Wadanda Ke Bauta wa Allah Suna Farin Ciki
“Masu farin ciki ne mutanen da Jehobah ne Allahnsu.”—ZAB. 144:15, New World Translation.
1. Me ya sa masu bauta wa Jehobah suke farin ciki? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
SHAIDUN JEHOBAH mutane ne masu yin farin ciki sosai. A duk lokacin da suka halarci taron ikilisiya ko manyan taro ko kuma sa’ad da suke cuɗanya da juna, suna hira da kuma dariya domin farin cikin da suke yi. Mene ne ya sa suke farin ciki? Dalilin shi ne, sun san Jehobah, suna bauta masa kuma suna ƙoƙarin yin koyi da shi domin shi Allah ne mai farin ciki. (1 Tim. 1:11; Zab. 16:11) Da yake Jehobah Allah ne mai farin ciki, yana son mu riƙa farin ciki kuma ya ba mu dalilai da yawa na yin hakan.—M. Sha. 12:7; M. Wa. 3:12, 13.
2, 3. (a) Mene ne farin ciki yake nufi? (b) Me ya sa zai iya yi mana wuya mu riƙa farin ciki?
2 Kai kuma fa? Kana farin ciki? Za ka iya daɗa yin farin ciki? “Farin ciki yana nufin kasancewa da kwanciyar hankali da wadar zuci da kuma yin murna sosai.” Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa waɗanda suke da dangantaka mai kyau da Jehobah ne za su yi farin ciki na gaske. Amma a yau, yana da wuya mutane su yi farin ciki. Me ya sa?
3 Ba za mu yi farin ciki ba idan ɗan’uwanmu ya mutu ko an 1 Tim. 6:15; Mat. 11:28-30) A Huɗubarsa a Kan Dutse, Yesu ya bayyana halayen da za su iya taimaka mana mu yi farin ciki duk da matsalolin da muke fuskanta a wannan duniyar Shaiɗan.
yi masa yankan zumunci ko aurenmu ya mutu ko kuma idan an sallame mu daga wurin aiki. Yana iya yi mana wuya mu yi farin ciki idan babu kwanciyar hankali a gidanmu ko idan abokan aikinmu ko ’yan makarantarmu suna zolayar mu. Ƙari ga haka, idan muka soma rashin lafiya ko baƙin ciki ko muna fuskantar tsanantawa ko kuma an saka mu a kurkuku don imaninmu, hakan yana iya hana mu farin ciki. Amma muna bukatar mu tuna cewa Yesu wanda shi sarkinmu ne mai farin ciki, yana son ƙarfafa mutane kuma ya sa su farin ciki. (DANGANTAKA MAI KYAU DA JEHOBAH ZA TA SA MU FARIN CIKI
4, 5. Mene ne za mu yi don mu yi farin ciki kuma mu ci gaba da yin hakan?
4 Abin da Yesu Kristi ya soma ambatawa yana da muhimmanci sosai. Ya ce: “Masu farin ciki ne waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah, domin za su gāji mulkin sama.” (Mat. 5:3, NW ) Ta yaya za mu nuna cewa mun damu da dangantakarmu da Jehobah? Ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da bin dokokinsa da kuma ɗaukan ibadarmu a matsayin abin da ya fi muhimmancin a rayuwa. Idan mun yin hakan za mu yi farin ciki sosai kuma bangaskiyarmu cewa Allah zai cika alkawuransa za ta yi ƙarfi sosai. Ƙari ga haka, begen da Kalmar Allah take sa mu kasance da shi zai taimaka mana mu jimre matsalolin da muke fuskanta.—Tit. 2:13.
5 Ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah yana da muhimmanci idan muna so mu riƙa farin ciki. Manzo Bulus ya ce: “Ku yi farin ciki cikin Ubangiji [Jehobah] kullum. Ina sāke gaya muku ku, yi farin ciki.” (Filib. 4:4) Idan muna so mu kasance da irin wannan dangantaka mai kyau da Allah, muna bukatar mu sami hikimar da Allah ke bayarwa. Kalmar Allah ta ce: “Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima, wanda kuma ya sami fahimta. Hikima itacen rai ce ga waɗanda suka same ta, masu albarka ne waɗanda suka riƙe ta.”—K. Mag. 3:13, 18.
6. Mene ne muke bukatar mu yi don mu riƙa farin ciki?
6 Amma idan muna so mu riƙa farin ciki, muna bukatar mu karanta Littafi Mai Tsarki kuma mu riƙa yin abin da muka koya daga Kalmar Allah. Yesu ya nanata muhimmancin yin hakan sa’ad da ya ce: In “kun san waɗannan abubuwa za ku zama masu albarka [‘farin ciki’ NW ] idan kun yi su.” (Yoh. 13:17; Karanta Yaƙub 1:25.) Yin hakan yana da muhimmanci idan muna so mu ƙarfafa dangantakarmu da Allah kuma mu yi farin ciki. Amma ta yaya za mu yi farin ciki duk da cewa da akwai abubuwa da yawa da ke sa mu baƙin ciki? Bari mu tattauna abin da Yesu ya ƙara faɗa a Huɗubarsa a kan Dutse.
HALAYEN DA KE SA MU FARIN CIKI
7. Ta yaya waɗanda ke baƙin ciki za su yi farin ciki?
7 ‘Masu albarka ne masu baƙin ciki, gama za a yi musu ta’aziyya.’ (Mat. 5:4) Wasu na iya yin tunani, ‘Ta yaya mutum zai yi farin ciki idan yana baƙin ciki?’ Yesu ba ya nufin dukan waɗanda ke yin baƙin ciki. Mugaye da yawa suna baƙin ciki saboda wahalolin da ake sha a wannan “kwanaki na ƙarshe.” (2 Tim. 3:1) Amma suna tunanin kansu ne kaɗai ba Jehobah ba. Ba za su yi farin ciki ba domin ba su ƙulla dangantaka da Jehobah ba. Yesu yana magana ne game da waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah. Suna baƙin ciki ne don suna ganin yadda mutane da yawa suke taka dokar Allah kuma ba sa yin rayuwa yadda yake so. Ƙari ga haka, sun san cewa su ajizai ne kuma suna ganin abubuwan da ke faruwa a duniya. Jehobah yana lura da irin waɗannan mutanen da suke baƙin ciki, kuma yana amfani da Kalmarsa don ya ƙarfafa su su yi farin ciki.—Karanta Ezekiyel 5:11; 9:4.
8. Ta yaya zama masu tawali’u zai sa mu farin ciki? Ka bayyana.
8 Masu farin ciki ne ‘masu tawali’u, gama za su gāji duniya.’ (Mat. 5:5) Ta yaya zama masu tawali’u zai sa mu riƙa farin ciki? Sa’ad da mutane suka koyi gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki, hakan yana sa su canja salon rayuwarsu. Wataƙila a dā suna da zafin rai ko suna yawan faɗa ko kuma saurin fushi. Amma yanzu sun yafa “sabon hali” kuma suna ‘jin tausayin juna, suna yin alheri, suna nuna tawali’u da sauƙin kai da jimrewa.’ (Kol. 3:9-12) A sakamako, yanzu suna da kwanciyar hankali, suna zaman lafiya da mutane kuma suna farin ciki. Kalmar Allah ta ce irin waɗannan mutanen za su “gāji ƙasar.”—Zab. 37:8-10, 29.
9. (a) Ta yaya masu tawali’u za su “gāji duniya”? (b) Me ya sa waɗanda ke “jin yunwa da ƙishin yin adalci” za su yi farin ciki?
9 Ta yaya masu tawali’u za su “gāji duniya”? Shafaffu za su gāji duniya a lokacin da za su yi sarauta a sama bisa duniya kuma su zama firistoci. (R. Yar. 20:6) Miliyoyin mutane da ba shafaffu ba ne za su gāji duniya ta wajen yin rayuwa har abada a cikinta. Za su zama kamilai kuma za su yi rayuwa da kwanciyar hankali da kuma farin ciki. Su ne waɗanda Yesu ya ce suna “jin yunwa da ƙishin yin adalci.” (Mat. 5:6) Burinsu na yin adalci zai cika sa’ad da Jehobah ya halaka mugaye. (2 Bit. 3:13) Hakan zai sa mutane masu adalci farin ciki sosai kuma ba za su ƙara yin baƙin ciki domin abubuwan da mugaye ke yi ba.—Zab. 37:17.
10. Mene ne zama masu jinƙai yake nufi?
10 Masu farin ciki ne ‘masu nuna jinƙai, gama za a nuna musu jinƙai.’ (Mat. 5:7) Nuna jinƙai tana nufin nuna alheri da juyayi, wato jin tausayin waɗanda suke shan wahala. Amma jinƙai ba yadda muke ji kawai ba ne. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa jinƙai ya ƙunshi ɗaukan mataki don mu taimaka wa mutane.
11. Mene ne za mu iya koya game da nuna jinƙai daga kwatancin Basamariye?
11 Karanta Luka 10:30-37. A kwatancinsa na Basamariye, Yesu ya bayyana abin da nuna jinƙai yake nufi. Juyayi da kuma tausayi sun sa Basamariyen ya taimaka wa mutumin da ke shan wahala. Bayan Yesu ya kammala kwatancin, ya ce: “Sai kai ma ka tafi ka yi haka.” Muna bukatar mu tambayi kanmu: ‘Shin ina yin hakan? Ina yin abin da Basamariyen nan ya yi kuwa? Idan wasu na shan wahala, ina ƙoƙari don in nuna musu jinƙai? Ina ƙoƙari don in taimaka musu? Alal misali, zan iya taimaka wa tsofaffi a ikilisiya ko gwauraye ko kuma yaran da iyayensu ba sa bauta wa Jehobah? Shin zan iya “ƙarfafa waɗanda ba su da ƙarfin zuciya”?’—1 Tas. 5:14; Yaƙ. 1:27.
12. Ta yaya nuna jinƙai yake sa mu farin ciki?
A. M. 20:35; karanta Ibraniyawa 13:16.) Sarki Dawuda ya yi magana game da mutumin da ke nuna jinƙai. Ya ce: “Yahweh zai cece shi a lokacin wahala. Yahweh zai tsare shi ya kuma kiyaye ransa, a cikin ƙasar za a ce da shi mai albarka.” (Zab. 41:1, 2) Idan muna nuna jinƙai da kuma tausaya ma mutane, hakan zai sa Jehobah ma ya nuna mana jinƙai kuma za mu yi farin ciki har abada.—Yaƙ. 2:13.
12 Amma ta yaya zama masu jinƙai zai sa mu farin ciki? Sa’ad da muka nuna ma wasu jinƙai muna bayarwa ne, Yesu ya ce bayarwa tana sa mutum farin ciki. Wani dalili kuma shi ne don muna yin abin da Jehobah yake so. (ABIN DA YA SA “MASU TSABTAR ZUCIYA” SUKE FARIN CIKI
13, 14. Me ya sa “masu tsabtar zuciya” suke farin ciki?
13 Masu farin ciki ne ‘masu tsabtar zuciya, gama za su ga Allah.’ (Mat. 5:8) Idan muna son zuciyarmu ta kasance da tsabta, muna bukatar mu guji sha’awoyin banza. Muna bukatar mu riƙa tunani mai kyau idan muna so Jehobah ya amince da ibadarmu.—Karanta 2 Korintiyawa 4:2; 1 Tim. 1:5.
14 Waɗanda suke da zuciya mai tsabta za su more dangantaka da Allah, wanda ya ce: “Masu albarka ne waɗanda suke wanke rigunansu.” (R. Yar. 22:14) A wace hanya ce suke “wanke rigunansu”? Ga shafaffun Kiristoci, hakan yana nufin cewa Jehobah yana ɗaukan su a matsayin masu tsarki. Ƙari ga haka, zai ba su rai marar mutuwa kuma za su yi farin ciki a sama har abada. Ga taro mai-girma da suke da begen yin rayuwa a duniya, hakan yana nufin cewa Jehobah ya amince su zama abokansa domin su adilai ne. Kuma har yanzu suna kan “wanke rigunansu da jinin Ɗan Ragon” don rigunan su zama farare.—R. Yar. 7:9, 13, 14.
15, 16. A wace hanya ce masu tsabtar zuciya za su ga Allah?
15 Amma ta yaya masu tsabtar zuciya za su ga Allah tun da babu wanda “zai iya ganin [Allah]” ya rayu? (Fit. 33:20) Kalmar nan ‘gani’ a Helenanci tana iya nufin “gani da idon zuci ko sani ko kuma fahimta.” Don haka, ganin Allah yana nufin mu fahimce shi sosai kuma mu yi koyi da halayensa. (Afis. 1:18) Yesu yana da halayen Allah, shi ya sa ya ce: “Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban.”—Yoh. 14:7-9.
16 Ƙari ga sanin halayen Allah, masu bauta wa Allah suna iya ganin sa ta wurin lura da yadda yake taimaka masu. (Ayu. 42:5) Ban da haka ma, suna mai da hankali ga alkawuran da Allah ya yi ma waɗanda suka kasance da tsabta kuma suka bauta masa da aminci. Hakika, shafaffu da aka ta da daga mutuwa za su ga Allah sa’ad da suka je sama.—1 Yoh. 3:2.
ZA MU YI FARIN CIKI DUK DA MATSALOLI
17. Me ya sa masu sada zumunci suke farin ciki?
17 Yesu ya sake cewa: Masu farin ciki ne “masu sada zumunci.” (Mat. 5:9) Idan muka yi ƙoƙari mu zauna lafiya da mutane, za mu yi farin ciki. Manzo Yaƙub ya ce: “Daga ƙwayar salama wadda masu kawo salama suke shukawa, a kan girbe adalci.” (Yaƙ. 3:18) Idan muka sami saɓani da wani a ikilisiya ko kuma a iyalinmu, muna iya roƙon Jehobah ya taimaka mana mu zama masu sada zumunci. Jehobah zai ba mu ruhu mai tsarki don ya taimaka mana mu kasance da halaye masu kyau kuma ya sa mu farin ciki. Yesu ya nanata muhimmancin zama masu sada zumunci sa’ad da ya ce: “Idan kana cikin ba da baiko a kan bagaden hadaya, a nan ka tuna cewa ɗan’uwanka yana da wata damuwa game da kai, sai ka ajiye baikonka a gaban bagaden tukuna, ka je ka shirya da ɗan’uwanka. Sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.”—Mat. 5:23, 24.
18, 19. Me ya sa Kiristoci suke farin ciki ko da ana tsananta musu?
18 Masu farin ciki ne ku “sa’ad da mutane suka zage ku, suka tsananta muku, suka kuma yi muku mugunta iri-iri saboda ni.” Mene ne Yesu yake nufi? Ya ƙara da cewa: “Ku yi murna da farin ciki sosai, domin za ku sami lada mai yawa a sama, gama haka mutane suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.” (Mat. 5:11, 12) Sa’ad da aka yi wa manzannin Yesu dūka kuma aka umurce su su daina yin wa’azi, “manzannin suka tashi daga gaban majalisar suna farin ciki.” Hakika ba su yi farin ciki don an yi musu dūka ba, amma domin “sun isa su sha wulaƙanci saboda sunan Yesu.”—A. M. 5:41.
19 A yau, bayin Jehobah ma suna farin ciki yayin da suke jimre tsanantawa don imaninsu. (Karanta Yaƙub 1:2-4.) Kamar manzanni, ba ma farin ciki don wahalar da muke sha ko kuma tsanantawar da muke fuskanta don imaninmu. Amma idan muka riƙe amincinmu sa’ad da muke fuskantar gwaji, hakan zai sa Jehobah ya taimaka mana mu jimre. Alal misali, a watan Agusta na 1944, hukumomi sun tura Henryk Dornik da ɗan’uwansa zuwa sansani. Amma hukumomin sun ce: “Ba za mu iya tilasta musu yin kome ba. Suna jin daɗin wahalar da suke sha don imaninsu.” Ɗan’uwa Henryk Dornik ya ce: “Ko da yake ba na so a kashe ni, wahalar da nake sha don amincina ga Jehobah tana san ni farin ciki sosai. . . . Yin addu’a ya sa na kusaci Jehobah kuma ya taimaka mini.”
20. Me ya sa muke farin cikin bauta wa Allah mai farin ciki?
20 Idan Jehobah Allah mai farin ciki ya amince da mu, za mu yi farin ciki ko da ana tsananta mana don imaninmu ko ana tsananta mana a iyali ko muna rashin lafiya ko kuma don mun tsufa. (1 Tim. 1:11) Muna kuma yin farin ciki domin alkawuran da ‘Allah wanda ba ya ƙarya’ ya yi mana. (Tit. 1:2) Idan Jehobah ya cika alkawuransa, ba za mu tuna da dukan wahalolin da muke sha yanzu ba. A cikin Aljanna, Jehobah zai yi mana albarkun da ba mu taɓa tsammani ba. Hakika, za mu yi murna sosai domin za mu ‘sami farin ciki cikin salama a yalwace.’—Zab. 37:11.