“Bari Ku Zama Masu Haske” Don Ku Daukaka Jehobah
“Bari ku zama masu haske ga mutane, domin . . . su ɗaukaka Ubanku.”—MAT. 5:16.
1. Mene ne ya sa muke farin ciki sosai?
MUNA farin ciki sosai cewa mutanen Jehobah suna ƙara yawa! A shekarar da ta shige, mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane fiye da 10,000,000. Hakan ya nuna cewa bayin Allah sun zama masu haske ga mutane! Kuma mutane da yawa da suke son saƙonmu sun halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu. Sun koyi cewa Jehobah ya tura Ɗansa ya mutu a madadinmu don yana ƙaunar mu.—1 Yoh. 4:9.
2, 3. (a) Mene ne ba ya hana mu zama masu haske? (b) A wannan talifin, mene ne za mu tattauna game da furucin Yesu da ke Matiyu 5:14-16?
2 A faɗin duniya, mutanen Jehobah suna yin yaruka dabam-dabam. Amma, hakan bai hana mu kasancewa da haɗin kai a bautarmu ga Ubanmu, Jehobah ba. (R. Yar. 7:9) Ko da wane yare ne muke yi ko kuma wane ƙasa da muke zama, za mu iya zama masu haske a “duniya.”—Filib. 2:15.
3 Yadda muke ƙara yin yawa da haɗin kanmu da kuma yadda muke kasancewa a faɗake suna ɗaukaka Jehobah. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu zama masu haske ga Matiyu 5:14-16.
mutane a waɗannan hanyoyin.—KarantaKU TAIMAKA WA MUTANE SU BAUTA WA JEHOBAH
4, 5. (a) Ƙari ga yin wa’azi, ta yaya za mu zama masu haske ga mutane? (b) Wane sakamako mai kyau ne ake samu ta wurin kasancewa da halin kirki? (Ka duba hoton da ke shafi na 21.)
4 A cikin talifin da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuni, 1925, an ce: “Babu wanda zai iya kasancewa da aminci ga Ubangiji idan ba ya yin amfani da damar da yake da shi na zama mai haske ga mutane.” Talifin ya daɗa cewa: “Zai yi hakan ta wurin yin wa’azi da kuma kasancewa da halin kirki.” Hakika, hanya ɗaya da za mu iya zama masu haske ga mutane ita ce ta yin wa’azi da kuma sa mutane su zama almajiran Yesu. (Mat. 28:19, 20) Ƙari ga haka, za mu ɗaukaka Jehobah ta halinmu don mutane da yawa suna lura da halinmu. Idan muka yi musu murmushi ko kuma muka gaishe su, hakan yana taimaka musu su riƙa daraja mu kuma su ɗaukaka Allah.
5 Yesu ya ce wa almajiransa: “Sa’ad da kuka shiga gidan, ku ce, ‘Salama a gare ku.’” (Mat. 10:12) Ana gayyatar mutane su shigo cikin gida a yankin da Yesu da manzanninsa suka yi wa’azi kuma haka yake a wurare da yawa a yau. Har ila, kasancewa da fara’a sa’ad da kake bayyana dalilin da ya sa ka zo gidan wani, zai sa mutane su saki jiki kuma ka sanyaya musu zuciya. Ƙari ga haka, yin murmushi yana da kyau sosai musamman sa’ad da ’yan’uwa suke wa’azi da amalanke. Idan muna yin murmushi sa’ad da muke wa’azi da amalanke kuma muna gai da mutane, za mu ga cewa mutane za su so saƙonmu. Hakan yana iya sa su karɓi littattafanmu. Ban da haka ma, zai iya sa mu soma tattaunawa da su.
6. Ta yaya wasu ma’aurata tsofaffi suka ƙara ƙwazo a hidimarsu?
6 Akwai wasu ma’aurata tsofaffi a Ingila ba sa wa’azi gida-gida don suna rashin lafiya. Sai suka tsai da shawarar yin wa’azi a gaban gidansu. Sukan ajiye wasu littattafanmu a kan teburi a lokacin da iyaye suke zuwa su ɗauki yaransu daga makarantar da ke kusa da gidansu. Kuma hakan ya sa iyaye da yawa su karɓi littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Littafi na 1 da 2 da kuma ƙasidu. Wata majagaba a ikilisiyarsu takan yi wannan hidimar tare da su. Iyayen sun lura cewa tana da fara’a kuma ma’auratan suna son taimaka wa mutane. Hakan ya sa wani mutum ya ce a soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.
7. Ta yaya za ka iya taimaka wa ’yan gudun hijira a yankinku?
7 A kwana-kwanan nan, akwai masu gudun hijira a ƙasashe da yawa. Mene ne za ka iya yi don ka taimaka ma waɗannan mutane su koya game da Jehobah da kuma nufinsa? Za ka iya koyan yin gaisuwa a yarensu. Ƙari ga haka, ta yin amfani da manhajar JW Language, kana iya koyan wasu furuci da zai sa su so tattaunawa da kai. Sa’an nan, kana iya nuna musu bidiyoyi da littattafai na yarensu a dandalin jw.org.—M. Sha. 10:19.
8, 9. (a) Ta yaya taronmu na tsakiyar mako yake taimaka mana? (b) Ta yaya iyaye za su taimaka wa yaransu su kyautata yadda suke kalami a taro?
8 Jehobah ya yi tanadin taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu don mu ƙware a yin wa’azi. Shawara mai kyau da ake ba mu a wannan taron tana taimaka ma ’yan’uwa da yawa su kasance da gaba gaɗi sa’ad da suke koma ziyara da kuma gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki.
1 Kor. 14:25.
9 Kalamin da yaranmu suke yi a taro yana burge baƙi da yawa da ke halartan taronmu. Iyaye, ku taimaka wa yaranku su zama masu haske ga mutane ta wurin koya musu yin kalami da kansu. Kada su riƙa karanta amsar daga littafin da ake nazarinsa ko kuma su maimaita amsar da wani ya gaya musu. Wasu mutane sun soma bauta wa Jehobah don sun ji yara sun furta bangaskiyarsu da dukan zuciya.—YANA SA MU KASANCE DA HAƊIN KAI
10. Ta yaya ibada ta iyali take sa iyalai su kasance da haɗin kai?
10 Wata hanya kuma da za ku zama masu haske ga mutane ita ce ta wurin kasancewa da haɗin kai a iyalinku da kuma ikilisiyarku. Iyaye suna iya shirya su riƙa yin Ibada ta Iyali a kai a kai. Iyalai da yawa suna kallon Tashar JW kuma su tattauna yadda za su yi amfani da darussan da suka koya. Sa’ad da iyaye suke gudanar da ibada ta iyali, ya kamata su tuna cewa yadda za a yi renon yaro ƙarami ya yi dabam da yadda za a reni matashi. Saboda haka, ku yi iya ƙoƙarinku don kowa a iyalin ya amfana daga ibadar.—Zab. 148:12, 13.
11-13. Ta yaya dukanmu za mu sa ikilisiya ta kasance da haɗin kai kuma mu taimaka wa wasu su zama masu haske ga mutane?
11 Ta yaya matasa za su taimaka wajen sa ikilisiya ta kasance da haɗin kai kuma su ƙarfafa wasu su zama masu haske ga mutane? Hanya ɗaya ita ce ta yin abokantaka da ’yan’uwa tsofaffi. Kuna iya tambayar su abin da ya taimaka musu su ci gaba da bauta wa Jehobah shekaru da yawa. Hakan zai ƙarfafa ku sosai, kuma dukanku za ku daɗa ƙwazo ku zama masu haske ga mutane. Ƙari ga haka, dukanmu muna iya marabtar baƙi da suka halarci taronmu. Yin hakan zai sa mu kasance da haɗin kai kuma ya sa baƙin su so zama masu haske ga mutane. Kana iya gai da su da fara’a, kuma ka taimaka musu su sami wurin zama. Ban da haka, ka yi ƙoƙari ka gabatar da su ga wasu ’yan’uwa don su saki jiki a taron.
12 Idan kai ne za ka gudanar da taron fita wa’azi, za ka iya taimaka wa tsofaffi ma su yi wa’azi. Ka tabbatar da cewa ka ba su yankin da ya dace da yanayinsu. A wasu lokuta, kana iya sa su fita wa’azi tare da matasan da za su iya taimaka musu. Ƙari ga haka, kana iya yin la’akari
da waɗanda suke rashin lafiya da ba sa iya yin abubuwan da suke yi a dā. Yin hakan zai taimaka wa matasa da tsofaffi da waɗanda suka daɗe suna wa’azi da waɗanda ba su daɗe ba, su yi wa’azi da ƙwazo.—L.Fir. 19:32.13 Dauda marubucin wannan zabura ya ce: “Hakika, abu mai kyau ne, mai daɗi kuma ’yan’uwa su zauna tare kamar ɗaya!” (Karanta Zabura 133:1, 2.) Isra’ilawa sun ji daɗin bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwansu. Wannan cuɗanya tana kamar māi mai ƙamshi da ake shafe sarakuna da shi. Hakazalika, muna iya sa ’yan’uwanmu farin ciki ta wurin nuna musu alheri kuma hakan yana sa mu kasance da haɗin kai. Muna yaba maka idan kana hakan. Amma za ka iya ƙara nuna ƙauna ta wajen yin ƙoƙari ka san ’yan’uwa sosai.—2 Kor. 6:11-13.
14. Mene ne za ku iya yi don ku zama masu haske a unguwarku?
14 Ta yaya za ku ƙara zama masu haske a unguwarku? Furucinku da ayyukanku masu kyau za su iya sa maƙwabtanku su so su koya game da Jehobah. Ku tambayi kanku: ‘Ta yaya maƙwabtana suke ɗauka na? Ina tsabtace gidanmu da kuma mahallin don unguwarmu ta yi kyau sosai? Ina taimaka wa mutane ne?’ Sa’ad da kake tattaunawa da wasu Shaidu, ka tambaye su yadda alherinsu da misalinsu suka taimaka wa danginsu da maƙwabtansu da abokan aikinsu ko kuma abokan makarantarsu. Babu shakka, za su faɗi abubuwan da za su ƙarfafa ka.—Afis. 5:9.
KU YI TSARO
15. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa yin tsaro?
15 Idan muna so mu ci gaba da zama masu haske ga mutane, muna bukatar mu san lokacin da muke ciki. Yesu ya gaya wa almajiransa sau da yawa cewa: “Ku zauna da shiri” ko kuma “ku yi tsaro.” (Mat. 24:42; 25:13; 26:41) Idan muna ganin cewa lokacin da za a yi “azaba mai zafi,” wato ƙunci mai girma yana da nisa sosai ko kuma ba zai faru a lokacin da muke da rai ba, ba za mu sa ƙwazo a yin wa’azi ba. (Mat. 24:21) Maimakon mu riƙa zama masu haske a unguwarmu, za mu yi sanyi ko kuma mu daina bauta wa Jehobah.
16, 17. Mene ne za ka yi don ka ci gaba da zama a faɗake?
16 Muna bukatar mu zauna a faɗake yanzu fiye da dā don yanayin duniya na daɗa taɓarɓarewa. Babu shakka, Jehobah zai kawo ƙarshen mugunta a duniyar nan a daidai lokacin da ya ƙayyade. (Mat. 24:42-44) Amma kafin wannan lokacin, muna bukatar mu zama masu haƙuri kuma mu riƙa zama a faɗake. Ban da haka, ya kamata mu riƙa karanta Kalmar Allah a kowace rana kuma mu riƙa addu’a babu fasawa. (1 Bit. 4:7) Mu bi misalin ’yan’uwa da suka yi shekaru da yawa suna bauta wa Jehobah. Alal misali, muna iya karanta labarin da ke cikin wani talifi mai jigo, “Na Yi Shekara Saba’in Ina Riƙe da Ƙafar Bayahude,” da ke cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2012, shafuffuka na 18-21.
17 Ka kasance da ƙwazo a hidimarka ga Jehobah kuma ka riƙa cuɗanya sosai da ’yan’uwanka. Hakan zai sa ka farin ciki sosai, kuma za ka ga kamar lokaci yana saurin shigewa. (Afis. 5:16) Bayin Jehobah sun cim ma abubuwa da yawa cikin shekaru ɗari da suka shige. Amma da taimakon Jehobah, mun fi cim ma abubuwa da yawa a yau. Muna sa haskenmu ya haskaka ga mutane fiye da yadda muke tsammani.
18, 19. Ta yaya dattawa za su taimaka mana mu zauna a faɗake kuma mu zama masu ƙwazo? Ka ba da misali.
Afisawa 4:8, 11, 12.) Saboda haka, sa’ad da dattawa suka kawo maka ziyara, ka yi amfani da wannan zarafin don ka koyi abubuwa da yawa daga wurinsu.
18 Jehobah yana so mu riƙa bauta masa duk da cewa mu ajizai ne. Shi ya sa ya tanadar mana da dattawa don su riƙa taimaka mana. (Karanta19 Alal misali, akwai wasu ma’aurata a Ingila da suke fuskantar matsala a aurensu. Matar tana ganin cewa mijinta ba ya shugabanci a iyali yadda ya kamata. Mijin kuma yana ganin shi bai iya koyarwa ba. Don hakan, bai tsara yadda za su riƙa yin ibada ta iyali a kai a kai ba. Dattawan suka taimaka wa ma’auratan su yi tunani a kan misalin Yesu. Sun ƙarfafa mijin ya yi koyi da yadda Yesu ya kula da almajiransa kuma ya biya bukatunsu. Ban da haka, sun ƙarfafa matar ta riƙa haƙuri da mijinta. Dattawan sun ba ma’auratan wasu shawarwari a kan yadda za su riƙa yin ibada ta iyali da yaransu biyu. (Afis. 5:21-29) Daga baya, dattawan suka yaba wa mijin don ƙoƙarin da yake yi. Sun ƙarfafa shi ya ci gaba da yin iya ƙoƙarinsa kuma ya nemi taimakon ruhu mai tsarki don ya riƙa yin shugabanci da kyau a iyalinsa. Yadda dattawan suka taimaka ma wannan iyalin ya sa ma’auratan sun zama masu haske ga mutane.
20. Mene ne zai faru idan kuka zama masu haske ga mutane?
20 Wani marubucin zabura ya ce: “Masu albarka ne dukan masu tsoron Yahweh, masu tafiya cikin hanyarsa.” (Zab. 128:1) Za ku yi farin ciki sa’ad da kuka zama masu haske ga mutane. Saboda haka, ku riƙa koya wa mutane game da Allah, kuma ku yi iya ƙoƙarinku don ku taimaka wa iyalinku da ikilisiyarku su kasance da haɗin kai. Ƙari ga haka, ku zauna a faɗake. Idan kuka yi hakan, mutane za su ga nagargarun ayyukanku kuma za su so su ɗaukaka Ubanmu.—Mat. 5:16.