Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ta Yaya Za Ka San Gaskiya?

Ta Yaya Za Ka San Gaskiya?

Sanin gaskiya zai iya cetan ran mutum. Alal misali, ka yi la’akari da yadda sanin amsar wannan tambayar ya ceci rayukan mutane da yawa: Ta yaya cututtuka suke yaɗuwa?

Mutane sun yi dubban shekaru ba su san amsar tambayar nan ba. Kafin a sami amsar, mutane sun yi ta mutuwa saboda annoba da cututtukan da ke yaɗuwa. Daga baya ne ’yan kimiyya suka gano gaskiyar lamarin. Sun gano cewa wasu ƙwayoyin cuta da ba a iya gani da ido, waɗanda ake kira bacteria da virus ne suke yaɗa cututtuka. Sanin wannan gaskiyar ne ya sa mutane sun san yadda za su hana cuta yaɗuwa, da yadda za a magance cututtuka da dama. Hakan ya inganta rayuwar biliyoyin mutane kuma ya daɗa tsawonta.

Ban da wannan tambayar, akwai tambayoyi da dama da suke da muhimmanci, kamar waɗanda ke gaba.

  • Wane ne Allah na Gaskiya?

  • Wane ne Yesu Kristi?

  • Mene ne Mulkin Allah?

  • Me zai faru a nan gaba?

Miliyoyin mutane sun sami amsar waɗannan tambayoyin kuma hakan ya inganta rayuwarsu. Kai ma za ka amfana idan ka san amsoshin.

ZAI YIWU MUTUM YA SAN GASKIYA KUWA?

Za ka iya cewa, ‘Me zai taimaka mana mu san gaskiyar wani batu a yau?’ Samun bayanai na ƙwarai bai da sauƙi. Me ya sa?

Mutane da yawa sun daina yarda da shugabanni da ’yan kasuwa har ma da kafofin yaɗa labarai. Yana musu wuya su san ko ana gaya musu gaskiya ne ko ƙarya ko dai mutane suna ba da ra’ayinsu ne kawai, da dai sauransu. Da yake mutane ba su yarda da juna ba, kuma ƙarya ta bazu a ko’ina, mutane ba su san ko me za su yarda da shi a matsayin gaskiya ba, da kuma yadda hakan ya shafe su.

Duk da haka, zai yiwu mu san gaskiya game da batutuwan da suka fi muhimmanci a rayuwa. Ta yaya? Ta wurin ɗaukan matakan da muka saba ɗaukawa yayin da muke rayuwarmu ta yau da kullum.

YADDA ZA KA SAN GASKIYA

A kullum, kowannenmu yakan nemi ya san gaskiya game da wani batu. Alal misali, wata mata mai suna Jessica ta ce: “Cin gyaɗa yakan sa ’yata mummunar rashin lafiya.” Ta daɗa da cewa “ko ta ɗan ɗanɗana gyaɗa, hakan zai iya kashe ta.” Jessica takan tabbatar da cewa abincin da za ta saya ba zai yi wa ’yarta illa ba. Ta ce: “Idan zan sayi abincin gwangwani, abu na farko da nake yi shi ne, karanta abin da aka rubuta a jikin gwangwanin don in san ko me da me ke cikin abincin. Sai in yi bincike har ma in kira kamfanin da suka yi abincin don in tabbata cewa ba a yi kuskure an sa gyaɗa a ciki ba. Ƙari ga haka, nakan bincika don in ga ko an san kamfanin da yin abinci bisa ƙa’ida.”

Wataƙila abubuwan da kake ƙoƙarin ka san gaskiyarsu a yau ba su kai na Jessica muhimmanci ba, amma kamar yadda Jessica take yi, kai ma za ka iya bin matakan da ke ƙasa don ka sami amsar tambayoyinka:

  • Ka ƙoƙarta ka san gaskiyar.

  • Ka ƙara yin bincike.

  • Ka tabbata cewa an saba faɗin gaskiya a inda kake neman bayanai.

Matakan nan za su taimake ka ka san ainihin amsoshin tambayoyi mafi muhimmanci a rayuwa. Ta yaya?

LITTAFIN DA YA YI FICE WAJEN FAƊIN GASKIYA

Da Jessica take neman ta san amsoshin tambayoyi masu muhimmanci game da rayuwa, ta bi matakan da ta saba ɗaukawa sa’ad da take ƙoƙarin tabbatar da abincin da za ta saya wa ’yarta. Jessica ta ce, “Karanta Littafi Mai Tsarki sosai, da kuma yin bincike ya taimaka mini in gano amsoshin.” Kamar yadda Jessica ta yi, miliyoyin mutane sun gano abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da tambayoyin nan:

  • Me ya sa Allah ya halicce mu?

  • Me ke faruwa da mutum bayan ya mutu?

  • Me ya sa ake shan wahala a yau?

  • Me Allah yake yi don ’yan Adam su daina shan wahala?

  • Me za mu yi don iyalinmu ta zauna lafiya?

Za ka sami amsoshin tambayoyin nan da ma wasu da yawa idan ka karanta Littafi Mai Tsarki kuma ka ƙara yin bincike a dandalin www.dan124.com/ha.