Hali Mai Kyau Ya Fi Lu’ulu’u Tamani
Tun da daɗewa, mutane suna ɗaukan lu’ulu’u da tamani sosai. Sayan lu’ulu’u yana bukatar kuɗi mai yawa. Amma, shin a gaban Allah da akwai abubuwa da suke da tamani fiye da lu’ulu’u ko kuma wasu kayan ado?
Haykanush, mai shela da ba ta yi baftisma ba da ke zama a ƙasar Armeniya ta samu wani fasfo kusa da gidansu. A cikin fasfo ɗin da akwai katin ATM da kuma kuɗi mai yawan gaske. Sai ta gaya wa mijinta wanda shi ma bai yi baftisma ba.
A wannan lokacin, ma’auratan suna bukatar kuɗi sosai kuma ana bin su bashi. Duk da haka, sun yanke shawara su kai kuɗin wa mutumin da sunansa yake cikin fasfo ɗin. Mutumin da kuma iyalinsu sun yi mamaki sosai. Haykanush da mijinta sun bayyana cewa sun mayar da kuɗin domin abin da suke koya daga cikin Littafi Mai Tsarki. Suna ganin ya kamata su zama masu faɗin gaskiya. Ƙari ga haka, sun yi amfani da wannan zarafin don su yi musu magana game da Shaidun Jehobah kuma suka ba iyalin wasu littattafai.
Iyalin suna so su ba Haykanush ladar kuɗi don abin da ta yi, amma ta ƙi. Washegari, matar ta ziyarci Haykanush da mijinta a gidansu, kuma don su nuna godiyarsu suka nace wa Haykanush ta karɓi zoben lu’ulu’u.
Kamar wannan iyalin, mutane da yawa za su yi mamaki don abin da Haykanush da mijinta suka yi. Amma, shin Jehobah zai yi mamaki ne? Ta yaya zai ɗauki yadda suka faɗi gaskiya? Shin yadda suka faɗi gaskiya ya dace kuwa?
HALAYEN DA SUKA FI ABUBUWAN MALLAKA TAMANI
Amsoshin waɗannan tambayoyin ba su da wuya. Domin bayin Allah sun gaskata cewa halaye masu kyau sun fi lu’ulu’u da zinariya da wasu abubuwan mallaka tamani a gaban Allah. Hakika, abin da Jehobah yake ɗauka da tamani ya bambanta da abin da yawancin ’yan Adam suke ɗauka da tamani. (Isha. 55:8, 9) Kuma bayinsa suna ganin cewa ƙoƙarce-ƙoƙarcen da suke yi don su yi koyi da halaye masu kyau ya fi daraja.
Mun ga hakan daga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da fahimi da kuma hikima. Misalai 3:13-15 sun ce: “Mai-farinciki ne mutum wanda yake samun hikima, da mutum kuma wanda yake da fahimi. Gama cinikinta ya fi cinikin azurfa kyau, ribarta kuma ta fi sahihiyar zinariya. Ta fi lu’u lu’ai tamani: Cikin iyakar abin da za ka yi marmarinsu, babu abin da za a gama shi da ita.” Babu shakka, a gaban Jehobah waɗannan halayen suna da tamani sosai fiye da abin duniya.
Kwatanta gaskiya fa?
Hakika, Jehobah mai gaskiya ne domin “ba ya iya yin ƙarya.” (Tit. 1:2) Kuma ya hure manzo Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa ga Kiristoci Ibraniyawa a ƙarni na farko, ya ce: “Ku yi mana addu’a, gama mun tabbata muna da lamiri mai kyau, muna kuwa so mu tafiyar da al’amuranmu da halin kirki.”—Ibran. 13:18, Littafi Mai Tsarki.
Yesu Kristi ya kafa misali mai kyau a faɗin gaskiya. Alal misali, sa’ad da Kayafa Babban Firist ya ce: “Na gama ka da Allah mai-rai, ka faɗa mana, ko kai Kristi ne Ɗan Allah.” Yesu ya faɗi gaskiya cewa shi Almasihu ne ko da yin hakan zai sa ’yan Majalisa su yi masa sharri cewa shi mai saɓo ne kuma ya sa a kashe shi.—Mat. 26:63-67.
Mu kuma fa a yau? Shin za mu faɗi gaskiya a yanayin da yin ƙarya ko ƙin faɗin gaskiya zai sa mu sami abin duniya?
ABIN DA YA SA KWATANTA GASKIYA BA SHI DA SAUƘI
Hakika, yana da wuya mutum ya zama mai gaskiya a waɗannan kwanaki na ƙarshe da mutane da yawa sun zama “masu-son kansu, masu-son kuɗi.” (2 Tim. 3:2) Rashin kuɗi da rashin aiki za su iya sa mutane su zama masu rashin gaskiya. Mutane da yawa suna ganin cewa ya dace su yi sata ko su cuci mutane ko kuma su yi wasu ayyuka na rashin gaskiya. Wannan ra’ayin ya zama gama gari, kuma mutane da yawa suna ganin cewa ba zai yiwu ba mutum ya kasance mai gaskiya. Irin wannan ra’ayin da kuma “kwaɗayin ƙazamar riba” sun sa wasu Kiristoci sun yi abubuwan da ba su dace ba kuma hakan ya sa sun ɓata sunansu a cikin ikilisiya.—1 Tim. 3:8; Tit. 1:7.
Amma, yawancin Kiristoci suna yin koyi da Yesu. Sun fahimci cewa kasancewa da halaye masu kyau ya fi kowace dukiya ko riba daraja. Saboda haka, matasa Kiristoci ba sa satan amsa don su ci jarabawa a makaranta. (Mis. 20:23) Hakika, ba a kowane lokaci ba ne za mu sami lada domin zama masu gaskiya kamar Haykanush ba. Duk da haka, kasancewa mai gaskiya yana da muhimmanci a gaban Allah kuma yana sa mu kasance da lamiri mai kyau, hakan abu ne mai tamani sosai.
Misalin Gagik ya nuna cewa mutum zai iya kasancewa mai gaskiya. Ya ce: “Kafin na soma bauta wa Jehobah, na yi aiki a wani babban kamfani kuma mai kamfanin ba ya biyan dukan haraji da ya kamata kamfaninsa ya biya ta wajen faɗan cewa ba sa samun riba sosai a kamfanin. Da yake ni ne babban darektan kamfanin, an bukace ni in yi wata ‘yarjejeniya’ da masu karɓan haraji ta wajen ba su cin hanci don kada kamfanin ya biya harajin da ya wajaba. Saboda haka, ba na kwatanta gaskiya a lokacin. Amma, sa’ad da na zama Mashaidin Jehobah sai na daina yin rashin gaskiya duk cewa ana biya na kuɗi mai tsoka. Maimakon haka, na buɗe kamfanina. Ƙari ga haka, na yi rajistan kamfanin a ranar da na buɗe kuma na biya dukan harajin da ya kamata na biya.”—2 Kor. 8:21.
Gagik ya ce: “Rabin albashi na na dā shi ne nake samu yanzu, kuma saboda haka, biya bukatun iyalina bai da sauƙi. Amma, na fi yin farin ciki a yanzu. Ina da lamiri mai kyau a gaban Jehobah. Na kafa wa ’ya’yana maza biyu misali mai kyau, kuma na samu gata a cikin ikilisiya. Masu binciken haraji da waɗanda nake kasuwanci da su sun san cewa ni mai gaskiya ne yanzu.”
JEHOBAH YANA TAIMAKA MANA
Jehobah yana ƙaunar waɗanda suke ɗaukaka shi ta wajen yin koyi da halayensa masu kyau, kamar kasancewa mai gaskiya. (Tit. 2:10) Ta wajen ja-gorar ruhu mai tsarki, Sarki Dauda ya ce: “Dā yaro nake, yanzu kuwa na tsufa: Amma ban taɓa gani an yar da mai-adalci ba, ko kuwa zuriyarsa suna roƙon abincinsu” ba.—Zab. 37:25.
Misalin Ruth ya nuna cewa hakan gaskiya ne. Ta manne wa mahaifiyar mijinta, ba ta yi watsi da ita a lokacin da ta tsufa ba. Ruth ta ƙaura zuwa ƙasar Isra’ila don ta bauta wa Allah na gaskiya. (Ruth 1:16, 17) Ta kasance mai gaskiya da ƙwazo kuma ta bi Doka yayin da take kāla a cikin gona. Kamar Ruth da Naomi, Dauda ma ya shaida cewa Jehobah ba ya watsi da bayinsa a lokacin da suke fuskantar mawuyacin yanayi. (Ruth 2:2-18) Hakika, ba abin biyan bukata ba ne kawai Jehobah ya tanadar wa Ruth. Ya ba ta gatan kasancewa cikin zuriyar Sarki Dauda da kuma Almasihu!—Ruth 4:13-17; Mat. 1:5, 16.
Wasu bayin Jehobah a yau za su iya samun kansu a wani yanayi na rashin isashen abinci ko sutura da makamantansu. Suna yin ƙoƙari su yi aiki da ƙwazo maimakon su nemi mafita ta yin rashin gaskiya. Ta hakan, suna ɗaukan halaye masu kyau kamar faɗin Mis. 12:24; Afis. 4:28.
gaskiya da muhimmanci fiye da duk wani abin duniya.—Kamar Ruth da Littafi Mai Tsarki ya ambata, Kiristoci a faɗin duniya suna da bangaskiya cewa Jehobah yana da ikon taimakon bayinsa. Sun amince da Wanda ya yi wannan alkawarin da aka rubuta a cikin Kalmarsa: “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.” (Ibran. 13:5, LMT) Jehobah ya sha nuna cewa zai iya taimaka wa matalauta da suke gaskiya a kowane lokaci, kuma zai ci gaba da taimaka musu. Ya cika alkawarin da ya yi cewa zai biya mana bukatunmu.—Mat. 6:33.
Hakika, ’yan Adam suna daraja lu’ulu’u da kuma wasu abubuwa masu tamani sosai. Amma muna da tabbaci cewa nuna halaye masu kyau da kuma kwatanta gaskiya suna da muhimmanci a gaban Ubanmu na sama fiye da lu’ulu’ai!