Ta Yaya Ake Sanin Lokaci a Zamanin Dā?
MENE NE za ka yi idan kana son ka san ko ƙarfe nawa ne? Wataƙila za ka duba agogonka. Idan abokinka ne fa ya tambaye ka lokaci? Da akwai hanyoyi da yawa na faɗin lokaci. Waɗanne hanyoyi ke nan?
Faɗin lokaci ya dangana da inda kake da zama. Alal misali, kana iya gaya wa wani cewa ƙarfe ɗaya ya wuce da minti talatin ko kuma ƙarfe ɗaya da rabi. A wasu wurare, kana iya cewa, “ƙarfe biyu sauran minti 30.”
A matsayinka na mai karanta Littafi Mai Tsarki, kana iya yin tunanin yadda mutane a zamanin dā suke faɗin lokaci. Suna faɗin hakan a hanyoyi dabam-dabam. Nassosin Ibrananci sun yi amfani da furucin nan da “sassafe,” ko da “rana” ko “tsakar rana” ko kuma “yamma.” (Far. 8:11; 19:27; 43:16; M. Sha. 28:29; 1 Sar. 18:26) Amma a wasu lokuta, Littafi Mai Tsarki ya faɗi ainihin lokacin da wani abu ya faru.
A zamanin dā, ana yin amfani da masu tsaro domin ana bukatar su sosai daddare. Shekaru da yawa kafin a haifi Yesu, Isra’ilawa sukan raba lokacin yin tsaro daddare kashi uku. (Zab. 63:6) A littafin Alƙalai 7:19, an ambata “tsakar dare.” A zamanin Yesu, Yahudawa sun raba dare zuwa kashi huɗu yadda Girkawa da Romawa suke yi.
Littafin Linjila ya ambata waɗannan lokatan tsaro sau da yawa. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ambata cewa Yesu ya taka a kan ruwa zuwa wurin almajiransa a “wajen ƙarfe uku na dare.”—Mat. 14:25.
Yesu ya ambata dukan waɗannan lokatan tsaro guda huɗu sa’ad da ya gaya wa almajiransa cewa: “Ku zauna da shiri, don ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba. Gama zai iya dawowa ko da yamma, ko ka tsakar dare, ko da carar zakara, ko kuwa da safe.” (Mar. 13:35) Lokacin tsaro na farko shi ne “da yamma,” wato daga faɗuwar rana har zuwa misalin ƙarfe tara na dare. Lokacin tsaro na biyu, wato “tsakar dare” yana somawa daga misalin ƙarfe tara na dare zuwa tsakar dare. Lokacin tsaro na uku shi ne “da carar zakara,” wato daga tsakar dare zuwa wajen ƙarfe uku. Wataƙila a wannan lokacin ne zakara ya yi cara a daren da aka kama Yesu. (Mar. 14:72) Lokacin tsaro na huɗu shi ne daga ƙarfe uku zuwa fitowar rana.
Saboda haka, ko da yake mutane a zamanin dā ba sa yin amfani da agogo kamar mu a yau, amma akwai yadda suke sanin lokaci.