Amfanin Yin Gaisuwa
“BARKA DAI! Yaya kake?”
Babu shakka, ka taɓa yin irin wannan gaisuwar. Wataƙila kana shan hannu da mutane ko kuma kana rusuna musu. Yadda ake gaisuwa da kuma furucin da ake yi a ƙasashe dabam-dabam sun bambanta, amma dukansu gaisuwa ne. Idan mutum ba ya gaisuwa ko kuma ba ya amsa gaisuwa, za a riƙa ganin ba ya daraja mutane.
Amma ba dukan mutane ba ne suke son yin gaisuwa ba. Wasu ba sa gaisuwa don suna jin kunya ko kuma suna ganin ba su da daraja. Wasu ba sa gai da mutane saboda launin fatarsu ko al’adarsu ko matsayinsu, ko shekarunsu ko kuma jinsinsu. Amma, gaisuwa takan ƙarfafa mutane sosai.
Ka tambayi kanka: ‘Me ya sa gaisuwa take da muhimmanci? Wane darasi ne zan iya koya daga Kalmar Allah game da yin gaisuwa?’
KU RIƘA GAI DA “KOWA”
Sa’ad da Karniliyus wanda ba Bayahude ba ya zama Kirista, manzo Bitrus ya marabce shi sosai, kuma ya ce: “Allah ba ya nuna bambanci.” (A. M. 10:34) Bayan haka, Bitrus ya ce Allah yana so “kowa ya zo ya tuba.” (2 Bit. 3:9) Da farko muna iya ganin cewa wannan ayar tana nuni ne ga mutumin da yake nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma Bitrus ya gargaɗi Kiristoci ma cewa: “Ku ba da girma ga kowa, ku ƙaunaci ’yan’uwa masu bin Yesu.” (1 Bit. 2:17) Saboda haka, ya dace mu riƙa gai da mutane duk da launin fatarsu ko al’adarsu ko kuma ƙasarsu. Idan muka yi hakan, za mu nuna cewa muna daraja su kuma muna ƙaunar su.
Manzo Bulus ya gargaɗi waɗanda suke cikin ikilisiya cewa: “Ku karɓi juna hannu biyu-biyu kamar yadda Almasihu ya karɓe ku hannu biyu-biyu.” (Rom. 15:7) Bulus ya fi ambata ’yan’uwa da suka ƙarfafa shi. A yau, ’yan’uwa suna bukatar a ƙarfafa su sosai don Shaiɗan yana kai wa mutanen Allah hari.—Kol. 4:11; R. Yar. 12:12, 17.
Misalan da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa gaisuwa na sa mutane su saki jiki da dai sauransu.
AMFANIN GAI DA MUTANE
Sa’ad da lokaci ya yi da Maryamu za ta yi juna biyu, Jehobah ya tura wani mala’ika wurin ta. Mala’ikan ya soma da cewa: “A gaishe ki! Ubangiji yana tare da ke, ke da kike mai samun alheri!” Da Maryamu ta ji gaisuwar, ta “damu ƙwarai” don ba ta san abin da ya sa mala’ika yake mata magana ba. Sa’ad da mala’ikan ya ga hakan, sai ya ce mata: “Kada ki ji tsoro, Maryamu. Gama kin sami alheri a gaban Allah.” Ya bayyana mata cewa nufin Allah ne ta haifi Almasihu. Maimakon Maryamu ta ci gaba da damuwa, ta gaya wa mala’ikan cewa: “To, ni baiwar Allah ce, bari ya zama mini kamar yadda ka faɗa.”—Luk. 1:26-38.
Ko da mala’ikan yana ganin cewa gata ne Jehobah ya tura shi ya je ya idar da saƙo, ba ya ganin ba zai iya yin magana da ɗan Adam ajizi ba. Amma ya soma da gaisuwa. Shin akwai darasin da za mu koya daga wannan misalin? Ya kamata mu kasance a shirye mu riƙa gai da mutane da kuma ƙarfafa su. Ta wurin yin gajeriyar gaisuwa, muna sa mutane su kasance da tabbaci cewa bayin Jehobah suna ƙaunar su.
Bulus ya san ikilisiyoyi da yawa a Asiya Ƙarama da kuma Turai. Ya aika gaisuwa da yawa a wasiƙu da ya rubuta musu, kuma za mu iya ganin gaisuwar a littafin Romawa sura 16. Bulus ya tura wa ’yan’uwa da yawa gaisuwa. Ya ambata “’yar’uwarmu” Fibi, kuma ya gaya wa ’yan’uwan su “karɓe ta cikin sunan Ubangiji yadda ya dace a karɓi tsarkaka. Ku kuma ba ta kowane irin taimakon da take bukata.” Bulus ya gai da Biriskila da Akila, ya ce, “Ba ni kaɗai ne mai godiya a gare su ba, har ma da dukan jama’ar masu bi ta waɗanda ba Yahudawa ba.” Ya gai da wasu da ba a san su ba a yau, kamar su “Afanitus” da kuma “Tirayifina da Tirayifusa, matan nan masu fama cikin aikin Ubangiji.” Hakika, Bulus ya gai da ’yan’uwa sosai.—Rom. 16:1-16.
Babu shakka, waɗannan ’yan’uwan za su yi farin ciki sosai cewa Bulus ya tuna da su. Hakan zai sa su riƙa ƙaunar Bulus da kuma juna sosai. Ƙari ga haka, jin waɗannan gaisuwa ya ƙarfafa Kiristoci kuma ya sa su riƙe amincinsu. Hakika, yin gaisuwa da ke nuna cewa mun damu da ’yan’uwanmu da kuma yaba musu za su sa dangantakarmu da su ya yi danƙo kuma ya sa bayin Allah su kasance da haɗin kai.
Sa’ad da Bulus ya isa tashar jiragen ruwa na Futiyoli kuma ya kama hanyar zuwa Roma, ’yan’uwan sun zo don su marabce shi. Da Bulus ya gan su daga nesa, sai ya “yi godiya ga Allah, ya kuma ƙara samun ƙarfin gwiwa.” (A. M. 28:13-15) A wasu lokuta, muna iya yin murmushi kawai ko kuma mu ɗaga wa mutum hannu. Har wannan ma yana ƙarfafa mutum, wataƙila wani da ke baƙin ciki.
YA TAIMAKA MUSU SU SAURARE SHI
Almajiri Yaƙub yana bukatar ya yi ma wasu Kiristoci gargaɗi sosai don suna abokantaka da mutanen duniya. (Yaƙ. 4:4) Amma ka lura da yadda Yaƙub ya soma wasiƙarsa:
“Yakub bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga zuriya goma sha biyun nan da suke a warwatse ko’ina cikin duniya. Gaisuwa mai yawa.” (Yaƙ. 1:1) Babu shakka, ya yi ma waɗanda suka karanta wasiƙarsa sauƙi su bi shawararsa don sun ga cewa dukansu suna da daraja a gaban Allah. Hakika, yin gaisuwa da dukan zuciyarmu zai sa wasu su kasance a shirye su saurare mu sa’ad da muke musu gargaɗi.
Ya kamata mu yi gaisuwa da ta nuna cewa mun damu da ’yan’uwanmu kuma muna ƙaunar su. Ya dace mu yi hakan ko da mutane ba su amsa gaisuwar ba. (Mat. 22:39) Alal misali, akwai lokacin da wata ’yar’uwa a ƙasar Ireland ta zo taro gab da lokacin da ake son a soma taro. Yayin da take shigowa, wani ɗan’uwa ya juya ya yi mata murmushi kuma ya ce: “Sannu da zuwa, ina murnar ganin ki.” ’Yar’uwar ta yi zamanta kawai, ba ta ce kome ba.
Bayan ’yan makonni, ’yar’uwar ta je ta sami ɗan’uwan kuma ta ce ta ɗan daɗe tana fama da wasu matsaloli a gida. Ta ƙara cewa: “Ina baƙin ciki sosai a lokacin da na zo taro a ranar, sauran kaɗan da ban zo ba. Ba zan iya tuna da abin da aka tattauna a taron ba, amma na tuna da gaisuwarka kuma ta kwantar mini da hankali. Na gode.”
Ɗan’uwan bai san cewa ’yar gaisuwar da ya yi ta taimaka wa ’yar’uwar ba. Ya ce: “Sa’ad da ta gaya mini cewa gaisuwar ta taimaka mata sosai, na yi farin ciki cewa na gaishe ta. Hakan ya sa ni murna sosai.”
Sulemanu ya ce: “Ka bayar hannu sake, gama za ka same shi bayan kwanaki da yawa.” (M. Wa. 11:1) Idan mun san cewa yin gaisuwa yana da muhimmanci sosai, musamman ga ’yan’uwanmu, za mu ƙarfafa kanmu da kuma wasu. Saboda haka, mu riƙa yin gaisuwa don yin hakan yana da amfani sosai.