Jehobah ‘Yana Kula da Kai’
ME YA sa kake da tabbaci cewa Jehobah yana kula da kai da gaske? Dalili na farko shi ne cewa Littafi Mai Tsarki ya ambaci hakan. Littafin 1 Bitrus 5:7, ta ce: ‘Ka zuba dukan alhininka a bisansa, domin yana kula da kai.’ Waɗanne abubuwa ne suka nuna cewa Jehobah yana ƙaunarka?
JEHOBAH YANA BIYAN BUKATUN ’YAN ADAM
Jehobah yana da halaye masu kyau, wato irin halayen da kake so abokanka na kud da kud su kasance da su. Abokai da suke bi da juna cikin alheri da karimci sukan so juna sosai. Hakazalika, Jehobah yana nuna alheri da karimci ga ’yan Adam kullum. Alal misali: “Ya kan sa ranarsa ta fito ma miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu-adalci da marasa-adalci.” (Mat. 5:45) Ta yaya muke amfana daga rana da ruwan sama? Ta wajen tanadin waɗannan abubuwan, Jehobah ‘yana cika zukatanmu da abinci da farin ciki.’ (A. M. 14:17) Hakika, Jehobah yana sa ƙasa ta ba da amfani don mu sami isashen abinci. Ta hakan ne muke samun abinci, kuma mukan yi farin ciki ƙwarai idan muka ci abinci mai daɗi.
To me ya sa mutane da yawa suke kwana da yunwa? Don shugabanni ’yan Adam sukan mai da hankali ga neman mulki da kuma arziki maimakon su inganta rayuwar mutane. Jehobah zai magance wannan matsalar da haɗama ta jawo sa’ad da ya sauya gwamnatocin ’yan Adam da Mulkin sama da Ɗansa yake sarauta. A lokacin ba wanda zai ji yunwa. A yanzu haka, Jehobah yana kula da amintattun bayinsa. (Zab. 37:25) Hakan ya nuna cewa Jehobah yana ƙaunarmu, ko ba haka ba?
JEHOBAH YANA SHIRYE YA SAURARE MU A KOWANE LOKACI
Abokin kirki ba ya jinkirin ba da lokacinsa don kasancewa tare da kai. Zai iya kasancewa tare da kai don ku tattauna batutuwan da kuke so. Abokin kirki yana sauraro sa’ad da ka gaya masa matsalolinka da damuwarka. Shin Jehobah yana sauraronmu kamar abokin kirki kuwa? Hakika. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu cewa mu “lizima cikin addu’a” kuma mu “yi addu’a ba fasawa.”—Rom. 12:12; 1 Tas. 5:17.
Shin Jehobah zai gaji da sauraronmu ne idan muka yi sa’o’i da yawa muna addu’a? Za mu sami amsar idan muka yi la’akari da addu’ar da Yesu ya yi kafin ya zaɓi manzanninsa. Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya “kwana yana addu’a ga Allah.” (Luk. 6:12) Wataƙila sa’ad da Yesu yake addu’a, ya ambaci sunaye da halaye da kuma kasawar almajiransa da yawa kuma ya roƙi Ubansa ya taimake shi sa’ad da yake zaɓan su. Sa’ad da gari ya waye, Yesu ya san cewa ya zaɓi almajirai da suka fi cancanta su zama manzanninsa. Jehobah “mai jin addu’a” ne kuma ba ya jinkirin sauraron dukan addu’o’in da mutane suke yi daga zuciyarsu. (Zab. 65:2) Ko da mutumin ya yi sa’o’i da yawa yana addu’a a kan wani abu da yake damunsa sosai, Jehobah ba zai gaji da sauraronsa ba.
ALLAH YANA SHIRYE YA GAFARTA MANA ZUNUBANMU
A wani lokaci, yin gafara yakan kasance wa abokan kirki da wuya. A wasu lokatai, abokai sukan rabu don sun ƙi gafarta wa juna. Amma ba haka Jehobah yake ba. Littafi Mai Tsarki ya ce duk wanda ya roƙi gafara daga wurinsa, Jehobah zai ‘gafarta’ masa “a yalwace.” (Isha. 55:6, 7) Me ya sa Allah yake saurin gafartawa?
Dalilin shi ne babu wanda ya kai Allah ƙaunar ’yan Adam. Yana ƙaunar ’yan Adam sosai har ma ya ba da Ɗansa Yesu don ya cece su daga zunubi da kuma mugun sakamako da Yoh. 3:16) Wannan hadayar da Allah ya tanadar ta cim ma abubuwa da yawa. Ta hadayar Kristi, Allah yana gafarta wa waɗanda yake ƙauna. Manzo Yohanna ya ce: “Idan mun faɗi zunubanmu, shi mai-alkawari ne, mai-adalci kuma, da za shi gafarta mamu zunubanmu.” (1 Yoh. 1:9) Da yake Allah mai gafartawa ne, mutane za su iya zama abokansa na kud da kud kuma sanin hakan yana ratsa zuciya.
hakan ya jawo. (YANA TAIMAKONKA A LOKACIN DA YA DACE
Abokin kirki yana taimakon wasu sa’ad da suke cikin mawuyacin hali. Jehobah kuma fa? Kalmarsa ta ce: Ko da bawan Allah “ya fāɗi, ba za ya yi warwas ba, gama Ubangiji yana riƙe da shi a hannunsa.” (Zab. 37:24) Jehobah yana taimakon bayinsa a hanyoyi da yawa. Ka yi la’akari da wani misali daga tsibirin St. Croix.
Wata matashiya ta fuskanci matsi daga abokan ajinta don ta ƙi sara wa tuta saboda imaninta. Sai ta yi addu’a kuma ta ɗauki mataki a kan batun. Ta ba da rahoto a gaban ’yan ajin a kan batun sara wa tuta. Ta yi amfani da Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki kuma ta bayyana yadda labarin Shadrach da Meshach da kuma Abednego ya sa ta ƙi sara wa tuta. Ta ce, “Jehobah ya kāre waɗannan Ibraniyawa uku don sun ƙi su bauta wa gumaka.” Bayan haka, sai ta nuna wa waɗanda suke wurin littattafan. Ɗalibai guda sha ɗaya sun karɓi kofi ɗaɗɗaya na littafin. Ta yi farin ciki sosai sa’ad da ta ga cewa Jehobah ne ya ba ta ƙarfin zuciya da basira don ta yi magana game da imaninta.
Idan har kana shakka cewa Jehobah yana kula da kai, ka yi tunani a kan ayoyin Littafi Mai Tsarki kamar Zabura 34:17-19; 55:22; da kuma 145:18, 19. Ka tambayi ’yan’uwa da suka daɗe suna bauta wa Jehobah yadda ya kula da su. Ƙari ga haka, sa’ad da kake bukatar taimako daga wurin Allah, ka yi addu’a game da batun. Za ka shaida cewa Jehobah yana ‘kula da kai.’