Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Rika Waka da Farin Ciki!

Ka Rika Waka da Farin Ciki!

“Ya yi kyau a raira yabbai ga Allahnmu.”​—ZAB. 147:1.

WAƘOƘI: 10, 2

1. Mene ne waƙa takan sa mu yi?

WANI sanannen mawaƙi ya ce: “Kalmomi sukan sa ka yi tunani. Kiɗa takan sa ka yi farin ciki ko kuma baƙin ciki. Amma waƙa takan ratsa zuciyarka.” Duk da haka, abubuwan da za su sa mu farin ciki su ne kalaman da muke yi don mu yabi Jehobah mahaliccinmu, ko ba haka ba? Shi ya sa yin waƙa yake da muhimmanci a ibadarmu ga Jehobah, ko da mu kaɗai muka yi waƙar ko a taro.

2, 3. (a) Yaya wasu suke ɗaukan yin waƙa da babbar murya a taro? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?

2 Yaya kake ɗaukan yin waƙa da babbar murya a taro? Shin kana jin kunyar yin hakan? A wasu al’adu, maza ba sa son yin waƙa a cikin jama’a. Irin wannan ra’ayin zai iya shafan ’yan’uwa a ikilisiya musamman ma idan dattawa ko waɗanda suke taimaka musu ba sa waƙa ko sukan yi wasu hidimomi sa’ad da ake waƙa a taro.​—Zab. 30:12.

3 Idan muka ɗauki yin waƙa da muhimmanci, ba za mu riƙa fita sa’ad da ake yin waƙa a taro ba. Saboda haka, zai dace kowanenmu ya tambayi kansa: ‘Ina ɗaukan yin waƙa a taro da muhimmanci kuwa? Ta yaya zan shawo kan tsoron yin waƙa da babbar murya a taro? Me zan yi don in iya furta kalaman waƙa da ake yi a taro da kyau?’

YIN WAƘA YANA DA MUHIMMANCI A BAUTA TA GASKIYA

4, 5. Yaya Isra’ilawa suka tsara yadda za a riƙa waƙa don ibada a dā?

4 Bayin Jehobah masu aminci a dā sun yi amfani da kaɗe-kaɗe don su yabi Jehobah. Wannan dalilin ne ya sa Isra’ilawa da suka bauta wa Jehobah a dā da aminci suka ɗauki yin waƙa da muhimmanci a ibadarsu. Alal misali, Sarki Dauda ya tsara Lawiyawa 4,000 su riƙa kaɗe-kaɗe a haikali sa’ad da ake ibada. Akwai mutane 288 a cikinsu “waɗanda aka koya masu su yi waƙa ga Ubangiji, watau dukan gwannai.”​—1 Laba. 23:5; 25:7.

5 Mutane sun yi kaɗe-kaɗe da waƙa a lokacin da ake keɓe haikalin. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’anda masu-ƙaho da mawaƙa suka yi muwafaka, da za a ji muryarsu baki ɗaya ta yabo da godiya ga Ubangiji: sa’anda suka ta da muryarsu da ƙahoni, da kuge da kayan waƙa, suna yabon Ubangiji, . . . ɗaukakar Ubangiji ta cika gidan Allah.” Babu shakka, hakan ya ƙarfafa bangaskiyar duk waɗanda suke wurin.​—2 Laba. 5:​13, 14; 7:6.

6. Yaya Nehemiya ya tsara yin waƙa a lokacin da yake gwamnan Urushalima?

6 A lokacin da Nehemiya ya ja-goranci Isra’ilawa masu aminci wajen gina ganuwar Urushalima, ya tsara Lawiyawa su zama mawaƙa. Mutane sun ji daɗin waƙa na musamman da aka yi a lokacin da aka keɓe ganuwar da aka sake gina. A wannan lokacin, akwai “jama’an nan biyu na masu-yin godiya.” Wasu sun bi gefen dama suna waƙa a wannan gefen wasu kuma suka bi gefen hagu har suka haɗu a bangon da ke kusa da haikalin don mutane da ke nesa su ji waƙar da kiɗan. (Neh. 12:​27, 28, 31, 38, 40, 43) Babu shakka, Jehobah ya yi farin ciki sosai sa’ad da ya ji bayinsa suna waƙa don su yabe shi.

7. Ta yaya Yesu ya nuna muhimmancin yin waƙa a ibadarmu?

7 Tun daga lokacin da aka kafa ikilisiyar Kirista, ana ɗaukan yin waƙoƙi da muhimmanci sosai a ibada. A dare na ƙarshe kafin a kashe Yesu, shi da almajiransa sun yi waƙoƙi bayan da ya kafa Jibin Maraice na Ubangiji.​—Karanta Matta 26:30.

8. Ta yaya Kiristoci a ƙarni na farko suka kafa mana misali mai kyau a yin waƙa?

8 Kiristoci a ƙarni na farko ma sun yabi Allah da waƙoƙi tare. Ko da yake suna yin taro a gidajen ’yan’uwa, hakan bai hana su yin waƙoƙi don su yabi Jehobah ba. Shi ya sa Allah ya hure manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci cewa: “Kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matukar hikima ta yin waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma yi wa Allah waƙa, kuna gode masa a zuci.” (Kol. 3:​16, Littafi Mai Tsarki) Babu shakka, muna waƙoƙin da ke littafin waƙarmu don mu gode wa Allah ne. Waɗannan waƙoƙin suna cikin abubuwan da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya ba mu don mu ƙarfafa dangantakarmu da Allah.​—Mat. 24:45.

YADDA ZA KA DAINA TSORONYIN WAƘA

9. (a) Me zai iya hana wasu yin waƙa da babbar murya a taron ikilisiya da manyan taro? (b) Yaya za mu yabi Jehobah da waƙoƙi, kuma su wa ya kamata su kafa misali mai kyau? (Ka duba hoton da ke shafi na 3.)

9 Me za ka yi idan ba ka saba yin waƙa a iyalinku ko al’adarku da kuma a wurin da kake zama ba? Da yake fasaha yana ko’ina, za ka ji daɗin sauraron waƙoƙin mawaƙa da suka ƙware a yin waƙa. Amma za ka iya jin kunya ko kuma ka yi baƙin ciki a lokacin da ka gwada muryarka da nasu. Duk da haka, wannan bai kamata ya hana ka yabon Jehobah da waƙoƙi ba. A maimakon haka, zai dace ka riƙe littafin waƙarka da kyau ka kuma dāga kanka kuma ka yi waƙa da babbar murya! (Ezra 3:11; karanta Zabura 147:1.) A yawancin Majami’un Mulki, ana nuna waƙoƙin da ake yi a talabijin kuma hakan yana taimaka wa ’yan’uwa su yi waƙa da babbar murya. Ƙari ga haka, don a nuna cewa waƙoƙi suna da muhimmanci a ibadarmu, an saka sashen yin waƙa a Makarantar Hidima ta Mulki da dattawa suke zuwa. Hakan ya nuna cewa ya kamata dattawa su kafa misali mai kyau ta ɗaukan yin waƙa a taro da muhimmanci.

10. Me ya kamata mu tuna idan tsoro yana hana mu yin waƙa?

10 Wani abu kuma da yake hana wasu yin waƙa da babbar murya shi ne tsoro. Suna tsoro cewa za a ji muryarsu kuma wataƙila muryarsu ba ta da daɗi. Amma ya kamata mu tuna cewa “dukanmu mukan yi tuntuɓe” sa’ad da muke magana. (Yaƙ. 3:2) Kuma hakan ba ya hana mu yin magana. Don haka, me ya sa ba za mu yabi Jehobah ba don muryarmu ba ta daɗi?

11, 12. Wace shawara ce za ta taimaka mana mu kyautata yadda muke yin waƙa?

11 Wataƙila muna fargaban yin waƙa don ƙila ba mu san yadda za mu yi waƙar ba. Duk da haka, za mu iya kyautata yadda muke waƙa ta wurin bin wannan shawarar. *

12 Za ka iya koyan yin waƙa da babbar murya idan kana jan numfashi sosai kafin ka yi hakan. Kamar yadda wutan lantarki yake haskaka ƙwan wuta, numfashi yakan taimaka mana mu yi magana ko waƙa da kyau. Don haka, ya kamata ka yi waƙa da babbar murya fiye da yadda kake magana. (Ka duba shawarar da ke littafin Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafuffuka na 181 zuwa 184, mai jigo “Properly Control Your Air Supply.”) Hakika, a Nassosin da suka yi magana game da yin waƙa, an ƙarfafa bayin Jehobah su riƙa yin waƙa da “babban amo” ko murya.​—Zab. 33:​1-3.

13. Ka bayyana yadda za ka sami gaba gaɗin yin waƙa.

13 A lokacin da kuke ibada ta iyali ko kuma sa’ad da kake nazarinka, ka bi wannan shawarar: Ka zaɓi waƙar da ka fi so daga littafin waƙarmu. Ka karanta shi da babbar murya da kuma gaba gaɗi. Bayan haka, da wannan muryar ka furta kalmomin layi ɗaya a lokaci ɗaya. Sai ka yi waƙar da wannan babbar murya. (Isha. 24:14) Idan ka yi hakan, za ka kyautata muryarka kuma za ka ji daɗin yin waƙar. Kada tsoro ko kunya ya hana ka yin hakan!

14. (a) Ta yaya buɗe baki da kyau sa’ad da muke waƙa zai taimaka mana? (Ka duba akwatin nan “ Yadda Za Ka Kyautata Yadda Kake Waƙa.”) (b) Waɗanne shawarwari za su taimaka mana idan ba mu da muryar yin waƙa?

14 Ba za ka iya yin waƙa da babbar murya ba sai ka buɗe bakinka da kyau. Don haka, wani abu da zai taimaka maka shi ne idan kana buɗe bakinka da kyau sa’ad da kake waƙa fiye da yadda kake buɗewa idan kana magana. To, me za ka yi idan kana gani kamar ba ka da babbar murya ko kuma kana ji ba ka waƙar yadda ta dace? Za ka sami shawarwari da za su taimaka maka a littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, shafi na 184, a akwatin nan mai jigo “Overcoming Specific Problems.”

KA RIƘA YABON JEHOBAH DA DUKAN ZUCIYARKA

15. (a) Wace sanarwa aka yi a taron shekara-shekara da aka yi a 2016? (b) Me ya sa aka wallafa wannan sabon littafin waƙa?

15 ’Yan’uwa sun yi farin ciki sosai a taron shekara-shekara na 2016 da aka yi a Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania a lokacin da Ɗan’uwa Stephen Lett da ke cikin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ya sanar cewa an fito da sabon littafin waƙa mai jigo Ku Rera Waƙa da Murna ga Jehobah, kuma ya ce za a soma amfani da shi a taro ba da jimawa ba. Ɗan’uwa Lett ya bayyana cewa wani abu da ya sa aka kyautata littafin waƙar shi ne don kalaman su yi daidai da wanda ke cikin fassarar New World Translation of the Holy Scriptures na 2013. Don haka, an cire ko kuma canja wasu furuci da aka daina amfani da su a fassarar New World Translation na 2013. Ban da haka ma, an ƙara wasu waƙoƙi game da yin wa’azi da kuma waƙoƙin nuna godiya game da fansa. Ƙari ga haka, da yake yin waƙa yana da muhimmanci a ibadarmu, Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah sun so su wallafa wani littafin waƙa mai kyau da bangonsa zai yi daidai da na New World Translation na 2013 da aka kyautata.

16, 17. Wace gyara aka yi a littafin waƙarmu?

16 Ana son ya yi wa mutane sauƙi su yi amfani da littafin waƙar Ku Rera Waƙa da Murna ga Jehobah, shi ya sa aka tsara waƙoƙin bisa batun da suke magana a kai. Alal misali, waƙoƙi 12 na farko sun yi magana game da Jehobah ne. Waƙoƙi 8 da suke biye da su kuma sun yi magana ne game da Yesu da fansa da dai sauransu. Ban da haka ma, an saka fihirisa da zai taimaka ma masu jawabi wajen zaɓan waƙar da za a yi a jawabinsu.

17 Don a taimaka wa mutane su iya yin waƙar, an canja wasu kalamai kuma aka cire wasu da ba a amfani da su don mu fahimci waƙar da kyau. Alal misali, an cire furucin nan “tsawon-jimrewa” kuma aka saka “haƙuri” sai aka kyautata jimlar. Ƙari ga haka, an canja jigon nan “Guard Your Heart” (Ka Ƙāre Zuciyarka) a littafin waƙa na dā zuwa “Mu Riƙa Ƙāre Zuciyarmu.” Me ya sa? A cikin waɗanda suke halartar taron ikilisiya da manyan taro, akwai sababbi da waɗanda muke nazari da su da matasa da kuma ’yan’uwa mata da idan suna waƙar zai zama kamar suna gaya ma wasu abin da ya kamata su yi. Don haka, an canja jigon da wasu kalamai a ciki.

Ku koyi yin waƙa sa’ad da kuke yin ibada ta iyali (Ka duba sakin layi na 18)

18. Me ya sa yake da muhimmanci mu koyi waƙoƙin da ke sabon littafin waƙarmu? (Ka duba ƙarin bayani.)

18 Waƙoƙi da yawa addu’o’i ne a sabon littafin waƙarmu na Ku Rera Waƙa da Murna ga Jehobah. Waɗannan waƙoƙin za su taimaka mana mu bayyana wa Jehobah yadda muke ji. Wasu waƙoƙi kuma za su taimaka mana mu ƙarfafa “juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka.” (Ibran. 10:24) Don haka, ya kamata mu koyi yadda ake waƙar da kuma kalaman waƙoƙinmu. Idan muna yin waƙar a gida a kai a kai, za mu iya yin waƙoƙin da babbar murya kuma da gaba gaɗi. *

19. Ta yaya kowa a ikilisiya zai yi ibada ga Jehobah?

19 Bai kamata mu manta da cewa yin waƙa yana da muhimmanci a ibadarmu ba. Yin hakan hanya ce babba ta nuna godiya ga Jehobah da kuma nuna muna ƙaunarsa. (Karanta Ishaya 12:5.) Idan kana waƙa da babbar murya, hakan zai ƙarfafa wasu ma su yi hakan. Babu shakka, dukanmu a ikilisiya, wato yara da manya da kuma sababbi za mu iya yin waƙa a ibadarmu ga Jehobah. Don haka, kada ka yi fargaba sa’ad da kake waƙa. A maimakon haka, ka yi abin da marubucin wannan zabura da aka hure ya ce: “A raira ga Ubangiji.” Hakika, ka yi waƙa da babbar murya ga Jehobah!​—Zab. 96:1.

^ sakin layi na 11 Don samun ƙarin bayani a kan yadda za mu kyautata yadda muke yin waƙa, ka duba JW Broadcasting na watan Disamba na 2014 a Turanci (ka shiga video category FROM OUR STUDIO).

^ sakin layi na 18 Don mu ji daɗin manyan taro, ana soma tsarin ayyukan da kaɗe-kaɗe na minti goma. An tsara kowace waƙa don ta taimaka mana mu shirya zukatanmu don jawaban da za a yi. Saboda haka, ana ƙarfafa mu mu zauna don mu saurari waƙoƙin sa’ad da aka sa sautin.