Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 46

Sabbin Ma’aurata, Ku Mai da Ibada Abu na Farko a Rayuwarku

Sabbin Ma’aurata, Ku Mai da Ibada Abu na Farko a Rayuwarku

“Yahweh ne ƙarfina . . . zuciyata ta dogara gare shi.”​—ZAB. 28:7.

WAƘA TA 131 ‘Abin da Allah Ya Haɗa’

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) Me ya sa ya kamata ma’aurata da ba su daɗe da yin aure ba su dogara ga Jehobah? (Zabura 37:​3, 4) (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

KA KUSAN yin aure ne ko kuma bai daɗe da ka yi aure ba? Idan haka ne, babu shakka kana ɗokin yin rayuwa tare da wadda kake ƙauna sosai. Hakika yin aure yana tattare da matsaloli. Kuma akwai shawarwari masu muhimmanci da ma’aurata suke bukatar su yanke. Abin da za ku yi sa’ad da kuka fuskanci matsaloli da kuma shawarwarin da za ku yanke, za su iya sa ku farin ciki na shekaru da yawa. Idan kuka dogara ga Jehobah, za ku yanke shawarwari masu kyau, za ku ji daɗin aurenku, kuma za ku daɗa farin ciki. Idan ba ku bi shawarar da Allah ya bayar ba, za ku fuskanci matsaloli a aurenku, kuma ba za ku yi farin ciki ba.​—Karanta Zabura 37:​3, 4.

2 Ko da yake wannan talifin yana magana ne game da waɗanda ba su daɗe da yin aure ba, za a tattauna matsalolin da dukan ma’aurata za su iya fuskanta. Za a tattauna darussa da za mu iya koya daga mutane masu aminci a Littafi Mai Tsarki. Waɗannan misalan za su koya mana darussa masu kyau da za mu iya yin amfani da su a rayuwarmu, musamman a aure. Ƙari ga haka, za mu koyi darussa daga misalan wasu ma’aurata a zamaninmu.

WAƊANNE ƘALUBALE NE SABBIN MA’AURATA ZA SU IYA FUSKANTA?

Waɗanne matakai ne za su iya hana sabbin ma’aurata saka ƙwazo a hidimarsu? (Ka duba sakin layi na 3-4)

3-4. Waɗanne ƙalubale ne sabbin ma’aurata za su iya fuskanta?

3 Wasu mutane suna iya ƙarfafa sabbin ma’aurata su yi rayuwa kamar yadda mutane suke yi a yau. Alal misali, iyayen ma’auratan ko kuma danginsu za su iya matsa musu su soma haifan yara. Ko kuma wasu abokansu da ’yan’uwansu za su iya ƙarfafa su su gina gida kuma su cika shi da kayayyaki.

4 Idan ma’aurata ba su mai da hankali ba, za su iya yanke shawarar da za ta sa su ci bashi mai yawa. Hakan zai iya sa miji da matar su yi aiki na tsawon lokaci don su biya bashin. Yin aiki na dogon lokaci zai iya hana su samun lokaci na yin nazari da kansu ko ibada ta iyali ko kuma fita wa’azi. Ma’auratan za su ma iya fasa halartan taro a wasu lokuta don neman ƙarin kuɗi ko kuma domin kada a kore su daga aikin. A sakamakon haka, za su iya rasa damar more wasu abubuwa a ƙungiyar Jehobah.

5. Mene ne ka koya daga misalin Klaus da Marisa?

5 Misalai da yawa sun nuna cewa idan muka mai da hankali ga tara abin duniya, ba za mu yi farin ciki ba. Ka yi la’akari da abin da wasu ma’aurata masu suna Klaus da Marisa suka koya. * A lokacin da suka yi aure, dukansu biyu suna yin aiki don su ji daɗin rayuwa. Amma ba su yi farin ciki ba. Klaus ya ce: “Mun sami fiye da abubuwan da muke bukata, amma ba mu shirya yadda za mu daɗa ƙwazo a hidimarmu ba. Hakika mun yi ta wahalar da kanmu kawai.” Wataƙila kai ma ka lura cewa tara abin duniya ba ya sa ka farin ciki. Idan haka ne, kada ka yi sanyin gwiwa. Mai da hankali ga misali mai kyau na wasu zai iya taimaka maka ka yi canje-canje yadda ya kamata. Amma da farko, bari mu ga darasin da magidanta za su iya koya daga misalin Sarki Jehoshaphat.

KA DOGARA GA JEHOBAH KAMAR SARKI JEHOSHAPHAT

6. Bisa ga shawarar da ke Karin Magana 3:​5, 6, ta yaya Jehoshaphat ya magance ƙalubalen da ya fuskanta?

6 Magidanta, shin a wasu lokuta kukan ji kamar aikin da kuke da shi ya fi ƙarfinku? Idan haka ne, za ku iya amfana daga misalin Sarki Jehoshaphat. A matsayin sarki, Jehoshaphat ne yake da hakkin kula da al’ummar gabaki ɗaya! Ta yaya ya yi aikin? Ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kāre al’ummar. Ya sake gina katangar biranen Yahudiya kuma ya tara sojoji fiye da 1,160,000. (2 Tar. 17:​12-19) Daga baya, ya fuskanci babban ƙalubale. Dubban sojojin Ammonawa da Mowabawa da kuma mutanen kan tuddan Seir sun kai masa da iyalinsa da kuma mutanensa hari. (2 Tar. 20:​1, 2) Mene ne ya yi? Ya nemi taimakon Jehobah. Abin da ya yi ya jitu da shawarar da ke Karin Magana 3:​5, 6. (Karanta.) Addu’ar Jehoshaphat da ke 2 Tarihi 20:​5-12 ta nuna cewa ya dogara ga Jehobah sosai. Ta yaya Jehobah ya amsar addu’arsa?

7. Ta yaya Jehobah ya amsa addu’ar Jehoshaphat?

7 Jehobah ya yi magana da Jehoshaphat ta bakin wani Balawi mai suna Jahaziyel. Ya ce: “Ku kafa kanku, ku tsaya cik, ku ga yadda Yahweh zai yi nasara dominku.” (2 Tar. 20:​13-17) Hakika ba haka ake yaƙi ba! Amma ba ɗan Adam ba ne ya ba da umurnin nan, Jehobah ne. Jehoshaphat ya dogara ga Jehobah kuma ya bi umurnin. A lokacin da shi da mutanensa suka je su fuskanci maƙiyansu, ya sa mawaƙa da ba su riƙe makamai ba a gaban dāga maimakon sojoji da suka ƙware. Jehobah ya cika alkawarin da ya yi wa Jehoshaphat kuma ya hallaka maƙiyan.​—2 Tar. 20:​18-23.

Sabbin ma’aurata za su iya saka ibadarsu farko a rayuwa ta wajen yin addu’a da yin nazarin Kalmar Allah (Ka duba sakin layi na 8, 10)

8. Mene ne magidanta za su iya koya daga misalin Jehoshaphat?

8 Magidanta, za ku iya koyan darasi daga misalin Jehoshaphat. Ku ne kuke da hakkin kula da iyalinku, shi ya sa kuke aiki tuƙuru don ku kāre su da kuma yi musu tanadin abin da suke bukata. Idan ka fuskanci matsaloli, za ka iya ɗauka cewa za ka iya magance matsalolin da kanka. Amma kada ka dogara ga kanka. Sa’ad da kake kai kaɗai, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka. Ƙari ga haka, ka yi addu’a sosai tare da matarka. Ka nemi ja-gorancin Jehobah ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da littattafan da ƙungiyar Jehobah ta wallafa, kuma ka bi shawarwarin da ka samu. Wataƙila wasu ba za su amince da shawarwarin da ka yanke ba, za su ma iya gaya maka cewa ka yi wauta da ka yanke shawarar. Wasu kuma za su iya cewa kuɗi da dukiya ne za su iya kāre iyalinka. Ka tuna misalin Jehoshaphat. Ya dogara ga Jehobah kuma ya nuna hakan ta ayyukansa. Jehobah bai yi watsi da wannan mutum mai aminci ba, kuma ba zai yi watsi da kai ba. (Zab. 37:28; Ibran. 13:5) Mene ne ma’aurata za su iya yi don su ji daɗin rayuwarsu tare?

KA SA IBADARKA A KAN GABA KAMAR YADDA ANNABI ISHAYA DA MATARSA SUKA YI

9. Mene ne za mu iya faɗa game da annabi Ishaya da matarsa?

9 Annabi Ishaya da matarsa sun sa ibadarsu farko a rayuwarsu. Ishaya annabi ne, kuma wataƙila matarsa ma ta yi wannan hidimar da yake an kira ta “annabiya.” (Isha. 8:​1-4) Babu shakka a matsayin ma’aurata, sun sa ibadarsu farko a rayuwa. Hakika sun kafa wa ma’aurata misali mai kyau a yau!

10. Ta yaya yin nazarin annabce-annabce a Littafi Mai Tsarki zai taimaka wa ma’aurata su daɗa ƙwazo a hidimarsu?

10 Ma’aurata a yau za su iya bin misalin Ishaya ta wajen yin iya ƙoƙarinsu a ibadarsu. Yin nazarin annabce-annabcen da ke Littafi Mai Tsarki da kuma lura da yadda suke cika, zai taimaka wa ma’aurata su daɗa dogara ga Jehobah. * (Tit. 1:2) Za su iya yin tunanin yadda za su taimaka wajen cika wasu annabcin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, za su iya saka hannu a cika annabcin da Yesu ya yi cewa za yi wa’azin labari mai daɗi a dukan duniya kafin ƙarshe ya zo. (Mat. 24:14) Yayin da ma’aurata suke daɗa gaskata cewa annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suna cika, za su daɗa yin iya ƙoƙarinsu a hidimarsu ga Jehobah.

KA SA MULKIN ALLAH FARKO A RAYUWARKA KAMAR BIRISKILA DA AKILA

11. Mene ne Biriskila da Akila suka yi, kuma me ya sa?

11 Sabbin ma’aurata za su iya koyan darussa daga Biriskila da Akila, wasu ma’aurata Yahudawa da suka yi rayuwa a Roma. Sun ji labari mai daɗi game da Yesu kuma suka zama Kiristoci. Babu shakka, suna jin daɗin rayuwarsu a lokacin. Amma rayuwarsu ta canja farat ɗaya sa’ad da Sarki Kaludiyus ya umurci dukan Yahudawa su bar Roma. Biriskila da Akila za su bukaci su bar wurin da suka saba su koma sabon gida kuma su soma sana’arsu na kafa tanti a wurin. Shin wannan yanayin ya sa sun daina saka ƙwazo a hidimarsu ga Jehobah ne? Babu shakka ka san amsar wannan tambayar. A Korinti, Biriskila da Akila sun soma taimaka wa ’yan’uwa a sabuwar ikilisiyarsu, kuma sun yi aiki tare da manzo Bulus don su ƙarfafa ’yan’uwan da ke wurin. Daga baya, sun koma wasu garuruwa da ake bukatar masu wa’azi sosai. (A. M. 18:​18-21; Rom. 16:​3-5) Hakika sun ji daɗin rayuwarsu tare sosai!

12. Me ya sa ya kamata ma’aurata su kafa maƙasudai a hidimarsu?

12 Ma’aurata a yau za su iya bin misalin Biriskila da Akila ta wajen saka Mulkin Allah farko a rayuwarsu. A lokacin da saurayi da budurwa suke fita zance ne ya kamata su tattauna abubuwan da suke so su yi a rayuwa. Idan ma’aurata suka yanke shawara tare, kuma suka yi iya ƙoƙarinsu don su cim ma wani maƙasudi a hidimarsu ga Jehobah tare, hakan zai sa su ga yadda Jehobah yake taimaka musu. (M. Wa. 4:​9, 12) Ka yi la’akari da misalin wasu ma’aurata masu suna Russell da Elizabeth. Russell ya ce: “Tun kafin mu yi aure, mun tattauna abin da muke so mu yi wa Jehobah.” Elizabeth ta ce: “Mun tattauna wannan batun ne domin idan muna so mu yanke wasu shawarwari daga baya, za mu tabbata cewa shawarwarin ba za su hana mu cim ma maƙasudanmu ba.” Yanayin Russell da Elizabeth ya ba su damar ƙaura zuwa ƙasar Micronesia don su yi hidima a wannan wurin da ake bukatar masu shela sosai.

Sabbin ma’aurata za su iya saka ibadarsu farko a rayuwa ta wajen kafa maƙasudai (Ka duba sakin layi na 13)

13. Kamar yadda Zabura 28:7 ta nuna, mene ne zai faru idan muka dogara ga Jehobah?

13 Kamar yadda Russell da Elizabeth suka yi, ma’aurata da yawa sun yanke shawarar sauƙaƙa rayuwarsu don su mai da hankali ga yin wa’azi da kuma koyarwa sosai. Idan ma’aurata suka kafa maƙasudai tare a hidimarsu kuma suka yi ƙoƙari don su cim ma maƙasudan, za su amfana sosai. Za su ga yadda Jehobah yake kula da su, za su daɗa dogara gare shi kuma za su yi farin ciki sosai.​—Karanta Zabura 28:7.

KA GASKATA DA ALKAWURAN JEHOBAH KAMAR MANZO BITRUS DA MATARSA

14. Ta yaya manzo Bitrus da matarsa suka nuna cewa sun ba da gaskiya ga alkawarin da ke Matiyu 6:​25, 31-34?

14 Ma’aurata za su iya koyan darasi daga misalin manzo Bitrus da matarsa. Wajen wata shida zuwa shekara ɗaya bayan ya haɗu da Yesu, manzo Bitrus ya bukaci ya yanke wata shawara mai muhimmanci. Bitrus ya yi aikin kama kifi don ya kula da iyalinsa. Saboda haka, a lokacin da Yesu ya ce ya zama mabiyin shi, Bitrus ya bukaci ya yi tunanin yadda yanke wannan shawarar za ta shafi matarsa. (Luk. 5:​1-11) Bitrus ya yanke shawarar bin Yesu don su yi wa’azi tare. Wannan shawara ce mai kyau! Kuma muna da hujjar da ta nuna cewa matar Bitrus ta goyi bayansa. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa bayan Yesu ya tashi daga mutuwa, ta yi tafiya tare da Bitrus zuwa wasu wurare. (1 Kor. 9:5) Hakika da yake ita mace mai kirki ce, Bitrus ya sami ƙarfin gwiwar ba wa mazaje da matansu shawara. (1 Bit. 3:​1-7) Babu shakka Bitrus da matarsa sun ba da gaskiya ga alkawarin da Jehobah ya yi cewa zai yi musu tanadin abubuwan da suke bukata idan suka saka mulkinsa farko a rayuwarsu.​—Karanta Matiyu 6:​25, 31-34.

15. Mene ne ka koya daga misalin Tiago da Esther?

15 Idan kun yi kwan biyu da yin aure, ta yaya za ku ci gaba da ƙwazo a hidimarku ga Jehobah? Hanya ɗaya ita ce ta wajen koya daga misalin wasu ma’aurata. Alal misali, za ku iya karanta jerin talifofin nan mai jigo “Sun Ba da Kansu da Yardar Rai.” Irin waɗannan talifofin sun taimaka ma wasu ma’aurata masu suna Tiago da Esther da suka fito daga ƙasar Brazil, su yi marmarin ƙaura zuwa wurin da ake bukatar masu shela. Tiago ya ce: “Sa’ad da muka karanta labaran yadda Jehobah ya taimaka wa bayinsa a zamaninmu, sai mu ma muka ce za mu bi shawarar Jehobah don mu ga yadda zai taimaka mana.” A ƙarshe, sun ƙaura zuwa ƙasar Paraguay a shekara ta 2014, inda suke hidima a yaren Portuguese har yau. Esther ta ce: “Wani nassi da muke so sosai shi ne Afisawa 3:20. Mun ga yadda sau da yawa ayar nan ta cika a kanmu.” A wasiƙarsa ga ’yan’uwan da ke Afisa, Bulus ya yi musu alkawari cewa Jehobah zai yi musu tanadi fiye da abin da suka roƙa. Sau da yawa Jehobah ya cika wannan alkawarin!

Sabbin ma’aurata za su iya saka ibadarsu farko a rayuwa ta wajen neman shawara daga ma’aurata da suka manyanta (Ka duba sakin layi na 16)

16. Shawarar waye ne sabbin ma’aurata za su iya bi yayin da suke ƙoƙarin kafa maƙasudai a rayuwa?

16 Sabbin ma’aurata a yau za su iya amfana daga labaran wasu da suka dogara ga Jehobah. Wasu ma’aurata sun yi shekaru da yawa suna yin hidimar majagaba. Za ku iya neman shawara daga wurinsu idan kuna so ku kafa wasu maƙasudai. Wannan ma wata hanya ce da za ku nuna cewa kun dogara ga Jehobah. (K. Mag. 22:​17, 19) Dattawa ma za su iya taimaka wa sabbin ma’aurata su kafa maƙasudai a hidimarsu, kuma su cim ma maƙasudan.

17. Mene ne ya faru da Klaus da Marisa, kuma me muka koya daga labarinsu?

17 A wasu lokuta, za mu iya yanke shawarar yi wa Jehobah wani aiki, amma sai ya ba mu wani aiki dabam. Abin da ya faru da Klaus da Marisa ke nan, ma’auratan da aka ambata ɗazu. Bayan da suka yi shekara uku da aure, sai suka bar gidansu suka ƙaura zuwa ofishinmu da ke ƙasar Finland don su taimaka da aikin gine-gine. Amma an gaya musu cewa ba zai yiwu su zauna a ofishin fiye da wata shida ba. Da farko, hakan ya sa su baƙin ciki. Amma ba da daɗewa ba bayan hakan, an gayyace su su halarci makarantar da ake koyar da Larabci, yanzu suna farin cikin yin hidima a yaren Larabci a wata ƙasa dabam. Marisa ta tuna abin da ya faru kuma ta ce: “Na ji tsoron yin abin da ban taɓa yi ba, don haka, na bukaci in dogara ga Jehobah. Kuma na ga yadda ya taimaka mana a hanyoyin da ba mu yi zato ba. Abubuwan nan da suka faru da mu sun sa na daɗa dogara ga Jehobah.” Kamar yadda wannan labarin ya nuna, Jehobah zai yi muku albarka idan kuka dogara gare shi.

18. Mene ne ma’aurata za su iya yi don su ci gaba da dogara ga Jehobah?

18 Aure kyauta ce daga wurin Jehobah. (Mat. 19:​5, 6) Yana so ma’aurata su ji daɗin wannan kyautar. (K. Mag. 5:18) Sabbin ma’aurata, ku yi tunanin abubuwan da kuke yi da rayuwarku. Shin kuna yin iya ƙoƙarinku don ku nuna wa Jehobah cewa kuna godiya don wannan kyauta da ya ba ku? Ku yi addu’a ga Jehobah. Ku bincika Kalmarsa don ku ga ƙa’idodin da za su taimaka muku. Bayan haka, ku bi shawarar da Jehobah ya ba ku. Ku kasance da tabbaci cewa za ku yi farin ciki a aurenku idan kuka sa hidimar Jehobah a kan gaba!

WAƘA TA 132 Yanzu Mun Zama Ɗaya

^ sakin layi na 5 Wasu shawarwari da muka yanke za su iya taimaka mana mu bauta wa Jehobah da kyau ko kuma su hana mu yin hakan. Sabbin ma’aurata musamman za su bukaci su yanke shawarwari da za su iya shafansu a duk rayuwarsu. Wannan talifin zai taimaka musu su iya yanke shawarwarin da za su sa su yi farin ciki a rayuwa.

^ sakin layi na 5 An canja wasu sunayen.

^ sakin layi na 10 Alal misali, ka duba akwatin nan “Za Ka Iya Bayyana Waɗannan Annabci Ne?” da ke Hasumiyar Tsaro ta Yuli 2020, shafi na 11.