Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Rika Yin La’akari da Mutane Kamar Jehobah

Ka Rika Yin La’akari da Mutane Kamar Jehobah

“Mai albarka ne wanda yake kula da marasa ƙarfi.”​—ZAB. 41:1.

WAƘOƘI: 130, 107

1. Ta yaya mutanen Allah suke nuna suna ƙaunar juna?

MASU bauta wa Allah a faɗin duniya suna cikin iyali ɗaya don suna ƙaunar juna. (1 Yoh. 4:​16, 21) A wasu lokuta suna yin sadaukarwa sosai don ’yan’uwansu, amma a yawancin lokuta, suna nuna ƙaunarsu ta wurin yin abubuwan da ba na musamman ba. Alal misali, suna iya gaya wa ’yan’uwa magana mai ban ƙarfafa ko kuma nuna musu alheri. Muna yin koyi da Allah idan muka yi la’akari da mutane.​—Afis. 5:1.

2. Ta yaya Yesu ya nuna ƙauna kamar Jehobah?

2 Yesu ya bi misalin Jehobah sosai kuma ya ce: “Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji, kuma kuna fama da kaya masu nauyi a kanku, zan ba ku hutawa . . . , domin ni mai tawali’u ne, mai sauƙin kai.” (Mat. 11:​28, 29) Idan muka bi misalin Kristi ta wurin “kula da marasa ƙarfi,” za mu sami tagomashin Jehobah kuma za mu yi farin ciki sosai. (Zab. 41:1) Bari mu ga yadda za mu riƙa yin la’akari da mutane a cikin iyali da ikilisiya da kuma sa’ad da muke wa’azi.

KU RIƘA YIN LA’AKARI A IYALI

3. Ta yaya miji zai riƙa yin la’akari da matarsa? (Ka duba hoton da ke shafi na 28.)

3 Magidanta suna bukatar su riƙa kafa misali mai kyau wajen yin la’akari da waɗanda suke iyalinsu. (Afis. 5:25; 6:4) Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata magidanta su riƙa yin la’akari da matansu. (1 Bit. 3:7) Mai gidan da ya fahimci matarsa ya san cewa ko da shi da matarsa sun bambanta a hanyoyi da yawa, bai fi matarsa daraja ba. (Far. 2:18) Saboda haka, yana yin la’akari da yadda take ji kuma yana daraja ta. Wata mata a Kanada ta ce game da mijinta: “Yana yin la’akari da yadda nake ji kuma ba ya ce mini, ‘Bai kamata ki ji hakan ba.’ Daɗin daɗawa, yana kasa kunne sosai idan ina gaya masa wani abu. Kuma yana daidaita ra’ayina a kan wani batu a hankali idan bukata ta kama.”

4. Ta yaya miji zai nuna yana yin la’akari da yadda matarsa take ji sa’ad da yake sha’ani da wasu mata?

4 Mijin da yake yin la’akari da yadda matarsa take ji ba zai taɓa yin kwarkwasa da wasu mata ba ko kuma ya riƙa nuna yana son su. Ba ya yin amfani da shafofin sada zumunta don yin kwarkwasa kuma ba ya kallon abubuwan da ba su dace ba a intane. (Ayu. 31:1) Hakika, ba ya cin amanar matarsa domin yana ƙaunar ta da kuma Jehobah. Ƙari ga haka, yana hakan don ya tsani mugunta.​—Karanta Zabura 19:14; 97:10.

5. Ta yaya mata za ta nuna cewa tana yin la’akari da mijinta?

5 Idan miji ya yi koyi da misalin shugabansa, wato Yesu Kristi, zai yi wa matarsa sauƙi ta “girmama” shi. (Afis. 5:​22-25, 33) Kuma idan ta yi hakan, za ta yi ƙoƙari ta fahimci yadda yake ji kuma ta riƙa yin la’akari da shi sa’ad da ya shagala da yin aikin ikilisiya ko kuma wasu matsaloli suna damunsa. Wani ɗan’uwa a Biritaniya ya ce: “A wasu lokatai, matata takan gane cewa akwai abin da yake damu na domin ba na yin abu yadda na saba. Tana bin ƙa’idar da ke Littafin Karin Magana 20:5 ko da yin hakan na nufin cewa za ta jira sai lokacin da ya dace ta tambaye ni abin da ke faruwa, idan abu ne da take bukatar ta sani.”

6. Ta yaya dukanmu za mu iya koya wa yara su riƙa yin la’akari da mutane, kuma ta yaya yaran za su amfana?

6 Iyaye suna kafa wa yaransu misali mai kyau idan suna yin la’akari da juna. Hakika, iyaye ne suke da hakkin koyar da yaransu su riƙa yin la’akari da mutane. Alal misali, iyaye suna iya koya wa yaransu kada su riƙa guje-guje a Majami’ar Mulki. Ko idan suka je biki, iyaye suna iya gaya wa yaransu su bar tsofaffi su fara ɗiban abinci kafin su ɗiba. Hakika, dukan ’yan’uwa a ikilisiya suna iya taimaka wa iyaye. Alal misali, ya kamata mu yaba wa yaron da ya yi wani aiki mai kyau kamar buɗe mana ƙofa. Yin hakan zai sa yaron farin ciki, kuma zai taimaka masa ya san cewa “bayarwa ta fi karɓa albarka.”​—A. M. 20:35.

KU “LURA DA JUNA” A IKILISIYA

7. Ta yaya Yesu ya yi la’akari da wani kurma, kuma waɗanne darussa ne za mu iya koya daga abin da ya yi?

7 Wata rana da Yesu yake yankin Dakafolis, sai mutane suka “kawo masa wani kurma, wanda da kyar yakan yi magana.” (Mar. 7:​31-35) Yesu ya “ja kurman gefe” kuma ya warkar da shi, maimakon yin hakan a gaban jama’a. Me ya sa Yesu ya yi hakan? Wataƙila mutumin yana jin kunyar zama a cikin jama’a. Da Yesu ya ga hakan, sai ya ja shi gefe kuma ya warkar da shi. Ba za mu iya yin mu’ujizai a yau ba, amma ya kamata mu riƙa tunanin yadda za mu biya bukatun ’yan’uwanmu da kuma yin la’akari da yadda suke ji. Manzo Bulus ya ce: “Mu lura da juna ta yadda za mu iza juna ga nuna ƙauna da yin aikin nagarta.” (Ibran. 10:24) Yesu ya fahimci yadda kurman yake ji kuma ya yi la’akari da shi. Babu shakka, Yesu ya kafa mana misali mai kyau!

8, 9. A waɗanne hanyoyi ne za mu riƙa yin la’akari da tsofaffi da kuma naƙasassu? (Ka ba da misalai.)

8 Ka yi la’akari da tsofaffi da kuma marasa lafiya. Ba a fi sanin ikilisiyar Kirista da iya gudanar da ayyukanta yadda ya kamata ba, amma an fi sanin ta da nuna ƙauna. (Yoh. 13:​34, 35) Wannan ƙaunar tana motsa mu mu nemi hanyoyin taimaka wa tsofaffi da kuma naƙasassu don su iya halartan taro da kuma yin wa’azi. Suna bukatar hakan ko da abin da za su iya yi bai da yawa. (Mat. 13:23) Da akwai wani gurgu mai suna Michael da ba ya iya rabuwa da kekensa. Ya ce yana godiya sosai don taimakon da iyalinsa da kuma ’yan’uwan da suke wa’azi tare suke yi masa. Michael ya ce: “Taimakon da suka yi mini ya sa ina iya halartan yawancin taro da kuma yin wa’azi a kai a kai. Ina jin daɗin yin wa’azi sosai ga jama’a.”

9 Da akwai tsofaffi da naƙasassu a ofisoshinmu da yawa. Saboda haka, masu kula suna nuna ƙauna ta wurin shirya yadda za su riƙa wa’azi ta rubuta wasiƙu da kuma ta waya. Bill ɗan shekara 86 da ke rubuta wa mutane da ke wurare masu nisa wasiƙu ya ce: “Muna farin ciki don damar da muke da shi na rubuta wasiƙu.” Wata ’yar’uwa mai suna Nancy da ta kusan shekara 90 ta ce: “A ganina rubuta wasiƙa ba kawai saka takardu cikin ambulan ba. Ina wa’azi ne kuma mutane suna bukatar su koyi gaskiya!” Wata ’yar’uwa mai suna Ethel da aka haifa a shekara ta 1921 ta ce: “Ina rashin lafiya a kowane lokaci. A wasu ranaku, yana yi mini wuya in saka kaya.” Duk da haka, tana jin daɗin yin wa’azi ta waya kuma tana da wasu da take tattaunawa da su. Barbara ’yar shekara 85 ta ce: “Rashin lafiya yana sa ya yi mini wuya in riƙa wa’azi a kai a kai. Amma yin wa’azi ta waya yana taimaka mini. Ina godiya ga Jehobah!” Mene ne sakamakon hakan? Kafin a cika shekara ɗaya, wannan rukunin tsofaffi sun yi wa’azi na awoyi 1,228. Ƙari ga haka, sun rubuta wasiƙu 6,265, sun kira mutane a waya fiye da sau 2,000 kuma sun ba da littattafai da bidiyoyi guda 6,315! Babu shakka, abin da suka cim ma ya sa Jehobah farin ciki!​—K. Mag. 27:11.

10. Ta yaya za mu taimaka wa ’yan’uwanmu su amfana a taro?

10 Ka riƙa yin la’akari da mutane a taron ikilisiya. Muna son ’yan’uwanmu su amfana sosai a taro, kuma yin la’akari da su zai iya taimaka musu. Ta yaya? Hanya ɗaya da za mu iya yin hakan ita ce ta wurin zuwa taro da wuri don kada mu riƙa raba hankali ’yan’uwa. Hakika a wasu lokuta, akwai abin da zai iya sa mu makara. Amma bai kamata hakan ya zama halinmu ba. Idan muna hakan, ya kamata mu riƙa yin la’akari da mutane. Ƙari ga haka, ya kamata mu tuna cewa Jehobah da Ɗansa ne suka gayyato mu taron. (Mat. 18:20) Saboda haka, muna bukata mu riƙa daraja su.

11. Me ya sa ya kamata waɗanda suke yin jawabai su bi umurnin da ke 1 Korintiyawa 14:40?

11 Idan muna yin la’akari da ’yan’uwanmu za mu riƙa bin wannan umurni cewa: “A yi kome yadda ya kamata, a shirye kuma.” (1 Kor. 14:40) ’Yan’uwa da suke yin jawabai a taro suna bin wannan umurnin ta wurin yin jawabinsu ba tare da cin lokaci ba. Ta yin hakan, suna yin la’akari da mai jawabi na gaba da kuma dukan ’yan’uwa. Wataƙila wasu ’yan’uwa sun zo daga wurare masu nisa, wasu kuma za su shiga motar haya. Ban da haka, wasu suna da abokin aure da ba ya bauta wa Jehobah kuma mijin ko matar na jira ya dawo.

12. Me ya sa ya dace mu riƙa ‘mutunta’ dattawa da suke aiki da ƙwazo? (Ka duba akwatin nan “ Ku Riƙa Yin La’akari da Waɗanda Suke Ja-goranci.”)

12 Dattawa suna aiki tuƙuru a ikilisiya kuma suna yin wa’azi da ƙwazo. Shi ya sa ya kamata mu riƙa daraja su da kuma ƙaunar su. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:​12, 13.) Hakika, kuna godiya don dukan ayyukan da dattawa suke yi a madadinku. Saboda haka, ku riƙa nuna godiyarku ta wurin ba su haɗin kai da kuma tallafa musu. Me ya sa? Domin ‘suna kula da rayukanku, su kuma za su ba da lissafin aikinku.’​—Ibran. 13:​7, 17

KU RIƘA YIN LA’AKARI A WA’AZI

13. Mene ne za mu iya koya daga yadda Yesu ya yi sha’ani da mutane?

13 A wani annabcin da Ishaya ya yi game da Yesu, ya ce: “Karan da ya rasa ƙarfi, ba zai karya shi ba, fitilar da aka rage wutarta, ba zai kashe ta ba.” (Isha. 42:3) Yesu ya ji tausayin mutane don yana ƙaunar su. Ya fahimci yadda waɗanda suka yi sanyin gwiwa suke ji. Waɗannan sun karaya kamar kara marar ƙarfi ko kuma wutar lagwani da ta kusan mutuwa. Saboda haka, yana yin la’akari da su kuma yana haƙuri da su. Har ma yara suna so su kasance tare da Yesu. (Mar. 10:14) Hakika, ba za mu iya fahimtar yanayin mutane da kuma koyar da su kamar Yesu ba! Amma, muna iya nuna cewa muna yin la’akari da waɗanda suke yankinmu. Hakan ya ƙunshi yadda muke musu wa’azi da lokacin da muke musu wa’azi da yawan lokacin da muke hakan.

14. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali da yadda muke wa mutane wa’azi?

14 Yaya ya kamata mu yi wa mutane magana? ’Yan siyasa da masu kasuwanci da kuma shugabanan addinai suna wahalar da mutane da yawa a yau. (Mat. 9:36) Shi ya sa mutane da yawa ba sa yarda da kowa kuma sun fid da rai. Saboda haka, ya kamata mu nuna musu cewa mun damu da su ta yadda muke musu magana! Mutane da yawa a yau suna so su saurari saƙonmu ba kawai don muna amfani da Littafi Mai Tsarki ba, amma don mun damu da su kuma muna daraja su.

15. A waɗanne hanyoyi ne za mu riƙa yin la’akari da mutanen da muke musu wa’azi?

15 Da akwai hanyoyi da yawa da za mu nuna muna yin la’akari da mutane da muke musu wa’azi. Alal misali, yin tambayoyi yana da kyau, amma ya kamata mu yi hakan a hanyar da za ta nuna cewa muna daraja mutanen. Akwai wani majagaba da yake hidima a yankin da mutane da yawa suke jin kunya. Saboda haka, ba ya yin tambayoyin da za su kunyatar da su. Hakan ya ƙunshi yin tambayoyin da ba za su iya amsawa ba. Alal misali, ba ya tambayar su cewa, ‘Ka san sunan Allah?’ ko kuma ‘Ka san ko mene ne Mulkin Allah?’ Maimakon haka, yakan ce, “Na koyi a Littafi Mai Tsarki cewa Allah yana da suna. Za ka so in nuna maka sunan?” Ba a kowane wuri ba ne za a iya bin wannan tsarin domin mutane da al’adu sun bambanta. Amma, ya kamata mu riƙa yin la’akari da mutane a yankinmu a koyaushe. Saboda haka, muna bukatar mu san su sosai.

16, 17. Ta yaya yin la’akari da mutane zai shafi (a) lokacin da muke kai musu ziyara? (b) yawan lokacin da muke yi muna tattaunawa da su?

16 A wane lokaci ne ya dace mu ziyarci mutane? Sa’ad da muke wa’azi gida-gida mu baƙi ne domin mutanen ba su gayyace mu ba. Saboda haka, yana da muhimmanci mu ziyarce su a lokacin da za su tattauna da mu! (Mat. 7:12) Alal misali, wataƙila mutane a yankinku ba sa tashiwa daga barci da sauri a ƙarshen mako. Kana iya soma yin wa’azi a kan titi ko a wurin da jama’a suke ko kuma ka ziyarci mutanen da za su so su tattauna da kai.

17 Har tsawon wane lokaci za mu yi? Mutane da yawa sun shagala da aiki. Saboda haka, bai kamata mu riƙa daɗewa a gidansu ba, musamman a lokaci na farko da muka yi musu wa’azi. Ya fi kyau mu gama tattaunawa da sauri maimakon mu daɗe ainun. (1 Kor. 9:​20-23) Idan mutane suka lura cewa mun san cewa ba su da lokaci ko kuma suna aiki, za su yarda mu sake dawowa. Hakika, ya kamata mu nuna halayen da ruhun Allah yake sa mu kasance da su sa’ad da muke wa’azi. Idan muka yi hakan, za mu zama “abokan aiki na Allah.” Jehobah zai iya yin amfani da mu wajen sa wani ya soma bauta masa.​—1 Kor. 3:​6, 7, 9.

18. Wace albarka ce za mu samu idan muna yin la’akari da mutane?

18 Bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu riƙa yin la’akari da mutane a iyalinmu da ikilisiya da kuma sa’ad da muke wa’azi. Idan muka yi hakan, za mu sami albarka sosai a yanzu da kuma a nan gaba. Littafin Zabura 41:​1, 2, ya ce: “Mai albarka ne wanda yake kula da marasa ƙarfi, Yahweh zai cece shi a lokacin wahala. . . . Za a ce da shi mai albarka.”