Kamewa—Halin da Ke Faranta Ran Jehobah
Wani mai suna Paul ya ce: “Sa’ad da ɗan’uwana ya tsokane ni kuma muka soma faɗa, sai na shaƙe shi ina so in kashe shi.”
Wani mai suna Marco ya ce: “A gida, ina saurin fushi ko da abin da aka yi mini bai taka-ƙara-ya-ƙarya ba. Kuma ina farfasa dukan abubuwan da ke ɗaki.”
Wataƙila ba ma fushi kamar waɗannan mutanen. Amma a wasu lokuta yana iya mana wuya mu kame kanmu. Dalilin shi ne domin mun gāji zunubi daga Adamu. (Rom. 5:12) Kamar Paul da Marco, yana ma wasu mutane wuya su kame kansu sa’ad da suke fushi. Wasu kuma yana musu wuya su guji yin tunanin banza. Alal misali, suna yawan tunanin abubuwan da ke sa su sanyin gwiwa. Ƙari ga haka, yana ma wasu wuya su guji sha’awar yin lalata da yawan shan giya ko kuma shan ƙwayoyi.
Mutanen da ba sa iya guje wa yin tunanin banza da sha’awoyi da kuma ayyukan da ba su dace ba, ba za su ji daɗin rayuwa ba. Muna iya guje wa wannan sakamako. Ta yaya? Ta wajen kame kanmu. Don mu yi hakan, bari mu tattauna tambayoyi uku: (1) Mene ne kame kai yake nufi? (2) Me ya sa kame kai yake da muhimmanci? (3) Ta yaya za mu kasance da wannan hali da ke cikin halayen da ruhu mai tsarki yake ‘haifarwa’? (Gal. 5:22, 23) Ƙari ga haka, za mu tattauna abubuwan da za mu iya yi idan a wasu lokuta mun kasa kame kanmu.
MENE NE KAME KAI YAKE NUFI?
Mutumin da ke kame kansa ba ya yin dukan abubuwan da zuciyarsa ta gaya masa. A maimakon haka, yana guje wa faɗi ko kuma yin abubuwan da ke ɓata wa Allah rai.
Yesu ya nuna mana abin da kame kai ta ƙunsa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’ad da mutane suka zage shi, bai mai da zagin ba. Sa’ad da ya sha wahala, bai ce zai rama ba. Sai dai ya dogara ga Allah wanda yake yin shari’ar gaskiya.” (1 Bit. 2:23) Yesu ya nuna kamun kai sa’ad da maƙiyansa suka yi masa baƙar magana a lokacin da yake kan gungumen azaba. (Mat. 27:39-44) Kafin wannan lokacin, Yesu ya nuna kamun kai sa’ad da malaman addinai suka yi masa tambayoyi domin suna so ya yi saɓo. (Mat. 22:15-22) Kuma ya kafa mana misali mai kyau a lokacin da wasu Yahudawa da suke fushi suka ɗebo duwatsu domin su jejjefe shi! Maimakon ya rama, “Yesu ya ɓoye kansa, ya fita ya bar Haikalin.”—Yoh. 8:57-59.
Za mu iya yin koyi da Yesu kuwa? Ƙwarai kuwa. Manzo Bitrus ya ce: “Almasihu ma ya sha wahala dominku. Ta haka ya bar muku gurbi domin ku bi hanyarsa.” (1 Bit. 2:21) Ko da yake mu ajizai ne, muna iya yin koyi sosai da yadda Yesu ya kame kansa. Mene ne ya sa yin hakan yake da muhimmanci?
ME YA SA KAME KAI YAKE DA MUHIMMANCI?
Idan muna so Jehobah ya amince da mu, muna bukatar mu riƙa kame kanmu. Ko da mun yi shekaru da yawa muna bauta wa Jehobah, muna iya ɓata dangantakarmu da shi ta ayyukanmu da furucinmu.
Alal misali, Musa “mutum mai sauƙin kai ne sosai, fiye da kowane mutum a fuskar duniya” a zamaninsa. (L. Ƙid. 12:3) Amma akwai lokacin da Musa ya kasa kame kansa bayan ya yi shekaru yana jimre da gunagunin Isra’ilawa. Ya yi fushi sosai sa’ad da suka yi gunaguni cewa ba su da ruwan sha. Ya yi magana da fushi kuma ya ce: “Ku kasa kunne, ya ku ’yan tawaye! Daga wannan dutse kuke so mu fito muku da ruwa?”—L. Ƙid. 20:2-11.
Musa ya kasa kame kansa. Bai yabi Jehobah don mu’ujizar da ya yi ba. (Zab. 106:32, 33) Saboda haka, Jehobah ya hana shi shiga Ƙasar Alkawari. (L. Ƙid. 20:12) Wataƙila Musa ya yi da-na-sani don yadda ya kasa kame kansa.—M. Sha. 3:23-27.
Wane darasi ne za mu iya koya? Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah, bai kamata mu yi wa mutanen da suka ɓata mana rai ko kuma suke bukatar gyara magana da fushi ba. (Afis. 4:32; Kol. 3:12) Gaskiyar ita ce, yayin da muke tsufa, yana iya yi mana wuya mu riƙa yin haƙuri. Amma mu tuna Musa. Ba zai dace mu ɓata dangantakarmu da Jehobah domin mun kasa kame kanmu ba. Me zai taimaka mana mu kasance da halin nan mai muhimmanci?
YADDA ZA MU ZAMA MASU KAMUN KAI
Ka yi addu’a don samun taimakon ruhu mai tsarki. Me ya sa? Domin kamun kai yana cikin halayen da ruhu mai tsarki yake sa mu kasance da su, kuma Jehobah yana ba waɗanda suka roƙe shi wannan ruhun. (Luk. 11:13) Jehobah yana iya yin amfani da ruhunsa don ya taimaka mana mu zama masu kamun kai. (Filib. 4:13) Ƙari ga haka, zai taimaka mana mu kasance da wasu halaye masu kyau kamar ƙauna da za ta taimaka mana mu inganta yadda muke nuna kamun kai.—1 Kor. 13:5.
Ka guji dukan abin da zai sa ka kasa kame kanka. Alal misali, ka guji dandalin Yanar gizo da kuma nishaɗin da ake nuna abubuwan da ba su dace ba. (Afis. 5:3, 4) Wajibi ne mu guji dukan abubuwan da za su sa mu fāɗa cikin jarrabawa. (K. Mag. 22:3; 1 Kor. 6:12) Alal misali, mutumin da ke fama da sha’awar yin lalata, yana bukatar ya guji karanta littattafai da kallon fina-finan da ke ta da sha’awar yin lalata.
Yana iya yi mana wuya mu bi wannan shawarar. Amma idan mun yi iya ƙoƙarinmu, Jehobah zai taimaka mana mu riƙa kame kanmu. (2 Bit. 1:5-8) Zai taimaka mana mu riƙa yin tunani da furuci da kuma ayyukan da suka dace. Abin da ya faru da Paul da Marco da aka ambata ɗazu ke nan. Dukansu sun koyi yadda za su riƙa kame kansa sa’ad da suka yi fushi. Akwai wani ɗan’uwa da yake yawan fushi da direbobi sa’ad da yake tuƙi kuma yana faɗa da su. Mene ne ya yi don ya daina hakan? Ya ce: “Nakan yi addu’a sosai a kowace rana. Na yi nazarin talifofin da aka tattauna game da kamun kai kuma na haddace Nassosin da za su taimaka mini. Ko da yake na yi shekaru ina ƙoƙarin magance wannan matsalar, har ila a kowace safe ina tuna wa kaina cewa ina bukatar in yi ƙoƙari in riƙa kame kaina. Saboda haka, nakan bar gida da wuri domin in isa inda zan je ba tare da na yi hanzari ba.”
IDAN MUN KASA KAME KANMU
A wasu lokuta, yana iya yi mana wuya mu kame kanmu. Sa’ad da hakan ya faru, yana iya yi mana wuya mu yi addu’a ga Jehobah. Amma a irin wannan yanayin ne muke bukatar taimakon Jehobah. Saboda haka, ka yi addu’a ga Jehobah nan da nan. Ka roƙe shi ya gafarta maka, ka nemi taimakonsa, kuma ka ƙuduri niyyar guji sake yin kuskuren. (Zab. 51:9-11) Kada ka yi tunani cewa Jehobah ba zai saurari addu’arka ba. (Zab. 102:17) Manzo Yohanna ya ce jinin Yesu “yana tsabtace mu daga dukan zunubi.” (1 Yoh. 1:7; 2:1; Zab. 86:5) Ka tuna cewa Jehobah ya umurci bayinsa su riƙa gafartawa a kai a kai. Don haka, za mu kasance da tabbaci cewa shi ma zai gafarta mana.—Mat. 18:21, 22; Kol. 3:13.
Jehobah ya yi baƙin ciki sa’ad da Musa ya kasa kame kansa a cikin jeji. Duk da haka, Jehobah ya gafarta masa. Kalmar Allah ta nuna cewa Musa mutum ne mai aminci da ya kamata mu yi koyi da shi. (M. Sha. 34:10; Ibran. 11:24-28) Jehobah bai bar Musa ya shiga Ƙasar Alkawari ba, amma zai ba shi gatan yin rayuwa har abada a aljanna. Mu ma za mu ji daɗin yin rayuwa a aljanna idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance da wannan hali mai muhimmanci.—1 Kor. 9:25.