Ka Dogara ga Jehobah Don Ka Rayu!
Ka “Dogara ga Yahweh da dukan zuciyarka, kada ka dogara ga ganewarka.”—K. MAG. 3:5.
1. Me ya sa dukanmu muke bukatar a ƙarfafa mu?
DUKANMU muna bukatar a riƙa ƙarfafa mu don wataƙila muna yawan damuwa, ko an ci amanarmu ko kuma muna fuskantar matsaloli. Ƙari ga haka, mai yiwuwa an yi mana rasuwa ko kuma muna rashin lafiya don mun tsufa. Ban da haka, mutane suna wulaƙanta wasu cikinmu kuma muna ganin mugunta a ko’ina. Hakika, wannan yanayin ya nuna cewa mutane suna ‘shan wahala sosai’ don muna “kwanakin ƙarshe” kuma hakan yana nuna mana cewa Mulkin Allah ya kusa. (2 Tim. 3:1) Duk da haka, wataƙila mun daɗe muna jira mu ga cikar alkawuran Jehobah ko kuma matsalolinmu suna ƙaruwa. Saboda haka, a ina ne za mu sami ƙarfafa?
2, 3. (a) Mene ne muka sani game da Habakkuk? (b) Me ya sa za mu bincika littafin Habakkuk?
2 Za mu bincika littafin Habakkuk don mu sami amsar. Littafinsa ya ƙarfafa mu sosai ko da yake Nassosi ba su yi bayani dalla-dalla game da rayuwar Habakkuk da ayyukansa ba. Wataƙila sunansa yana nufin “runguma cikin ƙauna.” Hakan yana nuna yadda Jehobah yake ƙarfafa mu kamar yana Hab. 2:2.
rungumar mu ko kuma yadda bayinsa suke dogara gare shi. Habakkuk ya yi magana da Allah kuma ya yi masa wasu tambayoyi. Hakika, Habakkuk ya yi tambaya a madadinmu, tun da yake Jehobah ya hure shi ya rubuta abin da suka tattauna.—3 Yadda wannan annabi mai baƙin ciki ya tattauna da Jehobah ne kawai aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki. Littafin Habakkuk yana cikin littattafan da “aka rubuta tun dā” da ke cikin Kalmar Allah “domin a koyar da mu.” Ƙari ga haka, littafin na “sa mu zama da sa zuciya ta wurin jimrewa da ƙarfafawa waɗanda Rubutacciyar Maganar Allah sukan ba mu.” (Rom. 15:4) Ta yaya za mu amfana daga littafin Habakkuk? Littafin zai taimaka mana mu san abin da yake nufi mu dogara ga Jehobah. Ƙari ga haka, ya tabbatar mana da cewa zai yiwu mu natsu duk da cewa muna fuskantar matsaloli. Saboda haka, bari mu bincika littafin Habakkuk sosai.
KU YI ADDU’A GA JEHOBAH
4. Me ya sa Habakkuk ya yi baƙin ciki?
4 Karanta Habakkuk 1:2, 3. Habakkuk ya yi rayuwa a mawuyacin lokaci. Mutane da ke rayuwa a zamaninsa mugaye ne kuma hakan ya sa shi baƙin ciki. Ya so ya ga lokacin da za a daina mugunta. Me ya sa ya daɗe sosai kafin Jehobah ya ɗauki mataki? Habakkuk ya ga cewa mutane suna rashin adalci da zalunci a ko’ina. Sai ya ji kamar ba mai taimaka masa, shi ya sa ya roƙi Jehobah ya ɗauki mataki. Wataƙila Habakkuk ya soma tunani cewa Jehobah bai damu ba kuma ba zai ɗauki mataki nan da nan ba. Ka taɓa jin yadda wannan bawan Allah ya ji kuwa?
5. Wane darasi mai muhimmanci ne muka koya daga Habakkuk? (Ka duba hoton da ke shafi na 13.)
5 Habakkuk ya daina dogara ga Jehobah ne? Ya daina kasancewa da tabbaci cewa Allah zai cika alkawuransa? A’a! Da yake Habakkuk ya gaya wa Jehobah damuwarsa da matsalolinsa, hakan ya nuna cewa bai fid da rai ba. Ya damu domin bai san dalilin da ya sa Jehobah bai ɗauki mataki ba kuma ya bar shi ya riƙa shan wahala. Jehobah ya koya mana darasi mai muhimmanci tun da yake ya sa Habakkuk ya rubuta damuwarsa. Hakan ya nuna mana cewa bai kamata mu ji tsoron gaya wa Jehobah damuwarmu ba. Hakika, ya ce mu riƙa gaya masa duk abin da ke damun mu sa’ad da muke addu’a. (Zab. 50:15; 62:8) Littafin Karin Magana 3:5 ya ce mu ‘dogara ga Yahweh da dukan zuciyarmu, kada mu dogara ga ganewarmu.’ Babu shakka, Habakkuk ya bi wannan shawarar a rayuwarsa.
6. Me ya sa yin addu’a yake da muhimmanci?
6 Habakkuk ne ya ɗauki mataki ya kusaci Jehobah don shi Amininsa ne da kuma Ubansa. Habakkuk bai damu da yanayinsa kawai ba kuma bai dogara ga ganewarsa ba. Maimakon haka, ya gaya wa Jehobah yadda yake ji da kuma damuwarsa. Wannan misali ne mai kyau a gare mu. Jehobah mai jin addu’a ya ce mu dogara gare shi kuma mu gaya masa damuwarmu. (Zab. 65:2) Yin hakan zai sa mu ga yadda Jehobah yake amsa addu’o’inmu. Za mu ji kamar ya rungume mu sa’ad da yake ƙarfafa mu da kuma yi mana ja-goranci. (Zab. 73:23, 24) Jehobah zai taimaka mana mu fahimci yadda yake ɗaukan yanayinmu kome tsananin yanayin. Hanya ɗaya mafi kyau da za mu dogara ga Jehobah, ita ce ta yin addu’a.
KU SAURARI JEHOBAH
7. Me Jehobah ya yi sa’ad da Habakkuk ya gaya masa damuwarsa?
7 Karanta Habakkuk 1:5-7. Bayan da Habakkuk ya gaya wa Jehobah damuwarsa, wataƙila yana ganin cewa Jehobah zai yi fushi da shi. Amma da yake Jehobah Uba ne mai ƙauna, ya fahimci yadda Habakkuk yake ji kuma bai tsauta masa ba. Allah ya san cewa Habakkuk yana shan wahala kuma yana neman taimako. Jehobah ya gaya wa Habakkuk abin da ke gab da faruwa ga Yahudawa marasa aminci. Kuma wataƙila Habakkuk ne Jehobah ya fara sanar da cewa ba da daɗewa ba, zai hukunta su.
8. Me ya sa amsar da Jehobah ya ba Habakkuk ya sa shi mamaki?
8 Jehobah ya gaya wa Habakkuk cewa zai ɗauki mataki. Ba da daɗewa ba, zai hukunta waɗannan mugaye. Jehobah ya yi amfani da furucin nan “a cikin kwanakinka” don ya nuna cewa zai hukunta Yahudawa a zamanin Habakkuk ko kuma na tsararsa. Amma ba abin da Habakkuk yake son ya ji ke nan ba. Wataƙila ya yi tunani, wannan ne amsar roƙon da na yi ga Jehobah? Abin da Jehobah ya gaya wa Habakkuk ya nuna cewa wahala za ta ƙaru a Yahuda. * Babiloniyawa mazalunta ne fiye da Yahudawa don Yahudawa sun san ƙa’idodin Jehobah. Me ya sa Jehobah zai yi amfani da wannan al’umma mazalunta don ya sa mutanensa su sha wahala sosai? Yaya za ka ji da a ce kai ne Habakkuk?
9. Waɗanne tambayoyi ne Habakkuk ya yi wa kansa?
9 Karanta Habakkuk 1:12-14, 17. Habakkuk ya fahimci cewa Jehobah zai yi amfani da Babiloniyawa don ya hukunta mugaye a zamaninsa, amma har ila hakan ya ba shi mamaki. Duk da haka, Habakkuk ya ce Jehobah shi ne “Dutse.” (M. Sha. 32:4; Isha. 26:4) Zai ci gaba da dogara ga Allah don shi mai ƙauna ne da alheri. Kuma hakan ya taimaka masa ya sake yi ma Jehobah wasu tambayoyi, ya ce: Me ya sa Allah zai ƙyale yanayi ya daɗa muni a Yahuda? Me ya sa ba zai ɗauki mataki nan da nan ba? Me ya sa Maɗaukaki zai sa mutane su daɗa shan wahala? Me ya sa zai yi “shiru” sa’ad da ake mugunta a ko’ina? Jehobah ‘Mai Tsarki’ ne kuma ‘idanunsa masu tsarki ne, sun fi ƙarfin ganin mugunta.’
10. Me ya sa muke ji kamar Habakkuk a wasu lokatai?
10 A wasu lokuta, mukan ji kamar Habakkuk. Muna biyayya ga Jehobah kuma mun dogara gare shi. Ban da haka, muna karanta da kuma yin nazarin Kalmarsa kuma hakan yana sa mu kasance da bege. Muna kuma jin alkawuransa sa’ad da muka saurari abin da yake koya mana ta ƙungiyarsa. Duk da haka, muna iya yin tunani, ‘A wane lokaci ne za mu daina shan wahala?’ Mene ne za mu koya daga abin da Habakkuk ya yi da za mu tattauna yanzu?
KA JIRA JEHOBAH
11. Me Habakkuk ya ƙuduri niyyar yi bayan ya saurari Jehobah?
11 Karanta Habakkuk 2:1. Tattaunawar da Habakkuk ya yi da Jehobah ya taimaka masa ya kasance da kwanciyar rai. Ya sa ya ƙuduri niyyar jira har sai Jehobah ya ɗauki mataki. Ba a lokacin ba ne Habakkuk ya ƙuduri niyyar yin hakan ba, domin ya sake maimaita niyyarsa sa’ad da ya ce zai ‘yi shiru ya jira ranar azaba.’ (Hab. 3:16) Wasu bayin Allah masu aminci sun jira Jehobah ya ɗauki mataki, kuma hakan ya ƙarfafa mu mu ci gaba da jira har sai Jehobah ya ɗauki mataki.—Mik. 7:7; Yaƙ. 5:7, 8.
12. Waɗanne darussa ne muka koya daga Habakkuk?
12 Mene ne muka koya daga abin da Habakkuk ya ƙuduri niyyar yi? Na farko, bai kamata mu daina yin addu’a ga Jehobah ba ko da wace irin matsala ce muke fuskanta. Na biyu, muna bukatar mu saurari abin da Jehobah yake gaya mana ta Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa. Na uku, ya kamata mu jira Jehobah kuma mu kasance da tabbaci cewa zai magance matsalolinmu a lokacin da ya dace. Idan muka yi koyi da Habakkuk, za mu kasance da kwanciyar rai kuma mu jimre da matsalolinmu. Kasancewa da bege zai taimaka mana mu riƙa haƙuri da kuma farin ciki duk da matsalolin da muke fuskanta. Ƙari ga haka, yana sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ɗauki mataki.—Rom. 12:12.
13. Ta yaya Habakkuk 2:3 ya ƙarfafa mu?
13 Karanta Habakkuk 2:3. Babu shakka, Jehobah ya yi farin ciki cewa Habakkuk ya ƙuduri niyyar jiran sa. Maɗaukaki ya san cewa Habakkuk yana shan wahala. Saboda haka, ya ƙarfafa shi ta wurin tabbatar masa da cewa zai amsa tambayoyinsa, kuma zai biya bukatunsa nan ba da daɗewa ba. Kamar dai Allah yana gaya wa Habakkuk cewa: “Ka yi haƙuri kuma ka dogara da ni. Zan ɗauki mataki ko da yake za ka ga kamar ina jinkirin yin hakan!” Jehobah ya tuna masa cewa zai cika alkawuransa a lokacin da ya dace. Ya ba Habakkuk shawara ya jira har sai ya cim ma nufinsa. A ƙarshe, annabin ba zai yi da-na-sani ba.
14. Me ya kamata mu ƙuduri niyyar yi a lokacin da muke cikin matsala?
14 Mu ma muna bukatar mu jira Jehobah kuma mu saurari abin da yake gaya mana. Hakan zai sa mu dogara gare shi kuma mu kasance da kwanciyar rai duk da matsalolin da muke fuskanta. Yesu ya ce kada mu cika damuwa game da “lokatai da zamanai” da Allah bai gaya mana ba tukun. (A. M. 1:7) Muna bukatar mu yi imani cewa Jehobah ya san lokacin da ya dace ya ɗauki mataki. Saboda haka, kada mu fid da rai amma mu zama masu tawali’u da haƙuri da kuma bangaskiya. Yayin da muke jira, mu yi amfani da lokacinmu yadda ya dace kuma mu yi iya ƙoƙarinmu a hidimar Jehobah.—Mar. 13:35-37; Gal. 6:9.
JEHOBAH ZAI BA DA RAI MADAWWAMI GA MASU DOGARA A GARE SHI
15, 16. (a) Waɗanne alkawura ne suke cikin littafin Habakkuk? (b) Me muka koya daga waɗannan alkawuran?
15 Jehobah ya yi wa masu adalci da suka dogara gare shi alkawari cewa: “Masu adalci, ta wurin bangaskiyarsu, za su rayu” kuma “duniya za ta cika da sanin ɗaukakar Yahweh.” (Hab. 2:4, 14) Hakika, waɗanda suka dogara ga Jehobah za su sami rai na har abada.
16 Zai zama kamar dai alkawarin da ke Habakkuk 2:4 magana ne kawai da aka yi. Amma yana da muhimmanci sosai da har manzo Bulus ya yi ƙaulin ayar sau uku! (Rom. 1:17; Gal. 3:11; Ibran. 10:38) Muna da tabbaci cewa za mu ga cikar alkawuran Jehobah duk da matsalolin da muke fuskanta, idan mun kasance da aminci ga Jehobah kuma muka dogara gare shi. Saboda haka, Jehobah yana so mu mai da hankali ga begenmu na yin rayuwa har abada a nan gaba.
17. Me Jehobah ya tabbatar mana a littafin Habakkuk?
17 Da akwai darasi mai muhimmanci da muka koya daga littafin Habakkuk tun da yake muna cikin kwanaki na ƙarshe. Jehobah ya yi alkawari cewa mai adalci da Mat. 5:5; Ibran. 10:36-39.
ya dogara gare shi zai sami rai na har abada. Saboda haka, bari mu ci gaba da dogara gare shi duk da cewa muna fuskantar matsaloli sosai. Jehobah ya yi amfani da Habakkuk don ya tabbatar mana da cewa zai tallafa mana kuma ya cece mu. Ya ce mu dogara gare shi kuma mu jira lokacin da ya riga ya ƙayyade cewa Yesu zai soma sarauta bisa duniya. A lokacin, mutane masu farin ciki da son zaman lafiya ne kaɗai za su kasance a duniya.—KA DOGARA GA JEHOBAH KUMA KA RIƘA FARIN CIKI
18. Ta yaya abin da Jehobah ya ce ya shafi Habakkuk?
18 Karanta Habakkuk 3:16-19. Abin da Jehobah ya gaya wa Habakkuk ya shafe shi sosai. Sai ya yi bimbini a kan ayyuka masu ban al’ajabi da Jehobah ya yi a madadin mutanensa a dā. Hakan ya ƙarfafa shi ya ci gaba da dogara ga Jehobah. Ya san cewa Jehobah zai ɗauki mataki nan ba da daɗewa ba! Wannan ya ƙarfafa annabin ko da ya san cewa zai ci gaba da shan wahala har sai lokacin da Jehobah zai ɗauki mataki. Saboda haka, Habakkuk ya daina yin shakka, maimakon haka ya yi farin ciki cewa Jehobah zai cece shi. Kuma ya yi furuci mai ƙayatarwa da ya nuna cewa ya dogara sosai ga Jehobah. Wasu masana suna ganin cewa aya ta 18 tana nufin cewa “Zan yi farin ciki sosai cikin Ubangiji; kuma in taka rawa ina jujjuyawa don in nuna cewa ina murna.” Wane darasi ne wannan ya koya mana? Ya koya mana cewa Jehobah ya yi mana alkawura masu ban al’ajabi kuma ya tabbatar mana cewa yana aiki yanzu don ya cika alkawuransa.
19. Ta yaya za mu bar Jehobah ya ƙarfafa mu kamar Habakkuk?
19 Babu shakka, darasi mai muhimmanci da muka koya daga littafin Habakkuk shi ne mu ci gaba da dogara ga Jehobah. (Hab. 2:4) Za mu ci gaba da hakan idan muka ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah ta wurin (1) yin addu’a a kai a kai, mu riƙa gaya masa duk matsalolinmu; (2) mu saurari abin da Jehobah yake gaya mana a Kalmarsa da kuma ta ƙungiyarsa; kuma (3) mu kasance da aminci yayin da muke jira Jehobah ya cika alkawuransa. Abin da Habakkuk ya yi ke nan. Ko da yake yana baƙin ciki sa’ad da ya soma rubuta littafinsa, amma ya kammala shi da farin ciki. Idan muka bi misalin Habakkuk, za mu ga cewa Jehobah yana ƙarfafa mu sosai! Kuma wannan ne ƙarfafa mafi kyau da za mu samu a wannan duniyar da ke cike da mugaye.
^ sakin layi na 8 Ko da yake littafin Habakkuk 1:5 ya yi amfani da kalmar nan “ka,” amma yana magana ne game da wahalar da dukan Yahudawa za su sha.