Mu Zama Tsintsiya Madaurinki Daya Kamar Jehobah da Yesu
“Ina roƙo domin dukansu su zama ɗaya.”—YOH. 17:20, 21.
WAƘOƘI: 24, 99
1, 2. (a) Wane abu ne Yesu ya roƙa a addu’a ta ƙarshe da ya yi da almajiransa? (b) Mene ne wataƙila ya sa Yesu ya damu da batun haɗin kai?
A LOKACIN da Yesu ya ci abincin dare na ƙarshe da almajiransa, ya nuna cewa yana son mabiyansa su kasance da haɗin kai. Sa’ad da suke addu’a tare, ya bayyana cewa burinsa shi ne mabiyansa su zama ɗaya kamar yadda shi da Ubansa suke. (Karanta Yohanna 17:20, 21.) Idan mabiyan Yesu suka kasance da haɗin kai, hakan zai nuna wa mutane cewa Jehobah ne ya aiko Yesu duniya domin ya yi nufinsa. Kuma mutane za su gane mabiyan Yesu ta wajen ƙaunar da suke nuna wa juna da kuma haɗin kansu.—Yoh. 13:34, 35.
2 Yesu ya nanata wa almajiransa cewa su kasance da haɗin kai domin ya lura cewa ba sa yin hakan. Alal misali, almajiransa sun yi gardama ko wane ne a “cikinsu zai zama babba.” (Luk. 22:24-27; Mar. 9:33, 34) Ban da haka ma, akwai lokacin da Yaƙub da Yohanna suka roƙi Yesu ya ba su babban matsayi a mulkinsa.—Mar. 10:35-40.
3. Mene ne zai iya hana almajiran Yesu kasancewa da haɗin kai, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
3 Ba neman babban matsayi ba ne kaɗai zai sa almajiran Yesu su
kasa kasancewa da haɗin kai ba. Mutane a zamanin Yesu ba su da haɗin kai domin suna nuna bambanci kuma sun tsani juna. Hakika, almajiran Yesu suna bukatar su guji waɗannan halayen. A wannan talifin, za mu amsa tambayoyin nan: Mene ne Yesu ya yi sa’ad da aka nuna masa wariya? Ta yaya Yesu ya taimaka wa mabiyansa su daina nuna bambanci kuma su kasance da haɗin kai? Kuma ta yaya koyarwarsa za ta taimaka mana mu kasance da haɗin kai?YESU DA MABIYANSA SUN FUSKANCI WARIYA
4. Ta yaya aka nuna wa Yesu wariya?
4 An nuna wa Yesu wariya. Yaya muka san haka? Domin a lokacin da Filibus ya gaya wa Natanayilu cewa an gano Almasihu, Natanayilu ya tambaye shi cewa: “Wani abin kirki zai iya fitowa daga Nazaret kuwa?” (Yoh. 1:46) Babu shakka, Natanayilu ya san wurin da za a haifi Almasihu domin an yi annabcin hakan a littafin Mika 5:2. Amma a ganinsa, Nazaret ƙaramin gari ne da bai isa a ce za a haifi Almasihu a ciki ba. Ban da haka ma, akwai manyan mutane daga Yahudiya da suke wa Yesu kallon reni domin shi Bagalile ne. (Yoh. 7:52) Mutanen Yahudiya da yawa sun rena mutanen Galili sosai. Wasu Yahudawa ma sun zagi Yesu ta wajen kiran sa mutumin Samariya. (Yoh. 8:48) Al’adar Samariyawa da kuma addininsu sun bambanta da na Yahudawa. Don haka, mutanen Yahudiya da kuma na Galili ba sa daraja Samariyawa kuma ba sa cuɗanya da su.—Yoh. 4:9.
5. Ta yaya almajiran Yesu suka fuskanci wariya?
5 Malaman addinin Yahudawa ma sun rena almajiran Yesu. Farisiyawa suna kiran su “la’anannu.” (Yoh. 7:47-49) Hakika, Farisiyawa suna ganin cewa duk wanda bai yi karatu a makarantunsu na addini ba ko kuma ba ya bin al’adarsu matsiyaci ne. (A. M. 4:13) Yesu da almajiransa sun fuskanci wariya domin a zamaninsu, mutane suna fahariya don addininsu da matsayinsu da kuma al’ummarsu. Almajiran Yesu ma suna nuna wariya. Don haka, suna bukatar su canja halinsu idan suna so su kasance da haɗin kai.
6. Ka ba da misalin da ya nuna cewa nuna wariya takan shafe mu a yau.
6 Mutane a yau suna fuskantar wariya sosai. Wataƙila an taɓa nuna mana hakan ko kuma mu da kanmu mun taɓa nuna ma wasu. Wata ’yar’uwa wadda yanzu tana hidimar majagaba a ƙasar Ostareliya, ta ce: “Dalilin da ya sa na tsani fararen fata shi ne don na mai da hankali ga yadda ake nuna wa ’yan asalin ƙasar Ostareliya wariya. Ƙari ga haka, ƙiyayyar ta ƙaru sanaddiyar wulaƙancin da na fuskanta.” Wani ɗan’uwa daga Kanada ya bayyana yadda ya soma nuna bambanci ga mutanen da ba sa yarensu. Ya ce: “Na ɗauka cewa mutanen da ke Farasanci sun fi daraja, kuma hakan ne ya sa na soma ƙin jinin Turawa.”
7. Ta yaya Yesu ya guji nuna wariya?
7 Kamar yadda yake a zamanin Yesu, nuna wariya hali ne da ke da wuyan dainawa. Amma ta yaya Yesu ya guji nuna wariya? Da farko, ya nuna yana son dukan mutane. Ya yi wa’azi ga masu arziki da talakawa da Farisiyawa da Samariyawa da masu karɓan haraji da kuma masu zunubi. Na biyu, ta wajen koyarwarsa da kuma misalinsa, ya nuna wa almajiransa cewa suna bukatar su guji zargin mutane ko kuma nuna musu wariya.
ƘAUNA DA TAWALI’U ZA SU SA KA GUJI NUNA BAMBANCI
8. Wace ƙa’ida ce ta sa Kiristoci suke da haɗin kai? Ka bayyana.
8 Yesu ya koya wa mabiyansa wata ƙa’ida mai muhimmanci da ta sa muke da haɗin kai. Ya gaya musu cewa: “Dukanku kuwa ’yan’uwa ne.” (Karanta Matiyu 23:8, 9.) Hakika, mu “’yan’uwa” ne domin dukanmu ’ya’yan Adamu ne. (A. M. 17:26) Ban da haka, Yesu ya bayyana cewa mabiyansa ’yan’uwa ne domin dukansu sun ɗauki Jehobah a matsayin Ubansu. (Mat. 12:50) Ƙari ga haka, sun zama ’yan iyalin Allah kuma suna da haɗin kai domin suna ƙaunar juna kuma suna bauta wa Jehobah. Saboda haka, a wasiƙar da mazannin Yesu suka rubuta, sun kira sauran mabiyan Yesu “’yan’uwa.”—Rom. 1:13; 1 Bit. 2:17; 1 Yoh. 3:13. *
9, 10. (a) Me ya sa bai kamata Yahudawa su riƙa kishin ƙasarsu ba? (b) Ta yaya Yesu ya koyar da cewa bai dace mu rena mutanen da suka fito daga wata ƙasa ba? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.)
9 Bayan Yesu ya gaya wa mabiyansa su ɗauki juna a matsayin ’yan’uwa, ya nanata cewa suna bukatar su zama masu tawali’u. (Karanta Matiyu 23:11, 12.) Kamar yadda muka koya, fahariya ta kusan sa manzannin Yesu su kasa kasancewa da haɗin kai. Ban da haka ma, wataƙila bambanci launin fata ma ya jawo matsala. Shin fahariyar da Yahudawa suke yi don su ’ya’ya Ibrahim ne ya dace kuwa? A’a. Amma Yahudawa da yawa suna yin hakan. Shi ya sa Yohanna Mai Baftisma ya gaya musu cewa: “Allah yana da iko ya ta da ’ya’ya domin Ibrahim daga duwatsun nan.”—Luk. 3:8.
10 Yesu ya koyar da cewa bai dace mutane su riƙa fahariya don launin fatarsu ba. Ya nuna hakan a lokacin da wani mutumi ya tambaye shi cewa: “Shin, wane ne maƙwabcina?” Yesu ya amsa ta wajen ba da labarin Basamare da ya kula da Bayahuden da ɓarayi suka yi wa dūka. Yahudawan da ke wucewa sun ƙi taimaka ma wannan mutumin, amma Basamaren ne ya ji tausayin sa kuma ya taimaka masa. Sa’ad da Yesu ya gama ba da labarin, sai ya ce wa mutumin ya yi koyi da Basamaren. (Luk. 10:25-37) Yesu ya nuna wa Yahudawa cewa misalin Basamaren ne zai iya koya musu su riƙa ƙaunar mutane.
11. Me ya sa mabiyan Yesu suke bukatar su ƙaunaci dukan mutane, kuma ta yaya Yesu ya taimaka musu su fahimci hakan?
11 Almajiran Yesu suna bukatar su guji fahariya da kuma nuna wariya don su iya yin aikin da ya ba su. Kafin Yesu ya koma sama, ya umurci mabiyansa su yi wa’azi a “Yahudiya, da Samariya, har zuwa iyakar duniya.” (A. M. 1:8) Yesu ya shirya su don yin wannan aikin ta wajen nuna musu halaye masu kyau da baƙi suke da shi. Ya yaba ma wani babban soja da ba Bayahude ba ne domin yana da bangaskiya sosai. (Mat. 8:5-10) Ƙari ga haka, a lokacin da Yesu yake Nazarat, ya faɗa yadda Jehobah ya yi wa mutanen da ba Yahudawa ba ne albarka. Ya ambata gwauruwa ’yar Finikiya da ke Zarefat da kuma Na’aman mutumin Suriya. (Luk. 4:25-27) Ban da haka ma, Yesu ya yi wa Basamariya wa’azi, kuma ya yi kwana biyu a garin Samariyawa domin mutanen suna son bishara.—Yoh. 4:21-24, 40.
KIRISTOCI A DĀ SUN ƘOƘARTA SU DAINA NUNA WARIYA
12, 13. (a) Mene ne manzannin Yesu suka yi a lokacin da yake wa Basamariya wa’azi? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.) (b) Mene ne ya nuna cewa Yaƙub da Yohanna ba su fahimci darasin da Yesu yake koya musu ba?
12 Bai yi wa manzannin Yesu sauƙi su daina nuna wariya ba. Da akwai wani lokaci da Yesu ya koyar da wata Basamariya, kuma hakan ya sa almajiransa mamaki sosai. (Yoh. 4:9, 27) Malaman Yahudawa ba sa yi wa mata magana a cikin jama’a, balle ma Basamariya da ake zargin cewa ba ta da halin kirki. Manzannin sun gaya wa Yesu ya ci abinci, amma amsar da ya ba su ya nuna cewa yin nufin Allah ya fi abinci muhimmanci a gare shi. Nufin Allah ne Yesu ya yi wa Basamariyar wa’azi kuma wa’azin da yake mata kamar abinci ne a gare shi.—Yoh. 4:31-34.
13 Yaƙub da Yohanna ba su fahimci darasin da yake koya musu ba. A lokacin da su da Yesu suke wucewa ta Samariya, manzannin sun nemi masauki a wani ƙauyen da ke Samariya, amma mutanen sun ƙi ba su. Hakan ya sa Yohanna da Yaƙub fushi kuma suka ce a kira wuta daga sama ta halaka ƙauyen gabaki ɗaya. Yesu ya daidaita ra’ayinsu. (Luk. 9:51-56) Da a ce ƙauyen yana yankinsu, wato Galili, wataƙila Yaƙub da Yohanna ba za su yi fushi haka ba. Ban da haka, wataƙila nuna wariya ce ta sa su fushi sosai. Ƙari ga haka, wataƙila manzo Yohanna ya ji kunyar abin da ya yi domin daga baya, ya yi wa Samariyawa wa’azi kuma da yawa cikinsu sun saurare shi.—A. M. 8:14, 25.
14. Ta yaya aka magance matsalar da ta kunno kai bayan ranar Fentakos na 33?
14 Jim kaɗan bayan ranar Fentakos na 33, sai batun nuna wariya ya sake kunno kai. A lokacin da ake raba wa gwauraye abinci, ba a ba gwaurayen da ke Helenanci ba. (A. M. 6:1) Wataƙila hakan ya faru ne don suna yare dabam. Amma manzannin sun magance matsalar ta wajen naɗa mazan da suka ƙware don su raba abincin. Ban da haka, dukan mazan suna da sunayen Helas. Babu shakka, hakan ya ƙarfafa gwaurayen da aka ɓata wa rai.
15. Mene ne ya taimaka wa Bitrus ya daina nuna wariya? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.)
15 A shekara ta 36, almajiran Yesu suka soma yi wa mutane daga dukan al’ummai wa’azi. Kafin wannan lokacin, manzo Bitrus yana cuɗanya da Yahudawa kawai. Amma Bitrus ya yi wa Karniliyus wa’azi bayan da Allah ya nuna masa cewa bai kamata Kiristoci su riƙa nuna wariya ba. (Karanta Ayyukan Manzanni 10:28, 34, 35.) Bayan hakan, Bitrus ya ci abinci da Kiristocin da ba Yahudawa ba kuma ya yi cuɗanya da su. Amma bayan shekaru da yawa, Bitrus ya daina cin abinci tare da Kiristoci da ba Yahudawa ba a birnin Antakiya. (Gal. 2:11-14) Bulus ya yi wa Bitrus gyara don abin da ya yi, kuma Bitrus ya amince da gyarar da aka yi masa. Ta yaya muka sani? Don a wasiƙarsa ta farko zuwa ga Kiristoci Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba a Asiya Ƙarama, ya ƙarfafa su su riƙa ƙaunar dukan ’yan’uwa.—1 Bit. 1:1; 2:17.
16. Da wane irin hali ne aka san Kiristoci na farko?
16 Hakika, misalin da Yesu ya kafa wa manzanninsa ya sa su riƙa ƙaunar “dukan mutane.” (Yoh. 12:32; 1 Tim. 4:10) Sun daidaita tunaninsu ko da hakan ya ɗauki lokaci. An san Kiristoci na farko da nuna ƙauna ga juna. Wani marubuci a ƙarni na biyu mai suna Tertullian ya faɗi abin da mutanen da ba Kiristoci ba suka ce game da Kiristoci. Ya ce: “Suna ƙaunar juna . . . Har ma suna a shirye su mutu domin juna.” Domin waɗannan Kiristoci a ƙarni na farko sun yafa “sabon hali,” sun koyi su riƙa daraja kowa yadda Allah yake daraja su.—Kol. 3:10, 11.
17. Me zai taimaka mana mu daina nuna wariya a zuciyarmu? Ka ba da misalai.
17 A yau, yakan ɗauki lokaci kafin mu daina nuna wariya a zuciyarmu. Wata ’yar’uwa a Faransa ta faɗi yadda hakan yake mata wuya. Ta ce: “Jehobah ya koya mini abin da ƙauna take nufi da yadda zan zama mai yin alheri da kuma yadda zan ƙaunaci dukan mutane. Amma har ila, ina fama in daina nuna wariya kuma hakan bai da sauƙi. Shi ya sa na ci gaba da yin addu’a a kan batun.” Wata ’yar’uwa a ƙasar Sifen
tana fama da wannan halin. Ta ce: “A wasu lokuta, nakan yi ƙoƙari don kada in tsani wata ƙabila, kuma ina yin nasara a yawancin lokaci. Amma na san ina bukatar in ci gaba da ƙoƙari don in daina wannan halin. Ina godiya ga Jehobah cewa ina cikin ƙungiyarsa da ake da haɗin kai.” Ya kamata kowannenmu ya bincika kansa sosai. Shin muna bukatar mu yi ƙoƙari don mu daina nuna wariya yadda waɗannan ’yan’uwa mata biyu suka yi?NUNA ƘAUNA NA SA A DAINA NUNA BAMBANCI
18, 19. (a) Me ya sa muke bukatar mu marabci dukan mutane? (b) Ta yaya za mu yi hakan?
18 Ya kamata mu tuna cewa a dā, dukanmu “baƙi” ne, wato ba mu da dangantaka da Jehobah. (Afis. 2:12) Amma Jehobah ya jawo mu wajensa don yana ƙaunar mu. (Hos. 11:4; Yoh. 6:44) Ƙari ga haka, Yesu ya marabce mu, kuma ya sa mu zama ’yan iyalin Allah. (Karanta Romawa 15:7.) Don haka, ba zai dace mu ƙi mutane ba, domin mu ma Yesu ya marabce mu duk da cewa mu ajizai ne!
19 Da yake ƙarshen zamanin nan yana kusatowa, nuna bambanci da wariya da ƙin wasu zai daɗa ƙaruwa sosai. (Gal. 5:19-21; 2 Tim. 3:13) Amma da yake mu bayin Jehobah ne, muna son Jehobah ya ba mu hikima don hakan zai taimaka mana mu guji nuna wariya kuma mu kasance da salama. (Yaƙ. 3:17, 18) Ban da haka, muna farin cikin yin abokai da mutanen da suka fito daga wasu ƙasashe kuma muna amincewa da al’adarsu har ma wataƙila mu koyi yarensu. Yin hakan yana taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da salama kamar ruwan rafi, da adalci kuma kamar raƙuman ruwa.—Isha. 48:17, 18.
20. Mene ne ƙauna za ta sa mu riƙa yi?
20 ’Yar’uwar da take Ostareliya da aka ambata ɗazu, ta ce: “Na koyi abubuwa masu kyau daga Littafi Mai Tsarki. Abubuwan da na koya sun taimaka mini in canja ra’ayina, kuma na daina nuna bambanci da ƙin mutane.” Ɗan’uwan da ke Kanada kuma ya ce: “Yanzu na fahimci cewa mutane suna nuna bambanci ne domin ba su san mutanen yadda ya kamata ba. Na koyi cewa ko da a wace ƙasa ce aka haifi mutum, yana iya kasancewa da halaye masu kyau.” Ƙari ga haka, wannan ɗan’uwan ya auri Baturiya! Babu shakka, canje-canjen da mutanen nan suka yi sun nuna cewa ƙauna tana iya sa mu daina nuna wariya kuma mu kasance da haɗin kai sosai.—Kol. 3:14.
^ sakin layi na 8 Idan an ce “’yan’uwa,” hakan ya ƙunshi maza da mata a ikilisiya. Bulus ya rubuta wasiƙarsa ga “yan’uwan” da ke Roma. Babu shakka, wasiƙar ta shafi ’yan’uwa mata, kuma ya kira da yawa daga cikinsu da sunayensu. (Rom. 16:3, 6, 12) Ban da haka ma, Hasumiyar Tsaro da daɗewa tana kiran Kiristoci ‘’yan’uwa.’