Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—A Myanmar

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—A Myanmar

“GIRBIN yana da yawa, amma masu aikin kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi mai gonar ya aiko da masu aiki su yi masa girbi.” (Luk. 10:2) Abin da Yesu ya faɗa shekaru 2,000 da suka shige yana faruwa a ƙasar Myanmar. Me ya sa? Domin masu shela wajen 4,200 ne kawai suke wa’azi a ƙasar Myanmar da ke da yawan jama’a miliyan hamsin da biyar.

Amma, Jehobah “mai gonar” ya motsa ’yan’uwa da yawa daga ƙasashe dabam-dabam su zo su riƙa wa’azi a wannan ƙasar da ke Kudu maso Gabashin Asiya. Me ya sa suka bar ƙasarsu? Ta yaya aka taimaka musu su ƙaura zuwa Myanmar? Wace albarka ce suka samu? Bari mu gani.

“KU ZO MUNA BUKATAR ƘARIN MAJAGABA!”

Shekarun da suka shige, wani ɗan’uwa mai suna Kazuhiro da ke hidimar majagaba a Jafan ya sume don yana da ciwon farfaɗiya. Sai aka kai shi asibiti kuma likita ya ce kada ya yi tuƙi har shekara biyu. Hakan ya sa Kazuhiro baƙin ciki sosai don yana ta tunani, ‘Ta yaya zan ci gaba da hidimar majagaba?’ Amma, ya yi addu’a Jehobah ya taimaka masa ya ci gaba da hidimarsa.

Kazuhiro and Mari

Kazuhiro ya ce: “Bayan wata ɗaya, abokina da ke hidima a Myanmar ya ji abin da ya faru da ni kuma ya kira ya ce: ‘A ƙasar Myanmar an fi yin amfani da bas, idan ka ƙauro nan, za ka ci gaba da hidimarka don ba ka bukatar yin tuƙi!’ Sai na tambayi likitana ko zan iya ƙaura zuwa Myanmar duk da cewa ina da ciwon farfaɗiya. Abin da likitan ya ce ya sa ni farin ciki sosai, ya ce: ‘Wani likitan ƙwaƙwalwa daga Myanmar zai ziyarci Jafan. Zan bayyana masa yanayinka don ya kula da kai idan ka yi ciwo a Myanmar.’ Jehobah ne ya amsa addu’ata.”

Nan da nan, Kazuhiro ya tura saƙon imel zuwa ofishin Shaidun Jehobah da ke Myanmar. Ya gaya musu cewa shi da matarsa suna so su yi hidimar majagaba a ƙasar. Bayan kwana biyar kawai, sai aka amsa cewa: “Ku zo, muna bukatar ƙarin majagaba!” Sai Kazuhiro da matarsa Mari suka sayar da motocinsu guda biyu, suka samo biza kuma suka tafi. Yanzu, shi da matarsa suna hidima da rukunin da ake yaren kurame a birnin Mandalay. Kazuhiro ya ce: “Abin da ya faru ya sa muka gaskata da abin da Allah ya faɗa a Zabura 37:5 cewa: Ka ‘Danƙa wa Yahweh hanyar rayuwarka, ka dogara gare shi, zai lura da kai.’”

JEHOBAH YA SA MU SAMI ZARAFI

Shaidun Jehobah a Myanmar sun sami gatar yin taron yanki na musamman a shekara ta 2014. ’Yan’uwa da yawa daga wasu ƙasashe sun halarci taron. Wata ’yar’uwa ’yar shekara 34 mai suna Monique daga Amirka tana cikin waɗanda suka halarci taron. Ta ce: “Bayan na dawo daga taron, na roƙi Jehobah ya sa in san matakin da zan ɗauka. Ƙari ga haka, na gaya wa iyayena maƙasudina kuma muka tsai da shawara cewa in ƙaura zuwa Myanmar. Amma hakan ya ɗauki lokaci kuma na yi addu’a sosai kafin in cim ma burina.” Monique ta faɗi dalilin da ya sa ta yi hakan.

Monique da Li

“Yesu ya ƙarfafa mabiyansa su ‘yi lissafi.’ Sai na tambayi kaina: ‘Zan iya ƙaura kuwa? Zan iya biyan bukatuna a ƙasar ba tare da neman kuɗi ruwa a jallo ba?’” Ta ce: “Nan da nan na ga cewa ba ni da isashen kuɗin ƙaura zuwa wata ƙasa.” To, me ya taimaka mata?​—Luk. 14:28.

Monique ta ce: “Wata rana shugaban aikinmu ta ce tana so ta gan ni. Na tsorata don na ɗauka za a sallame ni daga aiki. Amma, maimakon haka, ta gode mini don aikin da nake yi. Sai ta ce za a ba ni kyautar kuɗi, kuma wannan daidai kuɗin da nake bukata ne don in biya bukatuna!”

Tun watan Disamba 2014 ne Monique take hidima a Myanmar. Yaya take ji game da hidima a inda ake bukatar masu shela sosai? Ta ce: “Ina farin ciki sosai, ƙari ga haka ina nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane uku. Ɗaya cikinsu ’yar shekara 67 ce. Tana murmushi sosai a duk lokacin da muke gaisawa kuma takan rungume ni. Ta yi farin ciki sosai sa’ad da ta koyi cewa Jehobah ne sunan Allah. Ta ce: ‘Ban taɓa sani cewa Jehobah ne sunan Allah ba. Ke matashiya ce, amma kin koya min abu mafi muhimmanci a rayuwata.’ Abin da ta faɗa ya sa ni farin ciki matuƙa. Irin wannan labarin yana sa ni jin daɗin yin hidima a inda ake bukatar masu shela sosai.” Ba da daɗewa ba, Monique ta sami gatar halartan Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki.

Wani abu kuma da ya ƙarfafa wasu ’yan’uwa su ƙaura zuwa Myanmar shi ne labarin da aka wallafa game da wannan ƙasar a littafin nan 2013 Yearbook of Jehovah’s Witnesses. Wata ’yar’uwa da ta ba shekara 30 baya mai suna Li tana zama a Kudu maso Gabashin Asiya. Tana aiki na cikakken lokaci, amma labarin da ke cikin littafin ya motsa ta ta soma tunanin yin hidima a Myanmar. Ta ce: “Sa’ad da na halarci taron yanki na musamman a Yangon a 2014, na haɗu da ma’auratan da suke hidima a yankin da ake yaren Caina a Myanmar. Da yake na iya yaren, sai na ƙaura zuwa Myanmar don na taimaka wa rukunin Caina. Na je na sami Monique kuma muka ƙaura zuwa birnin Mandalay. Jehobah ya taimaka mana mu sami aikin koyarwa a wata makaranta. Ƙari ga haka, mun sami gida kusa da wurin aikinmu. Duk da cewa ana zafi sosai a ƙasar da kuma wasu matsaloli, ina jin daɗin hidimata. Mutanen Myanmar ba sa yawan biɗan abin duniya kuma suna da fara’a. Ƙari ga haka, suna son su saurari wa’azinmu. Ina farin cikin ganin yadda Jehobah yake sa mutane su bauta masa. Na gaskata cewa nufin Jehobah ne in riƙa hidima a Mandalay.”

JEHOBAH YANA AMSA ADDU’O’I

Yin addu’a ya taimaka wa masu hidima a inda ake bukatar masu shela sosai. Alal misali, Jumpei ɗan shekara 37 da matarsa Nao ’yar shekara 35 suna hidima a ikilisiyar da ake yaren kurame a Jafan. Me ya sa suka ƙaura zuwa Myanmar? Jumpei ya ce: “Ni da matata muna son hidima a wata ƙasa. Wani ɗan’uwa da yake tare da mu a ikilisiyar da ake yaren kurame a Jafan ya ƙaura zuwa Myanmar. Saboda haka, ko da ba mu tara kuɗi da yawa ba, mu ma mun ƙaura a watan Mayu 2010. ’Yan’uwa da ke Myanmar sun marabce mu sosai!” Yaya yake ji game da hidima a yankin da ake yaren kurame a Myanmar? Ya ce: “Mutane suna son jin wa’azi sosai. Ƙari ga haka, kurame suna farin ciki sosai sa’ad da muka nuna musu bidiyoyi a yaren kurame. Mun yi farin ciki cewa mun tsai da shawarar ƙauro nan don mu bauta wa Jehobah!”

Nao da Jumpei

Ta yaya Jumpei da matarsa suka biya bukatunsu? Sun ce: “Bayan shekara uku, mun kusa kashe duk kuɗin da muka tara kuma ba mu da kuɗin da za mu biya haya a shekara ta gaba. Ni da matata mun yi addu’a sosai. Mun yi mamaki sa’ad da muka samu wasiƙa daga ofishinmu cewa mu soma hidimar majagaba na musamman na gajeren lokaci! Mun dogara da Jehobah, kuma muka ga cewa bai yasar da mu ba. Yana kula da mu sosai.” Kwanakin baya, Jumpei da matarsa Nao sun halarci Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki.

JEHOBAH YA MOTSA ’YAN’UWA DA YAWA

Me ya sa Simone ɗan shekara 43 daga Italiya, da matarsa Anna ’yar shekara 37 daga New Zealand, suka ƙaura zuwa Myanmar? Anna ta ce: “Labarin Myanmar da ke littafin 2013 Yearbook of Jehovah’s Witnesses ne ya sa muka yi hakan!” Simone ya daɗa cewa: “Gata ce babba yin hidima a Myanmar. Mutane a nan ba sa yawan biɗan abin duniya kuma hakan yana taimaka mini in saka ƙwazo a hidimata ga Jehobah. Ƙari ga haka, muna farin ciki sosai domin Jehobah yana kula da mu da yake muna hidima a inda ake bukatar masu shela sosai.” (Zab. 121:5) Anna ta ce: “Ban taɓa yin farin ciki haka ba. Mun sauƙaƙa salon rayuwarmu kuma da yake ni da mijina muna tare yawanci lokaci, hakan ya sa mun kusaci juna sosai. Kuma mun sami sabbin abokai. A ƙasar nan mutane ba sa nuna wa Shaidun Jehobah bambanci, kuma suna son saurarar wa’azi sosai!” Ta yaya suke hakan?

Simone da Anna

Anna ta ce: “Akwai ranar da na yi wa wata ɗalibar jami’a wa’azi a kasuwa kuma ta yarda in dawo mu ci gaba da tattaunawa. Da na koma, ta gayyato ƙawarta don in yi nazari da su. Da na sake komawa ziyarar, ta gayyato wasu ƙawayenta. Daga baya ta sake gayyato wasu. Yanzu, ina yin nazarin da su biyar.” Simone ya ce: “Mutanen masu fara’a ne kuma suna yin tambayoyi sosai. Ban da haka, suna son saurarar wa’azi, amma ba mu da lokacin yin nazari da dukansu.”

Sachio da Mizuho

Waɗanne matakai ne mutum yake bukatar ya ɗauka kafin ya tsai da shawarar ƙaura zuwa Myanmar? Wata ’yar’uwa daga Jafan mai suna Mizuho ta ce: “Ni da mijina Sachio, mun daɗe muna da burin yin hidima a ƙasar da ake bukatar masu shela sosai. Amma ina za mu je? Labari mai ƙayatarwa da muka karanta a littafin 2013 Yearbook of Jehovah’s Witnesses game da ƙasar Myanmar ya motsa mu sosai, sai muka soma tunanin ko za mu iya ƙaura zuwa Myanmar.” Mijinta Sachio ya ce: “Mun yanke shawarar ziyartar Yangon, babban birnin Myanmar, don mu ga yadda ƙasar take. Wannan ziyarar da muka kai ya taimaka mana mu ga cewa muna bukatar mu ƙaura zuwa Myanmar.”

ZA KA IYA ƘAURA NE?

Jane da Danica da Rodney da kuma Jordan

Tun shekara ta 2010, wani ɗan’uwa daga Ostareliya mai suna Rodney da matarsa Jane ’yar shekara 52, da kuma yaransu Jordan da Danica, suka soma yin hidima a inda ake bukatar masu shela a Myanmar. Rodney ya ce: “Yadda mutane a ƙasar nan suke son su koya game da Allah yana burge mu sosai. Kuma ina ba kowace iyali shawarar yin hidima a ƙasa kamar Myanmar.” Me ya sa? Rodney ya ce: “Yin hidima a nan ya taimaka mana mu kusaci juna sosai a iyalinmu! A yau, matasa da yawa sun fi mai da hankali ga wayoyinsu da motocinsu da ayyukansu da dai sauransu. Amma yaranmu sun mai da hankali ga koyan sabon yare don su yi wa mutane wa’azi. Suna koyan yadda za su yi nazari da mutanen da ba su san abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba, da kuma yadda za su yi kalami a taro. Ban da haka ma, sun duƙufa yin abubuwan da zai inganta hidimarsu ga Jehobah.”

Oliver da Anna

Wani ɗan’uwa ɗan shekara 37 daga ƙasar Amirka mai suna Oliver, ya faɗi dalilin da ya sa yake son wasu ma su yi irin wannan hidimar, ya ce: “Yi wa Jehobah hidima a wurin da ban saba ba, ya sa na amfana sosai. Barin gidanmu ya taimaka mini in dogara sosai ga Jehobah ko da mene ne zan fuskanta. Ƙari ga haka, yin hidima da ’yan’uwan da ban taɓa haɗuwa da su ba, ya taimaka mini in ga cewa babu abin da ya fi Mulkin Allah muhimmanci.” A yau, Oliver da kuma matarsa Anna sun ci gaba da hidima a yankin da ake yaren Caina.

Trazel

Tun shekara ta 2004, wata ’yar’uwa ’yar shekara 52 daga Ostareliya mai suna Trazel ta soma hidima a Myanmar. Ta ce: “Ina ƙarfafa ’yan’uwan da za su iya ƙaura, su je inda ake bukatar masu shela sosai. Don na ga cewa idan mutum yana da burin yi wa Jehobah hidima, zai albarkace shi sosai. Ban taɓa yin tunanin cewa zan yi irin wannan rayuwar ba, amma wannan ita ce rayuwar da take sa mutum farin ciki da kuma samun gamsuwa.”

Muna fata cewa waɗannan kalami masu ban ƙarfafa na ’yan’uwan da ke yin hidima a inda ake bukatar masu shela a Myanmar, ya motsa ka ka yi tunanin taimaka wa mutane a yankunan da babu masu wa’azi. Babu shakka, masu hidima a inda ake bukatar masu shela suna kira cewa: “Don Allah ku zo Myanmar ku taimake mu!”