Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Mene ne aikin wakili a zamanin dā?

A ZAMANIN dā, wakili yana kula da gidan maigidansa ko dukiyarsa. A Ibrananci da Helenanci, kalmar nan “wakili” tana iya nufin shugaba.

A lokacin da Yusuf ɗan Yakubu yake zaman bauta a ƙasar Masar, ya zama wakili a gidan maigidansa. Maigidan ya “bar dukan abin da yake da shi a hannun Yusuf.” (Far. 39:​2-6) Daga baya, sa’ad da Yusuf ya sami mukami a ƙasar Masar, ya naɗa wakili ya riƙa kula da gidansa.​—Far. 44:4.

A zamanin Yesu, manoma suna yawan zama a biranen da ke nesa da gonakinsu. Saboda haka, manoman suna naɗa wakilan da za su riƙa kula da ’yan ƙodago da suke aiki a gonar.

Su waye ne ake naɗawa? Wani marubuci ɗan Roma a ƙarni na farko mai suna Columella ya ce bawan da aka naɗa wakili ko kuma shugaba “mutum ne da ya ƙware a aiki sosai.” Kuma mutum ne da zai tabbata cewa “ma’aikatan sun yi aikinsu ba tare da ya zalunce su ba.” Marubucin ya ƙara cewa: “Abin da ya fi muhimmanci ga wakili shi ne ya ƙoƙarta ya koyi sababbin abubuwa maimakon ya riƙa tunanin cewa ya san kome.”

An yi amfani da misalin wakili da kuma ayyukan da yake yi a Kalmar Allah don a kwatanta wasu ayyukan da Kiristoci a ƙarni na farko suke yi. Alal misali, manzo Bitrus ya ƙarfafa Kiristoci su yi amfani da baiwarsu don ‘yin hidima ga ’yan’uwansu, a matsayinsu na masu riƙon amanar alherin Allah.’​—1 Bit. 4:10.

Yesu ma ya yi amfani da misalin wakili a kwatancinsa da ke Luka 16:​1-8. A annabci da Yesu ya yi game da lokacin da zai zo a matsayin Sarki, ya tabbatar wa mabiyansa cewa zai naɗa “bawan nan mai aminci, mai hikima” ko kuma “wakili mai aminci.” Aikin da wakilin zai riƙa yi shi ne yi wa mabiyan Yesu tanadin abubuwan da za su riƙa ƙarfafa dangantakarsu da Allah a kwanaki na ƙarshe. (Mat. 24:​45-47; Luk. 12:42) Muna farin ciki sosai cewa muna samun littattafai da bidiyoyi da suke ƙarfafa bangaskiyarmu. Ƙari ga haka, wannan wakili mai aminci yana rarraba waɗannan littattafai da bidiyoyi a dukan duniya.