Ku Rika Nuna Kauna Domin Tana Karfafa Mutane
“Ƙauna tana ginawa” ko ƙarfafawa.—1 KOR. 8:1.
1. Wane batu mai muhimmanci ne Yesu ya tattauna da almajiransa a darensa na ƙarshe?
YESU ya ambata ƙauna kusan sau 30 a dare na ƙarshe da ya yi da almajiransa. Ya faɗi cewa ya kamata almajiransa su “ƙaunaci juna.” (Yoh. 15:12, 17) Za su riƙa ƙaunar juna sosai kuma hakan zai sa mutane su san cewa su ne mabiyansa na gaske. (Yoh. 13:34, 35) Wannan ƙaunar ba yadda suke ji ba ne amma za su riƙa nuna ƙauna ba tare da son kai ba. Yesu ya ce: “Ba ƙaunar da ta fi wannan, wato mutum ya ba da ransa saboda abokansa. Ku abokaina ne in kun yi abin da na ce ku yi.”—Yoh. 15:13, 14.
2. (a) Wane hali ne bayin Allah suke nunawa a yau? (b) Waɗanne tambayoyi ne za a amsa a wannan talifin?
2 An san bayin Jehobah a yau don yadda suke ƙaunar juna ba tare da son kai ba kuma hakan yana sa su kasance da haɗin kai. (1 Yoh. 3:10, 11) Muna farin ciki cewa bayin Jehobah suna nuna irin wannan ƙaunar ko da ƙasarsu ko ƙabilarsu ko yarensu ko kuma yadda aka yi renonsu ya bambanta! Amma, muna iya yin tunani: ‘Me ya sa ƙauna take da muhimmanci a zamaninmu? Ta yaya Jehobah da Yesu suke ƙarfafa mu? Ta yaya kowannenmu zai nuna irin wannan ƙaunar da ke ƙarfafa mutane?’—1 Kor. 8:1.
ABIN DA YA SA ƘAUNA TAKE DA MUHIMMANCI YANZU
3. Ta yaya wahala a yau take shafan mutane?
3 Domin muna rayuwa a kwanakin ƙarshe, muna “fama . . . da wahala.” Kuma hakan yana sa mutane da yawa su fid da rai. (Zab. 90:10; 2 Tim. 3:1-5) Ƙari ga haka, mutane fiye da 800,000 suna kashe kansu a kowace shekara, wato mutum ɗaya a kowace sakan 40 ke nan. Abin baƙin ciki, har wasu Kiristoci sun karaya don matsaloli na rayuwa kuma suka kashe kansu.
4. Waɗanne mutane da aka ambata a Littafi Mai Tsarki ne suka so su mutu?
4 A zamanin dā, wasu bayin Allah masu aminci sun fuskanci matsaloli kuma hakan ya sa sun gwammace su mutu. Alal misali, Ayuba ya sha azaba da ya sa ya ce “ina ƙyamar raina, na gaji da rayuwa.” (Ayu. 7:16; 14:13) Yunana ya yi baƙin ciki don sakamakon hidimarsa, kuma ya ce: “Domin haka fa, ya Yahweh, ina roƙonka ka ɗauki raina. Gama gwamma in mutu da in rayu.” (Yon. 4:3) Akwai lokacin da yanayin annabi Iliya ya shafe shi sosai har ya so ya mutu. Ya ce: “Ya Yahweh, kome ya ishe ni. Bari ka ɗauki raina.” (1 Sar. 19:4) Amma Jehobah yana ƙaunar waɗannan bayinsa masu aminci kuma ya so su ci gaba da rayuwa. Bai tsauta musu ba don yadda suka ji, maimakon haka ya taimaka musu su so ci gaba da rayuwa don su riƙa bauta masa.
5. Me ya sa ’yan’uwa suke bukatar a nuna musu ƙauna musamman yanzu?
5 Ko da ’yan’uwanmu ba su ji kamar su fid rai ba, da yawa a cikinsu suna fama da matsaloli kuma muna bukatar mu riƙa ƙarfafa su. Ban da haka, ana tsananta ma wasu da kuma yi musu ba’a. Wasu kuma ana wulaƙanta su ko kuma riƙa gulma game da su a wurin aiki. Wasu kuma sun gaji da yin aiki na dogon lokaci ko kuma aiki mai wuya sosai. Har ila, wasu suna fuskantar matsaloli a iyalinsu, wataƙila don mijinsu ko kuma matarsu da ba ta bauta wa Jehobah tana zagin su a kai a kai. Domin waɗannan matsalolin, wasu suna gani sun gaji kuma suna ji ba su da amfani. Wane ne zai taimaka wa waɗanda suka karaya?
ƘAUNAR DA JEHOBAH KE MANA TANA ƘARFAFA MU
6. Ta yaya yadda Jehobah yake ƙaunar bayinsa yake ƙarfafa su?
6 Jehobah ya tabbatar wa bayinsa da cewa yana ƙaunar su kuma zai yi hakan har abada. Babu shakka, Isra’ilawa masu aminci sun sami ƙarfafa sa’ad da Jehobah ya ce: “Kana da daraja a idanuna, ina girmama ka, ina kuma ƙaunar ka. . . . Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai.” (Isha. 43:4, 5) A matsayinmu na bayin Jehobah, mun san cewa yana ƙaunar kowannenmu sosai. * Jehobah ya tabbatar wa bayinsa a Kalmarsa cewa zai cece su don shi ‘mai yaƙi ne mai ba da nasara. Zai yi farin ciki ya yi murna a kansu.’—Zaf. 3:16, 17.
7. A wace hanya ce Jehobah yake kamar mai jego? (Ka duba hoton da ke shafi na 12.)
7 Jehobah ya yi alkawari cewa zai ƙarfafa mutanensa da kuma yi musu ta’aziyya a kowace irin matsalar da Isha. 66:12, 13) Ka yi tunani yadda jariri yake ji a hannun mamarsa ko kuma sa’ad da take wasa da shi! Haka ne Jehobah yake ƙaunar bayinsa kuma yana so su kasance da kwanciyar hankali. Kada ka yi shakka cewa Jehobah yana ɗaukan ka da tamani sosai.—Irm. 31:3.
suke fuskanta. Ya ce: ‘Za ku ji daɗin renon da nake yi muku, ku ji daɗi yadda nake riƙe ku a hannu, kamar jariri mai jin daɗi a hannun mamarsa. Yadda mama take ta’azantar da yaronta, haka zan ta’azantar da ku.’ (8, 9. Ta yaya ƙaunar da Yesu ya nuna mana take ƙarfafa mu?
8 Kiristoci na gaske suna da wani dalili na sanin cewa Allah yana ƙaunar su: “Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya halaka, amma ya sami rai na har abada.” (Yoh. 3:16) Hadayar da Yesu ya yi da ransa a madadinmu ya nuna cewa shi ma yana ƙaunar mu, kuma hakan yana ƙarfafa mu! Kalmar Allah ta ce “azaba . . . ko wuya” ba za su iya “raba mu da ƙaunar da Almasihu yake yi mana” ba.—Rom. 8:35, 38, 39.
9 A wasu lokuta, muna fama da matsalolin da ke gajiyar da mu ko suke sa mu sanyin gwiwa. Hakan yana iya hana mu farin ciki a bautarmu ga Jehobah. Amma tuna yadda Kristi yake ƙaunar mu zai ƙarfafa mu mu jimre. (Karanta 2 Korintiyawa 5:14, 15.) Kuma ƙauna tana sa mu so ci gaba da rayuwa da kuma bauta wa Jehobah. Hakan zai hana mu fid da rai, ko da muna fuskantar bala’i ko ana tsananta mana ko an ci amanarmu ko kuma muna alhini.
MUNA BUKATAR MU RIƘA ƘAUNAR ’YAN’UWA
10, 11. Wane ne yake da hakkin ƙarfafa waɗanda suka yi sanyin gwiwa? Ka bayyana.
10 Jehobah yana amfani da ’yan’uwa a ikilisiya don ya ƙarfafa mu. Muna nuna ƙaunarmu ga Jehobah sa’ad da muka ƙaunaci ’yan’uwanmu. Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu taimaka wa ’yan’uwa su san cewa suna da daraja kuma Jehobah yana ƙaunar su. (1 Yoh. 4:19-21) Manzo Bulus ya ce: “Sai ku ƙarfafa juna, ku yi ta gina juna, kamar dai yadda kuke yi yanzu.” (1 Tas. 5:11) Kowannenmu zai iya yin koyi da Jehobah da kuma Yesu ta wajen ƙarfafa ’yan’uwanmu. Yin hakan ba aikin dattawa kaɗai ba ne amma na dukanmu ne.—Karanta Romawa 15:1, 2.
11 Wasu ’yan’uwa a ikilisiya da suke rashin lafiyar da ke shafan hankalinsu da tunaninsu suna iya bukaci taimakon likita. (Luk. 5:31) Dattawa da ’yan’uwa a ikilisiya ba likitoci ba ne, amma yana da muhimmanci su ‘ƙarfafa waɗanda ba su da ƙarfin zuciya, su taimaki marasa ƙarfi, su yi haƙuri da kowa.’ (1 Tas. 5:14) Dukan Kiristoci suna bukatar su nuna juyayi, su riƙa haƙuri da waɗanda suka yi sanyin gwiwa su kuma ƙarfafa su. Kana ƙoƙari ka ƙarfafa wasu? Mene ne za ka iya yi don ka ƙarfafa da kuma ta’azantar da mutane?
12. Ka ba da misalin wata da ’yan’uwa a ikilisiya suka ƙarfafa.
12 Ta yaya za mu ƙarfafa waɗanda suke baƙin ciki? Wata ’yar’uwa a Turai ta ce: “A wasu lokuta nakan ji kamar in kashe kaina, amma ina da masu taimaka mini. ’Yan’uwa a ikilisiyarmu sun cece ni. A koyaushe suna ƙarfafa ni kuma suna ƙauna ta. Ko da yake wasu ne kawai suka san cewa ina baƙin ciki sosai, amma ’yan’uwan suna taimaka min a kowane lokaci. Wasu ma’aurata suna kamar iyaye a gare ni. Suna kula da ni kusan kowane lokaci.” Hakika, ba kowa ba ne zai iya taimaka wa mutum hakan ba, amma kowannenmu zai iya yin iya ƙoƙarinsa don ya taimaka ma waɗanda suke baƙin ciki. *
YADDA ZA MU RIƘA ƘARFAFA WASU
13. Mene ne muke bukatar mu yi don mu ƙarfafa wasu?
13 Ka zama mai saurarawa da kyau. (Yaƙ. 1:19) Muna nuna cewa muna ƙaunar ɗan’uwan da ya yi sanyin gwiwa idan muka saurare shi kuma muka nuna masa juyayi. Ka yi ƙoƙari ka yi tunanin yadda za ka ji idan kai ne kake cikin yanayinsa. Ka yi tambayoyin da za su taimaka maka ka fahimci yanayinsa sosai kuma ka yi hakan cikin dabara. Yanayin fuskarka za ta nuna ko ka damu da shi da gaske. Sa’ad da mutumin yake magana, ka ƙyale shi ya faɗi abin da ke zuciyarsa ba tare da ka katse masa magana ba. Ta wurin saurarar sa da kyau, za ka san yadda yake ji kuma zai amince da kai. Ƙari ga haka, shi ma zai so ya bi shawarwarin da ka ba shi. Idan wasu sun san ka damu da su, za ka ƙarfafa su sosai.
14. Me ya sa muke bukatar mu guji halin kushe ’yan’uwanmu?
14 Ka guji kushe ’yan’uwanka. Mutum zai daɗa yin baƙin ciki idan yana gani kana kushe shi, kuma zai yi wuya ka iya taimaka masa. “Maganar da an yi da rashi tunani tana sa rauni kamar sokin takobi, amma harshe mai hikima yakan kawo warkewa.” (K. Mag. 12:18) Hakika, ba da gangan muke “sokin” waɗanda suke baƙin ciki da furucinmu ba. Amma, yakan yi zafi sosai ko da ba da gangan ba muka ‘soki’ mutumin ba. Don mu ƙarfafa ’yan’uwanmu, wajibi ne mu tabbatar musu da cewa muna ƙoƙari mu fahimci yanayinsu.—Mat. 7:12.
15. Wane abu ne za mu iya amfani da shi don mu ƙarfafa mutane?
15 Ka yi amfani da Kalmar Allah don Romawa 15:4, 5.) “Allah mai ba da jimrewa da ƙarfafawa” shi ne mawallafin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, za mu iya samun kalmomi masu ban-ƙarfafa a cikin Littafi Mai Tsarki. Ban da haka, muna da littattafan da suke taimaka mana mu fahimci Littafi Mai Tsarki. Za mu iya yin amfani da Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah. Littafin zai taimaka mana mu samo Nassosin da za su sa mu jimre da kowace irin matsala kuma zai taimaka mana mu ƙarfafa ’yan’uwanmu.
ka ƙarfafa mutane. (Karanta16. Waɗanne halaye ne muke bukata sa’ad da muke ƙarfafa ɗan’uwa da ya yi sanyin gwiwa?
16 Ka zama mai tausayi da sanin yakamata. Waɗannan halayen suna da muhimmanci sosai sa’ad da muke ƙarfafa wani. Jehobah ne “Uba mai yawan tausayi, Allah wanda yake yi mana kowace irin ta’aziyya” kuma yana nuna wa bayinsa ‘jinƙai.’ (Karanta 2 Korintiyawa 1:3-6; Luk. 1:78; Rom. 15:13) Bulus ya kafa mana misali mai kyau a wannan batun, ya ce: “Yadda mama take renon jaririnta ta kuma lura da shi, haka mun lura da ku cikin sauƙin kai. Saboda muna ƙaunarku ƙwarai, shi ya sa muka ji daɗin yi muku wa’azin labari mai daɗi na Allah, ba wa’azi kaɗai ba, amma mun ji daɗin ba da rayukanmu saboda kun shiga ranmu sosai.” (1 Tas. 2:7, 8) Idan muka zama masu tausayi kamar Jehobah, za mu iya ƙarfafa ɗan’uwa da ya yi sanyin gwiwa.
17. Wane ra’ayi game da ’yan’uwanmu ne zai ƙarfafa su?
17 Kada ka yi zato cewa ya kamata ’yan’uwa su zama kamilai. Ka kasance da ra’ayin da ya dace game da ’yan’uwa. Za ka yi baƙin ciki idan kana zato cewa ’yan’uwa za su riƙa yin abubuwan da suka dace a kowane lokaci. (M. Wa. 7:21, 22) Ka tuna cewa Jehobah ba ya bukatar mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. Idan muka yi koyi da shi, za mu kasance a shirye mu yi haƙuri da wasu. (Afis. 4:2, 32) Maimakon mu riƙa nuna wa ’yan’uwanmu cewa ba sa yin iya ƙoƙarinsu, ya fi kyau mu riƙa yaba musu. Hakan zai ƙarfafa su kuma ya sa su farin ciki a hidimarsu. Saboda haka, ya fi kyau mu yaba musu maimakon mu riƙa gwada su da wasu.—Gal. 6:4.
18. Me ya sa muke bukatar mu riƙa ƙarfafa ’yan’uwanmu?
18 Kowanne bawan Jehobah yana da tamani a gare shi da kuma Yesu wanda ya ba da ransa hadaya. (Gal. 2:20) Muna ƙaunar ’yan’uwanmu sosai, saboda haka ya kamata mu riƙa nuna musu juyayi. Don mu riƙa kwantar musu da hankali, “bari mu yi iyakacin ƙoƙarinmu don mu aikata abin da zai kawo salama da ƙarfafawar juna.” (Rom. 14:19) Muna ɗokin yin rayuwa a Aljanna sa’ad da babu wanda zai yi sanyin gwiwa! Ba za a ƙara yin ciwo ba, ko yaƙe-yaƙe ko mutuwa ko tsanantawa, ko matsalolin iyali ko cin amanar wani. A ƙarshen shekara dubu, dukan mutane za su zama kamilai. Waɗanda suka kasance da aminci a gwaji na ƙarshe za su zama ’ya’yan Allah a duniya kuma su more “ ’yancin nan na ɗaukakar da za a yi wa ’ya’yan Allah.” (Rom. 8:21) Saboda haka, ya kamata dukanmu mu riƙa nuna ƙauna kuma mu ƙarfafa juna don mu tsira mu shiga cikin sabuwar duniya da Allah ya yi mana alkawarin ta.
^ sakin layi na 12 Don sanin yadda za ka taimaka ma waɗanda suke tunanin kashe kansu, ka duba talifofin nan da ke Awake! mai jigo: “Why Go On? Three Reasons to Keep Living” (Afrilu 2014); “When You Feel Like Giving Up on Life” (Janairu 2012); da “Life Is Worth Living” (22 ga Oktoba, 2001).