Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 40

“Ka Lura da Abin da Aka Ba Ka Amana”

“Ka Lura da Abin da Aka Ba Ka Amana”

“Ya Timoti, ka lura da abin nan da aka ba ka amana.”​—1 TIM. 6:20.

WAƘA TA 29 Muna Ɗaukaka Sunanka

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Kamar yadda 1 Timoti 6:20 ta nuna, wane abu mai daraja ne aka ba Timoti?

IDAN muna da wani abu mai daraja, muna yawan ba mutane su kula da shi. Alal misali, muna saka kuɗi a banki. Idan muka yi hakan, muna kasancewa da tabbaci cewa za a kula da kuɗin kuma ɓarawo ba zai sace shi ba. Hakan ya sa mu fahimci ma’anar ba wani abu mai daraja don ya kula da shi.

2 Karanta 1 Timoti 6:20. Manzo Bulus ya tuna wa Timoti cewa an ba shi wani abu mai daraja, wato gaskiya game da nufin Allah ga ʼyan Adam. An kuma ba Timoti gatan yin “wa’azin kalmar Allah” da kuma “aikin mai shelar labari mai daɗi.” (2 Tim. 4:​2, 5) Bulus ya ƙarfafa Timoti ya kula da abin da aka ba shi amana. A yau, an ba mu amanar wasu abubuwa masu daraja. Me ke nan? Kuma me ya sa ya kamata mu kula da abubuwan nan da Jehobah ya ba mu?

AN BA MU GASKIYA MAI DARAJA

3-4. Me ya sa gaskiyar Littafi Mai Tsarki take da daraja?

3 Jehobah ya koya mana gaskiya game da Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Gaskiyar nan na da daraja domin tana koya mana yadda za mu ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma abin da zai sa mu farin ciki na gaske. Idan mun amince da gaskiya kuma muka bi ta, za mu sami ’yanci daga koyarwar ƙarya da kuma ɗabi’u marasa kyau.​—1 Kor. 6:​9-11.

4 Wani dalili kuma da ya sa gaskiyar nan ke da daraja shi ne domin Jehobah ya bayyana ta ga mutane masu sauƙin kai. (A. M. 13:48) Mutane masu sauƙin kai sun amince cewa Jehobah yana yin amfani da bawa mai hikima don ya koya mana gaskiya a yau. (Mat. 11:25; 24:45) Ba za mu iya koya wa kanmu gaskiyar nan ba, kuma sanin gaskiyar na da daraja sosai.​—K. Mag. 3:​13, 15.

5. Wane aiki ne kuma Jehobah ya ba mu?

5 Jehobah ya kuma ba mu gatan koya wa mutane gaskiya game da shi da kuma nufinsa. (Mat. 24:14) Gaskiyar nan tana da daraja sosai domin tana taimaka wa mutane su kasance cikin iyalin Jehobah kuma za ta sa su rayu har abada. (1 Tim. 4:16) Ko da muna wa’azi na sa’o’i da yawa ko a’a, muna ba da goyon baya ga aiki mafi muhimmanci da ake yi yanzu. (1 Tim. 2:​3, 4) Babu shakka, gata ne babba mu zama abokan aiki na Allah!​—1 Kor. 3:9.

KA DARAJA ABIN DA AKA BA KA!

Timoti ya bukaci ya ci gaba da bauta wa Jehobah sa’ad da wasu suka daina yin hakan (Ka duba sakin layi na 6)

6. Me ya faru da wasu da suka daina daraja gatan da aka ba su?

6 A zamanin Timoti, wasu Kiristoci ba su daraja gatan da suke da shi na zama abokan aiki na Allah ba. Demas ya daina hidima da Bulus domin yana son abin duniya. (2 Tim. 4:10) Faijelus da Hamojenis sun daina hidimarsu domin wataƙila suna tsoro cewa za a tsananta musu yadda ake tsananta wa manzo Bulus. (2 Tim. 1:15) Himinayas da Iskandari da kuma Filitas sun yi ridda kuma sun daina bin gaskiya. (1 Tim. 1:​19, 20; 2 Tim. 2:​16-18) Akwai lokacin da dukan mutanen nan suke ƙaunar Jehobah, amma daga baya, sun daina daraja abubuwan da aka ba su.

7. Waɗanne dabaru ne Shaiɗan yake amfani da su don ya rinjaye mu?

7 Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙarin sa mu daina daraja gatan da Jehobah ya ba mu? Ku yi la’akari da wasu cikin dabarun Shaiɗan. Yana yin amfani da fina-finai da Intane da kuma jaridu don ya cusa mana ra’ayinsa. Kuma sannu-a-hankali, hakan zai sa mu daina bauta wa Jehobah. Yana yin amfani da tsararmu ko kuma tsanantawa don ya hana mu yin wa’azi. Yana kuma neman ya rinjaye mu da ‘ilimin’ ƙarya na ʼyan ridda domin mu daina bin gaskiya.​—1 Tim. 6:​20, 21.

8. Wane darasi ne labarin wani mai suna Daniel ya koya maka?

8 Idan ba mu yi hankali ba, za mu iya barin gaskiya a hankali. Ka yi la’akari da misalin wani mai suna Daniel * da ke son wasan bidiyo sosai. Ya bayyana cewa: “Na soma wasan bidiyo sa’ad da nake ɗan shekara goma. Da farko, wasanni da nake bugawa masu kyau ne. Amma sannu a hankali, sai na soma buga wasannin yaƙi da na sihiri.” Daga baya, ya soma buga wasa har wajen sa’o’i 15 kowace rana. Ya ce: “A gaskiya, na san cewa irin wasannin da nake bugawa da kuma yawan sa’o’in da nake yi ina buga su yana nisanta ni daga Jehobah. Na soma tunani cewa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba su shafe ni ba.” Idan ba mu yi hankali ba, nishaɗi zai iya sanyaya dangantakarmu da Jehobah. Idan hakan ya faru, za mu iya yin hasarar abubuwa masu daraja da Jehobah ya ba mu.

YADDA ZA MU IYA DARAJA GASKIYA SOSAI

9. Kamar yadda 1 Timoti 1:​18, 19 suka nuna, da wane ne Bulus ya kamanta Timoti?

9 Karanta 1 Timoti 1:​18, 19. Manzo Bulus ya kamanta Timoti da soja, kuma ya ƙarfafa shi cewa ya ci gaba da yin “yaƙi” mai kyau. Wannan yaƙin ba na zahiri ba ne. A waɗanne hanyoyi ne Kiristoci suke kamar sojojin da ke yaƙi? A matsayinmu na sojojin Kristi, waɗanne halaye ne ya kamata mu kasance da su? Bari mu tattauna darussa biyar da za mu iya koya daga kwatancin Bulus. Darussan nan za su taimaka mana mu riƙa daraja gaskiya.

10. Mene ne zama masu ibada yake nufi, kuma me ya sa hakan ya dace?

10 Ka zama mai ibada. Sojan kirki yana da aminci. Yana iya ƙoƙarinsa don ya kāre wani da yake ƙauna ko kuma abin da ya daraja. Bulus ya ƙarfafa Timoti ya zama mai ibada, wato ya kasance da aminci ga Allah. (1 Tim. 4:7) Idan muna ƙaunar Allah kuma mun zama masu ibada, za mu riƙa daraja gaskiya.​—1 Tim. 4:​8-10; 6:6.

Bayan mun dawo daga aiki, muna bukatar mu yi ƙoƙari don mu halarci taro. Kuma Jehobah zai albarkace mu don yin hakan! (Ka duba sakin layi na 11)

11. Me ya sa muke bukatar mu horar da kanmu?

11 Ka koya wa kanka yin abu mai kyau. Dole ne soja ya riƙa horar da kansa domin ya kasance a shirye. Timoti ya yi tsayayya da Shaiɗan domin ya bi shawarar da manzo Bulus ya ba shi cewa ya guji mugayen sha’awoyi, ya zama mai ibada kuma ya riƙa cuɗanya da ʼyan’uwansa Kiristoci. (2 Tim. 2:22) Yin hakan na bukatar horar da kai sosai. Muna bukatar halin nan don mu magance sha’awoyin banza. (Rom. 7:​21-25) Muna kuma bukatar halin nan don mu ci gaba da tuɓe halinmu na dā, kuma mu saka sabon hali. (Afis. 4:​22, 24) Idan mun dawo gida a gajiye, muna bukatar mu tilasta wa kanmu don mu halarci taro.​—Ibran. 10:​24, 25.

12. Me zai sa mu ƙware a yin amfani da Littafi Mai Tsarki?

12 Idan soja yana so ya riƙa yin amfani da makamansa da kyau, dole ne ya riƙa koyar da kansa a kai a kai. Hakazalika, muna bukatar mu ƙware a yin amfani da Kalmar Allah. (2 Tim. 2:15) Za mu iya koyan wasu cikin dabarun nan a taronmu. Amma, idan muna so mu tabbatar wa mutane da cewa koyarwar Littafi Mai Tsarki tana da kyau, muna bukatar mu riƙa nazarinsa a kai a kai. Muna bukatar mu yi amfani da Kalmar Allah don mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Idan muna so mu yi haka, ba karanta Littafi Mai Tsarki kaɗai za mu riƙa yi ba. Muna bukatar mu riƙa bimbini a kan abin da muka karanta, mu yi bincike a littattafanmu domin mu fahimci abin da muka karanta kuma mu yi amfani da shi. (1 Tim. 4:​13-15) Idan mun yi hakan, za mu iya koya wa mutane Kalmar Allah. Yin hakan ba ya nufin karanta musu Littafi Mai Tsarki kawai ba. Ya kamata mu taimaka musu su fahimci ayoyin kuma su yi amfani da su. Idan muna nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai, za mu ƙware a yin amfani da Littafi Mai Tsarki don koyar da mutane.​—2 Tim. 3:​16, 17.

13. Kamar yadda Ibraniyawa 5:14 ta nuna, me ya wajaba mu yi don mu san bambanci tsakanin abu mai kyau da marar kyau?

13 Ka zama mai hikima. Wajibi ne soja ya san lokacin da bala’i yake tafe kuma ya kāre kansa. Wajibi ne mu ma mu san abubuwan da za su iya jawo mana la’ani kuma mu guje su. (K. Mag. 22:3; karanta Ibraniyawa 5:14.) Alal misali, ya kamata mu mai da hankali sa’ad da muke zaɓan nishaɗi da shaƙatawa. Ana yawan nuna lalata a fina-finai da kuma shirye-shiryen Talabijin. Abubuwan nan na ɓata wa Jehobah rai kuma za su jawo mana lahani. Saboda haka, ya kamata mu guji nishaɗin da zai raunana dangantakarmu da Jehobah.​—Afis. 5:​5, 6.

14. Ta yaya kasancewa da hikima ya taimaka wa Daniel?

14 Daniel da muka ambata ɗazu ya lura cewa bai dace ya riƙa wasan bidiyo na mugunta da kuma sihiri ba. Ya yi bincike a manhajar Watchtower Library don ya iya magance matsalar. Ta yaya hakan ya taimaka masa? Ya daina yin wasannin bidiyo da ba su dace ba. Daniel ya ce: “Maimakon in riƙa wasannin bidiyo, na soma cuɗanya da abokaina a ikilisiya.” A yanzu, Daniel majagaba ne da kuma dattijo.

15. Me ya sa labaran ƙarya suke da lahani?

15 Kamar Timoti, ya wajaba mu guji labaran ƙarya da ʼyan ridda suke yaɗawa. (1 Tim. 4:​1, 7; 2 Tim. 2:16) Alal misali, suna iya yaɗa labaran ƙarya game da ʼyan’uwanmu ko kuma su sa mu soma shakkar ƙungiyar Jehobah. Irin labaran nan suna iya raunana bangaskiyarmu. Kada mu yarda da ƙarairayin nan. Me ya sa? Domin mutanen da tunaninsu “ya zama banza, gaskiya kuma ta guje musu” ne suke yaɗa irin labaran nan. Suna so su jawo “gardama da muhawwara.” (1 Tim. 6:​4, 5) Suna so mu yarda da ƙarairayinsu kuma mu soma shakkar ʼyan’uwanmu.

16. Waɗanne abubuwan raba hankali ne za mu guje wa?

16 Ka guji abubuwan raba hankali. Da yake Timoti soja ne “mai aminci na Almasihu Yesu,” yana bukatar ya mai da hankali ga hidimarsa maimakon neman abin duniya. (2 Tim. 2:​3, 4) Kamar Timoti, kada mu bar abin duniya ya raba hankalinmu. “Son arziki” zai sa mu daina ƙaunar Jehobah da nuna godiya don Kalmar Allah kuma mu daina son yin wa’azi. (Mat. 13:22) Wajibi ne mu sauƙaƙa rayuwarmu kuma mu yi amfani da lokacinmu da kuzarinmu don mu ci gaba da sa al’amuran ‘mulkin’ Allah a kan gaba.​—Mat. 6:​22-25, 33.

17-18. Me ya kamata mu yi don mu kāre dangantakarmu da Jehobah?

17 Ka kasance a shirye domin ka ɗauki mataki nan da nan. Soja yana bukatar ya yi shirin abin da zai yi don ya kāre kansa. Idan za mu kāre abubuwan da Jehobah ya ba mu amana, muna bukatar mu ɗauki mataki nan da nan sa’ad da muka hangi haɗari. Mene ne zai taimaka mana mu yi hakan? Muna bukatar mu shirya abin da za mu yi tun kafin a kawo mana farmaki.

18 Alal misali, sa’ad da mutane suka halarci wani biki, ana yawan gaya wa mahalartan su nemi ƙofa da ke kusa da su kafin a soma bikin. Me ya sa? Domin su iya fita da wuri idan bukata ta gaggawa ta taso. Hakazalika, zai dace mu shirya abin da za mu yi idan muka ga hotunan lalata ko mugunta ko littattafan ’yan ridda a intane ko a fina-finai ko sa’ad da muke kallon talabijin. Idan muka yi shiri don abin da zai iya faruwa, za mu kāre dangantakarmu da Jehobah kuma mu kasance da tsabta a gabansa.​—Zab. 101:3; 1 Tim. 4:12.

19. Wace albarka ce za mu samu idan muka kāre abubuwa masu daraja da Jehobah ya ba mu?

19 Wajibi ne mu kāre abubuwa masu daraja da Jehobah ya ba mu, wato koyarwar Littafi Mai Tsarki da kuma gatan yin wa’azi. Idan muka yi hakan, zuciyarmu ba za ta riƙa damun mu ba, rayuwarmu za ta kasance da ma’ana kuma za mu yi farin ciki cewa muna koya wa mutane game da Jehobah. Ƙari ga haka, Jehobah zai taimaka mana mu kāre amanar da ya ba mu.​—1 Tim. 6:​12, 19.

WAƘA TA 127 Irin Mutumin da Ya Kamata In Zama

^ sakin layi na 5 Jehobah ya ba mu gatan sanin gaskiya da kuma koyar da ita ga mutane. Wannan talifin zai taimaka mana mu daraja gaskiyar nan.

^ sakin layi na 8 An canja sunan.