Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Mulkin Allah
Yesu ya koya wa mabiyansa su riƙa wannan addu’ar: “Ubanmu wanda yake cikin sama, a kiyaye sunanka da tsarki. Mulkinka ya zo, bari a yi nufinka a cikin duniya.” (Matiyu 6:9, 10) Mene ne Mulkin Allah? Mene ne Mulkin zai magance mana? Kuma me ya sa ya kamata mu riƙa addu’a Mulkin Allah ya zo?
Yesu ne Sarkin Mulkin Allah.
Luka 1:31-33: ‘Za ki ba shi suna Yesu. Zai zama babban mutum, kuma za a ce da shi Ɗan Mafi Ɗaukaka. Ubangiji Allah zai ba shi kujerar mulkin kakansa Dauda. Zai yi mulkin gidan Yakub har abada, mulkinsa kuma ba zai ƙare ba!’
Abin da Yesu ya yi wa’azi a kai musamman shi ne Mulkin Allah.
Matiyu 9:35: “Yesu ya bi dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’u, yana shelar labari mai daɗi na Mulkin Allah, yana kuma warkar da mutane daga kowane irin ciwo da rashin lafiya.”
Yesu ya gaya wa almajiransa alamar da za ta sa su san cewa Mulkin ya yi kusa.
Matiyu 24:7: ‘Al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki ya tasar wa mulki. Za a kuma yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam.’
A yau, mabiyan Yesu suna wa’azi game da Mulkin Allah a ko’ina a duniya.
Matiyu 24:14: “Kuma za a ba da wannan labari mai daɗi na mulkin sama domin shaida ga dukan al’umma, sa’an nan ƙarshen ya zo.”