yake taimaka mana.
YESU YA NAƊA BAWA
9. Kamar yadda Matiyu 24:45-47 suka nuna, mene ne aka annabta game da kwanakin ƙarshe?
9 Karanta Matiyu 24:45-47. Yesu ya yi annabci cewa a kwanakin ƙarshe, zai naɗa “bawan nan mai aminci, mai hikima” domin ya yi wa mabiyansa tanadin abin da zai ƙarfafa bangaskiyarsu. Hakan yana nufin bawan nan zai riƙa yin aiki tuƙuru a zamaninmu. Abin da yake faruwa ke nan. Shugabanmu ya yi amfani da ƙaramin rukunin maza da ya naɗa domin ya yi mana da kuma waɗanda suke so su koya game da Allah tanadin “abincinsu a kan lokaci.” Waɗannan mazan ba sa ɗaukan kansu a matsayin shugabannin mabiyan Yesu. (2 Kor. 1:24) A maimakon haka, sun san cewa Yesu ne ‘shugaba da mai-mulkinsu.’—Isha. 55:4, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
10. Wanne ne daga cikin littattafan da ke hoton ya taimaka maka ka soma bauta wa Jehobah?
10 Tun daga 1919, bawan nan mai aminci ya shirya littattafai dabam-dabam da suka taimaka wa masu son gaskiya su fara koya game da Allah. A 1921, bawan nan ya wallafa littafin nan, The Harp of God don a taimaka wa mutane su koyi gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. Da shigewar lokaci, bawan ya wallafa wasu littattafai. Wanne ne daga cikin waɗannan littattafan ya taimaka maka ka san Allah kuma ka soma ƙaunar sa? Shin littafin nan “Let God Be True,” ko Gaskiya Mai-bishe Zuwa Rai Madawwami, ko Kana Iya Rayuwa Har Abada Cikin Aljanna a Duniya, ko Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, ko Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? ko kuma Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! wanda shi ne sabon littafinmu? An wallafa waɗannan littattafan ne don mu taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu, kuma an wallafa kowannensu a daidai lokacin da muke bukatarsa.
11. Me ya sa yake da muhimmanci dukanmu mu ci gaba da koya game da Jehobah da kuma Littafi Mai Tsarki?
11 Ba sabbi ba ne kaɗai suke bukatar su koyi batutuwa masu zurfi game da Jehobah. Mu ma muna bukatar hakan. Manzo Bulus ya ce: “Abinci mai kauri shi ne na waɗanda suka yi girma.” Bulus ya ƙara da cewa idan muna cin irin abincin nan, za mu “iya bambanta nagarta da mugunta.” (Ibran. 5:14) A wannan lokaci da mutane da yawa ba su da ɗabi’u masu kyau, yana iya yi mana wuya mu bi ƙa’idodin Jehobah. Amma Yesu yana tabbata cewa muna samun abubuwan da muke bukata don mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu. Muna samun waɗannan abubuwan ne daga Kalmar Allah, wato Littafi Mai Tsarki. Bawan nan mai aminci yana shirya wannan abincin ne kuma yana rarraba shi a ƙarƙashin ja-gorancin Yesu.
12. Ta yaya muke ɗaukan sunan Allah kamar yadda Yesu ya yi?
12 Kamar yadda Yesu ya yi, muna ɗaukaka sunan Allah. (Yoh. 17:6, 26, THS) Alal misali, a shekara ta 1931, mun soma amfani da sunan nan Shaidun Jehobah, wanda aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki. Yin hakan ya nuna cewa sunan Allah yana da muhimmanci a gare mu. (Isha. 43:10-12) Kuma tun watan Oktoba na shekarar, sunan Allah ya ci gaba da bayyana a shafin farko na wannan mujallar. Ƙari ga haka, a juyin New World Translation of the Holy Scriptures mun maido da sunan Allah inda ya kamata ya kasance. Hakan ya sa mun bambanta da cocin Kiristendom da suka ciccire sunan Allah, Jehobah a Littafi Mai Tsarki da suka fassara!
YESU YA TSARA MABIYANSA
13. Mene ne ya tabbatar maka cewa Yesu yana amfani da “bawan nan mai aminci, mai hikima” a yau? (Yohanna 6:68)
13 Ta wajen yin amfani da “bawan nan mai aminci, mai hikima,” Yesu ya tsara ƙungiyar da take ɗaukaka bauta ta gaskiya a duniya. Mene ne ra’ayinka game da wannan ƙungiyar? Mai yiwuwa kai ma kana da ra’ayi ɗaya da manzo Bitrus da ya gaya wa Yesu cewa: “Wurin wane ne za mu je? Ai, kai ne kake da magana mai ba da rai na har abada.” (Yoh. 6:68) A ina za mu kasance a yau, da ba mu shiga ƙungiyar Jehobah ba? Yesu yana amfani da ƙungiyar nan don ya yi mana tanadin abubuwan da muke bukata don mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Yana koya mana yadda za mu yi wa’azi kuma mu sami sakamako mai kyau. Ƙari ga haka, yana taimaka mana mu koyi “sabon hali” don mu faranta wa Jehobah rai.—Afis. 4:24.
14. Ta yaya ka amfana daga kasancewa a ƙungiyar Jehobah a lokacin annobar korona?
14 Yesu yana mana ja-goranci mai kyau a mawuyacin lokaci. Mun ga amfanin wannan ja-gorancin a lokacin annobar korona. A lokacin da mutane da yawa a duniya ba su san abin da za su yi ba, Yesu ya ba mu umurnin da muke bukata domin mu kāre kanmu. An ƙarfafa mu mu riƙa saka takunkumin fuska idan za mu je wuraren da mutane suke kuma mu riƙa ba wa mutane tazara. An gaya wa dattawa su riƙa tuntuɓar ʼyan’uwa a ikilisiya don su san abubuwa da suke bukata don kāre lafiyarsu da kuma ƙarfafa bangaskiyarsu. (Isha. 32:1, 2) Ƙari ga haka, muna samun umurni da kuma ƙarfafa ta wajen ƙarin bayani daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu.
15. Wane umurni game da yin taro da kuma wa’azi ne muka samu a lokacin annobar korona, kuma wane sakamako ne aka samu?
15 A lokacin annobar korona, an ba mu umurni game da yadda za mu riƙa yin taron ikilisiya da kuma wa’azi. Nan da nan muka soma yin taron ikilisiya da babban taro ta intane. Ƙari ga haka, mun soma yin wa’azi ta wajen rubuta wasiƙu da kuma kira ta waya. Jehobah ya albarkaci ƙoƙarin da muka yi. Ofisoshinmu a ƙasashe da yawa sun ba da rahoto cewa ana samun ƙarin masu shela sosai. Akwai labarai da yawa game da hakan.—Ka duba akwatin nan “ Jehobah Yana Yi wa Wa’azin da Muke Yi Albarka.”
16. Wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi?
16 Wasu suna iya tunanin cewa matakan da ƙungiyar Jehobah ta ɗauka a kan annobar korona sun wuce gona da iri. Amma sau da yawa mun lura cewa matakan da ƙungiyar Jehobah ta ɗauka sun dace. (Mat. 11:19) Yayin da muke tunani a kan yadda Yesu yake yi wa mutanensa ja-goranci, zai dace mu kasance da tabbaci cewa ko da mene ne zai faru gobe, Jehobah da Ɗansa da yake ƙauna za su kasance tare da mu.—Karanta Ibraniyawa 13:5, 6.
17. Yaya kake ji domin kana aiki a ƙarƙashin ja-gorancin Yesu?
17 Muna farin ciki sosai cewa Yesu ne yake yi mana ja-goranci! Muna cikin ƙungiyar da ba a nuna bambancin al’ada ko ƙasa ko kuma yare. Muna samun umurni sosai daga Kalmar Allah da kuma horarwa da muke bukata don mu yi aikin da Allah ya ba mu. Ana koya wa kowannenmu yadda zai riƙa nuna sabon hali da kuma ƙauna. Muna da dalilai da yawa da za su sa mu yi alfahari da shugabanmu Yesu!
WAƘA TA 16 Mu Yabi Jehobah Domin Ɗansa
^ Akwai miliyoyin maza da mata da yara da suke yin wa’azin Mulkin Allah da ƙwazo. Kana cikinsu? Idan haka ne, kana bin ja-gorancin Ubangijinmu Yesu Kristi. A wannan talifin, za mu ga abin da ya tabbatar mana cewa Yesu yana yi mana ja-goranci a wa’azin da muke yi a yau. Yin tunani a kan abin da za mu tattauna zai taimaka mana mu ƙuduri niyyar ci gaba da bauta wa Jehobah a ƙarƙashin ja-gorancin Yesu.