Ka Yi Koyi da Halin Jehobah na Nuna Tausayi
‘Ubangiji da ke cike da tausayi, mai-jinƙai ne kuma.’—YAƘ. 5:11.
WAƘOƘI: 142, 12
1. Ta yaya Jehobah ya sa Musa ya san shi, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?
A LOKACIN da Allah yake son Musa ya san shi, ya gaya masa sunansa da kuma wasu halayensa. Ya fara ambata juyayi da alheri, wato tausayi. (Karanta Fitowa 34:5-7.) Da Jehobah ya ambata ikonsa ko hikimarsa da farko, amma bai yi hakan ba. Musa yana son Jehobah ya tabbatar masa cewa yana goyon bayansa, amma Jehobah ya ambaci halayen da suka nuna cewa Jehobah yana shirye ya taimaka wa bayinsa. (Fit. 33:13) Abin farin ciki ne sosai cewa Jehobah ya ambaci juyayi da tausayi kafin sauran halayen, ko ba haka ba? A wannan talifin, za a tattauna halin nan tausayi, wato sanin damuwa ko matsalar da mutane suke fuskanta da son taimaka musu.
2, 3. (a) Me ya nuna cewa an halicce mu mu riƙa nuna tausayi? (b) Me ya sa zai dace ka bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da tausayi?
2 Allah ya halicce mu da irin halayensa. Don haka, mutane har da waɗanda ba su san shi ba ma suna nuna tausayi don an halicce su da halin. (Far. 1:27) Muna da labarai da yawa a Littafi Mai Tsarki da suka tabbatar da hakan. Ka yi la’akari da labarin mata biyu da suka yi ta faɗa a kan ko wace ce mahaifiyar yaron da aka kawo wurin Sarki Sulemanu. A lokacin da Sulemanu ya gwada su kuma ya ce a raba yaron biyu, ainihin mahaifiyar yaron ta ji tausayinsa kuma ta ce kada a yi hakan, amma a ba ɗayan matar. (1 Sar. 3:23-27) Ban da haka ma, ka yi tunani game da labarin ’yar Fir’auna da ta ceci Musa a lokacin da yake yaro. Ko da yake ta san cewa yaron nan ɗan Ibraniyawa ne kuma ya kamata a kashe shi, “ta ji tausayinsa,” kuma ta tsai da shawara cewa za ta yi renonsa.—Fit. 2:5, 6.
3 Me ya sa ya kamata ka bincika batun tausayi? Dalilin shi ne Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu yi koyi da Allah. (Afis. 5:1) Amma duk da cewa an halicce mu mu riƙa nuna tausayi, ajizancin da muka gāda daga Adamu da Hawwa’u yakan sa ya mana wuya a wani lokaci mu yi hakan. A wasu lokuta yakan mana wuya mu tsai da shawara ko za mu taimaka wa kanmu ko kuma wasu. Ga wasu mutane, hakan yana musu wuya sosai ko kuma suna bukatar su yi wasu gyara. Me zai taimaka maka ka kasance da ra’ayin da ya dace game da su? Da farko, ka nemi lokaci ka bincika yadda Jehobah da kuma wasu suka nuna tausayi. Na biyu, ka bincika yadda za ka yi koyi da Allah da kuma yadda hakan zai amfane ka.
JEHOBAH YA KAFA MISALI MAFI KYAU NA NUNA TAUSAYI
4. (a) Me ya sa Jehobah ya aiki mala’iku zuwa Saduma? (b) Wane darasi muka koya daga labarin Lutu da yaransa biyu?
4 Muna da misalai da yawa da suka nuna yadda Jehobah ya nuna tausayi. Ka yi la’akari da yadda Allah ya bi da Lutu. Halin rashin da’a da mutanen Saduma da Gwamarata suke yi ya sa ran adalin nan Lutu ya “ɓaci ƙwarai.” Shi ya sa Allah ya tsai da shawara cewa ya kamata mutanen nan su mutu. (2 Bit. 2:7, 8) Amma Allah ya aiki mala’iku don su ceci Lutu. Waɗannan mala’ikun sun gaya ma Lutu da iyalinsa su fita da sauri daga waɗannan biranen. “Amma ya yi jinkiri; mutanen [mala’iku] fa suka kama hannunsa, da hannun matatasa, da hannuwan ɗiyansa su biyu mata; gama Ubangiji yana jinƙansa: suka fitar da shi, suka ajiye shi bayan birnin.” (Far. 19:16) Wannan labarin ya nuna cewa Jehobah yana sane da matsalolin da bayinsa masu aminci suke fuskanta a wasu lokuta, ko ba haka ba?—Isha. 63:7-9; Yaƙ. 5:11; 2 Bit. 2:9.
5. Ta yaya Kalmar Allah kamar 1 Yohanna 3:17 za ta taimaka mana mu riƙa nuna tausayi?
5 Jehobah bai nuna wa mutanensa tausayi kawai ba, amma ya koya musu yadda za su nuna wannan halin. Bari mu yi la’akari da dokar da Allah ya ba wa Isra’ilawa game da karɓan tufafin mutum a matsayin jingina. (Karanta Fitowa 22:26, 27.) Idan wanda aka karɓi bashi daga wurinsa bai da tausayi, zai ƙi mayar wa mutumin tufafin da ya karɓa jingina kuma mutumin ba zai sami abin da zai rufe jikinsa da shi ba idan yana barci. Amma Jehobah ya gaya wa bayinsa su guji irin wannan mugun halin domin ya kamata bayinsa su riƙa tausayin mutane. Wannan darasi da muka koya daga wannan labarin ya kamata ya sa mu riƙa tausayin mutane. Kuma ba zai dace mu ƙi taimaka wa ’yan’uwanmu da suke shan wahala ba idan muna da abin da za mu taimaka musu da shi ba.—Kol. 3:12; Yaƙ. 2:15, 16; karanta 1 Yohanna 3:17.
6. Wane darasi muka koya daga yadda Jehobah ya ci gaba da taimaka wa Isra’ilawa ko da yake sun yi masa laifi a kai a kai?
6 Jehobah ya ji tausayin Isra’ilawa har a lokacin da suka yi masa zunubi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji kuwa, Allah 2 Laba. 36:15) Zai dace mu ma mu ji tausayin mutanen da wataƙila za su tuba a nan gaba kuma Allah ya nuna musu alheri, ko ba haka ba? Jehobah ba ya son mutane su hallaka sa’ad da yake hukunta mugaye. (2 Bit. 3:9) Amma kafin Allah ya hallakar da mugayen mutane, bari mu ci gaba da yin wa’azi muna yi wa mutane kashedi game da wannan hallakar da ke nan tafe.
na ubanninsu, ya aike garesu ta wurin manzanninsa, yana tashi da wuri yana aikarsu; domin yana jin tausayin mutanensa, da mazauninsa kuma.” (7, 8. Me ya sa wata iyali ta gaskata cewa Jehobah ya ji tausayinsu?
7 Akwai misalai da yawa da suka nuna cewa Allah yana tausayin mutane. Ka yi la’akari da abin da ya faru da iyalin su Milan, wani yaro mai shekara 12. Wannan abin ya faru ne a lokacin da ake nuna wariyar kabila a shekara ta 1990 da wani abu. Milan da kanensa da iyayensa da kuma wasu Shaidu sun fita daga Bosnia za su je babban taro a Serbia da bas. Kuma iyayen Milan sun tsai da shawara cewa a wannan taron ne za su yi baftisma. Amma da suka kai iyakar ƙasar, sai sojoji suka fitar da iyalinsu gefe da yake su ba kabilarsu ba ne, amma suka ce wasu ’yan’uwan su tafi. Bayan da suka riƙe su na kwana biyu, sai sojan da yake kula da su ya kira shugabansa don ya tambaye shi matakin da za a ɗauka a kan wannan iyalin. Amma da yake sojan yana tsaye gabansu, sun ji amsar da aka ba shi cewa: “Ka kai su ka bindige su!”
8 Amma da wannan sojan yake wa mutanensa bayani, sai wasu mutane biyu suka zo suka gaya wa iyalin nan cewa su Shaidun Jehobah ne. Wasu sun riga sun gaya musu a bas cewa ana tashin hankali. Sai ’yan’uwa biyun suka gaya ma Milan da kanensa su shiga motarsu don su ketare zuwa iyaka da yake ba a bincika takardun yara. Kuma suka juya wurin iyayen Milan suka ce musu su ketare, za su same su a gaba. Milan bai san abin da zai yi ba ko ya yi dariya ko kuma ya yi kuka. Sai iyayensa suka tambayi ’yan’uwan, “Kuna ganin za su bar mu mu wuce kuwa?” Duk da haka, da suke tafiya sun ga kamar sojojin suna kallonsu amma ba su musu kome ba. Haka suka wuce kuma suka haɗu da yaransu a can. Sai suka tafi birnin da ake taron da tabbaci cewa Jehobah ya ji addu’arsu kuma ya taimaka musu. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa akwai wasu lokuta da Jehobah bai ceci bayinsa da kansa ba. (A. M. 7:58-60) Duk da haka, Milan ya faɗi yadda ya ji cewa, “Ina gani kamar mala’ikun sun makantar da idanun sojojin sai Jehobah ya cece mu.”—Zab. 97:10.
9. Ta yaya Yesu ya taimaka wa mutanen da suka bi shi? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.)
9 Wane darasi ne za mu koya daga Yesu? Ya ji tausayin mutanen da ya haɗu da su domin “suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” Ta yaya ya taimaka musu? Sai “ya fara koya masu abu da yawa.” (Mat. 9:36; karanta Markus 6:34.) Halinsa ya yi dabam da na Farisawa da suke rena talakawa. (Mat. 12:9-14; 23:4; Yoh. 7:49) Shin kai ma kana da halin Yesu na taimaka wa mutanen da suke shan wahala don suna son su koya game da Jehobah?
10, 11. Shin a kowane lokaci ne ya kamata mu ji tausayin mutane? Ka bayyana.
10 Hakan ba ya nufin cewa muna bukatar mu riƙa nuna tausayi a kowane yanayi. Misalan da ke Littafi Mai Tsarki sun nuna mana cewa Allah ya nuna tausayi a yanayin da ya dace. Sarki Saul ya yi rashin biyayya a lokacin da ya ji tausayin Agag wanda shi maƙiyin mutanen Allah ne, ban da haka ma, ya ƙi halaka dukan abubuwan 1 Sam. 15:3, 9, 15) Jehobah mai adalci ne, kuma yana ganin abin da ke zuciyar mutane, ban da haka ma, ya san yanayin da ya kamata ya ji tausayin mutane. (Mak. 2:17; Ezek. 5:11) Lokaci yana zuwa da Jehobah zai hallaka dukan waɗanda ba sa yi masa biyayya. (2 Tas. 1:6-10) Kuma a wannan lokacin ba zai ji tausayin mugaye ba, amma hallaka su zai nuna cewa yana jin tausayin adalai da za su yi rayuwa har abada.
da aka umurce shi ya halaka. Saboda wannan, Jehobah ya ƙi Saul a matsayin sarkin Isra’ila. (11 Babu shakka, ba mu da ikon yanke wa mutane hukuncin ko za a halaka su ko a’a, amma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka musu. Ta yaya a yau za mu iya nuna wa ’yan’uwanmu cewa muna jin tausayinsu? Bari mu bincika wasu hanyoyin da za mu iya yin hakan.
YADDA YA KAMATA MU RIƘA NUNA TAUSAYI
12. Ta yaya za ka nuna tausayi sa’ad kake ma’amala da wasu?
12 A kullum ka riƙa taimako. Da yake muna koyi da Yesu, ya kamata mu riƙa tausayin maƙwabtanmu da ’yan’uwanmu. (Yoh. 13:34, 35; 1 Bit. 3:8) Wani ƙamus ya ce kalmar nan tausayi tana nufin “shan wahala tare da wasu.” Mutumin da yake jin tausayi yana ƙoƙari don ya magance matsalar da wasu suke ciki ko kuma ya taimaka ma waɗanda suke shan wahala. Alal misali, za mu iya taimaka ma wasu ta wajen yi musu aikace-aikace a gidajensu da dai sauransu.—Mat. 7:12.
13. Waɗanne halayen Allah ne wasu ’yan’uwa suka nuna bayan wani bala’i?
13 Ka riƙa taimaka wa a yin aikin agaji. Mutanen da bala’i ya auko musu suna shan wahala sosai kuma hakan yana motsa mutane da yawa su ji tausayinsu. Mutane da yawa sun san cewa bayin Jehobah suna taimaka wa mutane a lokacin wahala. (1 Bit. 2:17) Wata ’yar’uwa daga Jafan ta yi zama a inda girgizan ƙasa da tsunami suka auku a shekara ta 2011. Ta ce yadda wasu suka zo daga wasu ɓangaren ƙasar Jafan har ma da ƙasashen waje don su yi musu gyare-gyare ya “ƙarfafa” su sosai. Ta ƙara da cewa: “Yadda suka taimaka mana ya sa na ga cewa Jehobah yana kula da mu kuma ’yan’uwa Shaidu ma suna ƙaunar juna sosai, kuma duka ’yan’uwa a faɗin duniya suna yi mana addu’a.”
14. Ta yaya za ka taimaka wa marasa lafiya da kuma tsofaffi?
14 Ka taimaka wa marasa lafiya da tsofaffi. Muna jin tausayin mutane idan muka ga yadda suke shan wahala saboda zunubin Adamu. Muna marmarin ganin yadda za a kawar da cuta da kuma tsufa. Don haka, muna addu’a don Mulkin Allah ya zo. Amma zai dace mu iya ƙoƙarinmu yanzu don mu taimaka wa mutanen da suke shan wahala. Ka yi la’akari da abin da wani mawallafi ya rubuta game da mahaifiyarsa. Ya ce a lokacin da take raye, ta tsufa kuma tana da wani ciwo da yake sa ta yawan mantuwa. Akwai wata rana da ta ɓata kayanta. Da take ƙoƙari ta canja kayan, sai aka ƙwanƙwasa ƙofarta. Da ta buɗe ƙofar, sai ta ga Shaidu biyu da suka saba zuwa wurinta. Sai suka tambaye ta ko akwai wani abu da take so su yi mata. Matar ta ce: “Na ji kunya sosai.” Amma baƙin sun taimaka mata kuma suka wanke mata kayanta. Sun yi shayi suka sha kuma suka zauna suna ta hira. Ɗanta ya yi farin ciki sosai. Kuma ya rubuta cewa: “Ina tsara ma Shaidun nan domin suna yin abin da suke wa’azinsa.” Shin kana jin tausayin tsofaffi da marasa lafiya da suke shan wahala kuma kana iya ƙoƙarinka don ka taimaka musu?—Filib. 2:3, 4.
15. Wane zarafi muke da shi sa’ad da muke yin wa’azi?
15 Ka taimaka wa mutane su zama abokan Jehobah. Matsalolin da mutane suke fuskanta suna sa mu taimaka musu su zama abokan Jehobah. Hanya mafi muhimmanci da za mu taimaka musu ita ce ta koya musu game da Allah da kuma abin da Mulkinsa zai yi wa mutane. Wata hanya kuma da za mu yi hakan ita ce mu taimaka musu su san muhimmancin bin ƙa’idodin Allah. (Isha. 48:17, 18) Zai dace ka yi ƙwazo sosai a wa’azi don wannan hidimar ce take ɗaukaka Jehobah da kuma nuna cewa kana tausayin mutane.—1 Tim. 2:3, 4.
ZA KA AMFANA IDAN KANA NUNA TAUSAYI!
16. Ta yaya mutumin da yake tausayin wasu yake amfana?
16 Masanan lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce idan kana tausayin mutane, za ka kyautata lafiyar jikinka kuma ka yi zaman lafiya da mutane. Idan ka taimaka ma mutanen da suke shan wahala, za ka yi farin ciki kuma ka kasance da ra’ayi mai kyau, ba za ka kaɗaita ba ko kuma ka riƙa tunanin banza ba. A gaskiya, idan kana tausayin mutane, za ka amfana sosai. (Afis. 4:31, 32) Kiristoci da suka taimaka ma wasu suna da kwanciyar hankali don sun sani cewa suna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Idan suna da irin wannan halin, za su kula da yaransu da matansu ko mazansu da abokansu da kyau. Ban da haka ma, mutanen da suke nuna tausayi ana yawan taimaka musu da kuma tallafa musu sa’ad da suke cikin matsala.—Karanta Matta 5:7; Luka 6:38.
17. Me ya sa kake so ka riƙa nuna tausayi?
17 Bai kamata sanin cewa za ka amfana idan kana tausayin mutane ya zama ainihin dalilin da ya sa kake so ka zama da wannan halin ba. Ya kamata dalilin ya zama cewa kana son ka yi koyi da kuma girmama wanda ya soma kafa mana misalin nuna ƙauna wato, Jehobah. (Mis. 14:31) Ya kafa mana misali mai kyau a yin hakan. Bari dukanmu mu yi iya ƙoƙarinmu mu yi koyi da shi ta wurin tausaya wa mutane muna sa ’yan’uwa su riƙa ƙaunar juna kuma mu yi zaman lafiya da maƙwabtanmu.—Gal. 6:10; 1 Yoh. 4:16.